Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TARIHI

Na Sadaukar da Kome don Hidimar Ubangiji

Na Sadaukar da Kome don Hidimar Ubangiji

“Idan ka je wa’azi kada ka dawo, don idan ka dawo zan kakkarya ƙafafunka.” Duk da abin da mahaifina ya gaya mini na yanke shawara cewa zan je kuma wannan shi ne lokaci na farko da na soma barin kome don hidimar Ubangiji. A lokacin, shekara na 16 ne.

TA YAYA na sami kaina a irin wannan yanayin? Bari in ba ku labarin. An haife ni a ranar 29 ga Yuli 1929, kuma na girma a wani ƙauye a yankin Bulacan a ƙasar Filifin. A lokacin mutane ba su da abin biyan bukata sosai kuma suna shan wahala don taɓarɓarewar tattalin arziki. Ƙari ga haka, an soma yaƙi a lokacin da nake matashi, sojojin Japan sun shigo ƙasar Filifin don su yaƙe ta. Da yake muna zama a ƙauye, ba a kawo hari a wurin ba. Kuma a lokacin ba mu da rediyo ko telibijin kuma ba a kawo jaridu a ƙauyen. Don haka, mutane ne suke ba mu labarin abin da ke faruwa.

Ni ne na biyu a cikin yara takwas, kuma da nake shekara takwas, iyayen mahaifiyata sun ɗauke ni in zauna da su. Ko da yake mu ’yan Katolika ne, kakana yakan saurari wa’azin wasu addinai kuma ya karɓi littattafan addinai da abokansa sukan ba shi. Na tuna cewa ya nuna min Littafi Mai Tsarki da kuma wasu littattafai a yaren Tagalog da ya ƙaryata koyarwar addinin ƙarya. Na ji daɗin karanta Littafi Mai Tsarkin, musamman ma Linjila guda huɗu, kuma karanta littafin ya sa in so yin koyi da misalin Yesu.​—⁠Yoh. 10:⁠27.

NA KOYI YADDA ZAN BI UBANGIJI

A shekara ta 1945, sojojin Japan sun bar ƙasar. Kuma a wannan lokacin ne iyayena suka ce in dawo gida, kuma kakana ya ce in koma.

Nan ba daɗewa ba bayan hakan a watan Disamba na shekara ta 1945, sai wasu Shaidun Jehobah suka zo ƙauyenmu daga garin Angat don su yi wa’azi. Ɗaya daga cikin waɗanda suka zo wa’azin ya bayyana mana abin da “kwanaki na ƙarshe” yake nufi. (2 Tim. 3:​1-5) Bayan haka, sai ya gayyace mu mu halarci taron da suke yi a ƙauyen da ke kusa da namu. Iyayena ba su halarci taron ba, amma ni na halarta. Kuma kusan mutane 20 ne suka halarta, a taron wasu sun yi tambayoyi da yawa game da Littafi Mai Tsarki.

Na so in bar taron don ban fahimci duk abin da ake faɗa a taron ba. Amma kafin in yi hakan, sai aka soma yin waƙa. Waƙar ta burge ni sosai kuma hakan ya sa ban tafi ba. Bayan an yi waƙa da addu’a, an gayyace dukanmu mu halarci taro a garin Angat da za a yi a ranar Lahadi.

Da yawa daga cikinmu mun yi tafiyar kilomita 8 don mu halarci taron a gidan wani ɗan’uwa mai suna Cruz. Kuma a cikin mutane kashi 50 da suka halarci taron akwai yara ƙanana da suke ta ba da amsa a kan batutuwan Littafi Mai Tsarki kuma hakan ya burge ni sosai. Da na ci gaba da halartan taro, sai wani ɗan’uwa majagaba mai suna Damian Santos da a dā magajin garin ne, ya gayyace ni in kwana a gidansa. Daddare mun yi hira sosai game da Littafi Mai Tsarki.

