Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 13

Ta Yaya Jehobah Yake Kāre Ka?

Ta Yaya Jehobah Yake Kāre Ka?

“Ubangiji mai aminci ne, zai ƙarfafa ku, ya tsare ku daga Mugun nan, wato, Shaiɗan.”​—2 TAS. 3:3.

WAƘA TA 124 Mu Kasance da Aminci

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Me ya sa Yesu ya ce Jehobah ya kāre almajiransa?

A DARE na ƙarshe kafin a kashe Yesu, ya yi tunani game da ƙalubale da almajiransa za su fuskanta. Domin Yesu yana ƙaunar almajiransa, ya roƙi Ubansa ya “tsare su daga mugun nan.” (Yoh. 17:​14, 15) Yesu ya san cewa bayan ya koma sama, Shaiɗan zai ci gaba da tsananta wa duk wanda yake so ya bauta wa Jehobah. Babu shakka, bayin Jehobah za su bukaci kāriya.

2. Me zai tabbatar mana da cewa Jehobah zai amsa addu’o’inmu?

2 Jehobah yana ƙaunar Yesu shi ya sa ya amsa addu’arsa. Idan muka yi iya ƙoƙarinmu don mu faranta ran Jehobah, zai ƙaunace mu kuma zai amsa addu’armu na neman taimako da kāriya. Jehobah Uba ne mai ƙaunar yaransa. Saboda haka, zai ci gaba da kula da su. Idan bai yi hakan ba, zai ɓata sunansa!

3. Me ya sa muke bukatar kāriyar Jehobah a yau?

3 Yanzu ne muka fi bukatar taimakon Jehobah. An kori Shaiɗan daga sama kuma yanzu yana “cike da fushi.” (R. Yar. 12:12) Shaiɗan ya sa wasu mutane su riƙa ganin cewa idan sun tsananta mana, suna “yin aikin Allah ne.” (Yoh. 16:2) Wasu da ba su yi imani da Allah ba suna tsananta mana domin mun yi dabam da mutanen duniya. Ko da mene ne ya sa mutane suke tsananta mana, ba ma jin tsoro. Me ya sa? Domin Kalmar Allah ta ce: “Ubangiji mai aminci ne, zai ƙarfafa ku, ya tsare ku daga Mugun nan, wato, Shaiɗan.” (2 Tas. 3:3) Ta yaya Jehobah yake kāre mu? Za mu tattauna hanyoyi biyu da yake yin hakan.

JEHOBAH YA YI TANADIN KAYAN KĀRIYA

4. Kamar yadda Afisawa 6:​13-17 suka nuna, waɗanne kayan kāriya ne Jehobah ya tanada mana?

4 Jehobah ya tanadar mana da kayan kāriya da za su kāre mu daga harin Shaiɗan. (Karanta Afisawa 6:​13-17.) Waɗannan kayan kāriyar suna da ƙarfi da kuma ban-taimako! Amma idan muna so su kāre mu, za mu riƙa saka su a kowane lokaci. Mene ne kowane kayan kāriyar ke wakilta? Bari mu tattauna kowannensu.

5. Wace ɗamara ce ya kamata mu sha, kuma me ya sa?

5 Gaskiya ta zama ɗamararku: Gaskiyar nan tana wakiltar gaskiyar da ke Kalmar Allah, wato Littafi Mai Tsarki. Me ya sa ya wajaba mu sha wannan ɗamarar? Domin Shaiɗan “uban ƙarya” ne. (Yoh. 8:44) Ya yi shekaru dubbai yana yin ƙarya da kuma ruɗan “dukan duniya”! (R. Yar. 12:9) Amma gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki tana kāre mu daga yaudara. Ta yaya za mu sha wannan ɗamarar? Ta wajen koyan gaskiya game da Jehobah da bauta masa “cikin ruhu, da cikin gaskiya” da kuma yin gaskiya a cikin ayyukanmu duka.​—Yoh. 4:24; Afis. 4:25; Ibran. 13:18.

