Ka Yi Shiri don Abubuwan da Za Ka Fuskanta
Ka Yi Shiri don Abubuwan da Za Ka Fuskanta
Wata mai suna Yoshimitsu daga kasar Japan ta ce: “Da na haifi ’yarmu, sai na tsai da shawarar daina shan taba don in kāre lafiyarta. Har na yi rubutu na saka a gidanmu cewa, ‘Ba a Shan Sigari a Nan.’ Amma awa daya bayan hakan, sai sha’awar shan sigari ta bi ta kama ni har sai da na nemo karar sigari na kunna kuma na kama sha.”
ABIN da ya faru da Yoshimitsu ya nuna cewa idan mutum yana son ya daina shan sigari, zai yi fama ba kadan ba. Wani bincike da aka yi ya nuna cewa, idan mutum dari suka ce za su daina shan taba kuma sha’awar ta taso har sun sha sau daya, mutane casa’in daga cikinsu sukan ci gaba da sha. Don haka, idan kana son ka daina shan taba, dole ka yi shiri sosai don matsalolin da za ka fuskanta. Abin da zai taimaka maka ka yi nasara ke nan. Wadanne matsaloli ne mutane suke yawan fuskanta?
Kwadayin shan Taba: Idan mutum ya daina shan taba, yakan soma jin kwadayin shan taba sosai musamman bayan kwana uku. Wannan kwadayin yakan soma raguwa in ya kai wajen sati biyu. Wani da ya daina shan taba ya ce “a wannan lokacin, kwadayin zai dinga zuwa yana tafiya.” Amma ba shi ke nan ba, don ko da mutum ya yi shekaru da daina shan taba, kwadayin taba zai iya zuwa masa babu zato. Idan hakan ya faru da kai, kada ka biye masa. Don in ka jimre na wajen minti biyar kawai, jarabar za ta wuce.
Wasu matsalolin kuma: Daina shan taba zai iya sa ya maka wuya ka natsu, zai iya sa ka jin barci kuma ka kara kiba. Zai iya sa jikinka ya maka ciwo, ka ji kaikayi, ka yi ta zufa da kuma tari. Zai kuma iya sa ka kasa yin hakuri, ka dinga saurin fushi, ko ka soma bakin ciki. Amma yawancin alamomin nan sukan ragu bayan sati hudu ko shida.
Akwai wasu abubuwan da idan ka yi za su taimaka maka sosai a wannan lokacin. Alal misali:
● Ka kara wa kanka lokacin barci.
● Ka dinga shan ruwa sosai ko ruwan lemu (juice). Kuma ka dinga cin abinci mai gina jiki.
● Ka dinga motsa jiki daidai wa daida.
● Ka dakata, ka ja numfashi da kyau kuma ka yi tunanin yadda iska mai tsabta yake shiga huhunka.
Abubuwan da ke sa kwadayin shan taba: Akwai wasu abubuwan da ka saba yi da za su iya sa ka kwadayin shan taba. Alal misali, kila idan kana shan giya, kakan hada da sigari. Idan haka ne, kar ka rika bata lokaci yayin da kake shan giya. Idan ka daina shan taba kwata-kwata, za ka iya soma daukan dogon lokaci kana shan giyarka a hankali.
Amma ko da ka kubuta daga jarabar shan taba, ba za a rasa wasu abubuwan da za su sa ka kwadayin shan taba ba. Torben da muka ambata a baya, ya ce: “Ko da yake na yi shekaru sha tara da barin shan taba, har ila idan na je shan kofi, nakan ji kwadayin shan taba.” Amma gaskiyar ita ce, a hankali a hankali, wannan kwadayin zai yi ta raguwa har ka shawo kansa.
Amma shan giya zai iya zama maka matsala. Idan kana kokarin daina shan taba, zai fi maka alheri ka guji shan giya da wuraren da ake ba da giya. Domin shan giya ne yake sa mutane da yawa su koma shan taba. Me ya sa hakan yake faruwa?
● Domin idan mutum ya sha giya ko da kadan ne, yana sa ya kara jin dadin shan duk wani abin da ke da sinadarin nicotine.
● Mutane da yawa sukan soma shan sigari idan suna shan giya.
