Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Nemi Taimako

Ka Nemi Taimako

Ka Nemi Taimako

“Idan mutum ya rinjayi wanda shi ke shi kadai, biyu za su iya tsaya masa.”​—Mai-Wa’azi 4:​12, Tsohuwar Hausa a Saukake.

IDAN aka taimaka mana, za mu iya yin nasara a kan duk wani abin da ke neman ya cutar da mu. Don haka idan kana so ka daina shan taba, ka ce abokanka ko danginka su taimake ka. Ko ka nemi taimako daga duk wani mutumin kirki da ka san zai iya taimaka maka. Yin hakan hikima ce.

Za ka iya ce ma wani da mashayin taba ne a dā ya taimake ka. Irin mutanen nan suna taimakawa kuma za su fahimce ka sosai. Wani Kirista daga Denmark mai suna Torben ya ce: “Yadda na amfana daga taimakon da mutane suka yi min ya wuce misali.” Wani kuma mai suna Abraham daga Indiya ya ce: “Kaunar da iyalina da kuma ’yan’uwana Kiristoci suka nuna min ne ya taimaka min in daina shan taba.” Amma a wasu lokuta, taimakon dangi da abokai ma ba ya sa mutum ya daina shan taba.

Wani mutum mai suna Bhagwandas ya ce: “Na yi shekaru 27 ina shan taba, amma da na koyi cewa Littafi Mai Tsarki ya haramta hakan, sai na tsai da shawara cewa zan daina. Na rage yawan sigarin da nake sha, kuma na daina yin tarayya da abokan da na saba zama da su, har na je wurin mashawarta sun ba ni shawara, amma ban yi nasara ba. Sai wata rana da dare na yi addu’a na roki Allah ya taimaka min in daina wannan hali. Da taimakon Jehobah, na kuwa ci nasara!”

Wani abu mai muhimmanci kuma da za ka yi shi ne, ka yi shiri don matsalolin da za ka fuskanta idan ka daina sha. Wadanne matsaloli ke nan? Za a bayyana su a talifi na gaba.

[Akwati]

ZAI DACE KA YI AMFANI DA MAGUNGUNAN DAINA SHAN TABA?

Mutane da yawa a yau sun shiga amfani da magungunan daina shan taba irin su nicotine patch, don haka sayar da su ya zama wa mutane babbar hanyar samun kudi. Kafin ka ce za ka yi amfani da magungunan nan, ka yi wa kanka tambayoyin da ke gaba:

Wane amfani zan samu idan na sha su? Masu tallen magungunan nan sukan ce magungunan za su rage maka radadin da za ka ji idan ka daina shan taba. Amma wasu sun ce ba wani taimakon kirki magungunan nan suke yi wa mutum ba.

Wane hadari ne ke tattare da shan su? Wasu magunguna suna da illa. Za su iya sa mutum tashin zuciya da ke sa yin amai, ko ciwon damuwa, ko ma ya soma tunanin kashe kansa. Ka kuma tuna cewa wadannan magungunan da ake ba mutum don ya daina shan taba su ma suna dauke da sinadarin nicotine. Don haka idan mutum yana shan su, har ila bai rabu da jarabar shan nicotine ba. Nicotine kuwa yana da illa sosai.

Ana iya dainawa ba tare da an sha magunguna ba? Kwarai kuwa. A wani bincike da aka yi, kashi 88 cikin 100 na mutanen da suka yi nasara wajen daina shan taba sun ce sun yi hakan ne ba tare da shan magunguna ba.