Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

“Ina da Bege ga Allah”

“Ina da Bege ga Allah”

“Adamu na ƙarshe ya zama ruhu mai-rayarwa.”​—1 KOR. 15:45.

WAƘOƘI: 151, 147

1-3. (a) Wace koyarwa ce muke bukata mu daɗa a cikin koyarwa masu muhimmanci da muka yi imani da su? (b) Me ya sa koyarwar tashin matattu take da muhimmanci? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

IDAN aka tambaye ka, ‘Waɗanne koyarwa masu muhimmanci ne ka yi imani da su?’ Me za ka ce? Babu shakka, za ka bayyana cewa Jehobah shi ne Mahalicci kuma shi ne yake ba da rai. Ban da haka ma, za ka faɗa cewa ka yi imani da Yesu Kristi wanda ya ba da ransa fansa. Ƙari ga haka, za ka bayyana cewa nan ba daɗewa ba, duniyar nan za ta zama aljanna kuma bayin Allah za su yi rayuwa a cikinta har abada. Amma za ka ambata cewa tashin matattu yana cikin koyarwa masu muhimmanci da ka yi imani da su?

2 Muna da dalilai masu kyau za su sa mu nuna cewa imaninmu na tashin matattu yana da muhimmanci ko da muna da begen tsira wa ƙunci mai girma da kuma yin rayuwa har abada a duniya. Manzo Bulus ya nuna muhimmancin tashin matattu shi ya sa ya ce: “Idan babu tashin matattu, Kristi kuma ba a tashe shi ba.” Da a ce ba a ta da Kristi daga mutuwa ba, da bai zama sarkinmu ba, kuma koyarwa game da sarautar Kristi za ta zama a banza. (Karanta 1 Korintiyawa 15:​12-19.) Amma muna da tabbaci cewa Yesu ya tashi daga mutuwa. Kuma don mun yi imani da hakan ne ya sa muka bambanta da Sadukiyawa waɗanda suka gaskata cewa ba za a ta da matattu ba. Ƙari ga haka, ko da ana zolayar mu, za mu riƙe imaninmu cewa za a ta da matattu.​—Mar. 12:18; A. M. 4:​2, 3; 17:32; 23:​6-8.

3 A lokacin da Bulus yake rubuta “ƙa’idodin farko na al’amarin Almasihu” ya ambata “koyarwa kan . . . tashin matattu.” (Ibran. 6:​1, 2, Littafi Mai Tsarki) Kuma ya nanata cewa ya yi imani da tashin matattu. (A. M. 24:​10, 15, 24, 25) Ko da yake koyarwar tashin matattu yana cikin “jigajigan farko na maganar Allah,” hakan ba ya nufin cewa koyarwa ce mai sauƙi. (Ibran. 5:​12, LMT) Me ya sa?

4. Waɗanne tambayoyi ne mutane suke yi game da tashin matattu?

4 Sa’ad da mutane suka soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki, yawancinsu suna karanta labaran mutane da aka ta da daga mutuwa kamar yadda aka ta da Li’azaru. Ban da haka ma, sun koyi cewa Ibrahim da Ayuba da Daniyel da sun kasance da tabbaci cewa a nan gaba za a ta da mutanen da suka mutu don su sake yin rayuwa. Amma wace amsa za ka bayar, idan aka ce ka ba da hujjar da ta nuna cewa za a cika alkawarin ta da matattu da aka yi shekaru da yawa da suka shige? Shin da gaske Littafi Mai Tsarki ya faɗa mana lokacin da za a ta da matattu? Sanin amsoshin nan suna da muhimmanci sosai don sun shafi bangaskiyarmu. Saboda haka, bari mu bincika hakan a Littafi Mai Tsarki.

