Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 9

Ta Yaya Matasa Za Su Sa A Rika Daraja Su?

Ta Yaya Matasa Za Su Sa A Rika Daraja Su?

“Ya Allah, tun ina ƙarami, ka koya mini ayyukanka na ban mamaki, har wa yau kuma ina shelarsu.”​—ZAB. 71:17.

WAƘA TA 39 Mu Yi Suna Mai Kyau a Wurin Allah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne matasa suke da shi?

’YAN’UWA maza matasa, kuna da ayyuka da yawa da za ku iya yi a ikilisiya. Da yawa cikinku kuna da kuzari sosai. (K. Mag. 20:29) Kuna yin ayyuka da yawa don ku taimaka wa ’yan’uwa a ikilisiya. Mai yiwuwa kuna so ku zama bayi masu hidima. Amma wataƙila kuna tunanin cewa wasu sun raina ku kuma suna ganin cewa ba ku cancanci a ba ku ƙarin aiki ba. Duk da cewa ku matasa ne, da akwai abubuwa da yawa da za ku iya yi don ku sa ’yan’uwa a ikilisiya su riƙa daraja ku.

2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 A wannan talifin, za mu tattauna game da Sarki Dauda. Ƙari ga haka, za mu ɗan tattauna game da Asa da kuma Jehoshaphat sarakunan Yahudiya. Za mu tattauna ƙalubalen da waɗannan maza uku suka fuskanta da matakan da suka ɗauka da kuma abin da ’yan’uwa maza matasa za su koya.

KU YI KOYI DA SARKI DAUDA

3. A wace hanya ce ’yan’uwa maza matasa za su iya taimaka wa tsofaffi a ikilisiya?

3 A lokacin da Dauda yake matashi, ya koyi abubuwa masu kyau. Ya yi aiki tuƙuru don ya zama ƙwararren mawaƙi, kuma ya yi amfani da ƙwarewarsa don ya taimaka wa Sarki Saul wanda Allah ya naɗa. (1 Sam. 16:​16, 23) Kuna da baiwar da za ku iya yin amfani da ita don ku taimaka wa ’yan’uwa a ikilisiya? Da yawa cikinku kuna da ita. Alal misali, tsofaffi da yawa suna farin ciki idan aka koya musu yadda za su yi amfani da waya ko kuma na’ura don taro da nazari. Za ku iya taimaka wa waɗannan tsofaffi domin kun iya amfani da na’urori sosai.

Dauda ya kula da tumakin mahaifinsa sosai, kuma ya kāre su daga wani dabbar beyar da ke so ya cinye su (Ka duba sakin layi na 4)

4. Kamar Dauda, waɗanne halaye ne ya kamata ’yan’uwa maza matasa su kasance da su? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

4 Dauda ya nuna cewa shi mutum ne da za a iya amincewa da shi. Alal misali, sa’ad da yake matashi, ya kula da tumakin mahaifinsa kuma wannan aiki ne mai wuya sosai. Daga baya, Dauda ya gaya wa Sarki Saul cewa: “Ranka ya daɗe! Ina lura da tumakin babana. Duk sa’ad da zaki ko beyar ya kama tunkiya daga garke, nakan bi shi in fāɗa masa in ƙwace tunkiyar daga bakinsa.” (1 Sam. 17:​34, 35) Dauda ya san cewa yana bukatar ya kula da tumakin. Saboda haka, ya yi faɗa da ƙarfin zuciya don ya kāre su. ’Yan’uwa matasa suna iya yin koyi da Dauda ta wajen yin ayyukan da aka ba su da kyau.

5. Kamar yadda Zabura 25:14 ta nuna, wane abu mafi muhimmanci ne ya kamata matasa su yi?

5 Dauda ya ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah. A gare shi, dangantakarsa da Jehobah ta fi nuna ƙarfin zuciya da kuma kaɗa molo muhimmanci. Jehobah Allahn Dauda ne da kuma abokinsa na kud da kud. (Karanta Zabura 25:14.) ’Yan’uwa maza matasa, abu mafi muhimmanci da za ku yi shi ne ƙarfafa dangantakarku da Ubanku na sama. Yin hakan zai sa ku sami ƙarin ayyuka a ikilisiya.

6. Yaya wasu mutane suka ɗauki Dauda?

6 Wasu sun raina Dauda kuma wannan wata matsala ce da ya fuskanta. Alal misali, sa’ad da ya ce zai yaƙi Goliath, Sarki Saul ya so ya hana shi, ya ce: “Kai ɗan saurayi ne.” (1 Sam. 17:​31-33) Kafin wannan lokacin, ɗan’uwan Dauda ya ce shi marar hankali ne. (1 Sam. 17:​26-30) Amma Jehobah bai ɗauki Dauda a matsayin ƙaramin yaro da bai manyanta ba, ya san Dauda sosai. Dauda ya dogara ga Jehobah, kuma hakan ya taimaka masa ya kashe Goliath.​—1 Sam. 17:​45, 48-51.

