Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 33

Ka Yi Farin Ciki don Ayyukan da Kake Yi a Kungiyar Jehobah

Ka Yi Farin Ciki don Ayyukan da Kake Yi a Kungiyar Jehobah

“Gwamma abin da ido ya gani, da a sa rai a kan abubuwa barkatai.”​—M. WA. 6:9.

WAƘA TA 111 Dalilan da Suke Sa Mu Murna

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Waɗanne ayyuka ne ’yan’uwa suke ƙoƙarin yi a ƙungiyar Jehobah?

 YANZU da wannan duniyar ta kusa ƙarewa, muna da ayyuka da yawa. (Mat. 24:14; Luk. 10:2; 1 Bit. 5:2) Dukanmu muna so mu yi iya ƙoƙarinmu a bautarmu ga Jehobah. ’Yan’uwa da yawa suna ƙara ƙwazo a hidimarsu. Wasu suna so su yi hidimar majagaba. Wasu kuma suna so su soma hidima a Bethel ko kuma a sashen gine-gine. ’Yan’uwa maza da dama suna ƙoƙartawa don su cim ma maƙasudinsu na zama bawa mai hidima ko dattijo. (1 Tim. 3:1, 8) Jehobah yana farin ciki a duk lokacin da ya ga mutanensa suna marmarin yi masa hidima!​—Zab. 110:3; Isha. 6:8.

2. Yaya za mu ji idan ba mu iya cim ma wasu maƙasudai a hidimarmu ga Jehobah ba?

2 Idan mun daɗe muna jira, amma mun kasa cim ma maƙasudinmu, hakan zai iya sa mu sanyin gwiwa. Kuma idan muka gano cewa ba za mu iya yin wasu abubuwa saboda shekarunmu ko kuma yanayinmu ba, hakan ma zai iya sa mu baƙin ciki. (K. Mag. 13:12) Abin da ya faru da wata ’yar’uwa mai suna Melissa * ke nan. Ta so ta yi hidima a Bethel ko kuma ta halarci Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki. Ga abin da ta faɗa, ta ce: “Ba zan iya yin hakan ba saboda yawan shekaruna. A wasu lokuta hakan yakan sa ni sanyin gwiwa.”

3. Waɗanne abubuwa ne wasu suke bukatar su yi kafin su sami ƙarin aiki a ƙungiyar Jehobah?

3 Wasu ’yan’uwa matasa ne kuma suna da ƙoshin lafiya, amma suna bukatar su manyanta kuma su kasance da wasu halaye masu kyau kafin su sami ƙarin ayyuka a ƙungiyar Jehobah. Alal misali, wataƙila suna da ilimi, suna iya yanke shawarwari da wuri, kuma suna da ƙwazon yin aiki, amma mai yiwuwa, za su bukaci su kasance da haƙuri, su riƙa kwantar da hankalinsu don su yi aiki da kyau, kuma su riƙa daraja mutane. Idan ka sa koyan waɗannan halayen a kan gaba, za ka iya samun ƙarin ayyuka a lokacin da ba ka yi tsammani ba. Ka yi la’akari da misalin Nick. A lokacin da yake shekara 20, ya yi baƙin ciki don ba a naɗa shi bawa mai hidima ba. Ya ce, “Na ɗauka cewa ina da matsala.” Amma Nick bai daina yin ƙoƙari ba. Ya yi iya ƙoƙarinsa a ikilisiya da kuma a wa’azi. A yanzu, yana hidima a matsayin memban kwamitin da ke kula da wani ofishinmu.

4. Me za mu tattauna a wannan talifin?

4 Shin kana sanyin gwiwa domin ba ka sami damar yin wani aikin da kake so ka yi a ƙungiyar Jehobah ba? Idan haka ne, ka gaya wa Jehobah yadda kake ji. (Zab. 37:​5-7) Ƙari ga haka, ka tambayi ’yan’uwan da suka manyanta su gaya maka abin da za ka iya yi don ka inganta hidimarka, kuma ka bi shawararsu. Idan ka yi hakan, za ka iya samun ƙarin aiki ko kuma ka cim ma maƙasudinka. Amma kamar Melissa, wataƙila kai ma ba za ka iya yin abubuwan da kake so ka yi a ƙungiyar Jehobah a yanzu ba. Ta yaya za ka ci gaba da yin farin ciki duk da hakan? Wannan talifin zai ba da amsar ta wajen tattauna (1) abin da zai sa ka farin ciki, (2) yadda za ka daɗa yin farin ciki, (3) maƙasudan da za ka iya kafa da za su sa ka farin ciki.

