Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 18

Kada Ka Yarda Wani Abu Ya Hana Ka Bin Yesu

Kada Ka Yarda Wani Abu Ya Hana Ka Bin Yesu

“Mai albarka ne wanda bai yi tuntuɓe saboda ni ba.”​—MAT. 11:​6, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.

WAƘA TA 54 ‘Wannan Ita Ce Hanyar Rai’

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne wataƙila ya ba ka mamaki a karo na farko da ka yi ƙoƙarin yin wa’azi?

KA TUNA lokacin da ka gano gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki? Ƙila ya yi maka sauƙi ka fahimci kome da kake koya a Littafi Mai Tsarki! Ka ɗauka cewa kowa zai amince da abin da ka yi imani da shi. Ka san cewa saƙon Littafi Mai Tsarki zai sa mutane su ji daɗin rayuwa kuma su kasance da bege game da nan gaba. (Zab. 119:105) Don haka, ka soma gaya wa abokanka da danginka dukan abubuwan da ka koya. Amma mene ne ya faru? Babu shakka, ka yi mamaki sa’ad da yawancinsu suka ƙi saurararka.

2-3. Mene ne yawancin mutane a zamanin Yesu suka yi sa’ad da suka ji saƙonsa?

2 Kada mu yi mamaki idan mutane sun ƙi saurarar wa’azinmu. A zamanin Yesu, mutane da yawa sun ƙi saurarar sa duk da cewa ya yi mu’ujizai da suka nuna cewa Allah ya amince da shi. Alal misali, Yesu ya tā da Li’azaru daga mutuwa kuma maƙiyansa ba su iya musanta hakan ba. Duk da haka, shugabannin Yahudawa ba su gaskata cewa Yesu ne Almasihu ba. A maimakon haka, sun yi ƙoƙari su kashe Yesu da Li’azaru!​—Yoh. 11:​47, 48, 53; 12:​9-11.

3 Yesu ya san cewa yawancin mutane za su ƙi gaskata cewa shi ne Almasihu. (Yoh. 5:​39-44) Ya gaya wa almajiran Yohanna Mai Baftisma cewa: “Mai albarka ne wanda bai yi tuntuɓe saboda ni ba.” (Mat. 11:​2, 3, 6, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Me ya sa mutane da yawa suka ƙi bin Yesu?

4. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

4 A wannan talifin da kuma na gaba, za mu tattauna dalilai da yawa da suka sa mutane a ƙarni na farko suka ƙi bin Yesu. Za mu kuma tattauna dalilin da ya sa mutane da yawa a yau ba sa saurarar wa’azinmu. Ƙari ga haka, za mu tattauna dalilin da ya sa muke bukatar bangaskiya sosai don kada mu daina bin Yesu.

(1) INDA YESU YA YI GIRMA

Mutane da yawa sun ƙi bin Yesu domin tarihinsa. Ta yaya waɗannan dalilan za su iya sa mutane su ƙi saurarar mu a yau? (Ka duba sakin layi na 5) *

5. Me ya sa wasu suka ɗauka cewa ba Yesu ba ne Almasihun da aka annabta?

5 Mutane da yawa sun ƙi saurarar Yesu domin wurin da ya yi girma. Sun yarda cewa shi malami ne na ƙwarai kuma ya yi mu’ujizai. Amma a wurinsu, shi ɗan kafinta ne matalauci. Kuma ya fito daga Nazarat, birnin da wataƙila mutane suna ganin bai isa kome ba. Da farko, Nataniyel wanda ya zama almajirin Yesu ya ce: “Wani abin kirki zai iya fitowa daga Nazaret kuwa?” (Yoh. 1:46) Wataƙila Nataniyel ba ya son birnin da Yesu ya fito. Ko kuma wataƙila yana tunanin annabcin da aka yi a Mika 5:2 cewa za a haifi Almasihu a Betelehem ba a Nazarat ba.