Ɗamara: Dukan gaskiyar da ke Kalmar Allah

6. Mene ne rigar ƙarfe ta adalci, kuma me ya sa ya wajaba mu riƙa saka ta?

6 Rigar ƙarfe ta adalci tana wakiltar ƙa’idodin Jehobah. Me ya sa ya wajaba mu saka wannan rigar ƙarfe? Kamar yadda rigar ƙarfe take kāre zuciyar soja daga harsashi, haka ma rigar ƙarfe ta adalci take kāre zuciyarmu ta alama daga ɓatanci na wannan duniyar. (K. Mag. 4:23) Jehobah yana so mu ƙaunace shi da kuma bauta masa da dukan zuciyarmu. (Mat. 22:​36, 37) Saboda haka, Shaiɗan yana nema ya hana mu bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya ta wajen sa mu so kayan duniya. (Yaƙ. 4:4; 1 Yoh. 2:​15, 16) Idan bai yi nasara ba, zai sa mu yi wani abu da zai ɓata wa Jehobah rai.

Rigar ƙarfe: Ƙa’idodin Jehobah

7. Ta yaya muke saka rigar ƙarfe ta adalci?

7 Muna saka rigar ƙarfe ta adalci ta wajen yin biyayya da ƙa’idodin Jehobah da kuma yin rayuwar da ta jitu da ƙa’idodinsa. (Zab. 97:10) Wasu suna iya ganin cewa ƙa’idodin Jehobah suna hana mu sākewa. Amma idan muka daina bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a rayuwarmu, za mu zama kamar soja da ya cire rigarsa ta ƙarfe a bakin dāga domin yana ganin tana da nauyi sosai. Yin hakan zai zama wawanci. Amma idan muna ƙaunar Jehobah, umurnansa ba za su yi mana “nauyi,” ba amma za su cece mu.​—1 Yoh. 5:3.

8. Me yake nufi mu sa labari mai daɗi na salama ya zama kamar takalma a ƙafafunmu?

8 Bulus ya kuma ƙarfafa mu mu sa labari mai daɗi na salama ya zama kamar takalma a ƙafafunmu. Hakan yana nufin mu kasance a shirye don mu riƙa wa’azi a kowane lokaci. Muna ƙarfafa bangaskiyarmu sa’ad da muke wa mutane wa’azi. Yana da ban ƙarfafa sa’ad da muka ga yadda bayin Jehobah a faɗin duniya suke amfani da kowane zarafi da suka samu don su yi wa’azi. Alal misali, suna wa’azi a wajen aikinsu ko a makaranta, ko a gida-gida ko kuma a yankin da ake kasuwanci. Suna yin hakan sa’ad da suka je yin sayayya da sa’ad da suka ziyarci danginsu da ba Shaidu ba ko kuma suke magana da mutane da suka sani da kuma sa’ad da ba sa iya fitowa daga gida na ɗan lokaci. Idan tsoro ya hana mu yin wa’azi, za mu zama kamar sojan da ya cire takalmansa a bakin dāga. Babu shakka, irin sojan nan zai ji rauni a ƙafarsa. Hakan zai sa ya yi wuya ya kāre kansa sa’ad da aka kawo masa hari, kuma ba zai iya bin umurnin kwamandarsa ba.

Takalma: Kasancewa a shirye don yin wa’azi

9. Me ya sa muke bukatar mu ɗauki garkuwarmu?

9 Bangaskiya ta zama garkuwarku: Garkuwar nan tana wakiltar bangaskiyarmu ga Jehobah. Muna da bangaskiya cewa Jehobah zai cika dukan alkawuransa. Wannan bangaskiyar za ta taimaka mana mu “kashe kibiyoyi na wutar Mugun nan.” Me ya sa muke bukatar mu ɗauki wannan garkuwar? Domin tana kāre mu daga koyarwar ’yan ridda kuma tana hana mu sanyin gwiwa sa’ad da mutane suka yi mana ba’a don imaninmu. Idan ba mu da bangaskiya, ba za mu iya yin biyayya ga Jehobah ba sa’ad da mutane suka matsa mana mu ƙarya dokokinsa. Amma bangaskiya tana kāre mu a duk lokacin da muka ƙi ƙarya dokokin Jehobah a wajen aiki ko a makaranta. (1 Bit. 3:15) Bangaskiya tana kāre mu a duk lokacin da muka ƙi yin aikin da zai hana mu bauta wa Jehobah yadda muke so. (Ibran. 13:​5, 6) Bangaskiyarmu tana kāre mu a duk lokacin da muka bauta wa Jehobah duk da tsanantawa.​—1 Tas. 2:2.