TASHIN MATATTUN DA AKA YI ANNABCINSA TUN DĀ

5. Me za mu bincika da farko game da tashin matattu?

5 Muna iya yin tunani cewa za a ta da mutumin da bai daɗe da mutuwa ba. (Yoh. 11:11; A. M. 20:​9, 10) Amma za mu iya tabbata da alkawarin da aka yi cewa a nan gaba za ta da mutum da ya mutu shekaru da yawa? Shin za mu iya tabbata da irin wannan alkawarin, ko da mutumin da za a ta da bai daɗe da mutuwa ba ko kuma ya daɗe da yin hakan? Gaskiyar ita ce, shekaru da yawa da suka shige, an yi alkawari cewa za a ta da wani kuma hakan ya faru. Babu shakka, ka gaskata cewa ya faru. Amma ta yaya hakan ya faru? Kuma ta yaya hakan ya shafi tashin matattu da muke ɗokin za a yi a nan gaba?

6. Ta yaya Yesu ya cika annabcin Zabura 118?

6 Bari mu tattauna batun ta da matattu da aka ambata shekaru da yawa da suka shige. Littafin Zabura 118 da wataƙila Dauda ne ya rubuta ya ce: “Ka yi wo ceto, ya Ubangiji, yanzu muna roƙonka, . . . Mai-albarka ne shi mai-zuwa cikin sunan Ubangiji.” Babu shakka, za ka iya tunawa cewa mutane sun faɗi abin da ayar nan ta ce a lokacin da Yesu ya zo Urushalima a ranar 9 ga Nisan kafin mutuwarsa. (Zab. 118:​25, 26; Mat. 21:​7-9) Amma ta yaya Zabura 118 ta yi maganar wani da za a ta da shekaru da yawa a nan gaba? Ka yi la’akari da wani annabci da aka yi a Zaburar cewa: “Dutse wanda magina suka wulaƙanta Shi ne ya zama kan kusurwa.”​—Zab. 118:22.

“Magina” sun ƙi Almasihu (Ka duba sakin layi na 7)

7. Wane ƙulli ne Yahudawa suka yi wa Yesu?

7 “Magina” wato shugabannin Yahudawa sun ƙi Almasihu. Sun ƙi koyarwarsa kuma ba su amince cewa shi ne Kristi ba. Ƙari ga haka, Yahudawa da yawa sun ƙi shi kuma suka ƙulla a kashe shi. (Luk. 23:​18-23) Babu shakka, dukansu sun haɗa kai don su kashe Yesu.

An ta da Yesu daga mutuwa don ya zama “kan ƙusurwa” (Ka duba sakin layi na 8, 9)

8. Ta yaya Yesu zai zama “kan ƙusurwa”?

8 Idan an wulaƙantar da kuma kashe Yesu, ta yaya zai zama “kan kusurwa”? Kafin hakan ya faru dole ne sai an ta da shi daga mutuwa. Yesu da kansa ya faɗi hakan sa’ad da ya ba da kwatanci game da manoma da suka wulaƙanta mutanen da mai gona ya turo musu kamar yadda Isra’ilawa suka wulaƙanta annabawa da Allah ya turo musu. A ƙarshen misalin da ya bayar, ya ce mai gonar ya tura ɗansa tilo wanda zai gāje shi wurin manoman. Sun marabci ɗan kuwa? A’a. Manoman sun wulaƙanta ɗan har suka kashe. Yesu ya ɗauko wannan kwatancin daga annabcin da ke Zabura 118:22. (Luk. 20:​9-17) Manzo Bitrus ma ya yi ƙaulin wannan annabcin a lokacin da yake yi wa mahukunta da dattawa da marubuta Yahudawa da suka taru a Urushalima magana. Ya ce: ‘Yesu Kristi na Nazarat, wanda kuka [“kashe,” NW ], wanda Allah ya tashe shi daga matattu.’ Bayan haka, Bitrus ya bayyana cewa: Yesu “shi ne dutsen da ku magina kuka waƙala, wanda an maishe shi kan ƙusurwa.”​—A. M. 3:15; 4:​5-11; 1 Bit. 2:​5-7.

