Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 14

“Ku Bi Hanyarsa” Sosai

“Ku Bi Hanyarsa” Sosai

“Almasihu ma ya sha wahala dominku. Ta haka ya bar muku gurbi domin ku bi hanyarsa.”​—1 BIT. 2:21.

WAƘA TA 13 Mu Riƙa Bin Misalin Yesu

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

Yesu ya bar mana gurbi da za mu riƙa bi (Ka duba sakin layi na 1-2)

1-2. A wace hanya ce za mu iya bin gurbin Yesu? Ka bayyana.

A CE kai da wasu mutane kuna tafiya a cikin hamada kuma wurin na da haɗari sosai. Wani mutum da ya san hanya sosai yana yi muku ja-goranci. Duk inda ya taƙa, alamar takalminsa na nunawa a ƙasa. Bayan wani lokaci, sai mutumin ya ɓace muku! Amma ba ka ji tsoro ba. Maimakon haka, kai da sauran mutanen da kuke tafiya tare kuna bin alamar takalminsa!

2 A matsayinmu na Kiristoci, muna kama da mutanen da ke tafiya a cikin hamada mai cike da haɗari sosai, wato duniyar nan! Amma muna farin ciki cewa Jehobah ya aiko mana mai ja-gora, wato Ɗansa, Yesu Kristi wanda muke bi sawu-da-ƙafa. (1 Bit. 2:21) Wani littafin da ke bayyana Littafi Mai Tsarki ya ce a wannan ayar, Bitrus ya kwatanta Yesu da mai yin ja-gora. Kamar yadda mai ja-gorar yake barin alamar takalminsa, haka Yesu ya bar mana gurbi da za mu bi. Bari mu tattauna tambayoyin nan uku, mene ne bin gurbin Yesu yake nufi? Me ya sa ya kamata mu bi gurbin Yesu? Ta yaya za mu bi gurbin Yesu?

MENE NE BIN GURBIN YESU YAKE NUFI?

3. Mene ne bin gurbin mutum yake nufi?

3 Mene ne bin gurbin wani yake nufi? A wasu lokuta, idan an yi amfani da kalmomin nan “tafiya” da “ƙafafunmu” a Littafi Mai Tsarki suna iya nufin salon rayuwar mutum. (Far. 17:1; Zab. 44:18) Ana iya kwatanta misalin da mutum ya kafa da alamar da takalminsa ya yi a ƙasa. Don haka, bin gurbin mutum yana nufin yin koyi da halayensa.

4. Mene ne bin gurbin Yesu yake nufi?

4 Mene ne bin gurbin Yesu yake nufi? Yana nufin yin koyi da halayensa. A ayar da aka ɗauko jigon wannan talifin, manzo Bitrus yana magana ne game da misali mai kyau da Yesu ya kafa sa’ad da ya jimre wahalar da ya sha. Amma da akwai abubuwa da yawa da Yesu ya yi da za mu iya yin koyi da shi. (1 Bit. 2:​18-25) Don haka, ya kamata mu koyi da dukan abubuwan da Yesu ya yi da kuma faɗa.

5. Mutane ajizai za su iya bin gurbin Yesu kuwa? Ka bayyana.

5 Da yake mu ajizai ne, za mu iya bin misalin Yesu? Ƙwarai kuwa. Ka tuna cewa Bitrus ya ƙarfafa mu mu bi gurbin Yesu, amma bai ce mu yi hakan daidai kamar Yesu ba. Idan muka bi gurbin Yesu sosai a matsayin ajizai, muna bin umurnin da manzo Yohanna ya ba da cewa: Mu ci gaba da yin ‘tafiya kamar yadda Yesu Almasihu ya yi.’​—1 Yoh. 2:6.

ME YA SA YA KAMATA MU BI GURBIN YESU?

6-7. Me ya sa yin koyi da Yesu zai sa mu kusaci Jehobah?

6 Bin gurbin Yesu zai sa mu kusaci Jehobah. Me ya sa muka ce haka? Na farko, Yesu ya kafa misali mai kyau a kan yadda za mu yi rayuwar da za ta faranta ran Allah. (Yoh. 8:29) Don haka, idan muka bi gurbin Yesu, za mu faranta wa Jehobah rai. Ƙari ga haka, za mu kasance da tabbaci cewa Ubanmu na sama yana kusantar waɗanda suke ƙoƙari su zama abokansa.​—Yak. 4:8.

