Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 12

Kauna Tana Sa Mu Jimre Kiyayya

Kauna Tana Sa Mu Jimre Kiyayya

“Umarnin da na ba ku shi ne ku ƙaunaci juna. Idan dai duniya ta ƙi ku, ku sani cewa ta ƙi ni kafin ta ƙi ku.” ​—YOH. 15:​17, 18.

WAƘA TA 129 Za Mu Riƙa Jimrewa

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Kamar yadda Matiyu 24:9 ta nuna, me ya sa ba za mu yi mamaki ba sa’ad da mutane suka tsane mu?

JEHOBAH ya halicce mu mu riƙa ƙaunar mutane kuma mu so mutane su ƙaunace mu. Saboda haka, idan wani ya tsane mu, muna baƙin ciki da kuma tsoro. Alal misali, wata ’yar’uwa mai suna Georgina da take zama a Turai ta ce: “A lokacin da nake ’yar shekara 14, mahaifiyata ta tsane ni don ina bauta wa Jehobah. Na yi baƙin ciki kuma na kaɗaita, sai na soma ganin cewa wataƙila ni ba ’yar kirki ba ce.” * Wani ɗan’uwa mai suna Danylo ya ce: “Sa’ad da sojoji suka yi mini dūka, suka zage ni kuma suka yi mini barazana don ni Mashaidi ne, na tsorata kuma na ji kunya.” Muna baƙin ciki sosai sa’ad da mutane suka tsane mu, amma hakan ba ya sa mu mamaki. Yesu ya annabta cewa za a tsane mu.​—Karanta Matiyu 24:9.

2-3. Me ya sa aka tsani mabiyan Yesu?

2 Mutane sun tsani mabiyan Yesu. Me ya sa? Domin kamar Yesu, mu “ba na duniya ba ne.” (Yoh. 15:​17-19) Saboda haka, ko da yake muna daraja gwamnatoci, ba ma sa hannu a siyasa, ba ma tsara wa tuta kuma ba ma yin taken ƙasa. Jehobah ne kaɗai muke bauta wa. Muna goyon bayan Mulkin Allah, amma Shaiɗan da mutanensa sun ce Allah bai cancanci yin sarauta ba. (Far. 3:​1-5, 15) Muna yin wa’azi cewa Mulkin Allah ne kawai zai magance matsalolin ’yan Adam kuma ba da daɗewa ba zai halaka dukan mutane da suke adawa da Mulkin. (Dan. 2:44; R. Yar. 19:​19-21) Saƙon labari ne mai daɗi ga masu sauƙin kai, amma labari marar daɗi ga mugaye.​—Zab. 37:​10, 11.

3 Ƙari ga haka, mutane sun tsane mu domin muna bin dokokin Allah. Abin da Allah ya ce bai dace ba shi ne mutanen duniya suke ganin ya dace. Alal misali, mutane da yawa a yau suna ganin ba laifi ba ne mutane su yi irin lalatar da mutanen Saduma da Gwamarata suka yi da ya sa Allah ya halaka su. (Yahu. 7) Mutane da yawa suna yi mana ba’a domin muna bin ƙa’idodin Jehobah kuma suna cewa muna da tsattsaurar ra’ayi.​—1 Bit. 4:​3, 4

4. Waɗanne halaye ne suke ƙarfafa mu sa’ad da mutane suka tsane mu?

4 Me zai taimaka mana mu jimre sa’ad da mutane suka tsane mu kuma suka zage mu? Muna bukatar mu kasance da bangaskiya cewa Jehobah zai taimaka mana. Kamar garkuwa, bangaskiyarmu za ta “kashe kibiyoyi na wutar Mugun.” (Afis. 6:16) Amma ba bangaskiya kaɗai muke bukata ba, muna bukatar ƙauna. Me ya sa? Domin ƙauna “ba ta jin tsokana,” amma tana haƙuri da kuma jimre da abubuwan da ke sa mu baƙin ciki. (1 Kor. 13:​4-7, 13) Bari mu ga yadda ƙaunarmu ga Jehobah da ’yan’uwanmu da kuma maƙiyanmu za ta taimaka mana mu jimre.

