Aboki Marar Kirki
Aboki Marar Kirki
Ka yi wani “aboki” a lokacin da kake matashi. Yana sa ka ji ka isa mutum kuma ta dalilinsa abokanka suna ji da kai. Yana sa ka ji “sauki” idan ka gaji, kuma kakan ji kamar in ba shi, ba kai.
Amma daga baya sai ka gano cewa shi mugu ne. Yana so lallai sai ya bi ka ko’ina. Alhali kuwa a wasu wuraren ba a son ganin ka da shi. Kuma ko da yake yana sa ka ji ka isa mutum, ya cutar da kai. Ban da haka ma, yana cikin masu cinye maka kudi.
Kwanan nan ka yi ka yi ka rabu da shi, amma ya ki ya bar ka. Yanzu shi yake iko da kai. Kana da-na-sanin abokantakarku.
RIN dangantakar da ke tsakanin yawancin masu shan taba da sigari ke nan. Wata mata mai suna Earline da ta yi shekaru 50 tana shan taba ta ce: “Sigarin yakan taimaka min fiye da abokaina. Shi babban abokina ne a dā. A wasu lokuta ma, shi kadai ne abokina.” Amma daga baya Earline ta fahimci cewa sigari ba abokin kirki ba ne kuma mugu ne. Ita ma ta yi fama kamar wanda muka kwatanta a farkon talifin nan. Abin da ya sa yanayinta ya zama dabam shi ne, da ta gano cewa shan taba zunubi ne, don yana bata jikinmu da Allah ya ba mu, sai ta daina.—2 Korintiyawa 7:1.
Wani mutum mai suna Frank shi ma ya tsai da shawara cewa zai daina shan sigari don ya faranta wa Allah rai. Amma ba da jimawa ba sai ya tsinci kansa a kasa yana rarrafe, yana neman guntayen karan sigari da ya sha ya rage. Frank ya ce: “Tun daga ranar na ce ba zan sake shan sigari ba. Yadda na sunkuya ina rarrafe ina neman raguwar sigari a cikin datti ya bata min rai. Daga ranar ban sake shan sigari ba.”
Me ya sa yake yi wa mutane wuya su daina shan taba? Ga wasu dalilai da masu bincike suka gano: (1) Ana kamuwa da jarabar shan taba kamar yadda ake kamuwa da jarabar shan kwaya. (2) Idan mutum ya shaki sinadarin nicotine da ke cikin taba, zai iya kai kwakwalwar mutumin cikin sakan bakwai kawai. (3) Shan taba yakan zama da muhimmanci a gun masu sha don akan hada shi da abinci da giya, ana shan ta yayin da ake hira, kuma ana cewa tana rage wa mutum gajiya da dai sauransu.
Amma kamar yadda labarin Earline da Frank suka nuna, zai yiwu mutum ya fita daga cikin wannan muguwar jarabar. Idan kana shan taba kuma kana so ka daina, talifofin da ke gaba za su taimaka maka ka yi hakan.