Da yawa daga cikinmu mun tsai da shawarar bauta wa Jehobah bayan mun koyi gaskiya game da Littafi Mai Tsarki. Shi ya sa da na halarci taro na ɗan lokaci, sai ’yan’uwan suka yi mana wannan tambayar “Kuna son a yi muku baftisma ne?” Na amsa na ce “E, ina so.” Na san cewa ina son in yi wa ‘Ubangiji Kristi’ hidima. (Kol. 3:24) Bayan haka, mun je wani kogi da ke kusa da wurin kuma aka yi mana baftisma a ranar 15 ga Fabrairu, 1946.

Da yake mu Kiristoci ne da suka yi baftisma, muna bukatar mu yi koyi da Yesu ta wajen yi wa mutane wa’azi. Amma hakan ya ɓata wa mahaifina rai kuma ya ce “Ka yi ƙarami ka riƙa wa’azi, ban da haka ma, baftismar da aka yi maka a kogi ba ya nufin ka zama mai wa’azi.” Na bayyana masa cewa Allah ya umurce mu mu yi wa’azi game da Mulkinsa. (Mat. 24:14) Bayan hakan, na ƙara cewa, “Ina bukatar in cika alkawarin da na yi wa Allah.” Wannan furucin ne ya sa mahaifina ya faɗi abin da na ambata ɗazu. Ya so ya hana ni yin wa’azi. Kuma wannan ne ya sa na sadaukar da kome don in bauta wa Jehobah.

Iyalin Cruz sun ce in zo in zauna da su a garin Angat. Ban da haka ma, sun ƙarfafa ni da kuma ’yarsu mai suna Nora mu soma yin hidimar majagaba. A ranar 1 ga Nuwamba 1947, mu biyun muka soma yin hidimar majagaba. Nora ta yi hidima a wani gari, ni kuma na ci gaba da yin wa’azi a garin Angat.

WATA DAMA NA YIN SADAUKARWA

Da na yi shekara uku ina hidimar majagaba, sai ɗan’uwa Earl Stewart ya zo daga ofishinmu da ke ƙasar don ya ba da jawabi a Angat kuma mutane fiye da 500 ne suka halarta. Ya ba da jawabin da Turanci kuma bayan ya kammala, sai na taƙaita jawabinsa a yaren Tagalog. Shekara bakwai kaɗai na yi a makaranta amma malamanmu suna yawan koyar da mu da Turanci. Wani abu kuma da ya taimaka mini in iya Turanci shi ne don ba mu da littattafai da yawa a yaren Tagalog. Don haka, na yi nazarin littattafai da yawa a Turanci. Kuma hakan ya taimaka mini in iya Turanci, har na fassara jawabin da ɗan’uwan ya bayar da kuma wasu jawabai.

A ranar da nake fassara jawabin Ɗan’uwa Stewart, ya gaya wa ikilisiyar cewa ana so a gayyaci majagaba ɗaya ko biyu don su je su yi hidima a Bethel. Za su riƙa taimaka da aikin kafin ’yan’uwa da suke hidima a ƙasar waje su dawo daga babban taro mai jigo Theocracy’s Increase da za a yi a birnin New York a Amirka a shekara ta 1950. Kuma ina cikin waɗanda aka gayyata. Hakan ya sa na bar inda na saba don in je in yi hidima a Bethel.

A ranar 19 ga Yuni 1950, na soma hidima a Bethel. Kuma girman Bethel ɗin eka biyu da rabi ne, wurin babban tsohon gida ne da aka dasa manyan itatuwa kewaye da shi. ’Yan’uwa maza marasa aure da yawa suna hidima a wurin. Da sassafe ina aiki a kicin, amma idan ƙarfe tara ya yi, ina zuwa aiki a wurin wanki da guga. Haka ma nake yi da rana. Bayan da ’yan’uwan suka dawo daga taron, na ci gaba da yin hidima a Bethel. Ina jera mujallu da za a tura ikilisiyoyi kuma nakan karɓi baki da dai sauransu, ina yin duk aikin da aka ce in yi.

