Zai Dace Ka Yi “Wasanni Masu Hadari Sosai”?
Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce
Zai Dace Ka Yi “Wasanni Masu Hadari Sosai”?
WATA JARIDA TA CE, “KWANAN NAN BA KALLON WASANNI KAWAI MUKE YI BA, AMMA ANA SAMUN KARIN MUTANEN DA SUKA SHIGA YIN WASANNI KAMAR DIROWA DAGA JIRGIN SAMA, AMFANI DA IGIYOYI WAJEN SAUKOWA DAGA KAN DUTWASU DA WASAN KWALE-KWALE A INDA RUWA YAKE SAUKOWA DAGA KAN TUDU DA KUMA YIN IWO A INDA AKWAI KIFAYEN SHARK.”—JARIDAR WILLOW GLEN RESIDENT.
HAKAN ya nuna yadda mutane suke kara son wasanni masu hadari. Yadda mutane suke kara son yin wasanni kamar dirowa daga jirgin sama da ake kira skydiving da paragliding da hawan dusar kankara da kuma wasan da ake kira BASE jumping * ya nuna cewa mutane da yawa suna son yin kasada da rayukansu. Masu gudu da takalma masu taya da wasan gudu a kan dusar kankara da masu hawan tudu da keke da masu wasa da abin da ake kira skateboards suna kokarin yin abubuwan da ba a taba yin ba. Wata jarida mai suna Time ta ce, yadda ake samun karin mutanen da suke yin “wasanni masu hadari sosai” ya nuna yadda miliyoyin mutane da suke yin wadannan wasannin suke marmarin su kai matsayin da za su yi abubuwa masu ban tsoro da ke da hadari kuma suke bukatar kwarewa sosai don su ma su ji cewa suna yin abin da ba su taba yi a dā ba.
Duk da cewa ana samun karin mutanen da suke son wasannin nan, wasannin na da hadari sosai. Saboda mutane suna wuce gona da iri sa’ad da suke yin wasa, hakan ya sa mutane da yawa suna jin raunuka. A 1997, yawan mutanen da suka je jinyar gaggawa a Amirka sanadiyyar wasan da ake kira skateboarding ya karu da fiye da kashi 33, masu gudu a kan kankara kuma sun karu da kashi 31, masu hawan dutse kuma da kashi 20. A wasu wasanni ma, adadin ya fi hakan yawa domin mutane da yawa suna mutuwa saboda sun wuce gona da iri a yin wasanni. Wadanda suke shirya wasannin nan sun san hadarurrukan da ke tattare da yin su. Wata mata da take wasan gudu a kan dusar kankara mai hadari sosai ta ce: “A kullum na san cewa a bakin mutuwa nake.” Wani kuma da ya kware wajen gudu kan dusar kankara ya ce, “Idan ba ka ji rauni ba, hakan na nufin cewa ba ka yin wasan da dukan karfinka.”
Bisa ga wadannan ra’ayoyin, zai dace Kirista ya yi irin wadannan wasannin? Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu san ko zai dace mu yi wasanni masu hadari sosai? Don mu san amsoshin tambayoyin nan, bari mu yi la’akari da yadda Allah yake daukan rai.
Yadda Allah Yake Daukan Rai
Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Allah ne “maɓuɓɓuga mai ba da ruwan rai.” (Zabura 36:9) Ba halittar mu kawai ya yi ba, amma ya ba mu abubuwan da muke bukata don mu ji dadin rayuwa. (Zabura 139:14; Ayyukan Manzanni 14:16, 17; 17:24-28) Don haka, babu shakka zai so mu kula da rai da ya ba mu kyauta. Dokoki da kuma ka’idodin da ya ba wa Isra’ilawa sun nuna mana hakan.
