Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Jumma’a

Jumma’a

‘Ku yi farin ciki cikin Ubangiji kullum. Ina sake gaya muku, ku yi farin ciki’​—Filibiyawa 4:4

DA SAFE

  • 9:20 Sauti da Bidiyo

  • 9:30 Waƙa ta 111 da Addu’a

  • 9:40 JAWABIN MAI KUJERA: Abin da Ya Sa Jehobah Ne “Allah Mai Farin Ciki” (1 Timoti 1:11)

  • 10:15 JERIN JAWABAI: Me Zai Taimaka Mana Mu Yi Murna a Rayuwa?

    • • Mu Sauƙaƙa Rayuwarmu (Mai-Wa’azi 5:12)

    • • Zuciya Mai Tsabta (Zabura 19:8)

    • • Yin Aiki Mai Gamsarwa (Mai-Wa’azi 4:6; 1 Korintiyawa 15:58)

    • • Abokan Kirki (Karin Magana 18:24; 19:​4, 6, 7)

  • 11:05 Waƙa ta 89 da Sanarwa

  • 11:15 WASAN KWAIKWAYO DAGA LITTAFI MAI TSARKI DA ZA A SAURARA: “Yahweh Ya Sa Su Su Yi Farin Ciki” (Ezra 1:1–6:22; Haggai 1:​2-11; 2:​3-9; Zakariya 1:​12-16; 2:​7-9; 3:​1, 2; 4:​6, 7)

  • 11:45 Ku Yi Murna don Jehobah Yana Ceton Bayinsa (Zabura 9:14; 34:19; 67:​1, 2; Ishaya 12:2)

  • 12:15 Waƙa ta 148 da Shaƙatawa

DA RANA

  • 1:30 Sauti da Bidiyo

  • 1:40 Waƙa ta 131

  • 1:45 JERIN JAWABAI: Ku Sa Iyalinku Farin Ciki

    • • Maigida, Ka Yi Farin Ciki da Matarka (Karin Magana 5:​18, 19; 1 Bitrus 3:7)

    • • Uwargida, Ki Yi Farin Ciki da Mijinki (Karin Magana 14:1)

    • • Iyaye, Ku Yi Farin Ciki da Yaranku (Karin Magana 23:​24, 25)

    • • Yara, Ku Yi Farin Ciki da Iyayenku (Karin Magana 23:22)

  • 2:50 Waƙa ta 135 da Sanarwa

  • 3:00 JERIN JAWABAI: Halittu Suna Nuna Cewa Jehobah Yana So Mu Yi Farin Ciki

    • • Furanni Masu Kyau (Zabura 111:2; Matiyu 6:​28-30)

    • • Abinci Mai Daɗi (Mai-Wa’azi 3:​12, 13; Matiyu 4:4)

    • • Kaloli Masu Ban Sha’awa (Zabura 94:9)

    • • Tsarin Jikin Ɗan Adam (Ayyukan Manzanni 17:28; Afisawa 4:16)

    • • Abubuwan da Muke Jin Daɗin Saurara (Karin Magana 20:12; Ishaya 30:21)

    • • Dabbobi Masu Ban Sha’awa (Farawa 1:26)

  • 4:00 Me Ya Sa Masu Son Zaman Lafiya Suke Farin Ciki? (Karin Magana 12:20; Yaƙub 3:​13-18; 1 Bitrus 3:​10, 11)

  • 4:20 Aminan Allah Za Su Yi Farin Ciki Sosai! (Zabura 25:14; Habakkuk 3:​17, 18)

  • 4:55 Waƙa ta 28 da Addu’ar Ƙarshe