Sabbin Mambobi Guda Biyu na Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu
A RANAR Laraba, 18 ga Janairu, 2023, an yi wata sanarwa mai muhimmanci a jw.org, cewa an naɗa Ɗanꞌuwa Gage Fleegle da Ɗanꞌuwa Jeffrey Winder su zama mambobin Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah. ꞌYanꞌuwa biyun nan sun daɗe suna bauta wa Jehobah da aminci.
Ɗanꞌuwa Fleegle ya yi girma a yammancin jihar Pennsylvania na ƙasar Amurka, kuma iyayensa Shaidun Jehobah ne. A lokacin da yake matashi, iyalinsa sun ƙaura zuwa wani ƙaramin ƙauye don su yi waꞌazi a inda ake da bukata. Jim kaɗan bayan haka, ya yi baftisma a ran 20 ga Nuwamba, 1988.
Iyayen Ɗanꞌuwa Fleegle sun yi ta ƙarfafa shi ya yi hidima ta cikakken lokaci. Masu kula da daꞌira da ꞌyanꞌuwan da suke hidima a Bethel suna yawan sauka a gidansu, kuma Ɗanꞌuwa Fleegle ya ga cewa ꞌyanꞌuwan suna farin ciki sosai. Jim kaɗan bayan ya yi baftisma, ya soma hidimar majagaba na kullum a ran 1 ga Satumba, 1989. Bayan shekara biyu, ya cim-ma maƙasudinsa na yin hidima a Bethel wanda ya kafa tun yana shekara 12. Ya fara hidima a Bethel da ke Brooklyn a watan Oktoba, 1991.
A Bethel, Ɗanꞌuwa Fleegle ya yi shekaru takwas yana aiki a wurin da ake haɗa littattafai. Bayan haka, an ce ya yi aiki a Sashen Kula da Hidima. A lokacin, ya yi ꞌyan shekaru yana hidima a wata ikilisiyar da ake yaren Rasha. A shekara ta 2006, ya auri wata ꞌyarꞌuwa mai suna Nadia, kuma ta zo Bethel suka ci-gaba da hidima tare. Sun yi hidima a ikilisiyar da ake yaren mutanen Portugal, kuma sun yi fiye da shekaru goma suna hidima a ikilisiyar da ake Sifanisanci. Bayan Ɗanꞌuwa Fleegle ya yi shekaru da yawa yana aiki a Sashen Kula da Hidima, an kai shi Ofishin Kwamitin Koyarwa. Kuma bayan haka, an kai shi Ofishin Kwamitin Hidima. A watan Maris 2022, an naɗa shi mataimakin Kwamitin Hidima.
Ɗanꞌuwa Winder kuma ya yi girma a garin Murrieta a jihar Kalifoniya na Amurka. Iyayensa Shaidun Jehobah ne kuma ya yi baftisma a ran 29 ga Maris, 1986. A watan Afrilu na shekarar kuma, ya soma yin hidimar majagaba na ɗan lokaci. Ya ji daɗin hidimar sosai. Don haka, bayan ya yi watanni yana hidimar majagaba na ɗan lokaci, sai ya soma hidimar majagaba na kullum a ran 1 ga Oktoba, 1986.
Saꞌad da Ɗanꞌuwa Winder yake matashi, ya ziyarci yayunsa biyu da suke hidima a Bethel a lokacin. Ziyarar nan ta sa ya ce shi ma zai so ya yi hidima a Bethel idan ya yi girma. A watan Mayu, 1990, an gayyace shi ya soma hidima a Bethel da ke Wallkill.
A Bethel, Ɗanꞌuwa Winder ya yi aiki a wurare dabam-dabam, har da Sashen Share-share, da gona, da kuma Sashen da Ke Kula da Maꞌaikatan Bethel. Ya auri wata ꞌyarꞌuwa mai suna Angela a shekara ta 1997, kuma tun daga lokacin suna hidima a Bethel tare. A shekara ta 2014, an kai su Warwick, inda Ɗanꞌuwa Winder ya taimaka wajen gina hedkwatarmu da ke wurin. A shekara ta 2016, an kai su Cibiyar Koyarwa da ke Patterson, kuma a wurin Ɗanꞌuwa Winder ya yi aiki a Sashen Bidiyo da Sauti. Bayan shekara huɗu, sun koma Warwick, kuma ya soma aiki a Ofishin Kwamiti Mai Kula da Maꞌaikata. A watan Maris 2022, an naɗa shi ya zama mataimakin Kwamiti Mai Kula da Maꞌaikata.
Adduꞌarmu ita ce, Jehobah ya yi wa waɗannan makiyaya albarka yayin da suke ci-gaba da yin hidima don Mulkin Allah.—Afis. 4:8.