ABIN DA ZAI SA KA FARIN CIKI

5. A kan me ya kamata mu mai da hankali idan muna so mu yi farin ciki? (Mai-Wa’azi 6:9)

5 Littafin Mai-Wa’azi 6:9 ta nuna mana abin da za mu iya yi don mu riƙa farin ciki. (Karanta.) Mutumin da yake mai da hankali ga “abin da ido ya gani” zai yi farin ciki da abin da yake da shi. Amma mutumin da yake sa rai a kan abubuwa barkatai ba zai taɓa gamsuwa ba. Wane darasi ne hakan ya koya mana? Idan muna so mu yi farin ciki, muna bukatar mu mai da hankali ga maƙasudan da za mu iya cim ma.

6. Wane kwatanci ne za mu tattauna, kuma wane darasi ne za mu koya daga kwatancin?

6 Zai yiwu ka gamsu da abin da kake da shi? Mutane da yawa suna ganin hakan ba zai yiwu ba, domin ’yan Adam suna son koyan sabbin abubuwa a kowane lokaci. Amma hakan zai yiwu. Za mu iya yin farin ciki da abin da muke da shi a yanzu. Ta yaya za mu iya yin hakan? Kwatancin da Yesu ya bayar a Matiyu 25:​14-30 game da kuɗin zinariya, * zai taimaka mana mu san yadda za mu yi hakan. Za mu koyi yadda za mu yi farin ciki har ma mu ƙara farin cikinmu don abin da muke da shi a yanzu.

YADDA ZA KA DAƊA YIN FARIN CIKI

7. Ka bayyana kwatancin Yesu game da kuɗin zinariya a taƙaice.

7 Kwatancin game da wani mutum da yake so ya yi tafiya ne. Kafin ya yi tafiyar, ya kira bayinsa kuma ya ba wa kowannensu kuɗin zinariya don su yi masa sana’a da shi. * Da yake ya san yanayin bayinsa, mutumin ya ba na farkon kuɗin zinariya dubu biyar, ya ba na biyun dubu biyu, kuma ya ba na ukun dubu ɗaya. Bawa na ɗaya da na biyu sun yi aiki da ƙwazo don su sami riba. Amma bawa na ukun bai yi kome da kuɗin da aka ba shi ba. Saboda haka, maigidansa ya kore shi daga aiki.

8. Me ya sa bawa na farko a kwatancin Yesu ya yi farin ciki?

8 Bawa na farkon ya yi farin ciki da maigidansa ya ba shi kuɗin zinariya dubu biyar. Wannan kuɗi ne mai ɗimbin yawa, kuma ya nuna cewa maigidan ya yarda da bawan sosai! Bawa na biyun kuma fa? Da kuɗin da aka ba shi ya sa shi sanyin gwiwa domin bai kai na bawa na farkon ba. Amma mene ne ya yi?

Wane darasi ne za mu iya koya daga bawa na biyu da Yesu ya ambata a kwatancinsa  (1) Maigidansa ya ba shi kuɗin zinariya dubu biyu. (2) Ya yi aiki tuƙuru don ya kawo wa maigidansa riba. (3) Ya ninka kuɗin da maigidansa ya ba sh (Ka duba sakin layi na 9-11)

9. Mene ne Yesu bai ce game da bawa na biyun ba? (Matiyu 25:22, 23)

9 Karanta Matiyu 25:22, 23. Yesu bai ce bawa na biyun ya yi baƙin ciki domin an ba shi kuɗin zinariya dubu biyu kawai ba. Kuma Yesu bai ce bawan ya yi gunaguni yana cewa: ‘Abin da zai ba ni ke nan? Me ya sa maigidana ya ba ni kuɗi kaɗan? Ai ni ma ina aiki da ƙwazo kamar wanda aka ba shi kuɗin zinariya dubu biyar! Idan maigidana yana ganin ba na aiki da ƙwazo, ni ma zan binne kuɗin in je in yi aikina.’