ƘAUNARMU GA JEHOBAH TANA SA MU JIMRE ƘIYAYYA

5. Mene ne Yesu ya yi domin yana ƙaunar Ubansa?

5 A dare na ƙarshe kafin a kashe Yesu, ya gaya wa mabiyansa cewa: “Ina yin daidai abin da Uba ya faɗa mini in yi ne domin duniya ta sani ina ƙaunar Uban.” (Yoh. 14:31) Yesu ya jimre da jarrabobi masu tsanani domin yana ƙaunar Jehobah. Mu ma za mu iya yin hakan idan muna ƙaunar Jehobah.

6. Kamar yadda yake a Romawa 5:​3-5, yaya bayin Jehobah suke ji sa’ad da mutane suke tsananta musu?

6 Bayin Jehobah sun jimre tsanantawa da yawa domin suna ƙaunar sa. Alal misali, a lokacin da majalisar Yahudawa suka ce wa manzannin su daina wa’azi, ƙaunar su ga Allah ta motsa su “yi wa Allah biyayya fiye da” mutane. (A. M. 5:29; 1 Yoh. 5:3) Irin wannan ƙaunar ta taimaka wa ’yan’uwanmu da hukuma take tsananta musu su kasance da aminci. Maimakon mu yi sanyin gwiwa, muna ganin gata ce a gare mu mu jimre da yadda mutanen duniya suka tsane mu.​—A. M. 5:41; karanta Romawa 5:​3-5.

7. Me ya kamata mu yi sa’ad da danginmu suka tsananta mana?

7 Idan danginmu suka tsananta mana, hakan zai kasance da wuya sosai mu jimre. Sa’ad da muka soma nazari, wasu cikinsu suna iya ganin cewa an yaudare mu. Wasu suna iya ganin cewa ba mu san abin da muke yi ba. (Gwada Markus 3:21.) Suna iya soma wulaƙanta mu. Bai kamata hakan ya sa mu mamaki ba. Yesu ya ce: “Mutanen gidan mutum ne kuma za su zama abokan gābansa.” (Mat. 10:36) Ko da danginmu sun tsane mu, bai kamata mu ɗauke su a matsayin maƙiyanmu ba. A maimakon haka, mu ci gaba da nuna ƙauna ga Jehobah, kuma hakan zai sa mu ƙaunaci mutane. (Mat. 22:​37-39) Amma ba za mu taɓa daina bin dokoki da kuma ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki don mu faranta wa ’yan Adam rai ba.

Muna iya shan wahala a wasu lokuta, amma Jehobah zai ci gaba da goyon bayanmu da kuma ƙarfafa mu (Ka duba sakin layi na 8-10)

8-9. Mene ne ya taimaka wa wata ’yar’uwa ta jimre duk da tsanantawa?

8 Georgina da aka ambata ɗazu ta yi tsayin dāka duk da cewa mahaifiyarta ta tsananta mata sosai. Georgina ta ce: “Ni da mahaifiyata mun soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidu. Amma bayan wata shida sa’ad da na so in halarci taro, sai mahaifiyata ta soma tsananta mini. Sai na gano cewa tana tattaunawa da ’yan ridda kuma tana amfani da abin da suka ce sa’ad da take magana da ni. Za ta zage ni, ta ja min gashi, ta shaƙe ni kuma ta jefar da littattafaina. Na yi baftisma sa’ad da na kai ’yar shekara 15. Mahaifiyata ta yi ƙoƙari ta hana ni bauta wa Jehobah ta wajen saka ni a wurin da ake kula da matasa masu taurin kai, wasu cikinsu suna shan ƙwaya da kuma aikata laifofi. Yana da wuya mutum ya jimre da tsanantawa idan wani da ya kamata ya ƙaunace ka da kuma kula da kai ne ke tsananta maka.”