7. Mene ne ka koya daga wani labari game da Dauda?

7 Mene ne ka koya daga abin da ya faru da Dauda? Mun koyi cewa muna bukatar mu zama masu haƙuri. Zai ɗauki lokaci kafin waɗanda suka san ka a lokacin da kake yaro su fahimci cewa ka girma. Amma ka kasance da tabbaci cewa Jehobah, ba ya mai da hankali ga siffarka. Ya san ka sosai da kuma abin da za ka iya yi. (1 Sam. 16:7) Wani darasi kuma daga labarin Dauda shi ne cewa kana bukatar ka ƙarfafa dangantakarka da Allah. Dauda ya yi hakan ta wajen lura da halittun Jehobah. Ya yi tunani sosai a kan abin da waɗannan halittun suka koya masa game da Mahaliccinmu. (Zab. 8:​3, 4; 139:14; Rom. 1:20) Wani abu kuma da za ka iya yi shi ne ka roƙi Jehobah ya ba ka ƙarfi. Alal misali, wasu cikin abokan makarantarku suna maka dariya domin kai Mashaidin Jehobah ne? Idan haka ne, ka roƙe Jehobah ya taimaka maka ka jimre da wannan matsalar. Kuma ka bi shawarwari masu kyau da ke cikin Kalmarsa da littattafanmu da kuma bidiyoyi. A duk lokacin da ka ga cewa Jehobah ya taimaka maka ka jimre matsala, bangaskiyarka za ta daɗa ƙarfi. Idan mutane suka ga cewa kana dogara ga Jehobah, za su soma daraja ka.

Matasa suna iya taimaka wa mutane a hanyoyi da yawa (Ka duba sakin layi na 8-9)

8-9. Mene ne ya taimaka wa Dauda ya jira har lokacin da zai soma sarauta, kuma mene ne matasa za su iya koya daga misalinsa?

8 Ka yi la’akari da wani ƙalubale da Dauda ya fuskanta. Bayan an zaɓe shi ya zama sarki, ya jira shekaru da yawa kafin ya soma sarauta a Yahudiya. (1 Sam. 16:13; 2 Sam. 2:​3, 4) Mene ne ya taimaka masa ya iya jimrewa? Maimakon ya yi sanyin gwiwa, ya mai da hankali ga abubuwa da zai iya yi. Alal misali, sa’ad da Dauda yake ɓoyewa a yankin Filistiyawa, ya yi amfani da wannan zarafin don ya yaƙi maƙiyan Isra’ilawa. Ta yin hakan, ya kāre iyakokin ƙasar Yahudiya.​—1 Sam. 27:​1-12.

9 Mene ne ’yan’uwa matasa za su iya koya daga misalin Dauda? Ku yi amfani da zarafin da kuke da shi don ku yi wa Jehobah da ’yan’uwanku hidima. Ka yi la’akari da labarin wani ɗan’uwa mai suna Ricardo. * A lokacin da yake wajen ɗan shekara 10, ya so ya zama majagaba na kullum. Amma dattawa sun gaya masa cewa ya ɗan jira. Maimakon Ricardo ya yi sanyin gwiwa ko kuma fushi, ya daɗa ƙwazo a hidimarsa. Ya ce: “Sa’ad da na tuna abin da ya faru a lokacin, na fahimci cewa na bukaci in yi wasu canje-canje a rayuwata. Na mai da hankali ga koma ziyara da kuma yin shiri kafin in je. Kuma na gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki a lokaci na farko. Yayin da na ci gaba da yin wa’azi, hakan ya sa na daina jin tsoro.” Yanzu Ricardo majagaba ne da ya ƙware kuma shi bawa mai hidima ne.

10. Mene ne Dauda ya yi a wani lokaci kafin ya yanke shawara mai muhimmanci?

10 Ka yi la’akari da wani abu kuma da ya faru da Dauda. A lokacin da yake ɓuya a yankin Filistiyawa, shi da sojojinsa sun bar iyalansu don su je yaƙi. Sai maƙiya suka kai wa iyalan hari kuma suka kwashe dukansu. Dauda bai yi tunanin cewa shi jarumi ne kuma zai ƙwato mutanen ba. Maimakon haka, ya nemi taimakon Jehobah. Wani firist mai suna Abiathar ya kawo wa Dauda efod don ya tuntuɓi Jehobah cewa: “In bi waɗannan da suka kawo mana hari?” Jehobah ya gaya wa Dauda ya bi su, kuma ya tabbatar masa cewa zai yi nasara. (1 Sam. 30:​7-10) Wane darasi ne ka koya daga wannan labarin?

