Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 19

Babu Abin da Zai Sa Mai Adalci Tuntuɓe

Babu Abin da Zai Sa Mai Adalci Tuntuɓe

“Masu ƙaunar koyarwarka suna da babbar salama, babu abu mai sa su tuntuɓe.”​—ZAB. 119:165.

WAƘA TA 122 Mu Tsaya Daram, Babu Tsoro!

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Mene ne wani marubuci ya ce, kuma me za mu tattauna a wannan talifin?

A YAU, mutane da yawa suna da’awa cewa sun yi imani da Yesu, amma ba su amince da abubuwan da ya koyar ba. (2 Tim. 4:​3, 4) Wani marubuci ya taɓa cewa: “Idan akwai wani mutum kamar Yesu da yake faɗin abubuwa yadda Yesu ya faɗe su . . . , shin za mu ƙi shi yadda aka ƙi Yesu shekaru dubu biyu da suka shige? . . . Halayen mutane da ayyukansu sun nuna cewa za su ƙi mutumin.”

2 Mutane da yawa a ƙarni na farko sun ji koyarwar Yesu kuma sun ga mu’ujizai da ya yi, amma sun ƙi ba da gaskiya a gare shi. Me ya sa? A talifin da ya gabata, mun tattauna dalilai huɗu da suka sa mutane suka ƙi bin Yesu. Bari mu ƙara tattauna wasu dalilai huɗu. Yayin da muke hakan, za mu ga dalilin da ya sa mutane a yau suke ƙin mabiyan Yesu. Za mu kuma ga yadda za mu guji barin kome ya hana mu bauta wa Jehobah.

(1) YESU BAI NUNA SON KAI BA

Mutane da yawa sun ƙi Yesu domin abokansa. Ta yaya waɗannan abubuwan suke sa wasu a yau su ƙi Shaidun Jehobah? (Ka duba sakin layi na 3) *

3. Me Yesu ya yi da ya sa wasu mutane suka ƙi shi?

3 Sa’ad da Yesu yake duniya, ya yi cuɗanya da mutane dabam-dabam. Ya ci abinci da masu arziki da masu iko, amma ya fi kasancewa tare da talakawa da marasa taimako. Ƙari ga haka, ya ji tausayin waɗanda mutane suke gani “masu zunubi” ne. Wasu mutane masu fahariya sun ƙi Yesu domin abin da ya yi. Sun tambayi almajiransa: “Don me kuke ci, kuke kuma sha da masu karɓar haraji da masu zunubi?” Sai Yesu ya amsa ya ce: “Masu lafiyar jiki ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya. Ban zo don in kira masu adalci ba, sai dai don masu zunubi su tuba, su kuma canja rayuwarsu.”​—Luk. 5:​29-32.

4. Kamar yadda annabi Ishaya ya faɗa, me ya kamata Yahudawa su sani game da Almasihu?

4 Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce? Tun da daɗewa kafin Almasihu ya zo, Ishaya ya annabta cewa mutane za su ƙi Almasihu. Ya ce: “Aka rena shi aka kuma ƙi shi . . . Da ganinsa, mutane suka kawar da fuskarsu, aka rena shi, aka ɗauke shi kamar shi ba kome ba.” (Isha. 53:3) An annabta cewa mutane za su “ƙi” Almasihu, saboda haka ya kamata Yahudawa a zamanin Yesu su san cewa za a ƙi shi.

5. Yaya mutane da yawa a yau suke ɗaukan mabiyan Yesu?

5 Shin muna fuskantar irin matsalar nan a yau? E. Limamai da yawa suna farin ciki sa’ad da shahararru da masu arziki da kuma waɗanda mutane suke ganin suna da hikima suka zama mabiyansu. Suna barin irin mutanen nan su riƙa zuwa cocinsu ko da suna yin abubuwan da Jehobah ya tsana. Waɗannan limaman sun rena bayin Jehobah masu ƙwazo da suke bin ƙa’idodinsa domin ba su shahara a duniya ba. Kamar yadda Bulus ya ce, Allah yana zaɓan waɗanda mutane suke ganin ba su da “amfani.” (1 Kor. 1:​26-29) Amma ga Jehobah dukan bayinsa masu aminci suna da daraja.