9 Mene ne ya taimaka wa Georgina ta jimre? Ta ce: “A ranar da na karance Littafi Mai Tsarki ne mahaifiyata ta tasar mini. Na kasance da tabbaci cewa na sami gaskiya, kuma na kusaci Jehobah sosai. Nakan yi addu’a a kai a kai ga Jehobah kuma ya saurara ni. Sa’ad da nake zama a wurin da ake kula da matasa masu taurin kai, wata ’yar’uwa ta gayyace ni gidanta, kuma muka yi nazarin Littafi Mai Tsarki tare. A wannan lokacin, ’yan’uwa a Majami’ar Mulki sun ƙarfafa ni. Sun sa na ji kamar ni ’yar iyalinsu ce. A bayyane yake cewa Jehobah ya fi masu tsananta mana ƙarfi, ko da su waye ne.”

10. Mene ne Jehobah zai yi don ya taimaka mana?

10 Manzo Bulus ya rubuta cewa babu abin da zai “raba mu da ƙaunar da Allah yake yi mana ta wurin Almasihu Yesu Ubangijinmu.” (Rom. 8:​38, 39) Ko da za mu sha wahala na wasu lokuta, Jehobah zai riƙa yi mana ta’aziyya da kuma ƙarfafa mu. Kuma kamar yadda muka gani a labarin Georgina, Jehobah zai yi amfani da ’yan’uwanmu don ya taimaka mana.

ƘAUNARMU GA ’YAN’UWA TANA SA MU JIMRE ƘIYAYYA

11. Ta yaya ƙaunar da Yesu ya ambata a Yohanna 15:​12, 13 za ta taimaka wa almajiransa? Ka ba da misali.

11 A dare na ƙarshe kafin a kashe Yesu, ya gaya wa almajiransa su riƙa ƙaunar juna. (Karanta Yohanna 15:​12, 13.) Ya san cewa ƙauna za ta taimaka musu su kasance da haɗin kai kuma su jimre tsanantawa. Ka yi la’akari da ikilisiya da ke Tasalonika. A lokacin da aka kafa wannan ikilisiya ne aka soma tsananta wa ’yan’uwa da ke wajen. Duk da haka, ’yan’uwan sun kafa misali mai kyau na jimrewa da kuma nuna ƙauna. (1 Tas. 1:​3, 6, 7) Bulus ya ƙarfafa su su ci gaba da nuna ƙauna “ƙwarai da gaske.” (1 Tas. 4:​9, 10) Ƙauna za ta sa su riƙa ƙarfafa waɗanda ba su da ƙarfin zuciya, da taimaka wa marasa ƙarfi. (1 Tas. 5:14) Da alama cewa sun bi shawarar Bulus don a wasiƙarsa ta biyu da ya rubuta musu bayan wajen shekara ɗaya, Bulus ya ce: “Ƙaunar kowane ɗayanku ga juna tana ta ƙaruwa.” (2 Tas. 1:​3-5) Ƙaunarsu ta taimaka musu su jimre mawuyanci yanayi da kuma tsanantawa.

Ƙauna za ta iya sa mu jimre da ƙiyayya (Ka duba sakin layi na 12) *

12. A lokacin yaƙi, ta yaya ’yan’uwa a wata ƙasa suka nuna cewa suna ƙaunar juna?

12 Ka yi la’akari da labarin Danylo da aka ambata ɗazu da matarsa. Sa’ad da aka soma yaƙi a garinsu, sun ci gaba da halartan taro da yin wa’azi iya ƙoƙarinsu da kuma raba abincinsu da ’yan’uwa. Wata rana, sojoji riƙe da bindiga suka je gidansu. Danylo ya ce: “Sun ce in daina bauta wa Jehobah. Sa’ad da na ƙi, sai suka yi mini dūka kuma suka yi harbi a sama kamar suna so su harbe ni. Kafin su tafi, suka yi barazana cewa za su dawo su yi wa matata fyaɗe. Amma ’yan’uwanmu suka sa mu a jirgin ƙasa zuwa wani gari. Ba zan taɓa manta da waɗannan ’yan’uwan ba. Kuma sa’ad da muka isa garin, ’yan’uwa sun ba mu abinci kuma suka samo mini aiki da gida! Daga baya, mun ba wasu Shaidu da yaƙin ya shafa masauki.” Irin waɗannan labaran sun nuna cewa ƙaunar juna za ta taimaka mana mu jimre da ƙiyayya.