7 Na biyu, Yesu ya yi koyi da Jehobah sosai. Shi ya sa Yesu ya ce: “Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban.” (Yoh. 14:9) Muna iya yi koyi da halayen Yesu da kuma yadda ya yi sha’ani da mutane. Alal misali, ya ji tausayin wani kuturu da wata mata da take rashin lafiya mai tsanani da kuma waɗanda aka yi musu rasuwa. Idan muka yi koyi da Yesu, muna yin koyi da Jehobah. (Mar. 1:​40, 41; 5:​25-34; Yoh. 11:​33-35) Idan muka yi koyi da halayen Jehobah, dangantakarmu da shi za ta yi ƙarfi.

8. Ka bayyana dalilin da ya sa yin koyi da Yesu zai taimaka mana mu yi “nasara” da duniya.

8 Idan muka bi gurbin Yesu, ba za mu bari Shaiɗan da duniyarsa su hana mu mai da hankali ga bautar Jehobah ba. A daren Yesu na ƙarshe a duniya, ya ce: “Na yi nasara a kan duniya.” (Yoh. 16:33) Yesu yana nufin cewa bai bari tunani da maƙasudai da kuma ayyukan mutanen duniyar nan su rinjaye shi ba. Yesu bai manta da abin da ya sa ya zo duniya ba, wato don ya tsarkake sunan Jehobah. Mu kuma fa? Da akwai abubuwa da yawa da za su iya janye hankalinmu a duniyar nan. Amma idan muka yi koyi da Yesu kuma muka mai da hankali ga yin nufin Jehobah, mu ma za mu yi “nasara” da duniya.​—1 Yoh. 5:5.

9. Mene ne muke bukatar mu yi don mu sami rai na har abada?

9 Bin gurbin Yesu zai sa mu sami rai na har abada. Sa’ad da wani matashi mai arziki ya tambayi Yesu abin da zai yi don ya sami rai na har abada, Yesu ya ce: “Ka zo ka bi ni.” (Mat. 19:​16-21) Yesu ya gaya wa wasu Yahudawa da ba su amince shi Almasihu ba ne cewa: “Tumakina . . . suna bina . . . . Ina ba su rai na har abada.” (Yoh. 10:​24-29) Yesu ya gaya wa Nikodimu memban ’yan Majalisa da yake so ya ƙara sanin koyarwar Yesu cewa waɗanda suka “ba da gaskiya gare shi” za su “sami rai na har abada.” (Yoh. 3:16) Muna nuna mun yi imani da Yesu ta yin abin da ya faɗa da kuma yin koyi da shi. Idan muka yi hakan, za mu sami rai na har abada.​—Mat. 7:14.

TA YAYA ZA MU BI GURBIN YESU?

10. Me muke bukatar mu yi don mu “san Yesu”? (Yohanna 17:3)

10 Wajibi ne mu san Yesu sosai kafin mu iya bin gurbinsa. (Karanta Yohanna 17:3.) ‘Sanin Yesu’ abu ne da za mu ci gaba da yi. Muna bukatar mu ci gaba da koyan abubuwa game da Yesu, wato halayensa da yadda yake tunani da kuma ƙa’idodinsa. Ko da mun daɗe muna bauta wa Jehobah, dole ne mu ci gaba da sanin Jehobah da kuma Ɗansa.

11. Mene ne ke littafin Matiyu da Markus da Luka da kuma Yohanna?

11 Jehobah ya sa an rubuta littafin Matiyu da Markus da Luka da kuma Yohanna domin ya taimaka mana mu san Ɗansa. Waɗannan littattafan suna ɗauke da tarihin Yesu da kuma hidimar da ya yi. Sun nuna mana abubuwan da Yesu ya faɗa, da abubuwan da ya yi da kuma yadda ya ji. Waɗannan littattafai huɗu suna taimaka mana mu yi koyi da Yesu sosai. (Ibran. 12:3) Suna ɗauke da gurbin da Yesu ya kafa mana. Don haka, ta yin nazarin waɗannan littattafan, za mu san Yesu da kyau. A sakamakon haka, za mu iya bin gurbinsa sosai.

12. Ta yaya za mu amfana daga littafin Matiyu da Markus da Luka da kuma Yohanna?

12 Idan muna so mu amfana sosai daga waɗannan littattafan, ba karanta su kawai za mu yi ba. Muna bukatar mu yi nazarinsu da kyau kuma mu yi bimbini a kan abin da muka karanta. (Yosh. 1:8) Bari mu tattauna abubuwa biyu da za su taimaka mana mu yi tunani sosai a kan abin da muka karanta a Linjilar kuma mu yi amfani da su.

