Aljanna a Duniya, Gaskiya Ce ko Kage?
Muna yawan ganin hotunan wurare masu kyau kamar “aljanna” a mujallu ko talabijin kuma hakan na sa mu yi marmarin zuwa hutu a wurin don mu manta da matsalolin rayuwa. Amma mun san cewa idan muka dawo gida, za mu tarar da matsalolin da muka bari.
Bugu da ƙari, mutane suna sha’awar aljanna sosai. Shi ya sa suke yawan tunani: ‘Shin “aljanna” tatsuniya ce kawai? Amma idan tatsuniya ce, me ya sa mutane suke marmarinta sosai? Za mu taɓa zama a cikinta da gaske kuwa?’
YADDA MUTANE SUKE ƊAUKAN ALJANNA
Mutane sun yi shekaru da yawa suna marmarin kasancewa cikin aljanna. Littafi Mai Tsarki ya ambata “gona daga wajen gabas, a cikin Adnin” kuma haka ne ya sa da yawa cikinsu suke wannan sha’awar. Amma me ya sa wannan lambun yake da ban sha’awa? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji Allah ya sa kowane itace mai kyan gani, mai amfani domin abinci, ya tsiro.” Wannan lambun wuri ne mai kyan gaske. Abu mafi ban sha’awa shi ne cewa ‘itacen rai yana tsakiyar gonar.’—Farawa 2:8, 9, Littafi Mai Tsarki.
Ƙari ga haka, littafin Farawa ya ambata koguna guda huɗu da ke fitowa daga lambun. Mun san biyu cikin waɗannan koguna a yau, wato kogin Tigris (Hiddekel) da kuma Yufiretis. (Farawa 2:10-14) Waɗannan koguna biyu suna gangarowa cikin Tekun Fasiya da kuma ƙasar Iraƙi wanda a dā ana kiranta Fasiya.
Babu shakka, a yankin Fasiya ne aljanna take a dā. Akwai wata kafet da aka adana a wata ma’ajiya da ake kira Philadelphia Museum of Art, a Pennsylvania, Amirka. A jikin kafet ɗin, an zana hoton lambu da aka shinge shi kuma akwai itatuwa da furanni masu kyau a cikinta. A yaren Fasiya, kalmar nan “lambun da aka shinge” yana nufin “aljanna,” kuma hoton da ke kafet ɗin yana nuni ne ga lambun Adnin da Littafi Mai Tsarki ya kwatanta.
Mutanen al’adu da kuma harsuna dabam-dabam a duniya suna faɗin labarin aljanna a duk faɗin duniya. Yayin da mutane suka soma zama a ɓangarori dabam-dabam na duniya, sun ci gaba da ba da labarin wannan aljannar. Kuma bayan ƙarnuka da yawa, sun gauraye wannan labarin da al’adu da kuma ƙage dabam-dabam. Har a zamaninmu, yawancin mutane suna kiran wurare masu kyau aljanna.
ANA NEMAN ALJANNA
Wasu masu bincike sun ce wai sun ga aljanna. Alal misali, wani janar a ƙasar Biritaniya mai suna Charles Gordon, ya ziyarci tsibirin Seychelles a shekara ta 1881. Kyaun lambun Vallée de Mai da ya burge shi sosai har ya ce ya ga lambun Adnin. A ƙarni na 15 kuma, wani mai tafiye-tafiye Ba’italiye mai suna Christopher Columbus ya yi tunanin cewa ya ga lambun Adnin sa’ad da ya je tsibirin Hispaniola da ake kira Jamhuriyar Dominika da kuma Haiti a yau.