10. Mene ne bawa na biyun ya yi da kuɗin da aka ba shi?

10 Kamar bawa na farkon, bawa na biyun ya ɗauki aikin da aka ba shi da muhimmanci sosai, kuma ya yi wa maigidansa aiki tuƙuru. A sakamakon haka, ya ƙara yawan kuɗin zinariyar zuwa dubu huɗu. Maigidan ya albarkaci bawan don ƙwazonsa. Ya yaba masa kuma ya ba shi ƙarin aiki!

11. Me za mu yi don mu daɗa yin farin ciki?

11 Mu ma za mu iya daɗa yin farin ciki idan muka yi iya ƙoƙarinmu wajen yin aikin da aka ba mu a ƙungiyar Jehobah. Ka yi ƙwazo sosai a wa’azi, kuma ka yi aiki tuƙuru a ikilisiya. (A. M. 18:5; Ibran. 10:24, 25) Ka yi shiri da kyau don ka iya ba da kalamai masu ban ƙarfafa a taro. Ka ɗauki kowane jawabi da aka ba ka a taron tsakiyar mako da muhimmanci. Idan an ba ka aikin yi a ikilisiya, ka riƙa zuwa taro da wuri. Kada ka ɗauka cewa ka fi ƙarfin aikin da aka ba ka. Ka yi ƙoƙari ka koyi aikinka da kyau. (K. Mag. 22:29) Idan ka yi aiki da ƙwazo a ikilisiya, za ka ƙarfafa dangantakarka da Jehobah kuma za ka yi farin ciki. (Gal. 6:4) Ƙari ga haka, zai yi maka sauƙi ka yi farin ciki idan aka ba wasu aikin da kake so a ba ka.​—Rom. 12:15; Gal. 5:26.

12. Me ya taimaka wa Melissa da Nick su daɗa farin ciki?

12 Shin ka tuna Melissa da aka ambata a sakin layi na 2, wadda take so ta yi hidima a Bethel ko kuma ta halarci Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki? Ko da yake ba zai yiwu ta cim ma maƙasudan nan ba, ta ce: “Ina yin iya ƙoƙarina a hidimar majagaba, kuma ina yin wa’azi ta hanyoyi dabam-dabam. Hakan ya sa ni farin ciki sosai.” Mene ne Nick ya yi sa’ad da ba a naɗa shi bawa mai hidima ba? Ya ce: “Na mai da hankali ga abubuwan da zan iya yi, kamar yin wa’azi da kuma ba da kalamai masu ban ƙarfafa a taro. Ƙari ga haka, na cika fom ɗin zuwa Bethel kuma aka gayyace ni bayan shekara ɗaya.”

13. Me zai faru idan ka sa ƙwazo a ayyukan da kake yi yanzu? (Mai-Wa’azi 2:24)

13 Idan ka mai da hankali sosai ga ayyukan da aka ba ka yanzu, shin hakan zai sa ka sami ƙarin ayyuka a nan gaba ne? Mai yiwuwa ka samu, kamar yadda muka gani a labarin Nick. Idan kuma ba ka sami ƙarin ayyuka ba, kamar Melissa, za ka iya daɗa yin farin ciki yanzu da abin da kake yi a ƙungiyar Jehobah. (Karanta Mai-Wa’azi 2:24.) Ban da haka, za ka sami kwanciyar hankali domin ka san cewa kana faranta ran Ubangijinmu, Yesu Kristi.

MAƘASUDAN DA ZA SU DAƊA SA MU FARIN CIKI

14. Me ya kamata mu riƙa tunawa game da maƙasudai a hidimar Jehobah?

14 Shin idan muna sa ƙwazo a ayyukan da aka ba mu yanzu, hakan yana nufin cewa ba za mu yi ƙoƙari mu faɗaɗa hidimarmu ga Jehobah ba ne? A’a! Ya kamata mu kafa maƙasudin inganta yadda muke wa’azi da koyarwa, kuma mu kyautata yadda muke taimaka ma ’yan’uwanmu. Za mu cim ma maƙasudanmu idan muka mai da hankali ga taimaka ma wasu maimakon kanmu kawai.​—K. Mag. 11:2; A. M. 20:35.