6. Mene ne ya kamata ya taimaka wa mutane a zamanin Yesu su san cewa shi ne Almasihu?

6 Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce? Ishaya ya annabta cewa maƙiyan Yesu ba za su ‘dami’ kansu da sanin zuriyar da ya fito ba. (Isha. 53:8) An annabta abubuwa da yawa game da hakan. Da a ce mutanen sun yi bincike, da sun san cewa a Betelehem aka haifi Yesu kuma daga zuriyar Sarki Dauda ya fito. (Luk. 2:​4-7) Don haka, an haifi Yesu a birnin da aka annabta a Mika 5:2. To mene ne matsalar su? Mutanen su yin saurin yanke shawara. Ba su san gaskiyar batun ba, amma sun ƙi amincewa da Yesu.

7. Me ya sa mutane da yawa a yau suke ƙin zama Shaidun Jehobah?

7 Shin muna fuskantar irin matsalar nan a yau? E. Yawancin Shaidun Jehobah talakawa ne. Kuma mutane suna ɗaukan su a matsayin “marasa ilimi.” (A. M. 4:13) Wasu mutane suna ganin kamar Shaidun Jehobah ba za su iya koyar da Littafi Mai Tsarki ba domin ba su yi karatu a makarantun addini ba. Wasu kuma suna ƙin Shaidun Jehobah domin sun ɗauka cewa “addinin ’yan Amirka ne.” Amma gaskiyar ita ce, yawancin Shaidun Jehobah ba ’yan Amirka ba ne. Wasu kuma ana koya musu cewa Shaidun Jehobah ba su amince da Yesu ba. Shekaru da yawa yanzu, mutane da yawa suna kiran Shaidun Jehobah “masu shan jini” da “mutanen da ba sa yin addu’a.” Don haka, mutane da yawa ba sa so su zama Shaidun Jehobah domin sun ji labaran nan kuma ba su damu su san gaskiya game da Shaidun Jehobah ba.

8. Kamar yadda Ayyukan Manzanni 17:11 ta nuna, mene ne ya kamata mutane su yi idan suna so su san Shaidun Jehobah?

8 Mene ne zai taimaka wa mutum ya riƙe bangaskiyarsa? Mutane suna bukatar su yi bincike don su san gaskiya. Abin da Luka ya ƙuduri niyyar yi ke nan. Ya yi ƙoƙarin “bincika abubuwan nan duka a hankali.” Ya yi hakan ne domin waɗanda za su karanta abin da ya rubuta su san labarin Yesu sosai. (Luk. 1:​1-4) Yahudawan da ke birnin Biriya sun yi abin da Luka ya yi. Sa’ad da aka yi musu wa’azi game da Yesu, sun bincika Nassosin Ibrananci don su tabbata cewa abin da aka gaya musu gaskiya ne. (Karanta Ayyukan Manzanni 17:11.) Haka ma, mutane a yau suna bukatar su yi bincike don su san gaskiya. Dole ne su gwada abin da Shaidun Jehobah suke koyarwa da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Ƙari ga haka, suna bukatar su bincika tarihin Shaidun Jehobah. Idan suka yi bincike sosai, ba za su bar abin da mutane suke faɗa ya shafe su ba.

(2) YESU YA ƘI NUNA MANYAN ALAMU

Mutane da yawa sun ƙi bin Yesu domin ya ƙi nuna manyan alamu. Ta yaya waɗannan dalilan za su iya sa mutane su ƙi saurarar mu a yau? (Ka duba sakin layi na 9-10) *

9. Mene ne ya faru sa’ad da Yesu ya ƙi nuna wata babbar alama?

9 Wasu a zamanin Yesu ba su gamsu da koyarwarsa ba don suna so ya yi wasu abubuwa. Suna so ya nuna cewa shi ne Almasihu ta wajen nuna musu “wata babbar alama da za ta bayyana ikonsa.” (Mat. 16:1) Wataƙila suna so ya yi hakan domin abin da suka karanta a Daniyel 7:​13, 14. Amma lokacin da Jehobah zai cika wannan annabcin bai yi ba. Ya kamata abubuwan da Yesu ya koyar su tabbatar musu cewa shi ne Almasihu. Amma da ya ƙi nuna musu wata alama, sai suka ƙi amince cewa shi ne Almasihu.​—Mat. 16:4.

