Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 10

Yadda Kowa a Ikilisiya Zai Taimaki Dalibi Ya Yi Baftisma

Yadda Kowa a Ikilisiya Zai Taimaki Dalibi Ya Yi Baftisma

“Kowace gaɓa . . . tana ƙara girmar” jiki.​—AFIS. 4:16.

WAƘA TA 85 Mu Riƙa Marabtar Juna

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Wane ne zai iya taimaka wa ɗalibi ya cancanci yin baftisma?

WATA mai suna Amy da ke zama a tsibirin Fiji ta ce: “Ina son abin da nake koya daga Littafi Mai Tsarki sosai. Na san cewa gaskiya ne. Amma sai da na soma yin cuɗanya da ’yan’uwa ne na soma yin canje-canje a rayuwata kuma na yi baftisma.” Labarin Amy ya koya mana wannan darasi mai muhimmanci: Ɗalibi zai sami ci gaba sosai kuma ya yi baftisma idan ’yan’uwa a ikilisiya suka taimaka masa.

2 Kowane mai shela zai iya taimaka wa sababbi su sami ci gaba a ikilisiya. (Afis. 4:16) Wata majagaba mai suna Leilani a tsibirin Vanuatu ta ce: “Masu magana sun ce, hannu ɗaya ba ya ɗaukan jinka. Haka ma yake da taimaka wa mutane su zama almajiran Yesu. Kowa a ikilisiya ne zai taimaka wa ɗalibi ya soma bauta wa Jehobah.” Membobin iyali da abokai da malamai suna taimaka wa yaro ya manyanta. Suna yin hakan ta wajen ƙarfafa yaron da kuma koya masa darussa masu kyau. Hakazalika, ’yan’uwa a ikilisiya za su iya ƙarfafa ɗalibi kuma su kafa masa misali mai kyau don ya cancanci yin baftisma.​—K. Mag. 15:22.

3. Wane darasi ne ka koya daga furucin Ana da Dorin da kuma Leilani?

3 Me ya sa ya kamata mai shela da ke gudanar da nazari ya nemi taimakon wasu ’yan’uwa? Ku lura da abin da wata majagaba ta musamman mai suna Ana a ƙasar Moldova ta ce, “A lokacin da ɗalibi ya soma samun ci gaba, yana bukatar taimako sosai, kuma ɗan’uwan da ke nazari da shi kaɗai ba zai iya taimaka masa ba.” Wani majagaba na musamman mai suna Dorin wanda shi ma yake Moldova ya ce, “A yawancin lokuta, masu shela suna faɗin abu da ya ratsa zuciyar ɗalibin, kuma abu ne da ban taɓa yin tunani a kai ba.” Leilani ta ambata wani dalili, ta ce, “Idan ’yan’uwa suka nuna wa ɗalibin ƙauna, zai taimaka masa ya san cewa yana tsakanin mutanen Jehobah.”​—Yoh. 13:35.

4. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

4 Amma za ka iya yin tunani cewa, ‘Ta yaya zan iya taimaka wa ɗalibi ya sami ci gaba da yake ba ni nake yin nazari da shi ba?’ Bari mu tattauna abin da za mu iya yi sa’ad da muka raka wani don ya gudanar da nazari da ɗalibinsa da kuma abin da za mu iya yi sa’ad da ya soma halartan taro. Za mu kuma tattauna yadda dattawa za su iya taimaka wa ɗalibi ya cancanci yin baftisma.

SA’AD DA KA RAKA WANI GUDANAR DA NAZARI

Sa’ad da za ka raka wani gudanar da nazari, ka shirya darasin da za a tattauna (Ka duba sakin layi na 5-7)

5. Me ya kamata ka yi sa’ad da ka raka wani gudanar da nazari?

5 Sa’ad da ake nazarin Littafi Mai Tsarki da ɗalibi, malamin ne yake da hakkin taimaka masa ya fahimci Kalmar Allah. Idan malamin ya ce ka raka shi yin nazari, ka san cewa kai abokin wa’azi ne kuma kana bukatar ka taimaka masa. (M. Wa. 4:​9, 10) Mene ne za ka iya yi don ka taimaka sa’ad da ake nazarin?

6. Sa’ad da za ka raka wani yin nazari, ta yaya za ka bi ƙa’idar da ke Karin Magana 20:18?

6 Ka yi shiri kafin a gudanar da nazarin. Da farko, ka ce wa malamin ya gaya maka wasu abubuwa game da ɗalibin. (Karanta Karin Magana 20:18.) Kana iya tambaya: “Me ka sani game da ɗalibin? Wane batu ne za ku tattauna? Me kake so ɗalibin ya koya? Akwai wani abu da ba ka so in yi ko kuma in faɗa a gaban ɗalibin? Ta yaya zan ƙarfafa ɗalibin ya sami ci gaba?” Ba zai dace malamin ya gaya maka batun sirri game da ɗalibin ba, amma ya gaya maka abin da zai taimaka wa ɗalibin. Wata mai wa’azi a ƙasar waje mai suna Joy tana yawan tattauna batutuwan nan da ’yan’uwa da suka raka ta yin nazari. Ta ce: “Bayanan nan suna taimaka wa abokin wa’azina ya so ya taimaka wa ɗalibin kuma ya san abin da ya kamata ya faɗa.”

