Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Yi Niyya Sosai

Ka Yi Niyya Sosai

Ka Yi Niyya Sosai

“Kudurin da wadanda suka daina shan taba suka yi cewa za su daina ko ta yaya, shi ne babban abin da yake taimaka musu su daina.”​—In ji wani littafi mai suna “Stop Smoking Now!”

TAKAICE, idan kana so ka daina shan taba, dole ka mai da hakan ya zama babban burinka. Me zai taimaka maka ka yi hakan? Da farko, ka yi tunani a kan yadda za ka amfana idan ka daina shan taba.

Za ka rage kudin da kake kashewa. Idan mutum yana shan kwalin sigari kowace rana, a shekara, zai iya kashe dubban daloli a kan taba. Wani mai suna Gyanu, daga kasar Nepal ya ce: “Ban san cewa kudin da nake kashewa a kan taba ya kai haka ba.”

Za ka inganta rayuwarka. Wata mai suna Regina daga Afirka ta Kudu ta ce: “Da na daina shan taba, rayuwata ta kara yin kyau sosai. Kuma a kullum rayuwata sai dada kyau take yi.” Idan mutum ya daina shan taba, hancinsa da harshensa sukan kara yin aiki da kyau. Ban da haka ma, yakan kara samun kuzari kuma jikinsa yakan kara yin kyau.

Za ka kyautata lafiyar jikinka. Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaduwa ta Amurka ta ce: “Wadanda suka daina shan taba sukan inganta lafiyar jikinsu nan da nan, ko da su mata ne ko maza, komin shekarunsu.”

Za ka iya tsara rayuwarka. Wani mai suna Henning daga kasar Denmark ya ce: “Abin da ya sa na daina shan taba shi ne, ban so ta dinga yin iko a kaina ba. Na so in sami ’yancin yin abin da nake so.”

Abokanka da danginka za su amfana. Wata kungiyar likitoci da ke yakar cutar kansa (American Cancer Society) ta ce: “Shan taba . . . yana shafan lafiyar wadanda suke kewaye da kai. . . . Binciken da aka yi ya nuna cewa a kowace shekara, ana samun dubban mutane da suke shakar hayakin da masu shan taba suke busa musu. Hayakin yana sa su kamu da cutar zuciya ko kansa ta huhu, kuma suna rasa rayukansu.”

Mahaliccinka zai ji dadi. “ ’Yan’uwa wadanda nake kauna, . . . bari mu tsabtace kanmu daga dukan abin da zai sa jiki da zuciyarmu ya kazantu.” (2 Korintiyawa 7:1) “Ku mika kanku hadaya . . . mai tsarki, da kuma abin karba ga Allah”​—Romawa 12:1.

Wata mai suna Sylvia daga kasar Spain ta ce: “Da na fahimci cewa Allah ba ya so mu yi duk wani abin da zai kazantar da jikinmu, nan da nan sai na tsai da shawarar daina shan taba.”

Amma a yawancin lokaci yin niyya kawai ba ya sa mutum ya daina shan taba. Za mu bukaci taimako, kuma wasu da za su iya taimaka mana su ne abokanmu da danginmu. Ta yaya za su taimaka?