Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

“Masu Adalci Za Su Yi Farin Ciki” Don Abotarsu da Jehobah

“Masu Adalci Za Su Yi Farin Ciki” Don Abotarsu da Jehobah

WATA ’yar’uwa mai suna Diana ta ba shekara 80 baya. Kafin mijinta ya rasu, an kai shi gidan kula da tsofaffi domin yana fama da ciwon mantuwa. Ban da haka, yaranta biyu sun rasu kuma tana fama da cutar kansa na mama. Duk da haka, a duk lokacin da ’yan’uwa suka gan ta a taro ko kuma a wa’azi, sun lura cewa tana yawan farin ciki.

Wani ɗan’uwa mai suna John ya yi hidimar mai kula mai ziyara fiye da shekaru 43 kuma yana son hidimar sosai! Amma ya daina wannan hidimar don yana bukatar ya kula da wani danginsa marar lafiya. A duk lokacin da mutanen da suka san John tun dā suka haɗu da shi a babban taro ko kuma a taron yanki, sun lura cewa har yanzu yana farin ciki kamar yadda yake yi dā.

Mene ne ya taimaka wa Diana da John su riƙa farin ciki? Ta yaya mutumin da yake fama da matsaloli sosai zai iya yin farin ciki? Kuma ta yaya mutumin da ba ya yin hidimar da yake yi a dā zai yi farin ciki? Littafi Mai Tsarki ya taimaka mana mu fahimci wannan batun sa’ad da ya ce: “Dukan masu adalci za su yi murna, saboda abin da Ubangiji ya aikata.” (Zab. 64:​10, Littafi Mai Tsarki.) Za mu iya fahimtar wannan gaskiyar sosai idan muka san abin da zai sa mutum farin cikin da ke jurewa da wanda ba ya jurewa.

FARIN CIKIN DA KE JUREWA

Akwai abubuwa da yawa da ke sa mu farin ciki. Alal misali, mutanen da ke son juna kuma suke so su yi aure suna farin ciki. Ƙari ga haka, mutane na farin ciki idan suka yi juna biyu ko kuma suka sami gata a ƙungiyar Jehobah. Waɗannan abubuwan kyauta ce daga Jehobah. Allah ne ya kafa aure kuma shi ne ya sa ake haihuwa. Bugu da ƙari, shi yake ba Kiristoci ayyuka a ƙungiyarsa.​—Far. 2:​18, 22; Zab. 127:3; 1 Tim. 3:1.

Amma, wasu abubuwan da ke sa mutane farin ciki ba sa jurewa. Abin taƙaici, miji ko mata na iya yin zina ko kuma ɗaya cikinsu ya rasu. (Ezek. 24:18; Hos. 3:1) An yi wa wasu yara yankan zumunci ko kuma suna wa iyayensu rashin biyayya. Alal misali, yaran annabi Sama’ila ba su bauta wa Jehobah yadda yake so ba, Dauda kuma ya yi abin da ya jawo tashin hankali a cikin iyalinsa. (1 Sam. 8:​1-3; 2 Sam. 12:11) Idan irin waɗannan abubuwa suka faru, suna jawo baƙin ciki sosai.

Ban da haka ma, muna iya rasa gatanmu a ƙungiyar Jehobah. Wataƙila domin muna rashin lafiya ko don muna bukatar mu biya bukatun iyalinmu ko kuma don wasu canje-canje a ƙungiyar Jehobah. Mutane da yawa da suka rasa gatansu a ƙungiyar Jehobah sun ce hidimar da suke yi a dā ta sa su wadar zuci sosai.

Wannan ya nuna mana cewa irin waɗannan abubuwan da ke sa mutane farin ciki ba sa jurewa. Shin da akwai abin da ke sa mutum farin ciki duk da cewa yana fuskantar matsaloli? Hakika akwai, domin Sama’ila da kuma Dauda da dai sauransu sun kasance da farin ciki duk da cewa sun fuskanci matsaloli sosai.

FARIN CIKIN DA KE JUREWA

Yesu ya san abin da farin ciki na gaske yake nufi. Kafin ya zo duniya, ‘yana farin ciki a gaban’ Jehobah koyaushe. (K. Mag. 8:30) Amma da ya zo duniya, ya fuskanci matsaloli a wasu lokuta. Duk da haka, Yesu ya yi farin ciki domin yana yin nufin Ubansa. (Yoh. 4:34) Sa’ad da yake gab da mutuwa fa? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Saboda farin cikin da aka sa a gabansa, ya jimre wa [gungumen azaba].” (Ibran. 12:2) Don haka, za mu iya koyan abubuwa biyu daga abin da Yesu ya ce game da farin ciki na gaske.

Wata rana mabiyan Yesu guda 70 sun dawo daga wa’azin da ya tura su. Suna farin ciki domin sun yi mu’ujizai kuma sun fitar da aljanu. Sai Yesu ya ce musu: “Kada ku yi murna don aljanu sun ji ku, ku yi murna dai domin an rubuta sunayenku a sama.” (Luk. 10:​1-9, 17, 20) Hakika, samun amincewar Jehobah ta fi samun kowace irin gata muhimmanci. Ƙari ga haka, za ta fi sa mutum farin ciki.

