TALIFIN NAZARI NA 11
Yadda Littafi Mai Tsarki Zai Sa Ka Jimre Matsaloli
“Allah [yana] ba da jimrewa.”—ROM. 15:5.
WAƘA TA 94 Muna Godiya Jehobah Don Kalmarka
ABIN DA ZA A TATTAUNA *
1. Waɗanne irin ƙalubale ne bayin Jehobah suke fuskanta?
KANA fuskantar wata matsala mai tsanani ne? Wataƙila wani ɗan’uwa a ikilisiya ya ɓata maka rai. (Yaƙ. 3:2) Ko kuma wataƙila abokan aikinka ko kuma abokan makarantarku suna yi maka ba’a domin kana bauta wa Jehobah. (1 Bit. 4:3, 4) Mai yiwuwa, ’yan iyalinku suna ƙoƙarin hana ka halartan taro da yin wa’azi. (Mat. 10:35, 36) Idan kana fuskantar matsaloli masu tsanani, hakan yana iya sa ka soma tunanin daina bauta wa Jehobah. Amma ka kasance da tabbaci cewa ko da wace irin matsala ce kake fuskanta, Jehobah zai ba ka hikimar tsai da shawarwarin da suka dace da kuma jimre matsalolin.
2. Kamar yadda Romawa 15:4 ta nuna, ta yaya karanta Kalmar Allah za ta taimaka mana?
2 Jehobah ya tabbata cewa an rubuta labaran mutane ajizai da suka jimre matsaloli masu wuya. Me ya sa? Domin mu koyi darasi. Shi ya sa Jehobah ya sa manzo Bulus ya rubuta abin da ke Romawa 15:4. (Karanta.) Karanta waɗannan nassosin za su ƙarfafa mu kuma su sa mu kasance da bege. Amma idan muna so mu amfana, ba karanta Littafi Mai Tsarki kaɗai muke bukatar mu yi ba. Muna bukatar mu bari Littafi Mai Tsarki ya canja ra’ayinmu da tunaninmu. Mene ne za mu yi idan muna neman shawara a kan yadda za mu magance wata matsala? Muna iya yin abubuwa huɗun nan: (1) Addu’a, (2) Tunani, (3) Bimbini da kuma (4) Yin abin da muka koya. Bari mu tattauna yadda za mu yi kowanne cikinsu. * Bayan haka, za mu yi amfani da wannan tsarin yin nazari don mu koyi darasi daga Sarki Dauda da kuma manzo Bulus.
3. Me ya kamata ka yi kafin ka soma karanta Littafi Mai Tsarki kuma me ya sa?
Filib. 4:6, 7; Yak. 1:5.
3 (1) Addu’a. Kafin ka soma karanta Littafi Mai Tsarki, ka roƙi Jehobah ya sa ka amfana daga karatun. Alal misali, idan kana neman shawara a kan yadda za ka magance wata matsala, ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka sami ƙa’idodi a cikin Kalmarsa da za su taimaka maka.—4. Mene ne zai taimaka maka ka ji daɗin karanta Littafi Mai Tsarki?
4 (2) Tunani. Jehobah ya ba mu baiwar yin tunani a kan yadda abubuwa za su iya kasancewa. Don ka ji daɗin karanta Littafi Mai Tsarki sosai, ka ji kamar kana wurin, kana ji da kuma ganin abubuwan da ke faruwa. Ka yi la’akari da yadda mutanen suka ji kuma ka saka kanka cikin yanayinsu.
5. Mene ne bimbini, kuma ta yaya za ka yi hakan?
5 (3) Bimbini. Yin bimbini yana nufin yin tunani sosai a kan abin da ka karanta da fahimtar yadda ya shafe ka da kuma sanin yadda za ka yi amfani da darasin. Yin bimbini zai taimaka maka ka fahimci wani batu sosai. Yin bimbini yana kama da dafa miya mai ɗanɗano. Idan ba mu yi amfani da dukan kayan miyar ba, miyar ba za ta yi daɗi ba. Hakazalika, yin nazari ba tare da bimbini ba, yana kama da miyar da ba a sa dukan kayan miya a ciki ba. Tambayoyin nan za su iya taimaka maka ka yi bimbini: ‘Mene ne mutumin da aka ambata a wannan labarin ya yi don ya taimaka wa kansa? Ta yaya Jehobah ya taimaka masa? Ta yaya darussan da na koya za su taimaka mini in jimre matsaloli?’