7. Me ya sa ya kamata ka yi shiri kafin ka raka wani gudanar da nazari?

7 Idan za ka raka wani gudanar da nazari, zai dace ka shirya darasin da za ku tattauna. (Ezra 7:10) Ɗan’uwa Dorin da muka ambata ɗazu ya ce: “Ina farin ciki idan ’yan’uwan da suka raka ni yin nazari suka shirya darasin. Hakan yana sa su yi kalamin da zai amfani ɗalibin.” Ƙari ga haka, ɗalibin zai lura cewa ku biyu kun shirya sosai, kuma hakan zai zama misali mai kyau a gare shi. Ko da ba za ka iya shirya darasin sosai ba, zai dace ka ɗauki ɗan lokaci don ka san muhimman darussan.

8. Me za ka yi don addu’ar da za ka yi ta amfani ɗalibin?

8 Addu’a ma abu ne mai muhimmanci a nazari. Saboda haka, ka shirya abin da za ka faɗa sa’ad da aka ce ka yi addu’a. Idan ka yi hakan, addu’arka za ta fi taimaka wa ɗalibin. (Zab. 141:2) Wata mai suna Hanae a ƙasar Jafan ta ce har yau, tana tunawa da addu’ar da wata ’yar’uwa da ta raka malamarta yin nazari da ita ta yi. Ta ce: “Na lura cewa tana da dangantaka mai kyau da Jehobah kuma na so in yi koyi da ita. Kuma sa’ad da ta ambata sunana a addu’ar na ga cewa tana ƙauna ta.”

9. Kamar yadda Yakub 1:19 ta nuna, me za ka iya yi don ka taimaka sa’ad da ake nazari da ɗalibi?

9 Ka taimaka wa malamin sa’ad da yake nazarin. Wata majagaba ta musamman a Nijeriya mai suna Omamuyovbi ta ce: “Abokin wa’azi mai ban-taimako yana saurarawa da kyau. Yana yin kalami, amma ba ya wuce gona da iri domin ya san cewa malamin ne ke ja-goranci.” Ta yaya za ka san lokacin da ya dace ka yi magana kuma me za ka ce? (K. Mag. 25:11) Ka saurara sosai yayin da malamin da ɗalibin suke tattaunawa. (Karanta Yakub 1:19.) Hakan zai sa ka iya taimaka sa’ad da bukata ta taso. Babu shakka, ya kamata ka yi tunani kafin ka yi magana. Alal misali, ba zai dace ka riƙa dogon jawabi ba ko ka katse wa malamin magana ko kuma ka ta da wani batu dabam ba. Amma za ka iya yin gajeren bayani ko kwatanci ko tambaya da za ta taimaka wa ɗalibin ya fahimci nazarin. A wasu lokuta, za ka iya ganin cewa ba ka da ƙarin bayani. Amma za ka iya yaba wa ɗalibin, ka nuna cewa ka damu da shi, kuma hakan zai taimaka masa ya sami ci gaba.

10. Ta yaya labarinka zai iya taimaka wa ɗalibi?

10 Ka faɗi labarinka. Idan zai dace, ka ɗan gaya wa ɗalibin yadda ka soma bauta wa Jehobah, yadda ka magance wani ƙalubale ko kuma yadda Jehobah ya taimaka maka. (Zab. 78:​4, 7) Labarinka zai iya taimaka wa ɗalibin. Zai iya ƙarfafa bangaskiyarsa ko kuma ya sa ya sami ci gaba har ya yi baftisma. Kuma zai iya taimaka masa ya magance jarrabawar da yake fuskanta. (1 Bit. 5:9) Wani mai suna Gabriel da ke zama a ƙasar Brazil kuma yana hidimar majagaba yanzu ya tuna abin da ya taimaka masa sa’ad da ake nazari da shi. Ya ce: “Sa’ad da na ji labarin ɗan’uwan, na ga cewa Jehobah ya san da ƙalubalen da muke fuskanta. Kuma idan ɗan’uwan ya magance su, to ni ma zan iya.”

SA’AD DA ƊALIBIN YA HALARCI TARO

Dukanmu za mu iya ƙarfafa ɗalibi ya ci gaba da halartan taro (Ka duba sakin layi na 11)

11-12. Me ya sa ya kamata mu marabci ɗalibin da ya halarci taro?