NA BAR ƘASAR FILIFIN DON MAKARANTAR GILEAD

A shekara ta 1952, na yi farin ciki da aka gayyace ni da wasu ’yan’uwa guda shida daga ƙasar Filifin zuwa aji na 20 na Makarantar Gilead. Abubuwa da yawa da muka gani da yanayin ƙasar Amirka sun yi dabam da abin da muka saba. Sun bambanta da wanda na saba da shi a ƙauyenmu.

Tare da ’yan ajinmu a makarantar Gilead

Alal misali, sai da muka koyi yin amfani da wasu abubuwa da ba mu saba da su ba. Ban da haka ma, ƙasar ta bambanta da namu! Akwai wata safiya da na fita waje sai na ga ko’ina ya yi fari fata. Kuma wannan shi ne lokaci na farko da na ga dusar ƙanƙara. A lokacin ne na fahimci irin sanyin da ake yi a wurin.

Amma waɗannan abubuwan ba su dame ni ba da yake ina jin daɗin abubuwan da nake koya a makarantar Gilead. Malamanmu sun yi amfani da hanyoyin koyarwa masu kyau don mu fahimci abubuwan da ake koya mana. Mun koyi yin bincike sosai. Ban da haka, makarantar Gilead ya taimaka mini in kusaci Jehobah sosai.

Bayan na sauke karatu, sai aka tura ni yin hidima na ɗan lokaci a matsayin majagaba na musamman a garin Bronx a birnin New York. Don haka, a watan Yuli na shekara ta 1953 na sami damar halartar babban taro mai jigo, New World Society Assembly da aka yi a wannan garin. Bayan taron, an dawo da ni ƙasar Filifin don in yi hidima a wurin.

YADDA NA BAR RAYUWAR BIRNI

Amma ’yan’uwa a ofishinmu da ke ƙasar Filifin suka ce mini: “Yanzu za a tura ka yin hidimar mai kula da da’ira.” Wannan hidimar za ta ba ni damar yin koyi da abin da Yesu ya yi, wato, tafiya wurare dabam-dabam don ya taimaka wa tumakin Jehobah. (1 Bit. 2:21) An tura ni yin hidima a wani babban yankin da ya haɗa da Luzon wanda shi ne tsibiri mafi girma a ƙasar Filifin. Kuma a wurin, akwai yankunan Bulacan da Nueva Ecija da Tarlac da kuma Zambales. Kafin in iya zuwa wasu garurruka, sai na haye dutsen Sierra Madre. Babu motar hayar da ke zuwa wuraren nan, don haka nakan roƙi direbobin manyan motocin da ke kwaso itatuwa don in zauna a kan itatuwan da suka kwaso. A wasu lokuta suna yarda in bi su, amma bin waɗannan motocin ba abu mai sauƙi ba ne.

A yawancin ikilisiyoyin da nake zuwa ba ’yan’uwan da yawa kuma sababbi ne. Amma ’yan’uwan suna farin ciki idan na taimaka musu wajen tsara taro da kuma wa’azi.

Daga baya, an tura ni wata da’ira dabam da ya ƙunshi yankin Bicol gabaki ɗaya. Kuma yankin ya haɗa da ƙananan rukunoni da majagaba na musamman suke wa’azi. A wani gida da muka je, ba hayan da suke amfani da shi a bayan gidan shi ne wanda aka saka itatuwa guda biyu a saman ramin. Da na hau yin ba haya sai ni da itatuwan muka fāɗa cikin ramin. Ya ɗau lokaci kafin in iya wanke jikina kuma in soma ayyukana na ranar!

Da nake wannan hidimar ne na soma tunanin Nora wadda ta soma hidimar majagaba a yankin Bulacan. Kuma yanzu tana hidimar majagaba na musamman a birnin Dumaguete, sai na je na ziyarce ta. Bayan haka, muka ci gaba da rubuta wa juna wasiƙa na ɗan lokaci, kuma a shekara ta 1956 ne muka yi aure. Mun ziyarci ikilisiyar da ke tsibirin Rapu Rapu, a makon farko bayan aurenmu. A wurin sai da muka hau duwatsu kuma muka yi tafiya mai nisa sosai. Amma, mun yi farin cikin kai wa ’yan’uwa da suke wuraren nan ziyara a matsayin ma’aurata.