6. Me ya sa ya kamata mu yi amfani da abin da muka koya?
6 (4) Ka yi abin da ka koya. Yesu ya ce idan ba mu yi abin da muka koya ba, mun zama kamar mutumin da ya gina gida a kan yashi. Ya yi aiki tuƙuru, amma a banza. Me ya sa? Domin sa’ad da guguwa da ambaliya suka bugi gidan, sai ya rushe. (Mat. 7:24-27) Hakazalika, idan mun yi addu’a da tunani da kuma bimbini, amma ba mu yi abin da muka koya ba, mun ɓata lokacinmu ne kawai. Kuma bangaskiyarmu ba za ta kasance da ƙarfi ba sa’ad da muka fuskanci matsaloli ko kuma tsanantawa. Amma idan muka yi nazari kuma muka yi abin da muka koya, za mu riƙa tsai da shawarwari masu kyau, bangaskiyarmu za ta daɗa ƙarfi kuma za mu kasance da kwanciyar hankali. (Isha. 48:17, 18) Yanzu, bari mu yi amfani da abubuwa huɗu da muka tattauna don mu koyi darasi daga wani abu da ya faru da Sarki Dauda.
WANE DARASI NE ZA KA KOYA DAGA SARKI DAUDA?
7. Labarin wane ne za mu tattauna?
7 Wani abokinka ko kuma danginka ya taɓa ɓata maka rai kuwa? Idan haka ne, za ka amfana daga yin nazari a kan labarin Absalom ɗan Sarki Dauda wanda ya ci amanar mahaifinsa kuma ya so ya yi masa juyin mulki.—2 Sam. 15:5-14, 31; 18:6-14.
8. Me za ka yi don Jehobah ya taimaka maka?
8 (1) Addu’a. Kafin ka karanta labarin, ka gaya wa Jehobah yadda kake ji don wulaƙancin da aka yi maka. (Zab. 6:6-9) Ka roƙe shi ya taimaka maka ka ga ƙa’idodin da za su taimaka maka ka jimre matsalar da kake fuskanta.
9. Ta yaya za ka taƙaita abin da ya faru tsakanin Dauda da Absalom?
9 (2) Tunani. Ka yi tunani a kan abubuwan da suka faru a wannan labarin da 2 Sam. 15:7) Sa’ad da ya ga cewa lokaci ya yi da yake so ya zama Sarki, sai ya tura ’yan leƙen asiri zuwa ƙasar gabaki ɗaya don su sa mutanen su yarda ya zama sarkinsu. Ya ma rinjayi wani mashawarcin Dauda mai suna Ahitofel. Absalom ya naɗa kansa sarki kuma ya yi ƙoƙarin ya kashe Dauda wanda wataƙila yake rashin lafiya a lokacin. (Zab. 41:1-9) Dauda ya gano abin da ke faruwa kuma ya gudu ya bar Urushalima. A ƙarshe, sojojin Absalom sun yin arangama da sojojin Dauda. Sojojin Absalom ba su yi nasara ba kuma aka kashe Absalom.
kuma yadda suka shafi Sarki Dauda. Absalom ya yi shekaru da yawa yana neman ya sa mutane su so shi. (10. Mene ne Sarki Dauda bai yi ba?
10 Ka yi tunanin yadda Dauda ya ji sa’ad da abubuwan nan suke faruwa. Yana ƙaunar Absalom sosai, kuma ya amince da Ahitofel. Amma su biyu sun ci amanarsa. Sun ɓata masa rai sosai kuma suka yi ƙoƙarin kashe shi. Dauda bai yi tunanin cewa sauran abokansa suna goyon bayan Absalom kuma ya daina amincewa da su ba. Bai yi tunanin kansa kawai kuma ya gudu ya bar ƙasar ba. Bai yi sanyin gwiwa don abin da ya faru ba. Maimakon haka, ya magance matsalolin. Me ya taimaka masa ya yi hakan?
11. Me Dauda ya yi sa’ad da yake fuskantar matsala?
11 (3) Bimbini. Waɗanne darussa ne ka koya daga labarin nan? Ka amsa tambayar nan, “Mene ne Dauda ya yi don ya taimaka wa kansa?” Dauda bai tsorata kuma ya yanke shawarwarin da ba su dace ba. Kuma bai bar tsoro ya hana shi sanin abin da ya kamata ya yi ba. A maimakon haka, ya nemi taimakon Jehobah da abokansa kuma ya aikata shawarar da ya tsai da nan da nan. Ko da yake an ɓata masa rai sosai, hakan bai hana shi amincewa da mutane ko kuma ya sa ya yi fushi da su ba. Ya ci gaba da dogara ga Jehobah da kuma amincewa da abokansa.
12. Mene ne Jehobah ya yi don ya taimaka wa Dauda?
12 Ta yaya Jehobah ya taimaka wa Dauda? Ta wajen yin bincike, za ka ga cewa Jehobah ya ba Dauda ƙarfin da yake bukata don ya jimre da matsalar. (Zab. 3:1-8; rubutu na sama) Jehobah ya albarkaci shawarar da Dauda ya tsai da kuma ya taimaka wa abokan Dauda masu aminci da suka kāre shi.
