3 Zai Sa Ka Jimre da Matsaloli
Akwai wasu matsalolin ba za mu iya guje musu ba balle ma mu magance su. Alal misali, idan wani ɗan’uwanka ya rasu ko kuma kana fama da cuta mai tsanani, ba abin da za ka iya yi sai dai ka jimre kawai. Shin Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka a irin wannan yanayi mai wuya?
CUTA MAI TSANANI
Rose ta ce: “Ina da wata cuta da na gāda daga iyayena, don haka, kullum ina cikin ƙunci. Ba na jin daɗin rayuwa yadda ya kamata.” Abin da ya fi damunta shi ne, a wasu lokuta ba ta iya mai da hankali wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma abubuwan da suka shafi ibada. Amma furucin Yesu da ke Matta 19:26 ya taimaka mata sosai. Wurin ya ce: “Ga Allah dukan abu ya yiwu.” Rose ta fahimci cewa akwai hanyoyi da yawa na yin nazari. Da yake ciwon da take da shi yana sa a wasu lokuta ba ta iya nazarin Littafi Mai Tsarki, sai ta soma sauraron sautin Littafi Mai Tsarki da kuma littattafanmu. * Ta ce: “Da a ce ban yi hakan ba, da ban san yadda zan iya kyautata dangantakata da Jehobah ba.”
Furucin da ke 2 Korintiyawa 8:12 ya ƙarfafa Rose a lokacin da take baƙin ciki don ba ta iya yin ayyukan da take yi a dā. Ayar ta ce: “Gama idan nufi yana nan, abin karɓa ne gwargwadon abin da ke wurin mutum, ba gwargwadon abin da ba shi da shi” ba. Waɗannan kalaman sun tuna wa Rose cewa Allah yana jin daɗin abin da take yi domin tana yin iya ƙoƙarinta.
BAƘIN CIKI
Delphine da aka ambata a baya ta ce: “Bayan da ’yata mai shekara 18 ta rasu, na yi baƙin ciki sosai domin ban taɓa sanin zan iya ci gaba da rayuwa ba tare da ita ba. Amma abubuwa ba za su taɓa kasancewa yadda suke a dā ba.” Furucin da ke Zabura 94:19 ya ƙarfafa ta sosai. A wurin marubucin zabura ya ce wa Allah: “A cikin yawan tunani da ke cikina ta’aziyyarka suna ji wa raina daɗi.” Ta ce, “Na yi addu’a ga Jehobah ya taimaka mini in san abubuwan da zan riƙa yi da za su taimaka mini in daina baƙin ciki.”
Sai ta soma ba da kai don ta taimaka a hidimar Jehobah. Bayan wani lokaci, ta kwatanta kanta da kala da yara suke amfani da ita. Za a iya yin amfani da kala ko da ta karye. Haka ma yake da yanayinta, ko da yake tana ganin ta naƙasa amma ta fahimci cewa za ta iya taimaka ma wasu. Ta ce: “Na fahimci cewa idan na yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da shawarar da ke cikinsa don in ƙarfafa ɗalibaina, Jehobah yana amfani da wannan hanyar don ya ƙarfafa ni.” Sai ta rubuta sunayen wasu a Littafi Mai Tsarki da su ma suka yi baƙin ciki sosai. Kuma ta ce: “Babu shakka, dukansu sun yi addu’a sosai ga Jehobah.” Ƙari ga haka, ta fahimci cewa, “ba za mu iya samun taimako ba idan ba ma karanta Littafi Mai Tsarki.”
Yin nazarin Littafi Mai Tsarki ya taimaka wa Delphine ta fahimci wani abu kuma. Me ke nan? Ta fahimci muhimmancin mai da hankali ga abin da zai faru a nan gaba ba abin da ya riga ya faru ba. Begen da muke da shi a littafin Ayyukan Manzanni 24:15 ya ƙarfafa ta sosai. Wurin ya ce: “Za a yi tashin matattu, na masu adalci da na marasa adalci.” Shin tana da tabbaci cewa Jehobah zai tayar da ’yarta ne? Delphine da kanta ta ba da amsar: “Ina ganin ’yata a sabuwar duniya. Kuma ina da tabbaci cewa Jehobah zai tayar da ita a daidai lokacinsa. Ina ganin mu biyun a lambunmu a aljanna kuma ina ƙaunar ta kamar lokaci na farko da na gan ta.”
^ sakin layi na 4 Muna da irin waɗannan sautin a dandalinmu na jw.org.
Littafi Mai Tsarki zai ƙarfafa ka a lokacin da kake baƙin ciki