6. Mene ne Yesu ya ce a Matiyu 11:​25, 26, kuma ta yaya za mu yi koyi da shi?

6 Mene ne zai taimaka mana mu riƙe bangaskiyarmu? (Karanta Matiyu 11:​25, 26.) Kada ka bar ra’ayin mutanen duniya game da bayin Allah ya shafe ka. Ka amince cewa Jehobah yana amfani da masu sauƙin kai ne kaɗai don yin nufinsa. (Zab. 138:6) Ka yi tunanin yadda Jehobah ya cim ma abubuwa da yawa ta wajen yin amfani da waɗanda mutanen duniya suke ganin ba su da hikima ko ilimi.

(2) YESU YA FALLASA KOYARWAR ƘARYA

7. Me ya sa Yesu ya kira Farisiyawa munafukai, kuma yaya suka ji?

7 Yesu ya nuna cewa abubuwan da shugabannin addinai a zamaninsa suke yi ba daidai ba ne. Alal misali, Yesu ya nuna cewa Farisiyawa munafukai ne domin sun fi mai da hankali ga wanke hannayensu maimakon kula da iyayensu. (Mat. 15:​1-11) Wataƙila abubuwan da Yesu ya faɗa sun ba almajiransa mamaki. Shi ya sa suka tambaye shi: “Ka san Farisiyawa sun ji haushi da suka ji maganar nan?” Sai Yesu ya amsa: “Duk shukar da ba Ubana na sama ne ya shuka ba, za a tumɓuke shi. Bar su kawai. Su makafi ne masu yi wa makafi ja-gora. Idan kuwa makaho ya yi wa wani makaho ja-gora, ai, dukansu za su fāɗi cikin rami.” (Mat. 15:​12-14) Duk da cewa limaman sun yi fushi da Yesu domin abubuwan da ya faɗa, ya ci gaba da gaya musu gaskiya.

8. Ta yaya Yesu ya nuna cewa ba dukan koyarwar addinai ba ne Allah yake amincewa da su?

8 Yesu ya nuna cewa wasu koyarwar Farisiyawa ba daidai ba ne. Ya ce ba dukan koyarwar addinai ne Allah yake amincewa da su ba. Kuma ya ce mutane da yawa za su bi hanyar da za ta kai su ga halaka, amma mutane kaɗan ne za su riƙa bin ƙaramar hanya ta rai. (Mat. 7:​13, 14) Yesu ya ce wasu mutane za su ce suna bauta wa Allah, amma da gaske ba sa yin hakan. Ya yi gargaɗin nan cewa: “Ku yi hankali da annabawan ƙarya waɗanda suke zuwa wurinku da kamannin tumaki, amma a ciki su kyarketai ne masu tsananin yunwa. Za ku gane su ta irin aikinsu.”​—Mat. 7:​15-20.

Mutane da yawa sun ƙi Yesu domin ya fallasa koyarwar ƙarya. Ta yaya waɗannan abubuwan suke sa wasu a yau su ƙi Shaidun Jehobah? (Ka duba sakin layi na 9) *

9. Waɗanne koyarwar addinan ƙarya ne Yesu ya fallasa?

9 Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce? A Littafi Mai Tsarki, an annabta cewa Almasihu zai nuna ƙwazo sosai don gidan Jehobah. (Zab. 69:9; Yoh. 2:​14-17) Ƙwazon Yesu ya sa ya fallasa koyarwar addinan ƙarya da ayyukansu. Alal misali, Farisiyawa sun gaskata cewa kurwa ba ta mutuwa, amma Yesu ya ce matattu, barci suke yi. (Yoh. 11:11) Sadukiyawa ba su yi imani da tashin matattu ba, amma Yesu ya tā da abokinsa Li’azaru daga mutuwa. (Yoh. 11:​43, 44; A. M. 23:8) Farisiyawa sun koyar da cewa Allah ne ke ƙaddara kome. Amma Yesu ya nuna cewa ’yan Adam za su iya zaɓan su bauta wa Allah ko su ƙi yin hakan.​—Mat. 11:28.

