Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
Shin Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka ka daina alhini?
Me za ka ce?
E
A’a
Wataƙila
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce
“Kuna zuba dukan alhininku [a wurin Allah], domin yana kula da ku.” (1 Bitrus 5:7) Littafi Mai Tsaki ya gaya mana cewa Allah zai iya taimaka mana mu magance yawan alhini.
Me kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?
Idan ka yi addu’a, za ka sami “salamar Allah” da za ta sa ka daina damuwa.—Filibiyawa 4:6, 7, Littafi Mai Tsarki.
Ƙari ga haka, karanta Kalmar Allah za ta taimaka maka ka jimre matsaloli.—Matta 11:28-30.
Shin za mu taɓa daina yin alhini kuwa?
Wasu sun yi imani cewa . . .wajibi ne mu yi alhini a matsayinmu na ’yan Adam, wasu kuma sun gaskata cewa mutum zai daina alhini ne bayan ya mutu. Mene ne ra’ayinka?
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce
Allah zai cire abubuwan da ke sa mu damuwa. “Mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba.”—Ru’ya ta Yohanna 21:4.
Me kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?
A Mulkin Allah, mutane za su yi rayuwa cikin kwanciyar hankali da kuma salama.—Ishaya 32:18.
Ba za mu tuna da abubuwan da ke sa mu damuwa ko baƙin ciki ba.—Ishaya 65:17.