10. Ta yaya Yesu ya cika annabcin da Ishaya ya yi game da Almasihu?

10 Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce? Annabi Ishaya ya rubuta game da Almasihu cewa: “Ba zai yi ihu ko ya tā da muryarsa ba, ko ya yi magana da ƙarfi a titi ba.” (Isha. 42:​1, 2) Yesu ya yi hidimarsa ba tare da yin abin da zai sa mutane su mai da hankali a kansa ba. Bai gina manyan haikalai ba, bai sa tufafi na musamman ko kuma ya sa a kira shi da wani laƙabi ba. Sa’ad da ake yi wa Yesu shari’a, ya ƙi yin mu’ujiza don ya burge Sarki Hiridus. (Luk. 23:​8-11) Yesu ya yi wasu mu’ujizai, amma ya fi mai da hankali ga yin wa’azi. Ya gaya wa almajiransa cewa: “Dalilin zuwana ke nan.”​—Mar. 1:38.

11. Mene ne mutane suke so Shaidun Jehobah su riƙa yi a yau?

11 Shin muna fuskantar irin matsalar nan a yau? E. A yau, abin da yake burge mutane shi ne, manya-manyan coci da aka gina da kaya masu tsada, da kuma limamai masu laƙabi na musamman. Ƙari ga haka, suna son yin bukukuwa da yawancin mutane sun manta cewa sun samo asali ne daga bautar ƙarya. Waɗannan mutanen ba sa koyan kome game da Allah da kuma nufinsa. Amma waɗanda suke halartan taronmu suna koyan abin da Jehobah yake bukata a gare su da kuma yadda za su yi nufinsa. Majami’un Mulkinmu suna da tsabta kuma ba a ƙawata su da kayayyaki masu tsada. Waɗanda suke yi mana ja-goranci ba sa saka tufafi na musamman kuma ba a kiran su da wani laƙabi na musamman. Abubuwan da muke koyarwa da kuma imaninmu sun fito ne daga Littafi Mai Tsarki. Duk da haka, mutane da yawa a yau ba sa saurarar mu domin ba ma yin bukukuwan da suke so. Kuma abubuwan da muke koyarwa ba abubuwan da suke so su ji ba ne.

12. Kamar yadda Ibraniyawa 11:​1, 6 suka nuna, ta yaya za mu ƙarfafa bangaskiyarmu?

12 Mene ne zai taimaka mana mu riƙe bangaskiyarmu? Manzo Bulus ya gaya wa Kiristocin da suke Roma cewa: “Akan ba da gaskiya ta wurin jin saƙon ne, kuma akan ji saƙon ta wa’azi a kan Almasihu ne.” (Rom. 10:17) Saboda haka, ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki ne za mu iya ƙarfafa bangaskiyarmu, ba ta yin bukukuwan da Kalmar Allah ta haramta ba, ko da mutane suna son yin su. Wajibi ne mu ƙarfafa bangaskiyarmu ta wajen yin nazari sosai domin “in ba tare da bangaskiya ba, ba ya yiwuwa a faranta wa Allah rai.” (Karanta Ibraniyawa 11:​1, 6.) Saboda haka, ba sai mun ga alama ta musamman kafin mu san cewa muna bin addini na gaskiya ba. Yin nazarin Littafi Mai Tsarki zai tabbatar mana da cewa mun sami gaskiya kuma zai sa mu daina shakka.

(3) YESU YA ƘI BIN AL’ADUN YAHUDAWA DA YAWA

Mutane da yawa sun ƙi bin Yesu domin bai bi wasu al’adun Yahudawa ba. Ta yaya waɗannan dalilan za su iya sa mutane su ƙi saurarar mu a yau? (Ka duba sakin layi na 13) *