10. Me ya sa mutane da yawa a yau suke ƙin mu?

10 Shin muna fuskantar irin matsalar nan a yau? E. Mutane da yawa ba sa saurarar mu, domin muna amfani da Littafi Mai Tsarki don mu fallasa koyarwarsu ta ƙarya. Limamai suna koya wa mabiyansu cewa Allah yana azabtar da mugaye a wutar jahannama. Suna amfani da wannan koyarwar don mutane su riƙa musu biyayya. A matsayin waɗanda suke bauta wa Jehobah Allah mai ƙauna, muna taimaka wa mutane su fahimci cewa wannan koyarwar ƙarya ce. Limamai suna koyar da cewa kurwa ba ta mutuwa. Idan wannan koyarwar gaskiya ce, ba za a yi tashin matattu ba. Saboda haka, muna nuna cewa wannan koyarwar ba ta cikin Littafi Mai Tsarki. Addinai da yawa suna koyar da cewa kome da yake faruwa ƙaddara ce. Amma muna koya wa mutane cewa muna da ’yanci kuma mu ke zaɓan mu bauta wa Allah. Mene ne limamai suke yi sa’ad da muka nuna cewa koyarwarsu ƙarya ce? Sau da yawa sukan yi fushi sosai.

11. Kamar yadda furucin Yesu a Yohanna 8:​45-47 ya nuna, mene ne Allah yake so mutanensa su yi?

11 Mene ne zai taimaka mana mu riƙe bangaskiyarmu? Idan muna son gaskiya, wajibi ne mu gaskata da koyarwar Allah kuma mu bi ta. (Karanta Yohanna 8:​45-47.) Ba za mu ƙi gaskiya kamar yadda Shaiɗan ya yi ba. Ba za mu taɓa yin abubuwan da ba su jitu da imaninmu ba. (Yoh. 8:44) Allah yana son bayinsa su “ƙi duk abin da yake mugu” kuma su “riƙe abin da yake mai kyau da ƙarfi sosai” kamar yadda Yesu ya yi.​—Rom. 12:9; Ibran. 1:9.

(3) AN TSANANTA WA YESU

Mutane da yawa sun ƙi Yesu domin ya mutu a kan gungumen azaba. Ta yaya waɗannan abubuwan suke sa wasu a yau su ƙi Shaidun Jehobah? (Ka duba sakin layi na 12) *

12. Me ya sa yadda aka kashe Yesu ya sa Yahudawa da yawa suka ƙi shi?

12 Wane dalili ne kuma ya sa wasu Yahudawa suka ƙi Yesu? Bulus ya ce: “Muna wa’azin Almasihu wanda ya mutu a kan [“gungumen azaba,” NW ] ne, abin da ya zama dalilin tuntuɓe ga Yahudawa.” (1 Kor. 1:23) Me ya sa Yahudawa da yawa suka ƙi Yesu don yadda aka kashe shi? A ganinsu, yadda aka kashe Yesu a kan gungumen azaba ya mai da shi kamar mai zunubi. Hakan ya sa sun ƙi gaskata cewa shi ne Almasihu.​—M. Sha. 21:​22, 23.

13. Mene ne waɗanda suka ƙi Yesu suka kasa ganewa?

13 Waɗanda suka ƙi Yesu ba su fahimci cewa bai yi wani laifi ba. An yi masa sharri ne kuma aka wulaƙanta shi. Waɗanda suka yi wa Yesu shari’a ba su yi masa adalci ba. Alƙalan kotun ƙoli na Yahudawa sun taru da gaggawa don su yi wa Yesu shari’a kuma ba su bi ƙa’idodin shari’a ba. (Luk. 22:54; Yoh. 18:24) Maimakon su saurari tuhumar da ake yi wa Yesu ba tare da son kai ba, su da kansu suka “nemi shaidar ƙarya da za a yi wa Yesu domin su sami damar kashe shi.” (Mat. 26:59; Mar. 14:​55-64) Da yake ba su yi nasara ba, sai babban firist ya yi ƙoƙari ya sa Yesu ya faɗi abin da zai sa a kama shi da laifi. Hakan ba daidai ba ne bisa doka. Bayan da aka tā da Yesu daga mutuwa, waɗannan alƙalai marasa adalci sun ba sojojin Roma da suke tsare kabarin Yesu “kuɗi mai yawa,” don su yaɗa labarin ƙarya.​—Mat. 28:​11-15.

14. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya annabta game da mutuwar Almasihu?

14 Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce? Yahudawa da yawa a zamanin Yesu ba su yi zato cewa za a kashe Almasihu ba. Amma an annabta a Littafi Mai Tsarki cewa: “Ya ba da ransa ya mutu, an lissafta shi a cikin masu zunubi, amma ya ɗauki laifofin mutane da yawa, ya kuma yi roƙo domin masu zunubi.” (Isa. 53:12) Saboda haka, bai kamata Yahudawa su ƙi Yesu don an zarge shi da aikata laifi kuma aka kashe shi a matsayin mai zunubi ba.

15. Wane zargi ne ake wa Shaidun Jehobah da ya sa wasu suka ƙi su?

15 Shin muna fuskantar irin matsalar nan a yau? Ƙwarai kuwa! An zargi Yesu da laifin da bai yi ba kuma abin da mutane suke yi wa Shaidun Jehobah a yau ke nan. Alal misali, a tsakanin shekara ta 1930 da 1950 a Amirka, mun kai ƙara a kotu da yawa don mu kāre ’yancinmu na bauta wa Allah. Wasu alƙalai sun nuna a fili cewa ba sa son mu. Alal misali, a yankin Quebec a ƙasar Kanada, shugabannin addinai sun haɗa baki da gwamnatin ƙasar don su tsananta wa Shaidun Jehobah. An saka masu shela da yawa a kurkuku don kawai sun yi wa maƙwabtansu wa’azi game da Mulkin Allah. A ƙasar Jamus, gwamnatin Nazi ta kashe matasa Shaidun Jehobah da yawa. Kwanan nan, gwamnatin Rasha ta saka ’yan’uwanmu da yawa a kurkuku domin suna wa’azi. Hukumomin sun ce Shaidun Jehobah “masu tsattsaurar ra’ayi ne.” Ban da haka, sun hana mutane yin amfani da juyin New World Translation of the Holy Scriptures na yaren Rasha. Sun ce “littafi ne mai ɗaukaka tsattsaurar ra’ayi” domin ya yi amfani da sunan nan Jehobah.

16. Kamar yadda aka nuna a 2 Bitrus 2:​1, me ya sa ba za mu yarda labaran ƙarya game da mutanen Jehobah su yaudare mu ba?

16 Mene ne zai taimaka mana mu riƙe bangaskiyarmu? Ka bincika gaskiyar batun. A Huɗuba da Yesu Ya Yi a kan Dutse, ya ce wasu za su yi ƙarya a kan mabiyansa kuma su yi musu “mugunta iri-iri.” (Matt. 5:11) Shaiɗan ne yake fifita wannan ƙaryar. Yana zuga masu tsananta mana su riƙa yaɗa ƙarairayi game da mu. (R. Yar. 12:​9, 10) Wajibi ne mu guji ƙaryace-ƙaryace da maƙiyanmu suke yaɗawa. Kada mu yarda su sa mu ji tsoron bauta wa Allah ko kuma su sa mu daina kasancewa da bangaskiya.​—Karanta 2 Bitrus 2:1.

(4) AN CI AMANAR YESU KUMA AN YASHE SHI

Mutane da yawa sun ƙi Yesu domin Yahuda ya ci amanarsa. Ta yaya waɗannan abubuwan suke sa wasu a yau su ƙi Shaidun Jehobah? (Ka duba sakin layi na 17-18) *

17. A wace hanya ce abubuwan da suka faru kafin mutuwar Yesu suka sa wasu mutane sun ƙi shi?

17 Kafin mutuwar Yesu, ɗaya daga cikin manzanninsa 12 ya ci amanarsa. Ɗaya kuma ya yi mūsun sanin Yesu sau uku, kuma dukan manzannin sun yashe shi a dare na ƙarshe kafin ya mutu. (Mat. 26:​14-16, 47, 56, 75) Yesu bai yi mamaki ba don ya annabta cewa hakan zai faru. (Yoh. 6:64; 13:​21, 26, 38; 16:32) Ganin waɗannan abubuwan zai iya sa wasu su ce, ‘Idan halin manzannin Yesu ke nan, ba na so in zama mabiyinsa ba!’