15. Waɗanne maƙasudai ne za su iya sa ka daɗa farin ciki?

15 Waɗanne maƙasudai ne za ka iya kafa wa kanka? Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka san maƙasudan da za ka iya cim ma. (K. Mag. 16:3; Yak. 1:5) Za ka iya kafa maƙasudan da aka ambata a  sakin layi na farko, alal misali, yin hidimar majagaba na ɗan lokaci ko na kullum, ko yin hidima a Bethel ko kuma taimakawa a sashen gine-gine? Kana iya koyan wani yare ko ka je wani wuri dabam don ka yi wa’azi. Za ka iya samun ƙarin bayani game da maƙasudan nan a babi na 10 na littafin nan Organized to Do Jehovah’s Will ko ka tattauna da dattawan ikilisiyarku. * Yayin da kake ƙoƙari ka cim ma maƙasudan nan, mutane za su ga cewa kana samun ci gaba kuma za ka daɗa yin farin ciki.

16. Me za ka yi idan ka kasa cim ma maƙasudin da ka kafa?

16 Amma idan ba za ka iya cim ma waɗannan maƙasudai da aka ambata ba kuma fa? Ka yi ƙoƙari ka kafa wani maƙasudin da za ka iya cim ma. Ga wasu abubuwan da za ka iya yi.

Waɗanne irin maƙasudai ne za ka iya kafawa? (Ka duba sakin layi na 17) *

17. Bisa ga 1 Timoti 4:13, 15, mene ne ɗan’uwa zai iya yi don ya inganta yadda yake koyarwa?

17 Karanta 1 Timoti 4:13, 15. Idan kai ɗan’uwa ne da ya yi baftisma, za ka iya kyautata yadda kake ba da jawabi da kuma koyarwa. Me ya sa hakan yake da muhimmanci? Domin idan ka yi ƙoƙari ka iya karatu da ba da jawabi da kuma koyarwa, za ka taimaka ma waɗanda suke saurararka. Ka kafa maƙasudin yin nazari da kuma bin shawarar da aka ba mu game da yin jawabi a littafin nan Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa. Ka yi nazarin darussan ɗaya bayan ɗaya, ka gwada bin shawarar a gida kuma ka yi amfani da abin da ka koya yayin da kake jawabi. Ka kuma nemi shawara daga wurin mai ba da shawara na biyu * ko kuma wasu dattawa da suka ƙware a yin “wa’azi da koyarwa.” (1 Tim. 5:17) Ba bin darussa da ke ƙasidar ne kaɗai za ka sa a gaba ba, amma ka mai da hankali ga yadda za ka taimaka wa masu sauraro su ƙarfafa bangaskiyarsu kuma su yi abin da suke koya. Ta yin hakan, za ka daɗa farin ciki kuma za ka sa masu saurararka su ma su daɗa farin ciki.

Waɗanne irin maƙasudai ne za ka iya kafawa? (Ka duba sakin layi na 18) *

18. Me zai taimaka mana mu cim ma maƙasudinmu a yin wa’azi?

18 Dukanmu muna da hakkin yin wa’azi da kuma koyar da mutane. (Mat. 28:19, 20; Rom. 10:14) Za ka so ka ƙware a yin wannan aiki mai muhimmanci? Ka yi nazarin ƙasidar nan Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa, kuma bayan ka yi hakan, sai ka kafa maƙasudin bin abin da ka koya. Za ka iya samun shawarwari masu kyau a Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu da bidiyoyin yadda za mu yi wa’azi da ake nunawa a taron tsakiyar mako. Ka gwada bin hanyoyin yin wa’azi dabam-dabam don ka ga wanda zai fi dacewa da kai. Idan ka bi shawarwarin nan za ka ƙware a yin wa’azi kuma hakan zai sa ka daɗa farin ciki.​—2 Tim. 4:5.