9. Mene ne Zabura 118:22 ta ce zai faru?

9 Shekaru da yawa da suka shige annabcin da ke Zabura 118:22 ya nuna cewa za a yi tashin matattu. Za a wulaƙanta Almasihu kuma a kashe shi, amma za a ta da shi don ya zama kan ƙusurwa. Yesu wanda aka ta da daga mutuwa shi ne kaɗai wanda aka ba da sunansa don mutane su “tsira.”​—A. M. 4:12; Afis. 1:20.

10. (a) Wane annabci ne aka yi a Zabura 16:10? (b) Mene ne ya tabbatar mana da cewa ba Dauda ba ne ya cika annabcin da ke Zabura 16:10?

10 Ka yi la’akari da wata aya kuma da ta nuna cewa a nan gaba za a ta da matattu. An rubuta wannan ayar ne wajen shekara dubu kafin hakan ya faru, kuma bincika wannan ayar zai sa ka ƙara kasancewa da tabbaci cewa za a ta da matattu, ko da yake an yi alkawarin da daɗewa. A Zabura ta 16 wadda wataƙila Dauda ne ya rubuta, ayar ta ce: “Ba za ka bar raina ga Lahira ba; ba kuwa za ka bar mai-tsarkinka shi ga ruɓa ba.” (Zab. 16:10) Dauda bai ce ba zai mutu ba ko kuma ba za a binne shi a kabari ba. Domin Littafi Mai Tsarki ya ce daga baya Dauda ya tsufa,.kuma ya mutu, wato “ya yi barci tare da ubanninsa, aka bizne shi cikin birnin Dauda.” (1 Sar. 2:​1, 10) Idan haka ne, to mene ne Zabura 16:10 take nufi?

11. Mene ne Bitrus ya ce game da Zabura 16:10?

11 An bayyana mana abin da ayar nan take nufi. Bayan fiye da shekara dubu da aka rubuta wannan zaburar, da kuma ’yan makonni bayan Yesu ya mutu, Bitrus ya yi wa Yahudawa da kuma baƙin da suka zama Kiristoci magana game da Zabura 16:10. (Karanta Ayyukan Manzanni 2:​29-32.) A jawabinsa, ya ambata cewa babu shakka Dauda ya mutu kuma an binne shi. Kuma mutanen da suka saurari jawabin sun san da hakan. Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki bai ce mutanen sun musanta abin da Bitrus ya faɗa game da Dauda cewa ya “rigaya ya ga wannan, zancen tashin” Almasihu daga mutuwa ba.

12. Ta yaya aka cika annabcin Zabura 16:​10, kuma me hakan ya tabbatar mana game da tashin matattu?

12 Bitrus ya tabbatar musu da abin da ya faɗa ta wajen yin ƙaulin abin da Dauda ya ce a Zabura 110:1. (Karanta Ayyukan Manzanni 2:​33-36.) Tattaunawar da Bitrus ya yi bisa abin da Littafi Mai Tsarki ya ce ya taimaka wa jama’ar su fahimci cewa Yesu shi ne “Ubangiji da Kristi.” Kuma wannan ya sa mutanen su gaskata cewa Zabura 16:10 ta cika ne a lokacin da aka ta da Yesu daga mutuwa. Ban da wannan ma, manzo Bulus ya yi amfani da abin da Bitrus ya ce sa’ad da yake yi wa Yahudawa a birnin Antakiya da ke Bisidiya wa’azi. Sun ji daɗin abin da ya faɗa kuma suka so ya ci gaba da koyar da su. (Karanta Ayyukan Manzanni 13:​32-37, 42.) Mu ma muna bukata mu yi farin ciki cewa annabce-annabcen da ke Littafi Mai Tsarki game da tashin matattu da za a yi a nan gaba zai faru, ko da yake an yi wannan annabcin ne shekaru da yawa da suka shige.

YAUSHE ZA A YI TASHIN MATATTU?