Ya kamata matasa su nemi shawara daga wurin dattawa (Ka duba sakin layi na 11)

11. Mene ne za ka iya yi kafin ka yanke shawara?

11 Ka nemi taimako kafin ka tsai da shawarwari. Ka nemi taimakon iyayenka. Za ka iya samun shawara mai kyau ta wajen tattaunawa da dattawan da suka manyanta. Jehobah ya amince da su, kai ma kana iya yin hakan. Jehobah yana ɗaukansu a matsayin “baiwa” ga ikilisiya. (Afis. 4:8) Za ka amfana idan ka yi koyi da bangaskiyarsu kuma ka yi amfani da shawarwari masu kyau da suka ba ka. Yanzu bari mu ga abin da za mu iya koya daga labarin Sarki Asa.

KU KOYI DARASI DAGA SARKI ASA

12. Waɗanne halaye ne Asa yake da su sa’ad da ya soma sarauta?

12 A lokacin da Sarki Asa yake matashi, shi mai tawali’u ne da ƙarfin zuciya. Alal misali, bayan mahaifinsa Abijah ya mutu, Asa ya zama sarki kuma ya soma kawar da gumaka daga ƙasar. Ban da haka, “ya umarci mutanen yankin Yahuda su nemi Yahweh Allahn kakanninsu, su kuma yi biyayya ga Koyarwarsa da umarnansa.” (2 Tar. 14:​1-7) Sa’ad da Zerah, Bahabashe ya kai wa Yahuda hari da sojoji guda 1,000,000, Asa ya nemi taimakon Jehobah kuma ya ce: “Ya Yahweh, babu mai taimako kamarka, wanda zai taimaki marar ƙarfi a kan masu ƙarfi. Ka taimake mu, ya Yahweh Allahnmu, gama muna dogara a gare ka!” Wannan furucin ya nuna cewa Asa yana da tabbaci cewa Jehobah zai cece shi da mutanensa. Asa ya dogara ga Ubansa na sama, “Yahweh kuwa ya halaka sojojin Itiyofiya.”​—2 Tar. 14:​8-12.

13. Mene ne ya faru da Asa daga baya, kuma me ya sa?

13 Babu shakka, yin yaƙi da sojoji 1,000,000 yana da ban tsoro, amma domin Asa ya dogara ga Jehobah, ya yi nasara. Sa’ad da Asa ya fuskanci wata matsala dabam, bai dogara ga Jehobah ba. A lokacin da mugun Sarki Ba’asha na Isra’ila ya yi wa Asa barazana, Asa ya nemi taimakon sarkin Suriya. Wannan shawarar ta jawo mugun sakamako. Jehobah ya tura annabi Hanani ya gaya wa Asa cewa: “Tun da yake ka dogara a kan Suriya maimakon ka dogara a kan Yahweh Allahnka, to, sojojin Suriya sun kuɓuta daga hannunka.” Tun daga wannan lokaci, Asa yana yin yaƙi a kowane lokaci. (2 Tar. 16:​7, 9; 1 Sar. 15:32) Wane darasi muka koya?

14. Me zai taimaka maka ka dogara ga Jehobah, kuma wane amfani ne za ka samu idan ka yi hakan kamar yadda 1 Timoti 4:12 ta nuna?

14 Ka zama mai tawali’u kuma ka ci gaba da dogara ga Jehobah. Sa’ad da ka yi baftisma, ka nuna cewa kana da bangaskiya kuma ka dogara ga Jehobah. Jehobah ya yi farin cikin sa ka kasance cikin ƙungiyarsa. Abin da kake bukatar ka yi yanzu shi ne ka ci gaba da dogara a gare shi. Yana da sauƙi ka dogara ga Jehobah sa’ad da kake so ka yanke shawarwari masu muhimmanci. Amma idan kana so ka yanke shawarwari game da nishaɗi da aiki da dai sauransu kuma fa? Yana da muhimmanci ka dogara ga Jehobah a wannan lokacin ma! Kada ka dogara ga hikimarka. Maimakon haka, ka nemi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka maka kuma ka yi amfani da su. (K. Mag. 3:​5, 6) Idan ka yi hakan, za ka faranta wa Jehobah rai kuma ’yan’uwa a ikilisiya za su daraja ka.​—Karanta 1 Timoti 4:12.