● Giya takan shafi tunanin mutum, za ta iya sa ka yi abubuwan da ba ka zata za ka yi ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Ruwan inabi yakan kawar da hankalin mutane.’—Hosiya 4:11.
Abokai: Ka rika zaban wadanda za ka rika tarayya da su. Ka guji yin tarayya da mutanen da suke shan taba ko wadanda za su maka tayin ta. Ka kauce ma mutanen da za su zolaye ka don ka daina shan taba.
Yadda kake ji: Wani binciken da aka yi ya nuna cewa wajen mutum biyu cikin uku da suka koma shan taba, sun yi hakan ne sa’ad da suka gaji ko suna jin fushi. Idan ka ji kwadayin shan taba don ka shiga wani yanayi, ka yi wani abin da zai dauke hankalinka. Alal misali, ka sha ruwa, ko ka ci cingam ko kuma ka fita ka dan zagaya. Ka mai da hankalinka ga abubuwa masu kyau, za ka iya yin addu’a ka roki Allah ya taimaka maka ko ka karanta wasu wurare a Littafi Mai Tsarki.—Zabura 19:14.
Ka Guji Ba da Hujja Irin Su:
● Sau daya kawai zan zuka.
Gaskiyar lamarin: Idan ka ja sigari ko da sau daya ne, zai ba ka rabin sinadarin nicotine da jikinka yake so har na tsawon awa uku. Shi ya sa yawancin mutanen da suka daina shan sigari amma suka ce bari su zuka sau daya kawai sukan koma sha.
● Shan taba yana taimaka min idan na gaji.
Gaskiyar lamarin: Bincike ya nuna cewa sinadarin nicotine da ke cikin taba yana kara wa mutum gajiya. Abin da kawai yake sa wasu su ji sauki shi ne domin jikinsu ya sami sinadarin nicotine da dā yake nema.
● Ba yau na soma ba, ya zama min jiki.
Gaskiyar lamarin: Idan ka ci gaba da tunanin cewa ba za ka iya daina shan taba ba, zai maka wuya ka daina. Littafi Mai Tsarki ya ce: “In ka nuna jikinka ya mutu a ranar wahala, to, lallai [karfinka zai kare, New World Translation].” (Karin Magana 24:10) Don haka, kar ka dauka cewa ya gagare ka. Duk wanda yake son ya daina shan taba da gaske kuma ya bi shawarwari masu kyau kamar wadanda aka bayar a mujallar nan, zai iya yin nasara.
● Abubuwan da na fuskanta sa’ad da na yi kokarin daina wa sun fi karfina.
Gaskiyar lamarin: Gaskiya ne cewa idan mutum ya daina shan taba, da farko zai yi fama da matsaloli sosai. Amma bayan ’yan makonni, za su ragu. Don haka, kar ka fid da rai. Ko da ka sake jin kwadayin shan sigari bayan wasu watanni ko shekaru, ba zai jima ba, zai wuce bayan ’yan mintoci idan ka dāge kuma ka ki shan sigari.
● Ina da rashin lafiyar da ke shafan tunanina.
Gaskiyar lamarin: Idan ana maka jinyar da ta shafi hankalinka, kamar cutar tsananin damuwa ko wanda ake kira schizophrenia, ka ce wa likitar da ke maka jinya ya taimaka maka ka daina shan taba. Mai yiwuwa shi ma zai so ya taimaka maka kuma ya yi hakan ta wajen canja irin magungunan da yake ba ka.
● A duk lokacin da na kasa guje wa jarabar, nakan ji kamar ba zan iya daina wa ba.
Gaskiyar lamarin: Mutane da yawa da suke kokarin daina shan taba sukan fada wa jarabar a wasu lokuta. Idan hakan ya faru da kai, baya nufin cewa ba za ka iya daina wa ba. Kada ka fid da rai, ka ci gaba da yin kokari. Ko da jarabar ta sa ka sake shan sigari, hakan ba ya nufin cewa ya gagare ka. Idan ka fid da rai ne abin zai gagare ka. Don haka, ka ci gaba da kokartawa, a kwana a tashi, za ka yi nasara.
