Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shawarar Littafi Mai Tsarki Tana da Amfani Har wa Yau?

Shawarar Littafi Mai Tsarki Tana da Amfani Har wa Yau?

WASU SUN CE A’A. Wani likita ya ƙwatanta bin shawarar Littafi Mai Tsarki da yin amfani da littafin kimiyya na tun 1920 wajen koyar da ɗaliban makaranta a yau. Mutanen da ba su yarda da Littafi Mai Tsarki ba suna iya tambayarka ko za ka iya bin littafin bayani na kwamfutar dā, wajen amfani da kwamfuta ta zamani. Har ila, wasu sun ce an daina yayin Littafi Mai Tsarki.

Me zai sa mutum ya bi shawarar tsohon littafin nan a zamanin nan da aka sami ci gaba a fasaha? Ban da haka, akwai shafuffukan intane da ke ɗauke da shawarwari da ɗumi-ɗuminsu. Ƙari ga haka, masana halayen ’yan Adam da ƙwararru a harkokin yau da kullum da kuma mawallafa suna ba da shawarwari a kafofin yaɗa labarai. Ana sayar da littattafai da ke nuna yadda mutane za su iya taimaka wa kansu kuma masu sayarwa suna biliyoyin daloli.

Tun da akwai hanyoyi da yawa da za mu iya samun shawarwari a cikin ’yan mintoci kaɗan, me zai sa mu damu da Littafi Mai Tsarki da aka rubuta kusan shekaru 2,000 da suka shige? Kamar yadda waɗanda suke ƙaryata Littafi Mai Tsarki suka faɗa, shin gaskiya ne bin shawarar Littafi Mai Tsarki yana kama da yin amfani da tsohon littafin kimiyya ko littafin bayani na kwamfutar dā? A’a. Hakan ba gaskiya ba ne. Ilimin kimiyya da fasaha suna canjawa a kullum, amma ainihin bukatun ’yan Adam ba sa canjawa. Har yanzu mutane suna son su yi rayuwa mai ma’ana, kwanciyar hankali da farin ciki, su zauna lafiya da iyalansu kuma su yi abokan kirki.

Littafi Mai Tsarki ya bayyana yadda za a iya cim ma hakan duk da cewa an daɗe da rubuta shi. Kuma ya ce Allah ne mawallafinsa. Yana yi mana ja-gora kuma yana taimaka mana mu jimre matsaloli. (2 Timotawus 3:​16, 17) Ƙari ga haka, yana ɗauke da gargaɗi da kuma shawarwari masu amfani a kullum! Littafi Mai Tsarki ya ce: “Maganar Allah mai-rai ce.”​—⁠Ibraniyawa 4:⁠12.

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce gaskiya ne? An daina yayinsa ne ko kuma shi ne littafin da ya fi muhimmanci? Ainihin dalilin da ya sa aka wallafa wannan Hasumiyar Tsaro wadda ita ce ta farko a cikin jerin mujallu na musamman, shi ne don ta taimaka maka ka san amsoshin waɗannan tambayoyin.