Garkuwa: Bangaskiyarmu ga Jehobah da kuma alkawuransa

10. Mene ne hular kwano na ceto, kuma me ya sa ya wajaba mu saka shi?

10 Hular kwano na ceto ita ce begen da Jehobah ya ba mu. Wato begen cewa zai albarkaci duk mutanen da ke yin nufinsa kuma zai ta da su idan suka mutu. (1 Tas. 5:8; 1 Tim. 4:10; Tit. 1:​1, 2) Kamar yadda hular kwano ke kāre kan soja, haka ne begenmu ke kāre tunaninmu. A wace hanya? Wannan begen yana sa mu mai da hankali ga alkawuran Allah kuma yana taimaka mana don kada matsaloli su shawo kanmu. Ta yaya muke saka wannan hular kwano? Muna yin hakan ta wajen sa tunaninmu ya jitu da na Allah. Alal misali, ba za mu sa rai a kan arziki marar tabbata ba, amma za mu dogara ga Allah.​—Zab. 26:2; 104:34; 1 Tim. 6:17.

Hular kwano: Begen rayuwa har abada

11. Mene ne takobin ruhu, kuma me ya sa muke bukatar mu yi amfani da shi?

11 Takobin ruhu shi ne Kalmar Allah, wato Littafi Mai Tsarki. Wannan takobin yana da ikon fallasa ƙarya da kuma ’yantar da mutane daga koyarwar ƙarya da kuma halayen banza. (2 Kor. 10:​4, 5; 2 Tim. 3:​16, 17; Ibran. 4:12) Nazarin da muke yi da kuma horarwa da ƙungiyar Allah take mana suna sa mu san yadda ake yin amfani da wannan takobin. (2 Tim. 2:15) Ban da kayan kāriyar nan, akwai wani abu kuma da Jehobah yake kāre mu da shi. Me ke nan?

Takobi: Kalmar Allah, wato Littafi Mai Tsarki

JEHOBAH YANA BA MU ƘARIN TAIMAKO

12. Wane abu ne kuma muke bukata, kuma me ya sa?

12 Sojan da ya ƙware ya san cewa ba zai iya yin yaƙi shi kaɗai ba, amma yana bukatar taimakon wasu sojoji. Hakazalika, ba za mu iya yin nasara a kan Shaiɗan mu kaɗai ba, muna bukatar taimakon ’yan’uwanmu. Jehobah ya tanadar mana da “ ’yan’uwa” a faɗin duniya da za su iya taimaka mana.​—1 Bit. 2:17.

13. Kamar yadda Ibraniyawa 10:​24, 25 suka nuna, ta yaya za ka amfana daga halartan taro?

13 Hanya ɗaya da muke samun taimako ita ce ta wajen halartan taro. (Karanta Ibraniyawa 10:​24, 25.) Dukanmu muna yin sanyin gwiwa a wasu lokuta, amma idan hakan ya faru, halartan taro zai ƙarfafa mu. Kalamin da ’yan’uwanmu suka yi da zuciya ɗaya yana ƙarfafa mu. Jawabai da kuma gwajin da suke yi suna ƙarfafa mu mu ci gaba da bauta wa Jehobah. Tattaunawa da ’yan’uwa kafin a soma taro da kuma bayan hakan yana ƙarfafa mu. (1 Tas. 5:14) Ƙari ga haka, taronmu na ba mu zarafin taimaka wa mutane, kuma hakan yana sa mu farin ciki. (A. M. 20:35; Rom. 1:​11, 12) Taronmu na taimaka mana a wasu hanyoyi ma. Suna sa mu ƙware a wa’azi da koyarwa. Alal misali, muna koyan yadda ake amfani da Kayan Aiki don Koyarwa da kyau. Saboda haka, ka yi shiri da kyau kafin ka halarci taro, kuma ka saurara da kyau a taro. Bayan taron, ka yi amfani da abin da ka koya. Ta wajen yin waɗannan abubuwa, za ka zama “soja mai aminci na Almasihu Yesu.”​—2 Tim. 2:3.