11 Idan ɗalibi yana so ya cancanci yin baftisma, wajibi ne ya riƙa halartan taro a kai a kai kuma ya amfana daga taron. (Ibran. 10:​24, 25) Mai yiwuwa, malamin zai gayyace shi zuwa taro a ƙaro na farko. Sa’ad da ya halarci taron, dukanmu za mu iya ƙarfafa shi ya ci gaba da halarta. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya yin hakan?

12 Ku marabci ɗalibin sosai. (Rom. 15:7) Idan mun marabci ɗalibin sosai, hakan zai sa ya sake halartan taron. Kada ku yi abin da zai sa ya ƙi sake jiki, a maimakon haka, ku gaishe shi kuma ku sa ya haɗu da sauran ’yan’uwa a ikilisiyar. Ku tattauna da shi domin wataƙila malaminsa bai zo taro ba tukun kuma wataƙila yana yin wasu ayyuka a majami’ar. Ku saurari abin da ɗalibin ya faɗa kuma ku nuna cewa kun damu da shi. Ta yaya hakan zai iya taimaka wa ɗalibin? Ku yi la’akari da labarin wani mai suna Dmitrii da bai daɗe da yin baftisma ba kuma shi bawa mai hidima ne a yau. Sa’ad da ya tuna abin da ya faru a taro na farko da ya halarta, ya ce: “Wani ɗan’uwa ya gan ni tsaye a waje, ina jin tsoron shigowa majami’ar. Sai ya raka ni ciki. Mutane da yawa sun zo sun gaishe ne. Hakan ya sa ni mamaki sosai. Na yi farin ciki ƙwarai, har na so a riƙa taro kowace rana. Na shaida abin da ban taɓa shaidawa ba a wani wuri.”

13. Ta yaya halinmu mai kyau zai iya shafar ɗalibi?

13 Ku kafa misali mai kyau. Halinku zai taimaka wa ɗalibin ya tabbata cewa mu Kiristoci ne na gaskiya. (Mat. 5:16) Wani mai suna Vitalii wanda shi majagaba ne a Moldova ya ce: “Na lura da halayen ’yan’uwa a ikilisiya da yadda suke tunani da kuma yadda suke rayuwa. Hakan ya tabbatar min da cewa Shaidun Jehobah mutanen Allah ne.”

14. Ta yaya halinmu zai iya taimaka wa ɗalibi ya sami ci gaba?

14 Ɗalibin yana bukatar ya riƙa yin abubuwan da yake koya don ya cancanci yin baftisma. Yin hakan bai da sauƙi. Amma idan ɗalibin ya lura da yadda bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki take amfanar ku, hakan zai iya motsa shi ya yi koyi da ku. (1 Kor. 11:1) Ku yi la’akari da labarin Hanae da muka ambata ɗazu. Ta ce: “’Yan’uwa maza da mata suna yin abubuwan da nake koya. Na koyi yadda zan riƙa ƙarfafa mutane, in riƙa gafartawa kuma in riƙa nuna ƙauna. ’Yan’uwan ba sa yin baƙar magana game da mutane. Na so in zama kamar su.”

15. Ta yaya Karin Magana 27:17 za ta iya shafan dangantakarmu da ɗalibanmu?

15 Ku zama abokan ɗalibin. Yayin da ɗalibin ya ci gaba da halartan taro, ku riƙa nuna masa cewa kun damu da shi. (Filib. 2:4) Zai dace ku yi ƙoƙari don ku san shi da kyau. Kuna iya yaba masa don ci gaba da yake samu. Za ku kuma iya yi masa tambaya game da nazarinsa da iyalinsa da aikinsa. Amma ku yi hankali don kada ku yi maganar da za ta kunyatar da shi. Tattaunawar nan za ta iya sa ku zama abokai. Idan kun zama abokan ɗalibin, za ku taimaka masa ya cancanci yin baftisma. (Karanta Karin Magana 27:17.) A yanzu, Hanae majagaba ce ta kullum. Ta tuna rana ta farko da ta halarci taro. Ta ce: “A lokacin da na sami abokai a ikilisiya, na soma marmarin halartan taro har a ranar da na gaji. Na ji daɗin yin cuɗanya da su kuma hakan ya taimaka mini in daina tarayya da mutanen da ba sa bauta wa Jehobah. Na so in kusaci Jehobah da kuma ’yan’uwa. Haka ya sa na yi baftisma.”