Ga labarin wani mai suna Romualdo. Ya yi shekaru 26 yana shan taba, amma yanzu ya fi shekaru 30 da barin sha. Mutumin ya ce: “Ba zan iya kirga ko sau nawa na fada wa jarabar a lokacin da nake kokarin daina shan taba ba. Na yi bakin ciki sosai a duk lokacin da hakan ya faru kuma na ji kamar ba zan iya daina shan taba ba. Amma sai na kudura cewa zan daina shan taba don in faranta wa Allah rai. Kuma na yi ta yin addu’a ina rokonsa ya taimaka min. A kwana a tashi, na kuwa daina shan taba.”
A talifi na gaba da ya tattauna wannan batun, za mu ga wasu ’yan shawarwari da za su kara taimaka maka ka yi hannun riga da shan taba.
[Akwati/Hoto]
AKWAI TABA KALA-KALA AMMA DUKANSU SUNA KISA
Wasu irin tabar har ana sayar da su a inda ake sayar da abinci da magungunan gargajiya. Amma Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, “Dukan ire-iren taba suna da illa sosai.” Shan taba yana sa mutane su kamu da cutar kansa da kuma cututtukan da ke shafan zuciya da jijiyoyin jini. Kuma cututtukan nan suna kashe mutane. Idan mace mai ciki tana shan taba, hakan zai iya zama da illa ga yaron da ke cikinta. Wadanne ire-iren taba ne mutane suke sha a yau?
Sigari: Ana yin sigari ne ta wurin murza taba a saka a ganyen taba ko takardar da aka yi da tabar, sa’an nan a nannade shi. Yadda ake yin sigari, yana sa ya yiwu mutum ya shaki sinadarin nicotine da ke cikinsa ko bai cinna masa wuta ba.
Tabar da ake hada wa da kananfari (Kreteks): Akan yi irin wannan sigarin ne ta wurin hada taba da kananfari. Kashi 60 cikin dari yakan zama taba, kashi 40 kuma kananfari. Sinadarin nicotine da ke cikin sa ya fi na sigarin da aka saba yi, kuma shi ya fi hayaki.
Shan taba da lofe: Shan taba ta bututun da ake kira lofe da shan sigari duk daya ne. Domin dukansu za su iya sa mutum ya kamu da cutar kansa iri daya da ma wasu cututtuka.
Tabar da ba a kunna wa: Wannan ya hada da tabar da ake taunawa, da tabar hanci. Akwai wani ma da ake kira gutkha da ake amfani da shi a kudancin Asiya. Sinadarin nicotine da ke cikin su yakan bi ta bakin mutum ne ya shiga jininsa. Irin wannan tabar ma tana da illa sosai kamar sauran ire-iren taba da ake da su.
Shisha: Hayakin tabar shisha yakan bi ta kan ruwa kafin ya isa bakin mutum. Amma ba lallai hakan ya rage gubar da ke shiga jikin mutum ba. Har da wadanda suke shiga huhun mutum kuma su jawo cutar kansa.
[Akwati/Hoto]
YADDA ZA A TAIMAKA WA MUTUM YA DAINA SHAN TABA
● Ka rika karfafa shi. Maimakon ka rika kushe shi, zai dace ka rika yaba masa don kokarin da yake yi kuma ka ba shi kwarin gwiwa. Maimakon ka ce: “Har yanzu ba ka bar halin nan naka ba?” Zai fi alheri idan ka ce, “Ka kara kokari, na san za ka iya.”
● Ka rika sassauta masa: Idan wanda yake kokari ya daina shan tabar ya yi fushi da kai ko ya gaya maka wata bakar magana, ka yi hakuri. Ka gaya masa abin da zai kwantar masa da hankali. Alal misali, ka ce, “Na san abin ba sauki, amma gaskiya kokarin da kake yi yana sa ni farin ciki.” Kar ka taba ce masa, “Fushin nan naka da irin maganganun da kake gaya min, gwamma lokacin da kake shan taba!”
● Ka zama abokin kirki. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Abokin kirki yana nuna kauna a koyaushe kuma shi dan’uwa ne da ke ba da taimako a lokacin damuwa.” (Karin Magana 17:17, New World Translation) Don haka, ka rika hakuri da wanda yake kokari ya daina shan taba kuma ka nuna masa kauna a koyaushe, ko da a wane yanayi ka same shi a ciki.