14. Waɗanne ƙarin taimako ne muke da shi?

14 Miliyoyin mala’iku suna goyon bayan mu. Ka yi tunanin abin da mala’ika guda zai iya yi! (Isha. 37:36) Yanzu, ka yi tunanin abin da rundunar mala’iku za su iya cim ma. Babu ɗan Adam ko aljani da yake da iko kamar rundunar Jehobah. Idan Jehobah yana tare da mu, babu abin da masu tsananta mana za su iya yi mana ko da su nawa ne domin Jehobah ya fi su iko. (Alƙa. 6:16) A duk lokacin da ka yi sanyin gwiwa don abin da abokin aikinka ko abokin makarantarku ko kuma danginka suka ce ko kuma suka yi, ka tuna cewa Jehobah da rundunarsa suna tare da kai.

JEHOBAH ZAI CI GABA DA KĀRE MU

15. Kamar yadda aka nuna a Ishaya 54:​15, 17, me ya sa mutanen Allah ba za su taɓa daina yin wa’azi ba?

15 Akwai dalilai da yawa da suka sa mutanen duniya suka tsane mu. Ba ma taɓa saka hannu a siyasa kuma ba ma yin yaƙi. Muna shelar sunan Allah da wa’azi cewa Mulkinsa ne kaɗai zai kawo zaman lafiya kuma muna biyayya da ƙa’idodinsa. Muna gaya wa mutane cewa mai sarautar wannan duniya mugun maƙaryaci ne da mai kisan kai. (Yoh. 8:44) Kuma muna sanar cewa nan ba da daɗewa ba, za a halaka wannan duniyar. Shaiɗan da mabiyansa ba za su taɓa sa mu daina yin wa’azi ba. Maimakon haka, za mu ci gaba da yabon Jehobah iya gwargwadonmu! Ko da yake Shaiɗan yana da iko, ya kasa hana mu yin wa’azi a faɗin duniya. Hakan ya yiwu ne domin Jehobah yana kāre mu.​—Karanta Ishaya 54:​15, 17.

16. Ta yaya Jehobah zai ceci mutanensa a lokacin ƙunci mai girma?

16 Mene ne zai faru a nan gaba? A lokacin ƙunci mai girma, Jehobah zai cece mu a hanyoyi biyu masu ban mamaki. Na farko, zai ceci bayinsa masu aminci a lokacin da zai sa sarakunan duniya su halaka Babila Babba, wato daular addinan ƙarya. (R. Yar. 17:​16-18; 18:​2, 4) Bayan haka, zai ceci mutanensa a lokacin da ya halaka sauran magoyan bayan Shaiɗan a Armageddon.​—R. Yar. 7:​9, 10; 16:​14, 16.

17. Ta yaya za mu amfana idan muka kusaci Jehobah?

17 Idan muka kusaci Jehobah, Shaiɗan ba zai yi mana abin da zai jawo mana lahani na dindindin ba. Shaiɗan ne za a halaka har abada. (Rom. 16:20) Saboda haka, ka saka kayan kāriya kuma ka ci gaba da amfani da su! Kada ka yaƙi Shaiɗan da mutanensa kai kaɗai. Ka taimaka wa ’yan’uwanka, kuma ka bi umurnin Jehobah. Idan ka yi hakan, Ubanmu da ke sama zai ƙarfafa ka kuma zai kāre ka.​—Isha. 41:10.

WAƘA TA 149 Waƙar Nasara

^ sakin layi na 5 Jehobah ya yi alkawari a cikin Kalmarsa cewa zai ƙarfafa mu, kuma zai kāre mu daga kowane abu da zai iya ɓata dangantakarmu da shi da kuma jawo mana lahani na dindindin. Za mu amsa tambayoyin nan a wannan talifin: Me ya sa muke bukatar Jehobah ya kāre mu? Ta yaya Jehobah yake kāre mu? Me ya wajaba mu yi don Jehobah ya kāre mu?