18. Waɗanne annabce-annabce ne suka cika kafin mutuwar Yesu?

18 Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce? Shekaru da yawa kafin Yesu ya zo duniya, Jehobah ya faɗa a Kalmarsa cewa za a ci amanar Almasihu a kan kuɗin azurfa 30. (Zak. 11:​12, 13) Abokin Yesu na kud da kud ne zai ci amanar shi. (Zab. 41:9) Annabi Zakariya ya daɗa da cewa: “Bugi makiyayin tumaki, tumakin kuwa za su warwatse.” (Zech. 13:7) Mutane masu zuciyar kirki ba za su yarda waɗannan abubuwa su sa su ƙi Yesu ba, amma ganin yadda waɗannan annabce-annabce suke cika a kan Yesu zai ƙarfafa bangaskiyarsu.

19. Mene ne mabiyan Yesu na gaskiya suka sani?

19 Shin muna fuskantar irin matsalar nan a yau? E. A zamaninmu, wasu sanannun Shaidu sun daina bauta wa Jehobah, sun zama ’yan ridda kuma suna ƙoƙarin sa wasu su daina bauta wa Jehobah. Suna yaɗa labaran ƙarya game da Shaidun Jehobah a kafofin yaɗa labarai da kuma intane. Amma ba a yaudari mabiyan Yesu na gaskiya ba. Maimakon haka, sun fahimci cewa Littafi Mai Tsarki ya ce irin waɗannan abubuwan za su faru.​—Mat. 24:24; 2 Bit. 2:​18-22.

20. Ta yaya za mu ƙi barin waɗanda suka daina bauta wa Jehobah su yaudare mu? (2 Tim. 4:​4, 5)

20 Mene ne zai taimaka mana mu riƙe bangaskiyarmu? Muna bukatar mu ƙarfafa bangaskiyarmu ta wajen yin nazari da kuma addu’a a kai a kai. Ban da haka, ya kamata mu shagala da yin aikin da Jehobah ya ba mu. (Karanta 2 Timoti 4:​4, 5.) Idan muna da bangaskiya, ba za mu ji tsoro ba sa’ad da muka ji labarin ƙarya game da Shaidun Jehobah. (Isha. 28:16) Yadda muke ƙaunar Jehobah da Kalmarsa da kuma ’yan’uwanmu za ta sa mu ƙi barin waɗanda suka daina bauta wa Jehobah su yaudare mu.

21. Ko da yawancin mutane a yau suna ƙin saƙonmu, wane tabbaci ne muke da shi?

21 A ƙarni na farko, mutane da yawa sun ƙi Yesu. Duk da haka, mutane da yawa sun amince da shi. Wani ɗan Majalisar Yahudawa yana cikin waɗanda suka amince da shi, tare da “firistoci masu yawa sosai.” (A. M. 6:7; Mat. 27:​57-60; Mar. 15:43) A yau, miliyoyin mutane ba su daina bin Yesu ba. Me ya sa? Domin sun san gaskiya da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuma suna son wannan gaskiyar. Kalmar Allah ta ce: “Masu ƙaunar koyarwarka suna da babbar salama, babu abu mai sa su tuntuɓe.”​—Zab. 119:165.

WAƘA TA 124 Mu Kasance da Aminci

^ sakin layi na 5 A talifin da ya gabata, mun tattauna dalilai huɗu da suka sa mutane a zamanin dā suka ƙi bin Yesu da kuma abin da ya sa mutane suke ƙin mabiyansa a yau. A wannan talifin, za mu ƙara tattauna dalilai huɗu. Za mu kuma ga abin da ya sa mutane da suke ƙaunar Jehobah ba sa barin kome ya sa su ƙi shi.

^ sakin layi na 60 BAYANI A KAN HOTUNA: Yesu ya ci abinci da Matiyu da masu karɓan haraji.

^ sakin layi na 62 BAYANI A KAN HOTUNA: Yesu yana koran masu kasuwanci a haikali.

^ sakin layi na 64 BAYANI A KAN HOTUNA: An sa Yesu ya ɗauki gungumen azaba.

^ sakin layi na 66 BAYANI A KAN HOTUNA: Yahuda ya ci amanar Yesu ta wajen yi masa sumba.