AN DAWO DA MU BETHEL

Bayan da muka yi kusan shekara huɗu muna hidimar masu kula da da’ira, sai aka tura mu yin hidima a ofishinmu da ke ƙasar. Kuma a watan Janairu 1960 ne muka soma yin hidima a Bethel. Na koyi abubuwa da yawa daga yin hidima tare da ’yan’uwa waɗanda suke ja-goranci a ƙungiyar Jehobah. Kuma Nora ta yi hidima a wurare dabam-dabam a Bethel.

Ina ba da jawabi a taron yanki, wani kuma yana fassara zuwa yaren Cebuano

A Bethel na sami damar ganin yadda mutane da yawa suka soma bauta wa Jehobah a ƙasar Filifin. A lokacin da nake matashi da na fara yin hidima a Bethel, akwai kusan masu shela 10,000 a ƙasar. Amma yanzu akwai masu shela fiye da 200,000 a ƙasar Filifin. Kuma akwai ’yan’uwa guda 435 da ke hidima a Bethel a ƙasar don su tallafa ma wa’azin da ake yi a wurin.

Daga baya wurin ya kasa mana don adadin mutane da suka soma bauta wa Jehobah ya ƙaru. Sai hukumar da ke kula da ayyukanmu suka ce mu nemi babban wuri. Ni da mai kula da sashen buga littattafai mun bi gida-gida a wurin da Bethel ɗin yake kuma a wurin akwai ’yan Caina da yawa, sai muka kama tambayar mutane ko akwai wanda yake son ya sayar da filinsa. Ba wanda ya yarda ya sayar mana. Sai wani mutumin ya ce mana: “’Yan Caina ba sa sayar da fili, sai dai su saya.”

Ina fassara jawabin Ɗan’uwa Albert Schroeder

Amma wata rana sai wani mutum da ke da gida a kusa da wurin ya tambaye mu ko za mu so mu sayi filinsa don zai ƙaura zuwa ƙasar Amirka. Kuma wannan ya sa wasu abubuwan ban mamaki suka faru. Wani maƙwabcinmu ma ya sayar mana filinsa kuma ya ƙarfafa sauran ma su yi hakan. Har ma mutumin da ya ce “’yan Caina ba sa sayar da fili” ya sayar mana da filinsa. Nan ba da daɗewa ba, ofishinmu ya girma har ya ninka na dā sau uku. Waɗannan abubuwa sun tabbatar mini cewa Jehobah ne ya sa hakan ya faru.

A shekara ta 1950, ni ne ƙarami a iyalin Bethel. Amma yanzu ni da matata ne muka fi tsufa. Kuma ba na yin da-na-sani cewa na bi ja-gorancin Ubangiji. Gaskiya ne cewa iyayena sun kore ni daga gidansu, amma Jehobah ya ba ni iyali mai girma na ’yan’uwa da suke bauta masa. Babu shakka, Jehobah ne yake biyan bukatunmu a duk hidimar da ya ce mu yi. Ni da matata Nora muna yi wa Jehobah godiya don yadda ya nuna mana alheri, kuma muna ƙarfafa wasu ma su gwada Jehobah don su ga yadda zai yi musu albarka.​—Mal. 3:10.

Yesu ya taɓa gayyatar wani mai karɓan haraji mai suna Matta Lawi ya ce masa: “Ka biyo ni.” Me ya yi? “Ya bar abu duka, ya tashi ya bi [Yesu].” (Luk. 5:​27, 28) Ni ma na sami damar yin hakan, kuma ina ƙarfafa wasu su yi hakan don su ga irin albarkar da za su samu idan suka yi hakan.

Ina farin cikin cewa ina cikin waɗanda suke taimaka wa don a yi wa’azi a Filifin