KU KOYI DARASI DAGA SARKI JEHOSHAPHAT

15. Kamar yadda 2 Tarihi 18:​1-3 da 19:2 suka nuna, wace shawara marar kyau ce Jehoshaphat ya yanke?

15 Babu shakka, dukanmu ajizai ne kuma muna yin kuskure. Amma kada ka bar hakan ya hana ka yin iya ƙoƙarinka a hidimar Jehobah. Ka yi la’akari da labarin Sarki Jehoshaphat. Yana da halaye masu kyau. Daga lokacin da ya soma sarauta, “ya nemi Yahweh Allahn babansa, ya bi umurnansa.” Ban da haka, ya aika hakimansa zuwa biranen Yahudiya don su koyar da mutane game da Jehobah. (2 Tar. 17:​4, 7) Ko da yake Jehoshaphat mutumin kirki ne, a wasu lokuta ya tsai da shawarwarin da ba su dace ba. Akwai lokacin da Jehoshaphat ya yanke shawara da ba ta dace ba, sai Jehobah ya tura annabinsa ya yi masa gargaɗi. (Karanta 2 Tarihi 18:​1-3; 19:2.) Wane darasi ne za mu iya koya daga labarin?

’Yan’uwa suna daraja matasa da suke da ƙwazo da kuma aminci (Ka duba sakin layi na 16)

16. Mene ne ka koya daga labarin Rajeev?

16 Ka bi shawarar da aka ba ka. Wataƙila kamar matasa da yawa, yana yi maka wuya ka sa bautar Jehobah ta zama abu mafi muhimmanci a rayuwarka. Kada ka yi sanyin gwiwa. Ka yi la’akari da labarin wani ɗan’uwa matashi mai suna Rajeev. Sa’ad da yake magana game da lokacin da yake girma, ya ce: “A wasu lokuta, ban san abin da zan yi da rayuwata ba. Ina kamar sauran matasa domin na fi son wasanni da jin daɗin rayuwa fiye da halartan taro da kuma yin wa’azi.” Mene ne ya taimaka wa Rajeev? Wani dattijo mai kirki ya ba shi shawara. Rajeev ya ce: “Dattijon ya taimaka mini in yi tunani a kan ƙa’idar da ke 1 Timoti 4:8.” Rajeev ya bi shawarar kuma ya yi tunani a kan abubuwan da suka fi muhimmanci a rayuwarsa. Ya ce: “Na tsai da shawarar mai da hankali ga ibadata ga Jehobah.” Mene ne sakamakon yin hakan? Rajeev ya ce: “ ’Yan shekaru bayan dattijon ya ba ni shawara, sai aka naɗa ni bawa mai hidima.”

KA SA JEHOBAH YA YI ALFAHARI DA KAI

17. Yaya ’yan’uwan da suka manyanta suke ɗaukan matasa da suke bauta wa Jehobah?

17 ’Yan’uwa maza da mata a ikilisiya suna daraja ku matasa da kuke bauta wa Jehobah tare da su “da zuciya ɗaya”! (Zaf. 3:9) Suna son yadda kuke sa ƙwazo a aikin da aka ba ku. Suna ƙaunar ku sosai.​—1 Yoh. 2:14.

18. Kamar yadda Karin Magana 27:11 ta nuna, yaya Jehobah yake ji game da matasa da suke bauta masa?

18 ’Yan’uwa maza matasa, ku tuna cewa Jehobah yana ƙaunar ku kuma ya amince da ku. Ya annabta cewa a kwanaki na ƙarshe, matasa da yawa za su ba da kansu da yardar rai. (Zab. 110:​1-3) Jehobah ya san cewa kana ƙaunar shi kuma kana so ka yi iya ƙoƙarinka a hidimarsa. Ka riƙa yin haƙuri da kanka da kuma ’yan’uwanka. Sa’ad da ka yi kuskure, ka amince da horon da aka yi maka kuma ka tuna cewa Jehobah ne yake yi maka horon. (Ibran. 12:6) Ka yi iya ƙoƙarinka a hidimar da aka ba ka. Kuma abu mafi muhimmanci, ka sa Ubanka da ke sama ya yi alfahari da kai.​—Karanta Karin Magana 27:11.

WAƘA TA 135 Jehobah Ya Ce: “Ɗana Ka Yi Hikima”

^ sakin layi na 5 Yayin da ’yan’uwa maza matasa suke manyanta, za su so su ƙara ƙwazo a hidimarsu ga Jehobah. Don su cancanci zama bayi masu hidima, suna bukatar ’yan’uwa a ikilisiya su riƙa daraja su. Mene ne za su yi don a riƙa daraja su?

^ sakin layi na 9 An canja wasu sunaye.