Wani littafin tarihi mai suna Mapping Paradise yana ɗauke da bayanai a kan yankuna 190 na zamanin dā kuma da yawa cikinsu, an nuna hoton Adamu da Hauwa’u a lambun Adnin. Ɗaya daga cikinsu shi ne taswirar da wani mai suna Beatus a yankin Liébana ya rubuta a ƙarni na 13. An zana wani hoto mai siffar akwati da hoton aljanna a tsakiyarsa. Kuma da akwai koguna guda huɗu da ke fitowa daga aljannar, wato kogin “Tigris” da “Yufiretis” da “Indus” da kuma “Urdun.” An ce kogunan suna wakiltar yadda Kiristanci ya yaɗu a dukan duniya. Irin waɗannan hotunan sun nuna cewa har yanzu muna marmarin Aljanna ko da yake ba mu san ainihin yankin da yake tun asali ba.
An san wani marubuci da ya yi rayuwa a ƙarni na 17 mai suna John Milton da wani waƙa da ya rubuta mai jigo Paradise Lost (Aljannar da Aka Rasa). Ya ɗauko waƙar daga littafin Farawa a kan yadda Adamu ya yi zunubi kuma aka kore shi daga lambun Adnin. Ya yi magana a kan yadda mutane za su sake yin rayuwa har abada. Ya ce: “A lokacin, duniya za ta zama aljanna.” Daga baya, sai Milton ya sake rubuta wata mai jigo Paradise Regained (An Maido da Aljanna).
AN CANJA KOYARWAR
A bayyane yake cewa zancen kasancewa cikin aljanna ya zama wa mutane kashi a wuya. Amma me ya sa mutane da yawa suka soma kaucewa daga koyarwar? Littafin nan Mapping Paradise ya ce: “Limaman coci sun . . . yi watsi da wurin da asalin aljanna take.”
Ana koya wa yawancin mutane da ke zuwa coci cewa za su sami lada a sama, ba a aljanna a duniya ba. Duk da haka, Zabura 37:29 ta ce: ‘Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.’ Da yake ba ma cikin aljanna a yau, mene ne zai iya sa mu kasance da tabbaci cewa wannan alkawarin zai cika?
GASKIYA GAME DA ALJANNA A DUNIYA
Jehobah, Allahn da ya yi Aljanna a zamanin Adamu da Hauwa’u, ya yi alkawari cewa zai sake dawo da aljannar. Amma ta yaya zai yi haka? Ku tuna cewa Yesu ya ce mu riƙa addu’a muna cewa: ‘Mulkinka ya zo. Abin da kake so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda ake yinsa cikin sama.’ (Matta 6:10) Wannan Mulkin gwamnati ce kuma Yesu Kristi ne sarkinta. Mulkin zai cire dukan mulkokin ʼyan Adam. (Daniyel 2:44) Nufin Allah cewa duniya ta zama aljanna zai cika sa’ad da Yesu ya soma sarauta.
An hure annabi Ishaya ya bayyana yadda rayuwa za ta kasance a Aljanna. A lokacin dukan matsalolin da ke shafan ʼyan Adam za su zama labari. (Ishaya 11:6-9; 35:5-7; 65:21-23) Don Allah ku ɗan nemi lokaci ku karanta waɗannan ayoyi a cikin naku Littafi Mai Tsarki. Hakan zai sa ku kasance da tabbaci cewa Allah zai cika alkawuransa ga mutane masu adalci. Mutanen da za su zauna a cikin aljanna za su more abubuwan da Adamu ya rasa, wato alherin Allah da kuma jin daɗin rayuwa.—Ru’ya ta Yohanna 21:3.
Me ya sa za mu iya kasancewa da tabbaci cewa duniyar nan za ta zama Aljanna. Domin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sammai na Ubangiji ne; amma ya ba da duniya ga ’yan Adam.” Kuma begen yin rayuwa a duniya yana ɗaya daga cikin alkawuran da Allah wanda “ba ya iya yin ƙarya, ya alkawarta tun gaban madawwaman zamanu.” (Zabura 115:16; Titus 1:2) Babu shakka, Allah ya yi mana alkawari cikin Littafi Mai Tsarki cewa za mu yi rayuwa har abada a Aljanna!