Mene Ne Ra’ayinka Game da Nan Gaba?
Shin duniyar nan za ta . . .
-
ci gaba da kasancewa yadda take ne?
-
ƙara lalacewa ne?
-
gyaru ne?
ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE
“Allah . . . zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.”—Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4, Littafi Mai Tsarki.
ABIN DA ZA KA IYA MORA SABODA ALKAWARIN NAN
Za ka more aiki mai kyau kuma mai gamsarwa.—Ishaya 65:21-23.
Ba za ka ƙara yin ciwo ko wahala ba.—Ishaya 25:8; 33:24.
Za ka yi farin ciki sosai tare da iyali da abokai har abada.—Zabura 37:11, 29.
ZA MU IYA GASKATA DA LITTAFI MAI TSARKI KUWA?
Hakika, aƙalla saboda waɗannan dalilai biyu:
-
Allah yana da iko ya cika alkawarin da ya yi. A cikin Littafi Mai Tsarki, Jehobah Allah ne kaɗai aka kira “Mai-iko duka” domin shi ne ke da iko marar iyaka. (Ru’ya ta Yohanna 15:3) Saboda haka, zai iya cika alkawarinsa na mai da wannan duniya ta zama wuri mai kyau. Littafi Mai Tsarki ya ce, “Ga Allah dukan abu ya yiwu.”—Matta 19:26.
-
Allah yana ɗokin cika alkawarinsa. Alal misali, Jehobah yana “marmarin” ta da matattu don su sake rayuwa.—Ayuba 14:14, 15.
Littafi Mai Tsarki ya kuma nuna cewa Yesu, Ɗan Allah ya warkar da masu ciwo. Me ya sa ya yi hakan? Domin yana son yin hakan. (Markus 1:40, 41) Kamar Ubansa, Yesu ya so ya taimaki mabukata.—Yohanna 14:9.
Saboda haka, za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah da Yesu suna so su taimaka mana mu ji daɗin rayuwa a nan gaba!—Zabura 72:12-14; 145:16; 2 Bitrus 3:9.
KA YI TUNANI A KAN WANNAN TAMBAYAR
Ta yaya Allah zai mai da duniya ta zama wuri mai kyau?
Littafi Mai Tsarki ya ba da amsar a MATTA 6:9, 10 da kuma DANIYEL 2:44.