13. Me za ka yi don ka amfana sosai daga Linjila?

13 Na farko, ka sa labarin ya zama kamar yana faruwa a gabanka. Ka yi tunanin cewa kana gani da kuma jin abubuwan da ke faruwa. Don ka yi hakan, ka yi bincike a littattafan da ƙungiyar Jehobah ta tanadar don nazari. Ka duba mahallin labarin da kake nazartawa. Ka nemi bayani game da wurare da mutanen da aka ambata a labarin. Idan kana karanta wani labari a Linjila, ka gwada shi da labarin da ke sauran Linjilar. A wasu lokuta, wani marubuci yakan faɗi wani abu mai muhimmanci da wani bai faɗa ba.

14-15. Ta yaya za mu iya yin amfani da darussan da muka koya a Linjila?

14 Na biyu, ka yi amfani da abin da ka koya a rayuwarka. (Yoh. 13:17) Bayan ka yi nazarin wani Linjila da kyau, ka tambayi kanka: ‘Akwai wani darasi da zan iya koya a wannan labarin? Ta yaya zan iya yin amfani da wannan darasin don in taimaka wa wani?’ Ka yi tunanin wani da zai amfana daga darasin, kuma a lokacin da ya dace ka gaya masa.

15 Bari mu tattauna yadda za mu iya yin amfani da waɗannan shawarwarin. Za mu tattauna labarin wata gwauruwa matalauciya wadda Yesu ya lura da abin da ta yi a haikali.

WATA GWAURUWA A HAIKALI

16. Ka bayyana labarin da ke Markus 12:41.

16 Ka sa labarin ya zama kamar yana faruwa a gabanka. (Karanta Markus 12:41.) Akwai wani abin da ya faru a ranar 11 ga Nisan, shekara ta 33 wato ’yan kwanaki kafin Yesu ya mutu. Yesu ya yi amfani da yawancin lokacinsa yana koyarwa a haikali. Limamai a lokacin sun tsananta masa. Wasu daga cikinsu sun tambaye shi daga ina ya sami ikon yin ayyukansa. Wasu kuma sun yi masa tambayoyin da suke ganin ba zai iya amsawa ba. (Mar. 11:​27-33; 12:​13-34) Sai Yesu ya je wani sashen haikalin in da ake kira Farfajiyar Mata, a wurin yana iya ganin akwatin da ake saka gudummawa. Ya zauna yana kallon yadda mutane suke saka gudummawa a akwatin. Ya ga masu arziki suna saka kuɗaɗe da yawa a akwatin. Wataƙila yana jin ƙarar kuɗaɗen sa’ad da suke shiga akwatin.

17. Mene ne gwauruwa matalauciya da aka ambata a Markus 12:42 ta yi?

17 Karanta Markus 12:42. Bayan wani lokaci, sai Yesu ya lura da “wata matalauciya wadda mijinta ya mutu.” (Mar. 12:42) Tana shan wahala sosai, kuma ba ta da kuɗin sayan abubuwan biyan bukatu. Duk da haka, ta je wurin wani akwati kuma ta saka ’yan tagulla biyu da ba su kai kobo ba, wataƙila ba su yi ƙara ba yayin da suke shiga akwatin. Yesu ya san nawa ta saka a akwatin. Ta saka ’yan tagulla biyu kuma su ne kuɗi mafi ƙanƙanta a zamanin. Kuɗin ba zai ma iya sayan ɗan tsuntsu da ake sayarwa da araha don abinci ba.

18. Kamar yadda Markus 12:​43, 44 suka nuna, mene ne Yesu ya ce game da gudummawar da gwauruwar ta ba da?

18 Karanta Markus 12:​43, 44. Gwauruwar ta burge Yesu sosai. Don haka, Yesu ya kira almajiransa ya nuna musu gwauruwar kuma ya ce: “Abin da matalauciyar nan wadda mijinta ya mutu, ta zuba cikin akwatin, ya fi na sauransu duka.” Yesu ya bayyana dalilin da ya sa ya faɗi hakan, ya ce: “Dukansu [musamman masu arziki] sun bayar daga yawan abin da suke da shi ne, amma ita kuwa daga cikin talaucinta ta ba da dukan kome, har ma dukan abin da take dogara da shi.” Sa’ad da wannan gwauruwa ta ba da dukan kuɗin da take da shi, ta nuna cewa tana dogara ga Jehobah ya kula da ita.​—Zab. 26:3.

