Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 18

Yaya Muke Taimaka Wa ’Yan’uwanmu da Bala’i Ya Shafa?

Yaya Muke Taimaka Wa ’Yan’uwanmu da Bala’i Ya Shafa?

Jamhuriyar Dominikan

Jafan

Haiti

Sa’ad da bala’i ya auku, Shaidun Jehobah ba sa ɓata lokaci wajen tattara kayan agaji don su taimaka wa ’yan’uwansu da bala’in ya shafa. Irin wannan taimakon yana nuna cewa muna ƙaunar junanmu sosai. (Yohanna 13:34, 35; 1 Yohanna 3:17, 18) A waɗanne hanyoyi ne muke taimakawa?

Muna ba da gudummawar kuɗi. Sa’ad da aka yi yunwa mai tsanani a Yahudiya, Kiristoci na farko a Antakiya sun aika wa ’yan’uwansu gudummawar kuɗi. (Ayyukan Manzanni 11:27-30) Hakazalika, idan muka ji cewa ’yan’uwanmu a wasu sassan duniya suna fuskantar matsaloli, muna ba da gudummawa ta hanyar ikilisiyarmu don a kai kayan agaji ga ’yan’uwanmu mabukata.—2 Korintiyawa 8:13-15.

Muna ba da taimako. Dattawan da ke inda bala’in ya auku suna tabbatar da cewa sun nemo ’yan’uwan da ke ikilisiyar gabaki ɗaya kuma suna nan lafiya lau. Kwamitin agaji ne zai kula da yadda za a kai abinci da ruwan sha da tufafi da wurin kwanciya da kuma magani. Shaidu da yawa, waɗanda ake bukatar irin aikin da suke yi, suna biyan kuɗi daga aljihunsu don su je su taimaka wajen aikin agaji ko kuma gyara gidaje da Majami’un Mulki da suka lalace. Haɗin kan da ke tsakaninmu a matsayin ƙungiya da kuma yadda muka ƙware saboda muna aiki tare, suna taimaka mana mu tara kayan agaji, kuma mu samu mutanen da za su taimaka a lokacin da bukata ta taso. Ko da yake muna taimaka wa ‘waɗanda su ke da imani’ ɗaya da mu, muna kuma taimaka wa mutanen da ke wasu addinai dabam, idan bukatar yin hakan ta taso.—Galatiyawa 6:10.

Muna amfani da Nassi mu ƙarfafa mutane kuma muna taimaka musu su jimre da baƙin ciki. Waɗanda bala’i ya shafa suna bukatar ƙarfafawa. A irin waɗannan lokatan, muna samun ƙarfafawa daga Jehobah, “Allah na dukan ta’aziyya.” (2 Korintiyawa 1:3, 4) Muna farin cikin gaya wa waɗanda suke cikin matsala alkawarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki, kuma muna ba su tabbaci cewa, ba da daɗewa ba Mulkin Allah zai kawar da masifun da suke haddasa azaba da wahala.—Ru’ya ta Yohanna 21:4.

  • Me ya sa Shaidu suke kai agaji nan da nan a lokacin da bala’i ya auku?

  • Wane ƙarfafawa daga Nassi ne za mu iya ba waɗanda suka tsira daga bala’i?