NUNA ƘAUNA GA MAƘIYANMU TANA SA MU JIMRE DA ƘIYAYYA

13. Ta yaya ruhu mai tsarki yake taimaka mana mu jimre a hidimarmu ga Jehobah ko da mutane sun tsane mu?

13 Yesu ya gaya wa mabiyansa su riƙa ƙaunar maƙiyansu. (Mat. 5:​44, 45) Hakan yana da sauƙi ne? A’a! Amma hakan zai yiwu da taimakon ruhun Allah. Wasu cikin ’ya’yan da ruhun Allah yake haifarwa su ne haƙuri da kirki da tawali’u da shan ƙarfin sha’awar jiki. (Gal. 5:​22, 23) Waɗannan halayen sun taimaka mana mu jimre da ƙiyayya. Mutane da yawa sun daina tsananta mana domin mijinsu ko matarsu ko yaronsu ko kuma maƙwabcinsu ya nuna musu waɗannan halayen. Da yawa a cikin masu tsananta mana sun zama ’yan’uwanmu. Saboda haka, idan yana maka wuya ka ƙaunaci waɗanda suka tsane ka domin kana bauta wa Jehobah, ka roƙe shi ya ba ka ruhunsa. (Luk. 11:13) Kuma ka kasance da tabbaci cewa yin biyayya ne ga Allah ya fi kyau a kowane lokaci.​K. Mag. 3:​5-7.

14-15. Ta yaya Romawa 12:​17-21 ya taimaka wa Yasmeen ta nuna wa mijinta ƙauna duk da cewa yana tsananta mata?

14 Ka yi la’akari da Yasmeen wadda take zama a Gabas ta Tsakiya. Sa’ad da ta zama Mashaidiya, mijinta ya ɗauka cewa an yaudare ta kuma ya yi ƙoƙari ya hana ta bauta wa Allah. Ya zage ta kuma ya zuga danginsu da wani limami da kuma boka su yi mata barazana kuma suka ce tana so ta raba kan iyalinta. Mijinta ya zagi ’yan’uwa sa’ad da suke taro! Sau da yawa, Yasmeen tana kuka don yadda ake wulaƙanta ta.

15 ’Yan’uwa sun ƙarfafa Yasmeen a Majami’ar Mulki. Dattawa sun ce ta bi shawarar da ke Romawa 12:​17-21. (Karanta.) Yasmeen ta ce: “Ya yi mini wuya sosai, amma na roƙi Jehobah ya taimaka mini, kuma na yi iya ƙoƙarina don na bi abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Saboda haka, sa’ad da maigidana ya zuba shara a kicin da fushi, ina sharewa. Sa’ad da ya zage ni, ba na yi masa baƙar magana. Kuma sa’ad da yake rashin lafiya, nakan kula da shi sosai.”

Masu tsananta mana suna iya canja halinsu sa’ad da muka nuna musu ƙauna (Ka duba sakin layi na 16-17) *

16-17. Wane darasi ne ka koya daga misalin Yasmeen?

16 Yasmeen ta samu albarka don yadda ta nuna wa mijinta ƙauna. Ta ce: “Maigidana ya soma amincewa da ni sosai domin ya san cewa zan faɗi gaskiya a kowane lokaci. Sai ya soma saurarawa sa’ad da muke tattaunawa game da addini kuma ya yarda mu zauna lafiya. Yanzu yana ƙarfafa ni in je taro kuma dangantakarmu ta gyaru. Ina fatan cewa mijina zai soma bauta wa Jehobah tare da ni.”