Kamar Yesu, ka riƙa yaba wa mutane da suke yin iya ƙoƙarinsu a hidimar Jehobah (Ka duba sakin layi na 19-20) *

19. Wane darasi mai muhimmanci ne za mu iya koya daga abin da Yesu ya ce game da wata gwauruwa matalauciya?

19 Ka yi amfani da abin da ka koya a rayuwarka. Ka tambayi kanka, ‘Wane darasi ne na koya daga abin da Yesu ya ce game da gwauruwa matalauciyar nan?’ Ka yi tunani game da wannan gwauruwar. Hakika ta so ta ba Jehobah gudummawa da ya fi hakan yawa. Amma ta yi iya gwargwadon ƙarfinta, ta ba Jehobah abin da take da shi. Yesu ya san cewa Jehobah ya daraja gudummawar da ta ba da. Ga darasi mai muhimmanci da za mu iya koya: Jehobah yana farin ciki idan muka yi masa hidima da dukan zuciyarmu da kuma ƙarfinmu. (Mat. 22:37; Kol. 3:23) Yana farin ciki idan ya ga muna yin iya ƙoƙarinmu! Wannan ƙa’idar ta shafi yawan lokaci da kuzari da muke amfani da shi a wa’azi da kuma halartan taro.

20. Ta yaya za ka yi amfani da darasin da ka koya daga labarin gwauruwar? Ka ba da misali.

20 Ta yaya za ka yi amfani da darasin da ka koya daga labarin gwauruwar nan? Ka yi tunanin ’yan’uwan da suke bukatar a tabbatar musu cewa Jehobah yana farin ciki don ayyukan da suke yi. Alal misali, ka san wata ’yar’uwa tsohuwa da take ganin ba ta da daraja domin rashin lafiya yana hana ta yin ƙwazo a wa’azi? Ko kuma ka san wani ɗan’uwa da yake fama da rashin lafiya mai tsanani da yake sanyin gwiwa domin ba ya iya halartan kowane taro a Majami’ar Mulki? Ka taimaka wa irin waɗannan ’yan’uwa ta wajen yin kalamin da yake da “amfani domin ƙarfafawar juna.” (Afis. 4:29) Ka gaya musu darasi mai kyau da ka koya daga labarin wannan gwauruwa matalauciya. Kalmominka masu ban ƙarfafa za su tabbatar musu da cewa Jehobah yana farin ciki idan muka yi iya ƙoƙarinmu a hidimarsa. (K. Mag. 15:23; 1 Tas. 5:11) Idan ka yaba wa mutane domin suna yin iya ƙoƙarinsu a hidimar Jehobah, kana yin koyi da Yesu.

21. Mene ne ka ƙuduri niyyar yi?

21 Muna farin ciki sosai domin littafin Matiyu da Markus da Luka da kuma Yohanna sun ba da labarin rayuwar Yesu kuma hakan ya sa za mu iya bin gurbinsa sosai! Zai dace ku yi nazarin waɗannan littattafan a Ibadarku ta Iyali. Ku tuna cewa idan muna so mu amfana daga wannan nazarin, muna bukatar mu sa labarin ya zama kamar yana faruwa a gabanmu kuma mu yi amfani da darussan da muka koya a rayuwarmu. Ƙari ga yin koyi da abin da Yesu ya yi, muna bukatar mu saurari abin da ya ce. A talifi na gaba, za mu tattauna abin da muka koya daga furucin Yesu na ƙarshe a duniya.

WAƘA TA 15 Mu Yabi Ɗan Allah!

^ sakin layi na 5 Da yake mu Kiristoci na gaske ne, muna bukatar mu riƙa bin gurbin Yesu sosai. Wane gurbi ne Yesu ya bar mana? Za a amsa tambayar a wannan talifin. Za mu kuma tattauna dalilin da ya sa ya kamata mu riƙa bin gurbinsa da kuma yadda za mu iya yin hakan.

^ sakin layi na 60 BAYANI A KAN HOTUNA: Bayan ta yi tunani a kan abin da Yesu ya ce game da gwauruwa matalauciya, wata ’yar’uwa ta yaba wa wata ’yar’uwa tsohuwa domin hidimar da take yi.