13. Mene ne ya sa mutane da yawa suka ƙi bin Yesu?

13 A zamanin Yesu, almajiran Yohanna mai baftisma sun yi mamaki da suka ga almajiran Yesu ba sa yin azumi. Yesu ya bayyana cewa almajiransa ba sa bukatar su yi azumi tun da yana tare da su. (Mat. 9:​14-17) Duk da haka, Farisiyawa da wasu maƙiyansa sun ƙi Yesu don bai bi al’adunsu ba. Sun yi fushi sa’ad da ya warkar da marasa lafiya a ranar Assabaci. (Mar. 3:​1-6; Yoh. 9:16) Suna da’awar bin dokar Assabaci, amma sun amince a yi kasuwanci a haikali. Sun yi fushi sosai sa’ad da Yesu ya nuna musu cewa abin da suke yi bai dace ba. (Mat. 21:​12, 13, 15) Mutane a majami’a a Nazarat sun yi fushi domin Yesu ya ba da misalai a tarihin Isra’ilawa da suka nuna cewa su masu son kai ne da marasa bangaskiya. (Luk. 4:​16, 25-30) Mutane da yawa sun ƙi saurarar Yesu domin bai yi abubuwan da suke zaton zai yi ba.​—Mat. 11:​16-19.

14. Me ya sa Yesu ya ce kada mu bi al’adun da ba su jitu da Kalmar Allah ba?

14 Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce? Jehobah ta wajen annabinsa Ishaya ya ce: “Mutanen nan fa, da baki kawai suke yi mini sujada, da magana kawai suke girmama ni, amma zuciyarsu suna nesa da ni, sujadarsu ba wani abu ba ne, sai umarnai ne da suka haddace.” (Isha. 29:13) Ya dace da Yesu ya ce kada mu bi al’adun da ba su jitu da koyarwar Littafi Mai Tsarki ba. Waɗanda suke ganin kamar dokokin ’yan Adam sun fi na Littafi Mai Tsarki sun ƙi Jehobah da kuma wanda ya aiko wato Almasihu.

15. Me ya sa mutane da yawa a yau ba sa son Shaidun Jehobah?

15 Shin muna fuskantar irin matsalar nan a yau? E. Mutane da yawa suna fushi domin Shaidun Jehobah ba sa yin bukukuwan da ba su jitu da Littafi Mai Tsarki ba, kamar tuna ranar haihuwa da kuma Kirsimati. Wasu kuma suna fushi domin Shaidun Jehobah ba sa saka hannu a bukukuwan da suke ɗaukaka ƙasa ko kuma irin jana’izar da ba ta jitu da Littafi Mai Tsarki ba. Mai yiwuwa waɗanda suke fushi da mu domin waɗannan dalilan sun gaskata cewa Allah yana amincewa da ibadarsu. Amma ba za su faranta masa rai ba idan sun fi son al’adun mutanen duniya a kan koyarwar da ke Littafi Mai Tsarki.​—Mar. 7:​7-9.

16. Me ya kamata mu yi kuma me za mu guje wa? (Zabura 119:​97, 113, 163-165)

16 Mene ne zai taimaka mana mu riƙe bangaskiyarmu? Muna bukatar mu so dokokin Jehobah da ƙa’idodinsa da dukan zuciyarmu. (Karanta Zabura 119:​97, 113, 163-165.) Idan muna ƙaunar Jehobah, za mu guji duk wata al’ada da za ta ɓata masa rai. Ba za mu ƙaunaci wani abu fiye da Jehobah ba.

(4) YESU BAI CANJA GWAMNATI BA

Mutane da yawa sun ƙi bin Yesu domin bai saka hannu a siyasa ba. Ta yaya waɗannan dalilan za su iya sa mutane su ƙi saurarar mu a yau? (Ka duba sakin layi na 17) *

17. Mene ne mutane da yawa a zamanin Yesu suke zato Almasihu zai yi?

17 Wasu a zamanin Yesu sun so a canja masu mulki a kansu nan da nan. Sun ɗauka Almasihu zai ’yantar da su daga gwamnatin Roma da ke takura musu. Amma da suka yi ƙoƙarin naɗa Yesu sarki, sai ya ƙi. (Yoh. 6:​14, 15) Firistoci da wasu kuma, sun ji tsoro cewa Yesu zai yi ƙoƙarin canja gwamnatin Roma. Suna ganin idan ya yi hakan, Romawan za su kwace ikon da suka ba firistocin. Yahudawa da yawa sun ƙi Yesu don sun mai da hankali sosai ga harkokin siyasa.