A Dokar da aka bayar ta Hannun Musa, Allah ya bukaci mutum ya yi iya kokarinsa don ya kāre lafiyar mutane. Idan mutum ya yi sakaci har aka rasa rai, alhakin jinin wanda ya mutu yana kansa. Alal misali, an dokaci kowanne maigida ya gina guntun katanga kewaye da rufin sama gidansa. In ba haka ba, idan wani ya fadi, alhakin jininsa yana kan mutanen gidan. (Maimaitawar Shari’a 22:8) Idan tsautsayi ya sa bijimi ya kai wa mutum hari har ya kashe shi, ba za a kama mai bijimin da laifi ba. Amma idan bijimin ya saba kai wa mutane hari kuma an ja wa mai shi kunne amma ya ki ya dauki mataki, in har bijimin ya soki wani, alhakin jini zai kasance a bisan mai bijimin kuma za a iya kashe shi. (Fitowa 21:28, 29) Da yake Jehobah yana daukan rai da daraja sosai, ya ba da dokoki da za su sa a kāre da kuma kula da lafiyar mutane.
Bayin Allah masu aminci sun san cewa ka’idodin nan suna nufin su guji yin kasada a rayuwa. Akwai lokacin da Dauda ya so ya sha ruwa daga “rijiyar da take bakin kofar Betelehem!” A lokacin, Betelehem yana hannun Filistiyawa. Da sojojinsa suka ji hakan, sai uku daga cikinsu suka je inda Filistiyawa suke kuma da karfi da yaji suka dibi ruwa daga rijiyar suka kawo wa Dauda. Me Dauda ya yi? Maimakon ya sha ruwan, ya zubar da shi a kasa. Ya ce: “Allah ya sawwake in sha daga wannan ruwa. Ai, zai zama mini kamar jinin mutanen nan nake sha, gama a bakin ransu suka kawo ruwan nan.” (1 Tarihi 11:17-19) A gun Dauda, bai dace da suka sadaukar da ransu don su samar masa abin da yake so ba.
Abin da Yesu ya yi ke nan sa’ad da Shaidan ya jarabce shi. Da alama cewa a cikin wahayi ne Shaidan ya yi hakan. Ya ce wa Yesu ya fado daga kan haikali, ya ga ko mala’iku za su tsare shi don kar ya ji rauni. Sai Yesu ya ce masa, “Kada ka gwada Ubangiji Allahnka!” (Matiyu 4:5-7) Hakika, Dauda da Yesu sun san cewa Allah ba ya so mu yi abin da zai sa ranmu cikin hadari.
Da wannan bayanin, za mu iya tambayar kanmu cewa, ‘Ta yaya za mu gane wasannin da suka wuce gona da iri ko suke da hadari sosai? Da yake ko wasa mara hadari zai iya zama da hadari idan aka wuce gona da iri wajen yinsa, ta yaya za mu san ko wasan da muke yi ya soma wuce gona da iri?’
Zai Dace Ka Yi Wannan Kasadar?
Za mu san amsar tambayar nan idan muka bincika wasan da muke so mu yi da kyau. Alal misali za mu iya tambayar kanmu‚ ‘Ya yawan mutanen da suke jin rauni sanadiyyar wannan wasan yake? An horar da ni a wannan wasan ko kuma ina da abubuwan da za su kāre ni a wasan nan? Me zai faru idan na fadi ko na yi tuntube ko kuma kayan da suke kāre ni sun lalace? Raunin da zan ji kadan ne ko mai tsanani ko kuma ma in mutu?’
Idan Kirista yana sa ransa cikin hadari da sunan wasa, hakan zai iya bata dangantakarsa da Jehobah kuma zai iya sa a hana shi yin wasu ayyuka a ikilisiya. (1 Timoti 3:2, 8-10; 4:12; Titus 2:6-8) Hakika, ya kamata Kiristoci su yi tunani a kan yadda Allah yake daukan rai da daraja sa’ad da suke yin wasanni.
[Ƙarin bayani]
^ sakin layi na 4 BASE yana nufin building, antenna, span da kuma earth. Irin wannan wasan da mutum yakan diro daga gida mai tsawo ko kuma manyan duwatsu yana da hadari sosai, shi ya sa hukumar National Park Service da ke Amirka ta hana yin sa.