Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Me ya sa ya kamata Kiristoci su yi hankali da yadda suke amfani da manhajar tura saƙonni?

Wasu Kiristoci suna amfani da na’urori don su riƙa magana da iyalinsu da kuma ’yan’uwa Shaidu. Amma Kirista da ya manyanta zai riƙa tuna da wannan shawarar: “Mai hankali yakan ga hatsari, ya kauce, amma marar tunani yakan sa kai, ya sha wahala.”​—K. Mag. 27:12.

Mun san cewa Jehobah yana so ya kāre mu. Saboda haka, ba ma cuɗanya da mutane da ke raba kan ’yan’uwa a ikilisiya ko waɗanda aka yi musu yankan zumunci ko kuma waɗanda suke yaɗa koyarwar ƙarya. (Rom. 16:17; 1 Kor. 5:11; 2 Yoh. 10, 11) Wasu ’yan’uwa a ikilisiya ko kuma wasu da ke tarayya da ’yan’uwanmu ba sa bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. (2 Tim. 2:​20, 21) Ya kamata mu riƙa tunawa da hakan sa’ad da muke zaɓan abokai. Zaɓan abokan kirki ta manhajar tura saƙonni zai iya yin wuya.

Ya kamata mu mai da hankali musamman idan muna so mu shiga babban rukuni a manhajar tura saƙonni. Wasu Kiristoci sun shiga irin rukunin nan kuma hakan ya jawo musu mugun sakamako. Zai yi wuya Kirista ya yi hattara idan ɗarurruwan mutane ko kuma dubbai ne ke rukunin. Ba zai yiwu ba mu san ko dukansu suna da dangantaka mai kyau da Jehobah. Zabura 26:4 ta ce: “Ba na sha’ani da mutanen banza, ba ruwana da munafukai.” Hakan ya nuna cewa ya dace mu riƙa aika saƙonni ga mutanen da muka sani kawai.

Ko da mutanen da ke rukunin ba su da yawa, ya kamata Kirista ya mai da hankali don yawan lokacin da yake yi a dandalin da kuma abubuwan da ake tattaunawa. Kada mu ɗauka cewa dole ne mu amsa kowane saƙo ko da batu mai kyau ake tattaunawa ko kuma ba zai ɗauki lokaci ba. Bulus ya gargaɗi Timoti cewa ya guji mutanen da ke ‘gulma, suna shiga al’amuran waɗansu.’ (1 Tim. 5:13) A yau, muna iya yin hakan ta na’ura.

Kirista da ya manyanta ba zai faɗa ko kuma ya saurari baƙar magana ko batun sirri da aka yi game da ’yan’uwansu Shaidu ba. (Zab. 15:3; K. Mag. 20:19) Ba zai dace ya riƙa yaɗa labarai da aka ƙara gishiri ko kuma waɗanda ba a san ko gaskiya ba ne. (Afis. 4:25) Muna samun labarai da aka tabbatar da su a dandalin jw.org da kuma shirye-shiryen Tashar JW da ake yi kowane wata.

Wasu Shaidun Jehobah suna yin amfani da manhajar aika saƙonni don su yi talla da saya-da-sayarwa kuma su ba mutane aiki. Yin hakan kasuwanci ne kuma bai da wata alaƙa da ibadarmu. Bai kamata Kiristoci da suke so su guji “son kuɗi” su riƙa amfani da ’yan’uwansu don yin kasuwanci ba.​—Ibran. 13:5.

Ba zai dace mu yi amfani da manhajar tura saƙonni don mu roƙi kuɗi a madadin ’yan’uwa da ke cikin matsaloli ba. Muna ƙaunar ’yan’uwanmu kuma muna so mu taimaka wa mabukata da kuma ƙarfafa su. (Yak. 2:​15, 16) Amma yin hakan ta babban rukunin aika saƙonni zai ɓata shirin da reshen ofishinmu ko kuma ikilisiya take yi don a taimaka musu. (1 Tim. 5:​3, 4, 9, 10, 16) Kuma ba zai dace mu sa mutane su riƙa ganin cewa an zaɓe mu mu riƙa kula da ’yan’uwanmu ba.

Muna so mu yi abin da zai sa a ɗaukaka Allah. (1 Kor. 10:31) Saboda haka, sa’ad da kake so ka yi amfani da manhajar tura saƙonni ko kuma wasu hanyoyin sadarwa, ka yi tunani a kan haɗarurruka da ke tattare da yin hakan.