Da akwai wani lokaci da Yesu yake yi wa jama’a magana. Sai wata Bayahudiya da ta ji daɗin abin da yake koyarwa ta ce matar da ta haife shi za ta yi murna sosai. Yesu ya ce mata: “I, amma albarka ta fi tabbata ga waɗanda suke jin kalmar Allah, suke kuma kiyaye ta!” (Luk. 11:​27, 28) Babu shakka, haifan yaro mai halaye masu kyau yana sa iyaye farin ciki. Amma abin da zai fi sa mu farin ciki shi ne yin biyayya ga Jehobah da kuma kasancewa da dangantaka mai kyau da shi.

Za mu yi farin ciki idan Jehobah ya amince da mu. Duk da cewa matsaloli na jawo baƙin ciki, amma ba za su hana mu yin farin ciki ba. Za mu yi farin ciki sosai idan muka kasance da aminci a lokacin da muke fuskantar matsaloli. (Rom. 5:​3-5) Ƙari ga haka, Jehobah yana ba waɗanda suka dogara gare shi ruhu mai tsarki kuma wannan ruhun na sa mu farin ciki. (Gal. 5:22) Hakan ya taimaka mana mu fahimci abin da ya sa Zabura 64:10 ya ce: “Dukan masu adalci za su yi murna, saboda abin da Ubangiji ya aikata.”

Mene ne ya taimaka wa John ya ci gaba da yin farin ciki?

Ƙari ga haka, hakan ya sa mu fahimci dalilin da ya sa Diana da John da aka ambata ɗazu suke farin ciki duk da cewa suna fuskantar matsaloli. Diana ta ce: “Na dogara ga Jehobah kamar yadda yaro yake dogara ga iyayensa.” Ta ƙara da cewa: “Jehobah ya albarkace ni da ƙarfin yin wa’azi a kai a kai kuma ina yin fara’a.” Me ya taimaka wa John ya yi farin ciki kuma ya ci gaba da ƙwazo a wa’azi duk da cewa ya daina hidimar mai kula mai ziyara? Ya ce: “Tun daga shekara ta 1998 da nake koyarwa a Makarantar Koyar da Masu Hidima, na yi nazarin Littafi Mai Tsarki fiye da dā.” Ya ƙara cewa: “Canje-canjen da ni da matata muka yi ya kasance da sauƙi domin a koyaushe muna yin dukan ayyukan da Jehobah ya ba mu, ba tare da yin da-na-sani ba.”

Mutane da yawa sun shaida abin da littafin Zabura 64:10 ya ce. Alal misali, an tura wasu ma’aurata da suka yi fiye da shekara 30 suna hidima a Bethel a Amirka, yin hidimar majagaba na musamman. Sun ce: “Kowa yana baƙin ciki sa’ad da ya rasa wani abin da yake so sosai, amma mutum ba zai yi baƙin ciki har abada ba.” Da zarar ma’auratan sun isa wurin da aka tura su hidima, sai suka soma wa’azi tare da ’yan’uwa a ikilisiyar. Ma’auratan sun ƙara da cewa: “Mun yi addu’a ga Jehobah game da abubuwan da muke bukata. Ganin yadda Jehobah ya amsa addu’armu ya ƙarfafa mu sosai kuma hakan ya sa mu farin ciki. Bayan isowar mu wurin da aka tura mu hidima, sai wasu a ikilisiyarmu suka soma yin hidimar majagaba. Ƙari ga haka, mun soma yin nazari da mutane biyu kuma suna samun ci gaba.”

ZA MU YI “FARIN CIKI HAR ABADA”

Gaskiyar ita ce, akwai wasu lokuta da mutum ba zai yi farin ciki ba. Amma Jehobah ya ƙarfafa mu da kalmomin da ke Zabura 64:10. A wasu lokuta muna iya yin sanyin gwiwa, amma muna bukatar mu kasance da tabbaci cewa “masu adalci” da suka kasance da aminci ga Jehobah duk da matsalar da suke fuskanta, za su yi farin ciki saboda abotarsu da shi. Ban da haka, muna ɗokin ganin lokacin da Jehobah zai cika alkawarinsa na kawo “sabon sama da sabuwar ƙasa.” A wannan lokacin, kowa zai zama kamili kuma mutanen Allah za su “yi murna da farin ciki har abada” saboda abubuwan da Jehobah ya halitta da kuma waɗanda ya yi tanadinsu.​—Isha. 65:​17, 18.

Ka yi tunanin abin da hakan yake nufi. Za mu kasance da ƙoshin lafiya kuma a duk lokacin da muka tashi daga barci, za mu cika da kuzari. Ko da wace irin matsala ce muke fuskanta, ba za ta sake kasancewa ba. An tabbatar mana cewa ‘ba za mu sāke tunawa da abubuwan dā ba, tunaninsu ma ba zai zo wa mutane ba.’ Za mu marabci mutanen da suka tashi daga matattu, kuma miliyoyin mutane za su ji kamar yadda iyayen yarinya ’yar shekara goma sha biyu da Yesu ya ta da daga mutuwa suka ji. Littafi Mai Tsarki ya ce iyayen sun yi “mamaki sosai.” (Mar. 5:42) A taƙaice dai, kowane mutum a duniya zai zama ‘mai adalci’ kuma ya yi farin ciki saboda abotarsa da Jehobah.