17 Labarin Yasmeen ya nuna cewa “ƙauna takan sa haƙuri cikin kowane hali, . . . da sa zuciya cikin kowane hali, da kuma jimiri cikin kowane hali.” (1 Kor. 13:​4, 7) Ƙiyayya tana da ƙarfi kuma tana sa mutum baƙin ciki, amma ƙauna ta fi ta ƙarfi. Idan muka nuna wa mutane ƙauna, suna iya daina tsananta mana kuma hakan na faranta ran Jehobah. Amma ko da masu tsananta mana sun ci gaba da yin hakan, za mu ci gaba da yin farin ciki. Ta yaya?

KU YI FARIN CIKI SA’AD DA AKE TSANANTA MUKU

18. Me ya sa ya dace mu yi farin ciki sa’ad da aka ƙi mu?

18 Yesu ya ce: “Masu albarka ne ku idan mutane suka ƙi ku!” (Luk. 6:22) Ba ma son a ƙi mu, domin ba ma farin ciki sa’ad da ake tsananta mana don imaninmu. Saboda haka, me ya sa ya kamata mu riƙa farin ciki sa’ad da aka ƙi mu? Ka yi la’akari da dalilai uku. Na farko, muna faranta wa Allah rai sa’ad da muka jimre. (1 Bit. 4:​13, 14) Na biyu, bangaskiyarmu za ta daɗa ƙarfi. (1 Bit. 1:7) Na uku, za mu sami ladar rai na har abada.​—Rom. 2:​6, 7.

19. Me ya sa manzannin Yesu suka yi farin ciki bayan an bulale su?

19 Jim kaɗan bayan an ta da Yesu daga matattu, manzanninsa sun shaida farin cikin da ya ce za su yi. Sun yi farin ciki bayan an yi musu dūka kuma aka ce su daina yin wa’azi. Me ya sa? Domin “an ga sun isa su sha wulaƙanci saboda sunan Yesu.” (A. M. 5:​40-42) Suna ƙaunar Shugabansu fiye da yadda suke tsoron tsanantawa. Kuma sun nuna ƙaunarsu ta wajen yin wa’azi sosai. ’Yan’uwa da yawa a yau sun ci gaba da bauta wa Jehobah da aminci duk da matsalolin da suke fuskanta. Sun san cewa Jehobah ba zai manta da ayyukansu da kuma ƙaunarsu ga sunansa ba.​—Ibran. 6:10.

20. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

20 Mutane za su ci gaba da tsananta mana. (Yoh. 15:19) Amma bai kamata mu ji tsoro ba. A talifi na gaba, za mu ga cewa Jehobah “zai ƙarfafa . . . ya kuma tsare” bayinsa masu aminci. (2 Tas. 3:3) Saboda haka, bari mu ci gaba da ƙaunar Jehobah da ’yan’uwanmu, har da maƙiyanmu. Idan muka bi wannan shawarar, za mu kasance da haɗin kai kuma bangaskiyarmu za ta yi ƙarfi. Ban da haka, za mu ɗaukaka Jehobah kuma za mu nuna cewa ƙaunarmu ta fi ƙiyayya ƙarfi.

WAƘA TA 106 Mu Riƙa Nuna Ƙauna

^ sakin layi na 5 A wannan talifin, za mu ga yadda ƙaunarmu ga Jehobah da ’yan’uwanmu da kuma maƙiyanmu za ta taimaka mana mu jimre da ƙiyayya. Za mu kuma ga abin da ya sa Yesu ya ce za mu iya yin farin ciki sa’ad da aka tsane mu.

^ sakin layi na 1 An canja sunayen.

^ sakin layi na 58 BAYANI A KAN HOTO: Bayan sojoji sun yi wa Danylo barazana, ’yan’uwa sun taimaka wa shi da matarsa su ƙaura, kuma ’yan’uwan da ke wurin da suka koma sun marabce su sosai.

^ sakin layi na 60 BAYANI A KAN HOTO: Mijin Yasmeen ya tsananta mata, amma dattawa sun ba ta shawara mai kyau. Ta nuna cewa ita matar kirki ce kuma ta kula da shi sa’ad da yake rashin lafiya.