13. Wace tambaya ce wasu za su iya yi game da tashin matattu?

13 Muna samun ƙarfafa daga alkawarin tashin matattu da aka yi shekaru da yawa da suka shige. Amma wasu suna iya yin wannan tambayar: ‘Shin hakan yana nufin cewa ina bukatar in jira na tsawon lokaci kafin in ga mutanena da suka mutu? Yaushe ne za a yi tashin matattu da nake begensa?’ Yesu ya faɗa wa manzanninsa cewa akwai abubuwan da ba za su sani ba. Akwai bayani game da “zamanu da wokatai waɗanda Uba ya sanya a cikin nasa hukunci.” (A. M. 1:​6, 7; Yoh. 16:12) Amma hakan ba ya nufin cewa an bar mu a cikin duhu game da lokacin da za a yi tashin matattu.

14. Ta yaya tashiwar Yesu daga mutuwa ya bambanta da wanda aka yi dā?

14 Don ka fahimci batun, ka tuna da abin da Littafi Mai Tsarki ya annabta game da tashin matattu. Babu shakka, wanda ya fi muhimmanci a cikinsu shi ne yadda aka ta da Yesu daga mutuwa. Domin da a ce bai tashi ba, da babu wani a cikinmu da zai kasance da begen ganin ’yan’uwansa da suka mutu. Waɗanda aka ta da daga mutuwa kafin Yesu, kamar waɗanda Iliya da Elisha suka ta da sun sake mutuwa bayan wani lokaci kuma aka binne su. Amma, Yesu ya “tashi daga matattu [kuma] ba shi koma mutuwa ba; nan gaba mutuwa ba ta da sauran mulki a kansa.” Domin a sama zai yi rayuwa “har abada.”​—Rom. 6:9; R. Yoh. 1:​5, 18; Kol. 1:18; 1 Bit. 3:18.

15. Me ya sa yadda Yesu ya zama “nunan fari” yake da muhimmanci?

15 Ta da Yesu da aka yi zuwa sama a matsayin ruhu shi ne na farko da aka yi kuma shi ne ya fi muhimmanci. (A. M. 26:23) Amma ba shi kaɗai ba ne aka yi alkawarin za a ta da zuwa sama a matsayin ruhu ba. Yesu ya ba wa manzanninsa tabbacin cewa za su yi sarauta da shi a sama. (Luk. 22:​28-30) Amma sai sun mutu kafin su sami wannan ladan. Bayan haka, kamar yadda aka yi wa Kristi, za a ta da su da jiki na ruhu. Bulus ya rubuta cewa, ‘an ta da Almasihu daga matattu, shi ne ma nunan fari na waɗanda suka yi barci.’ Bulus ya ƙara da cewa za a ta da wasu ma su yi rayuwa a sama. Ya ce: ‘Amma kowanne bi da bi, Almasihu ne nunan fari, sa’an nan a lokacin bayyanuwarsa, waɗanda ke na Almasihu.’​—1 Kor. 15:​20, 23NW.

16. Ta yaya muka san lokacin da za a ta da mutanen da za su je sama?

16 Wannan ya bayyana mana lokacin da za a ta da waɗanda za su je sama. Hakan zai faru ne a “lokacin bayyanuwarsa.” Shaidun Jehobah sun yi imani cewa tun daga shekara ta 1914 ne muka soma rayuwa a “lokacin bayyanuwar” da Yesu ya yi alkawari, kuma haka Littafi Mai Tsarki ya faɗa. Ban da haka ma, mun yi imani cewa ƙarshen mugun zamanin nan ya kusa.

17, 18. Me zai faru da wasu shafaffu a lokacin bayyanuwar Kristi?

17 Littafi Mai Tsarki ya ba da ƙarin bayani game da waɗanda za a ta da zuwa sama. Ya ce: “Ba mu son ku da jahilci, ’yan’uwa, ga zancen waɗanda sun yi barci, . . . gama idan mun ba da gaskiya Yesu ya mutu ya tashi kuma, haka nan kuma waɗanda suka yi barci cikin Kristi, Allah zai kawo su tare da shi, . . . mu da muke da rai, wanzazzu kuma har [“bayyanuwar” NW ] Ubangiji, ba za mu riga waɗanda sun yi barci ba ko kaɗan. Gama Ubangiji da kansa za ya sauko daga sama, da kira mai-ƙarfi, . . . matattun da ke cikin Kristi za su fara tashi. Sa’an nan mu da muke da rai, mun wanzu, tare da su za a fyauce mu zuwa cikin gizagizai, mu tarbi Ubangiji a sararin sama: haka nan za mu zauna har abada tare da Ubangiji.”​—1 Tas. 4:​13-17.

18 An riga an soma tashin matattu na farko jim kaɗan bayan “bayyanuwar” Kristi. Amma shafaffun da suke raye a duniya a lokacin ƙunci mai girma, za a ɗauke su zuwa sama. Kuma waɗanda aka ɗauke su ba za su “yi barci” ba wato ba za su daɗe a mace ba. ‘Amma za a sāke su duka, farat ɗaya, da ƙyaftar ido, da ƙarar ƙaho na ƙarshe.’​—1 Kor. 15:​51, 52; Mat. 24:31.

19. Wane “tashi mafi kyau” ne za a yi a nan gaba?

19 A yau, Kiristoci da yawa masu aminci ba su da begen yin rayuwa a sama tare da Kristi. Amma, suna jiran ƙarshen mugun zamanin nan a “ranar Ubangiji.” Ba wanda ya san daidai lokacin da hakan zai faru, amma alamu sun nuna cewa lokacin ya yi kusa. (1 Tas. 5:​1-3) Bayan haka, za a yi wani tashin matattu da za a ta da mutanen da za su yi rayuwa a aljanna a duniya. Waɗanda aka ta da ba za su sake mutuwa ba amma za su zama kamiltattu su ci gaba da rayuwa. Hakika, wannan zai zama “tashi mafi kyau” da ya fi wanda aka yi a zamanin dā da “mata suka karɓi matattunsu,” amma daga baya suka sake mutuwa.​—Ibran. 11:35.

20. Me ya sa muke da tabbaci cewa za a yi tashin matattu bisa tsari?

20 Game da mutanen da za a ta da zuwa sama, Littafi Mai Tsarki ya ce za a ta da su “bi da bi.” (1 Kor. 15:​23, LMT) Sanin hakan ya sa mu fahimci cewa za a ta da matattu a duniya bi da bi. Babu shakka, abu ne da muke ɗokin gani. Shin waɗanda ba su daɗe da mutuwa ba ne za a ta da a kusan lokacin da Kristi zai soma sarautarsa na shekaru dubu don ’yan’uwansu su marabce su? Shin za a fara ta da mutane masu aminci da suka ja-goranci mutanen Allah a dā don su sa mutane su riƙa yin abubuwa bisa tsari? Mutanen da ba su taɓa bauta wa Jehobah ba fa? Yaushe da kuma a ina ne za a tashe su? Za mu iya yin tambayoyi da yawa. Amma, muna bukatar mu riƙa yin tunani game da waɗannan tambayoyin ne? Shin ba zai dace mu jira don mu gani da kanmu ba? Muna bukatar mu kasance da tabbaci cewa za mu yi farin ciki sosai sa’ad da muka ga yadda Jehobah yake magance matsalolin nan.

21. Wane bege kake da shi game da tashin matattu?

21 Kafin wannan lokacin, bari mu ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarmu ga Jehobah wanda ya yi amfani da Yesu don ya tabbatar mana cewa babu abin da zai hana Jehobah ta da bayinsa. (Yoh. 5:​28, 29; 11:23) Don ya tabbatar mana da cewa Jehobah zai ta da matattu, Yesu ya taɓa cewa Ibrahim da Ishaku da Yakubu “duka suna rayuwa gareshi.” (Luk. 20:​37, 38) Ƙari ga haka ma, muna da dalilai da yawa da zai sa mu ma mu faɗi abin da Bulus ya faɗa cewa: “Ina da bege ga Allah . . . za a yi tashin matattu.”​—A. M. 24:15.