13. Ta yaya za ka yi koyi da Dauda idan wani ya ɓata maka rai sosai? (Matiyu 18:15-17)
13 (4) Ka yi abin da ka koya. Ka tambayi kanka, ‘Ta yaya zan yi koyi da Dauda?’ Za ka bukaci ɗaukan mataki nan da nan don ka magance matsalolinka. Dangane da yanayin, kana iya bin shawarar Yesu da ke Matiyu sura 18 ko kuma ka bi ƙa’idar da ke ayoyin. (Karanta Matiyu 18:15-17.) Amma kada ka yi saurin tsai da shawarwari sa’ad da kake fushi. Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka natsu kuma ya ba ka hikimar sanin abin da za ka yi. Kada ka daina amincewa da ’yan’uwanka. A maimakon haka, idan suna so su taimaka maka, ka amince da hakan. (K. Mag. 17:17) Abu mafi muhimmanci ma, ka bi shawarar Jehobah da ke Kalmarsa.—K. Mag. 3:5, 6.
ME ZA KA IYA KOYA DAGA BULUS?
14. A wane lokaci ne littafin 2 Timoti 1:12-16 da kuma 4:6-11, 17-22, za su ƙarfafa ka?
14 ’Yan iyalinka suna tsananta maka ne domin kana bauta wa Jehobah? Kana zama ne a wurin da aka saka wa aikin Shaidun Jehobah takunkumi? Idan 2 Timoti 1:12-16 da kuma 4:6-11, 17-22 za su ƙarfafa ka. * Bulus ya rubuta waɗannan ayoyin sa’ad da yake kurkuku.
haka ne,15. Mene ne za ka iya roƙan Jehobah?
15 (1) Addu’a. Kafin ka karanta ayoyin, ka gaya wa Jehobah ainihin matsalolinka da kuma yadda suke sa ka ji. Ka roƙe shi ya taimaka maka ka ga ƙa’idodi a labarin tsanantawar da Bulus ya fuskanta, da za su taimaka maka ka san abin da za ka yi sa’ad da kake fuskantar tsanantawa.
16. Ta yaya za ka taƙaita abin da ya faru da Bulus?
16 (2) Tunani. Ka yi tunanin cewa kana cikin irin yanayin da Bulus yake ciki. Yana kurkuku a Roma kuma an ɗaure shi da sarƙa. Ba lokaci na farko da aka saka shi a kurkuku ke nan ba, amma a wannan lokacin, ya san cewa za a kashe shi. Wasu cikin abokan tafiyarsa sun yashe shi, kuma ya gaji sosai.—2 Tim. 1:15.
17. Mene ne Bulus bai yi ba?
17 Bulus bai mai da hankali ga rayuwarsa a dā ba, kuma ya soma tunani cewa in da bai zama Kirista ba, da ba a kama shi ba. Bai soma fushi da mutanen Asiya da suka yashe shi ba kuma ya ƙi amincewa da sauran abokansa ba. Me ya tabbatar masa da cewa abokansa za su kasance da shi kuma Jehobah zai albarkace shi?
18. Mene ne Bulus ya yi sa’ad da yake fuskantar tsanantawa?
18 (3) Bimbini. Ka amsa tambayar nan, “Ta yaya Bulus ya taimaka wa kansa?” Duk da yake Bulus ya san cewa ya kusan mutuwa, ya ci gaba da mai da hankali ga abu mafi muhimmanci, wato ɗaukaka Jehobah. Ya ci gaba da yin tunani a kan yadda zai ƙarfafa ’yan’uwansa. Ya dogara ga Jehobah ta wajen yin addu’a a kai a kai. (2 Tim. 1:3) Maimakon ya mai da hankali a kan mutanen da suka yashe shi, ya nuna godiya domin yadda abokansa suka taimaka masa a hanyoyi da yawa. Ƙari ga haka, Bulus ya ci gaba da yin nazarin Kalmar Allah. (2 Tim. 3:16, 17; 4:13) Abu mafi muhimmanci, yana da tabbaci cewa Jehobah da kuma Yesu suna ƙaunar sa. Ba su yashe shi ba kuma za su albarkace shi domin amincinsa.
19. Ta yaya Jehobah ya taimaka wa Bulus?
19 Jehobah ya riga ya gaya wa Bulus cewa za a tsananta masa domin ya zama Kirista. (A. M. 21:11-13) Ta yaya Jehobah ya taimaka wa Bulus? Ya amsa addu’o’insa kuma ya ƙarfafa shi. (2 Tim. 4:17) An gaya wa Bulus cewa zai sami lada domin ya yi aiki tuƙuru. Ƙari ga haka, Jehobah ya sa abokan Bulus su taimaka masa.