Waɗanne irin maƙasudai ne za ka iya kafawa? (Ka duba sakin layi na 19) *

19. Ta yaya za ka koyi halayen da Jehobah yake so?

19 Yayin da kake kafa maƙasudi, kar ka manta cewa ɗaya da cikin abubuwan da suka fi muhimmanci shi ne koyan halaye da za su faranta ran Allah. (Gal. 5:22, 23; Kol. 3:12; 2 Bit. 1:5-8) Mene ne za ka yi don ka cim ma maƙasudin nan? A ce kana so ka ƙarfafa bangaskiyarka, me za ka yi? Za ka iya karanta talifofi a littattafanmu da suka ba da shawarwari a kan yadda za ka iya ƙarfafa bangaskiyarka. Ƙari ga haka, za ka iya kallon sashen Tashar JW da ke nuna yadda ’yan’uwa suke nuna bangaskiya yayin da suke jimre matsaloli dabam-dabam. Sai ka yi tunanin yadda za ka yi koyi da bangaskiyarsu a rayuwarka.

20. Mene ne za mu yi don mu daɗa farin ciki kuma mu rage baƙin ciki?

20 Babu shakka dukanmu za mu so mu daɗa ƙwazo a hidimarmu ga Jehobah fiye da yadda muke yi yanzu. A sabuwar duniya, za mu sami damar bauta wa Allah ba tare da matsaloli ba. Amma kafin wannan lokaci, idan muka yi iya ƙoƙarinmu a yin ayyukan da aka ba mu, za mu yi farin ciki kuma ba za mu ɓata rai ba ko da ba a ba mu aikin da muke sa ran yi ba. Abu mafi muhimmanci shi ne, za mu ɗaukaka da kuma yabi Jehobah, ‘Allahnmu mai farin ciki.’ (1 Tim. 1:11, New World Translation) Don haka, mu ci gaba da yin farin ciki domin ayyukan da muke yi a ƙungiyar Jehobah!

WAƘA TA 82 ‘Mu Bari Haskenmu Ya Haskaka’

^ sakin layi na 5 Muna ƙaunar Jehobah sosai, kuma muna so mu yi iya ƙoƙarinmu a hidimar da muke masa. Shi ya sa da yawa a cikinmu suna so su daɗa yin ƙwazo a wa’azi, ko kuma su sami ƙarin ayyuka a ikilisiya. Amma idan mun kasa cim ma wasu maƙasudai duk da cewa mun yi iya ƙoƙarinmu fa? Ta yaya za mu ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu kuma mu yi farin ciki? Za mu sami amsar a kwatancin kuɗin zinariya da Yesu ya bayar.

^ sakin layi na 2 An canja wasu sunayen.

^ sakin layi na 6 Ko da yake juyin Littafi Mai Tsarki da aka yi amfani da shi a wannan talifin ya ambata zinariya dubu biyar, da zinariya dubu biyu, da zinariya dubu ɗaya, asalin nassosin Helenanci sun yi amfani da talanti 5 da talanti 2 da talanti 1.

^ sakin layi na 7 MA’ANAR WASU KALMOMI: A zamanin dā, kuɗin zinariya dubu ɗaya ko talanti ɗaya, shi ne kuɗin da lebura zai samu idan ya yi aiki wajen shekara 20.

^ sakin layi na 15 Muna ƙarfafa ’yan’uwa maza da suka yi baftisma su kafa maƙasudin zama bayi masu hidima da kuma dattawa. Don ka san abubuwan da za ka yi don ka cancanci zama bawa mai hidima ko dattijo, ka duba babi na 5 da 6 na littafin nan Organized to Do Jehovah’s Will.

^ sakin layi na 17 MA’ANAR WASU KALMOMI: Mai ba da shawara na biyu dattijo ne da aka ba shi aikin ba da shawara ga dattawa da bayi masu hidima bayan sun yi jawabi a ikilisiya.

^ sakin layi na 65 BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗan’uwa yana bincike a littattafanmu domin ya cim ma maƙasudinsa na inganta yadda yake koyarwa.

^ sakin layi na 67 BAYANI A KAN HOTUNA: Bayan wata ’yar’uwa ta kafa maƙasudin yin wa’azi sa’ad da take yin ayyukanta na yau da kullum, ta ba da katin JW ga wata mata mai sayar da abinci.

^ sakin layi na 69 BAYANI A KAN HOTUNA: Wata ’yar’uwa da ta kafa maƙasudin zama mai bayarwa ta ba ma wata ’yar’uwa kyauta.