18. Waɗanne annabce-annabce game da Almasihu ne mutane da yawa suka yi watsi da su?

18 Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce? Ko da yake annabce-annabce da yawa sun nuna cewa daga baya Almasihu zai zama Jarumi mai nasara, wasu annabce-annabcen sun nuna cewa zai mutu don zunubanmu kafin hakan ya faru. (Isha. 53:​9, 12) To me ya sa Yahudawa suke da ra’ayin da bai dace ba game da Almasihu? Mutane da yawa a zamanin Yesu sun yi watsi da annabce-annabcen da suka nuna cewa ba za a magance matsalolinsu nan take ba.​—Yoh. 6:​26, 27.

19. Wane ra’ayin da bai dace ba ne ya sa mutane suke ƙin mu?

19 Shin muna fuskantar irin matsalar nan a yau? E. Mutane da yawa a yau suna ƙin mu domin ba ma saka hannu a siyasa. Suna so mu riƙa jefa ƙuri’a a lokacin zaɓe. Amma mun san cewa idan muka zaɓi shugaba ɗan Adam, mun ƙi Jehobah ke nan. (1 Sam. 8:​4-7) Mutane suna ganin cewa ya kamata mu gina asibitoci da makarantu kuma mu yi wasu ayyuka don tallafa wa yankunanmu. Ba sa son saurarar mu domin muna mai da hankali ga yin wa’azi maimakon ƙoƙarin magance matsalolin mutane nan da nan.

20. Kamar yadda Matiyu 7:​21-23 suka nuna, me ya kamata mu sa a gaba?

20 Mene ne zai taimaka mana mu riƙe bangaskiyarmu? (Karanta Matiyu 7:​21-23.) Abin da ya kamata mu sa a gaba shi ne aikin da Yesu ya ba mu. (Mat. 28:​19, 20) Bai kamata mu mai da hankali ga magance matsalolin duniya ba. Muna ƙaunar mutane kuma mun damu da su, amma hanya mafi kyau da za mu taimaka musu ita ce ta koya musu game da Mulkin Allah da kuma taimaka musu su ƙulla dangantaka mai kyau da shi.

21. Mene ne muke bukatar mu ƙuduri niyyar yi?

21 A wannan talifin, mun tattauna dalilai huɗu da suka sa mutane a ƙarni na farko suka ƙi Yesu. Kuma waɗannan dalilai a yau suna iya sa mutane su ƙi mu. Amma waɗannan abubuwan ne kaɗai ya kamata mu guje wa? A’a. A talifi na gaba, za mu tattauna ƙarin dalilai huɗu da suke sa mutane su ƙi mu. Bari mu ƙuduri niyyar ci gaba da bin Yesu da kuma ƙarfafa bangaskiyarmu!

WAƘA TA 56 Ka Riƙe Gaskiya

^ sakin layi na 5 Duk da cewa Yesu shi ne babban Malami da ya taɓa yin rayuwa a duniya, yawancin mutane a zamaninsa sun ƙi bin shi. Me ya sa? A wannan talifin, za mu tattauna dalilai huɗu da suka sa hakan. Za mu kuma ga abin da ya sa mutane da yawa ba sa saurarar mabiyan Yesu na gaskiya a yau. Mafi muhimmanci ma, za mu ga abin da ya sa ya kamata mu kasance da bangaskiya sosai don kada mu daina bin Yesu.

^ sakin layi na 60 BAYANI A KAN HOTUNA: Filibus yana ƙarfafa Nataniyel ya je ya sami Yesu.

^ sakin layi na 62 BAYANI A KAN HOTUNA: Yesu ya yi wa’azin labari mai daɗi.

^ sakin layi na 64 BAYANI A KAN HOTUNA: Yesu ya warkar da wani mutumin da hannunsa ya shanye.

^ sakin layi na 66 BAYANI A KAN HOTUNA: Yesu ya hau dutse shi kaɗai.