20. Kamar yadda Romawa 8:38, 39 suka nuna, ta yaya za mu yi koyi da bangaskiyar Bulus?
20 (4) Ka yi abin da ka koya. Ka tambayi kanka, ‘Ta yaya zan yi koyi da Bulus?’ Kamar Bulus, ya kamata mu sa rai cewa za a tsananta mana don imaninmu. (Mar. 10:29, 30) Don mu kasance da aminci sa’ad da ake tsananta mana, muna bukatar mu riƙa addu’a ga Jehobah da yin nazari a kai a kai da kuma tuna cewa abu mafi muhimmanci da za mu yi shi ne ɗaukaka Jehobah. Jehobah ba zai taɓa yasar da mu ba kuma babu wani da ya isa ya hana shi ya ƙaunace mu.—Karanta Romawa 8:38, 39; Ibran. 13:5, 6.
KA YI KOYI DA BAYIN ALLAH MASU AMINCI NA ZAMANIN DĀ
21. Mene ne ya taimaka wa Ayoko da kuma Hector su jimre matsalolin da suka fuskanta?
21 Ko da a wane yanayi ne muke ciki, labarin bayin Allah masu aminci zai taimaka * ta ce labarin Yunana ya taimaka mata ta daina jin tsoron yin wa’azi ga jama’a. Labarin Ruth ya taimaka wa wani matashi mai suna Hector a Indonisiya ya koya game da Jehobah kuma ya soma bauta masa.
mana mu jimre. Alal misali, wata majagaba a ƙasar Jafan mai suna Ayoko22. Ta yaya za ka amfana daga wasannin kwaikwayo na Littafi Mai Tsarki ko jerin talifofin nan “Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu”?
22 A ina ne za ka iya samun misalai a Littafi Mai Tsarki da za su ƙarfafa ka? Bidiyoyinmu da wasannin kwaikwayo na Littafi Mai Tsarki da kuma jerin talifofin nan “Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu” suna sa mu ga kamar labarin Littafi Mai Tsarki yana faruwa a yanzu. * Kafin ka kalli ko saurari ko kuma karanta labaran nan da aka yi bincike a kansu da kyau, ka nemi taimakon Jehobah don ka ga darussa masu muhimmanci da za ka yi amfani da su. Ka yi tunanin cewa kana cikin yanayin mutumin da aka ambata a labarin. Ka yi bimbini a kan abin da waɗannan bayin Jehobah suka yi da kuma yadda ya taimaka musu su magance matsaloli. Sai ka yi amfani da darussan da ka koya a yanayinka. Ka gode wa Jehobah domin taimakon da yake yi maka. Ka nuna cewa kana godiya ta wajen neman hanyoyin ƙarfafa mutane da kuma taimaka musu.
23. Kamar yadda Ishaya 41:10, 13 suka nuna, wane alkawari ne Jehobah ya yi mana?
23 Rayuwa a wannan duniyar Shaiɗan tana da wuya sosai, kuma a wasu lokuta ba mu san abin da za mu yi ba. (2 Tim. 3:1) Amma ba ma bukatar mu ji tsoro. Jehobah ya san matsalar da muke fuskanta. Ya yi alkawari cewa zai riƙe mu da hannun damarsa na adalci a duk lokacin da muke bukatar taimako. (Karanta Ishaya 41:10, 13.) Muna da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mana kuma abin da ke Littafi Mai Tsarki zai ba mu ƙarfin da muke bukata don mu ci gaba da jimre matsalolinmu.
WAƘA TA 96 Kalmar Allah Tana da Daraja
^ sakin layi na 5 Labarai da yawa a Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa Jehobah yana ƙaunar bayinsa kuma zai taimaka musu su jimre matsaloli. A wannan talifin, za mu tattauna yadda za ka karanta Littafi Mai Tsarki don ka amfana.
^ sakin layi na 2 Ban da hanyar yin nazari da aka tattauna a talifin nan, da akwai wasu hanyoyi da za ka iya yin nazari. Don samun hanyoyin nan, ka duba Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah a ƙarƙashin batun nan “Littafi Mai Tsarki,” a ƙaramin jigon nan “Karatu da Kuma Fahimtar Littafi Mai Tsarki.”
^ sakin layi na 14 Kada ku karanta waɗannan ayoyin sa’ad da kuke nazarin Hasumiyar Tsaro a ikilisiya.
^ sakin layi na 21 An canja wasu sunayen.
^ sakin layi na 22 Ka duba “Ka Yi Koyi da Bangaskiyar Maza da Mata na Zamanin Dā” a jw.org. (Ka je KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI > IMANI GA ALLAH.)