16. Me kuma za ku iya yi don ku taimaka wa ɗalibi ya yi farin ciki a ikilisiya?

16 Yayin da ɗalibin ya ci gaba da yin canje-canje a rayuwarsa, ku taimaka masa ya san cewa yana da daraja a ikilisiya. Za ku iya yin hakan ta wajen nuna masa karimci. (Ibran. 13:2) Denis da ke hidima a Moldova ya tuna lokacin da ake nazari da shi. Ya ce: “’Yan’uwa sun gayyace ni da matata liyafa sau da yawa. Sun gaya mana yadda Jehobah ya taimaka musu kuma hakan ya ƙarfafa mu. Hakan ya tabbatar mana da cewa muna bukatar mu bauta wa Jehobah kuma za mu ji daɗin yin hakan.” Da zarar an yarda ɗalibin ya soma fita wa’azi, za ku iya yin shiri don ku fita wa’azi tare. Wani ɗan’uwa a Brazil mai suna Diego ya ce: “’Yan’uwa da yawa sun ce mu fita wa’azi tare. Hakan ya taimaka mini in san su sosai. Yin hakan ya taimaka mini in koyi abubuwa da dama kuma in kusaci Jehobah da Yesu.”

YADDA DATTAWA ZA SU IYA TAIMAKA

Dattawa, za ku taimaki ɗalibi ya sami ci gaba idan kun nuna cewa kun damu da su (Ka duba sakin layi na 17)

17. Ta yaya dattawa za su iya taimaka wa ɗalibai?

17 Ku riƙa kasancewa da ɗaliban. Dattawa, idan kuna nuna wa ɗalibai cewa kuna ƙaunar su kuma kun damu da su, za ku taimaka musu su cancanci yin baftisma. Ku riƙa tattaunawa da su a kai a kai a taro. Za su ga cewa kun damu da su idan kun kira su da sunansu, musamman sa’ad da suke so su yi kalami. Za ku iya keɓe lokaci don ku fita wa’azi tare da mai shela sa’ad da yake so ya gudanar da nazari? Hakan zai iya taimaka wa ɗalibin sosai fiye da yadda kake tsammani. Wata majagaba mai suna Jackie a Nijeriya ta ce: “Ɗalibai da yawa suna mamaki cewa ɗan’uwan da ya raka ni yin nazari da su dattijo ne. Wani ɗalibi ya ce: ‘Abin da fastonmu ba zai taɓa yi ke nan ba. Masu kuɗi ne kawai yake ziyarta idan suka biya shi!’” Wannan ɗalibin yana halartan taro yanzu.

18. Ta yaya dattawa za su yi aikin da aka ba su a Ayyukan Manzanni 20:28?

18 Ku horar da kuma ƙarfafa malamai. Dattawa, kuna da hakkin taimaka wa masu shela su ƙware a wa’azi, har da gudanar da nazari. (Karanta Ayyukan Manzanni 20:28.) Idan wani yana jin kunyar yin nazarin a gabanku, ku tambaye shi in yana so ku taya shi yin nazarin. Jackie da aka ambata ɗazun ta ce: “Dattawa suna yawan tambaya ta game da ɗalibaina. Sa’ad da na fuskanci ƙalubale a nazarin da nake yi, suna ba ni shawara mai kyau.” Dattawa za su iya taimaka wa masu shela da ke da ɗalibai don kada su gaji da ɗaliban. (1 Tas. 5:11) Jackie ta ƙara da cewa: “Ina farin ciki sa’ad da dattawa suka ƙarfafa ni kuma suka yaba mini don aikin da nake yi. Hakan na kwantar mini da hankali kamar na sha ruwan sanyi a lokacin zafi. Furucinsu yana sa ni farin ciki kuma yana sa in san cewa ina yin iya ƙoƙarina.”​—K. Mag. 25:25.

19. Me zai iya sa dukanmu farin ciki?

19 Ko da ba ma gudanar da nazari yanzu, za mu iya taimaka wa wani ya cancanci yin baftisma. Ba tare da yin dogon jawabi ba, za ka iya taimaka wa ɗalibin da kalamin da ka shirya sosai. Za mu iya zama abokan ɗaliban sa’ad da suka halarci taro kuma za mu iya kafa musu misali mai kyau. Dattawa kuma za su iya ƙarfafa su ta wajen keɓe lokaci don su kasance da su. Za su kuma iya ƙarfafa malaman ta wajen horar da su da kuma yaba musu. Za mu yi farin ciki idan muka taimaka wa ɗalibi ya ƙaunaci Jehobah kuma ya bauta masa.

WAƘA TA 79 Mu Koya Musu Su Kasance da Aminci

^ sakin layi na 5 Ba kowannenmu ba ne yake da ɗalibin da yake nazari da shi a yanzu ba. Amma, dukanmu za mu iya taimaka wa ɗalibai su cancanci yin baftisma. A wannan talifin, za mu ga yadda kowannenmu zai taimaka wa ɗalibi ya yi hakan.