TAMBAYA TA 3
Ta Yaya Zan Rika Tattaunawa da Iyayena?
MENE NE ZA KA YI?
Ka yi tunanin wannan yanayin: Ranar Laraba da dare, Geoffrey, ɗan shekara 17 ya gama aikace-aikacen gida kuma yana so ya ɗan huta! Ya kunna talabijin kuma ya zauna a kan kujera mai taushi.
Yana zaune, sai ga mahaifinsa tsaye a baƙin kofa, ransa a ɓace kuma ya ce:
“Geoffrey! Me ya sa kake ɓata lokaci a nan kana kallon talabijin bayan ka san cewa ya kamata ka taimaki ƙaninka da aikin da aka ba shi a makaranta? Me ya sa ba ka jin magana?”
Geoffrey ya yi gunaguni kuma ya ce: “Na shiga uku a gidan nan,” kuma mahaifinsa ya ji abin da ya ce.
Mahaifinsa ya matso kusa kuma ya ce: “Me ka ce?”
Geoffrey yana jujjuya idanunsa kuma ya numfasa, ya ce: “Ban ce kome ba, Baba.”
Hakan ya sa mahaifinsa ya fusata kuma ya ce: “Ni za ka yi wa rashin kunya?”
Da a ce kai ne Geoffrey, mene ne za ka yi don ka hana wannan ka-ce-na-ce daga faruwa?
KA DAKATA KA YI TUNANI!
Za a iya kwatanta tattaunawa da iyayenka da tuƙa mota. Idan kana tuƙi kuma ka ga cewa an rufe hanyar da kake bi, za ka nemi wata hanyar.
ALAL MISALI:
Wata yarinya mai suna Leah ta ce: “Ba na son tattaunawa da mahaifina. A wasu lokatai, idan ina magana da shi, zuwa can sai ya ce, ‘Yi haƙuri, da ni kike magana?’”
LEAH TANA DA ZAƁI UKU.
-
Ta daka wa mahaifinta tsawa.
Leah ta daka tsawa kuma ta ce, “Haba mana, ka saurare ni! Wannan maganar tana da muhimmanci sosai!”
-
Ta daina yi wa mahaifinta magana.
Leah ta daina gaya wa mahaifinta abin da yake damunta.
-
Ta yi masa magana game da batun, amma a wani lokaci dabam.
Leah ta tattauna da mahaifinta a wani lokaci dabam ko kuma ta rubuta masa wasiƙa game da matsalarta.
A cikin abubuwa ukun nan, wanne ne za ka gaya wa Leah ta yi?
KA YI LA’AKARI DA WANNAN: Hankalin mahaifin Leah ya rabu, don haka bai san damuwarta ba. Idan Leah ta Zaɓi na 1, mahaifinta ba zai fahimci abin da ya sa take daka masa tsawa ba, kuma hakan ba zai sa ya saurare ta ba. Ƙari ga haka, zai nuna cewa ta raina shi. (Afisawa 6:2) Hakika, wannan zaɓi ba zai amfane su ba.
Zaɓi na 2 yana da sauƙi amma hakan ba shi da kyau. Me ya sa? Domin idan tana so ta magance matsalolinta, tana bukatar ta yi magana da mahaifinta kuma dole ya san abin da yake damunta kafin ya taimaka mata. Saboda haka, yin shiru ba zai taimaka ba.
Idan Leah ta Zaɓi na 3, hakan yana nufin cewa ba ta bar abin da ya faru ya hana ta tattaunawa da mahaifinta ba. Maimakon haka, za ta tattauna da shi a wani lokaci. Amma idan ta zaɓi ta rubuta wa mahaifinta wasiƙa, wataƙila hakan zai sa ta samu sauƙi nan da nan.
Ƙari ga haka, wataƙila rubuta wasiƙa zai taimaka wa Leah ta rubuta duka abubuwan da take so ta gaya masa. Idan mahaifinta ya karanta wasiƙar, zai fahimci abin da take so ta gaya masa, kuma hakan zai taimaka masa ya san yanayin da take ciki. Saboda haka, zaɓi na 3 zai amfane Leah da kuma mahaifinta. Ko da sun tattauna batun ne ko kuma ta rubuta masa wasiƙa, yin hakan ya nuna cewa ta bi wannan shawarar da ke Littafi Mai Tsarki da ta ce, “mu himmantu ga yin abubuwan da ke kawo salama.”—Romawa 14:19, LMT.
Waɗanne zaɓi ne Leah take da su kuma?
Duba ka ga ko za ka iya yin tunanin guda, kuma ka rubuta shi a wajen da aka tanadar. Bayan haka, sai ka rubuta sakamakon da zaɓin zai kawo.
KA GUJI YIN ABIN DA ZAI SA BA ZA A FAHIMCE KA BA
Ka tuna cewa a wasu lokatai, iyayenka suna iya zato cewa abin da ka faɗa tana da wata ma’ana dabam.
ALAL MISALI:
Iyayenka sun tambaye ka abin da ya sa ranka ya ɓace, sai ka ce, “Ba kome.”
Iyayenka suna iya ɗauka cewa ba ka yarda da su ba, shi ya sa ka ƙi gaya musu damuwarka. Ka fi amincewa da abokanka fiye da su.
A ce kana fuskantar wata matsala kuma iyayenka suna so su taimake ka. Sai ka ce: “Kar ku damu, zan iya magance matsalar da kaina.”
-
Daga baya iyayenka suna iya ɗauka cewa:
-
Abin da ya kamata ka ce shi ne: