Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Ta yaya aka ɗauke manzo Bulus zuwa “sama na uku” da kuma “aljanna”?​—2 Kor. 12:​2-4, New World Translation.

A littafin 2 Korintiyawa 12:​2, 3, Bulus ya ambata wani mutum da aka ɗauke zuwa “sama na uku.” Wane ne wannan mutumin? Sa’ad da Bulus yake rubuta wasiƙa ga ’yan’uwan da ke ikilisiyar Korinti, ya gaya musu cewa Allah yana amfani da shi a matsayin manzo. (2 Kor. 11:​5, 23) Bayan haka, ya ambata ‘abubuwan da Ubangiji Yesu Almasihu ya bayyana masa kamar a mafarki da kuma cikin ru’uya.’ Sa’ad da Bulus yake wannan magana bai ambata wasu ’yan’uwa ba. Saboda haka, Bulus yana nufin cewa shi ne mutumin da aka bayyana wa abubuwa ta mafarki da kuma ru’uya.​—2 Kor. 12:​1, 5.

A taƙaice dai, Bulus shi ne mutumin da aka ɗauke zuwa “sama na uku” da kuma “aljanna.” (2 Kor. 12:​2-4, NW ) Kalmar nan “ru’uya” da ya yi amfani da ita ta nuna cewa abin da ya bayyana zai faru ne a nan gaba.

Mene ne Bulus ya gani a “sama na uku”?

A Littafi Mai Tsarki, kalmar nan “sama” tana iya nufin sararin sama. (Far. 11:4; 27:28; Mat. 6:26) Amma kalmar tana iya nufin wani abu dabam. A wasu lokuta, kalmar tana nufin mulkin ’yan Adam. (Dan. 4:​20-22) A wasu kuma, tana nufin Mulkin Allah.​—R. Yar. 21:1.

Mene ne Bulus yake nufi sa’ad da ya ce ya ga ‘sama na uku’? A wasu lokuta ana ambata abu sau uku a Littafi Mai Tsarki don a nanata muhimmancin abun. (Isha. 6:3; Ezek. 21:27; R. Yar. 4:8) Kamar dai sa’ad da Bulus yake magana game da ‘sama na uku,’ yana bayyana wani mulki ne da ya fi kowanne kyau, wato mulkin da Yesu da kuma abokan sarautarsa 144,000 za su yi. (Ka duba littafin nan Insight on the Scriptures, Littafi na 1, shafi na 1059 da 1062.) Manzo Bitrus ya rubuta cewa bisa ga alkawarin Allah, muna jiran “sabon sammai.”​—2 Bit. 3:13.

“Aljanna” da Bulus ya ambata kuma fa?

Kalmar nan “aljanna” tana iya nufin abubuwa da yawa: (1) Da yake ’yan Adam sun yi rayuwa a aljanna a dā, tana iya nufin Aljanna a duniya da muke jira. (2) Tana iya nufin cikakkiyar salamar da mutanen Allah za su mora a sama da kuma duniya. (3) Tana iya nufin yanayi mai kyau a sama, wato “gonar Allah” da aka ambata a littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 2:7.​—Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli, 2015, shafi na 8 sakin layi na 8.

Wataƙila a littafin 2 Korintiyawa 12:​4, Bulus yana magana ne game da abubuwan nan uku.

A taƙaice:

“Sama na uku” da aka ambata a littafin 2 Korintiyawa 12:2 tana iya nufin Mulkin da Yesu Kristi da kuma abokan sarautarsa 144,000 za su yi, wato “sabon sammai.”​—2 Bit. 3:13.

Ana kiran sa “sama na uku” ne domin shi ne mulki mafi kyau da kuma mafi daraja.

“Aljanna” da Bulus ya gani a wahayi tana nufin (1) Aljannar da za a yi a duniya, (2) a wannan lokacin, mutanen Allah za su more cikakkiyar salama fiye da wanda suke mora a yau, kuma (3) yana nufin yanayi mai kyau da zai kasance a sama da kuma duniya.

Saboda haka, sabuwar duniya tana nufin sabuwar gwamnati da za ta yi mulki daga sama da kuma mutanen da za su bauta wa Jehobah a aljanna a duniya.