Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Sani?

Ka Sani?

Shin mutane a zamanin dā sun yi amfani da ciyawar iwa, wato papyrus, wajen yin kwalekwale?

Ciyawar iwa

MUTANE da yawa sun san cewa a zamanin dā, Masarawa sun yi amfani da takardar da aka yi da ciyawar iwa. * Helenawa da Romawa ma sun yi amfani da irin wannan takardar. Amma mutane kaɗan ne suka san cewa an yi amfani da wannan ciyawar don ƙera kwalekwale.

Kwalekwale guda biyu da aka samo a wani kabari a Masar, kuma da ciyawar iwa aka yi shi

Fiye da shekaru 2,500 da suka shige, annabi Ishaya ya rubuta cewa mutanen da suke zama a “ƙetaren kogunan Itiyofiya” sun aika mutane ta “jiragen da aka yi da ciyawar iwa.” Daga baya, Irmiya ya annabta cewa mutanen Midiya da Farisa za su ci birnin Babila da yaƙi kuma za su ƙona jiragen ruwan Babiloniyawa domin kada jiragen su tsere.​—Isha. 18:​1, 2; Irm. 51:32.

Allah ne ya hure mutanen da suka rubuta Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, ɗaliban Littafi Mai Tsarki ba su yi mamaki ba sa’ad da masanan neman kayan tarihi cikin ƙasa suka tono abubuwan da suka nuna cewa a zamanin dā an yi amfani da ciyawar iwa don ƙera kwalekwale ba. (2 Tim. 3:16) Mene ne suka binciko? Masanan neman kayan tarihi cikin ƙasa sun samo abin da ya tabbatar cewa an ƙera kwalekwale da ciyawar iwa a Masar.

TA YAYA AKE ƘERA KWALEKWALE DA CIYAWAR IWA?

A cikin kaburbura a Masar, akwai zane-zane a bango da suka nuna yadda mutane suke girbe da kuma yi amfani da ciyawar iwa don ƙera kwalekwale. Mutane sukan yanka ciyawar kuma su ɗaura su dami-dami, bayan hakan, sai su ɗaura dukan damin tare. Ciyawar iwa tana da kusurwa uku. Don haka, idan aka ɗaure ciyawar tare, damin yana ƙarfi sosai. A wani littafin tarihin ƙasar Masar, an ce kwalekwale da ake yi da ciyawar iwa sukan kai tsawon ƙafa 55 kuma suna da faɗi sosai.

Zanen da ke nuna yadda Masarawa ke ƙera kwalekwale da ciyawar iwa

ME YA SA MASU ƘERA KWALEKWALE SUKA YI AMFANI DA CIYAWAR IWA?

A ƙasar Masar, ciyawar iwa tana girma sosai a ƙwarin kogin Nilu. Ban da haka, ƙera kwalekwale da ciyawar iwa yana da sauƙi sosai. Har ma a lokacin da mutane suka soma amfani da katako don gina manyan jirage, masu kamun kifi da kuma mafarauta sun ci gaba da yin amfani da kwalekwale da aka ƙera da ciyawar iwa.

Mutane sun daɗe suna amfani da kwalekwale da aka ƙera da ciyawar. Wani marubuci Baheleni mai suna Plutarch wanda ya yi rayuwa a zamanin manzanni ya ce mutane a zamaninsa suna amfani da wannan ciyawar wajen ƙera kwalekwale.

^ sakin layi na 3 Ciyawar iwa tana girma ne a wurin da ruwa ba ya gudu sosai. Tsayin ciyawar iwa tana iya kai kafa 16 girmanta kuma yana iya kai inci 6 a ta ƙasa.