Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Matasa, Mahaliccinku Yana So Ku Yi Farin Ciki

Matasa, Mahaliccinku Yana So Ku Yi Farin Ciki

Shi “mai ƙosar da kai da abubuwa masu kyau ne.”​—ZAB. 103:5.

WAƘOƘI: 135, 39

1, 2. Me ya sa ya dace ku saurari Mahaliccinku sa’ad da kuke son ku kafa maƙasudai? (Ka duba hotunan da ke shafin nan.)

MUTANE da yawa sukan ba matasa shawara a kan abin da za su yi a rayuwa. Malamai da masu ba da shawara ko kuma wasu suna iya ƙarfafa ku ku je jami’a ko kuma ku biɗi sana’a da za ta sa ku yi arziki. Amma Jehobah yana so ku ɗauki wani mataki, yana so ku ƙoƙarta sosai a makaranta don ku biya bukatunku bayan kun sauke karatu. (Kol. 3:23) Ƙari ga haka, tun da yake za ku tsai da shawarar abin da za ku yi a rayuwa, ya ƙarfafa ku ku bi ƙa’idodin da za su taimaka muku kuma ku yi rayuwar da za ta sa ku faranta masa rai a waɗannan kwanaki na ƙarshe.​—Mat. 24:14.

2 Ban da haka, ku tuna cewa Jehobah ya san kome, ya san abin da zai faru a nan gaba, kuma ya san cewa ba da daɗewa ba zai halaka mugaye. (Isha. 46:10; Mat. 24:​3, 36) Jehobah ya san ku, ya san abin da zai sa ku farin ciki da abin da zai sa ku baƙin ciki. Saboda haka, ko da shawarar da ’yan Adam suka ba ku tana da kyau, ba za ta sa ku zama masu hikima ba idan ba ta da tushe daga Kalmar Allah.​—K. Mag. 19:21.

“BABU HIKIMA . . . WADDA ZA TA CI NASARA A KAN” JEHOBAH

3, 4. Ta yaya bin shawarar da ba ta dace ba ta shafi Adamu da Hauwa’u da yaransu?

3 Tun lokacin da Shaiɗan ya ruɗi Adamu da Hauwa’u ne aka soma ba da shawarar da ba ta dace ba. Shaiɗan mai girman kai ya gaya wa Hauwa’u cewa ita da mijinta za su yi farin ciki sosai idan suka yi zaɓin kansu. (Far. 3:​1-6) Amma, Shaiɗan ya yi hakan don son kansa ne. Yana son Adamu da Hauwa’u da ’ya’yansu su riƙa bauta masa maimakon Jehobah. Babu wani abin kirki da Shaiɗan ya yi wa mutane. Jehobah ne ya ba su kome da suke da shi. Ya sa su riƙa zama tare a matsayin mata da miji, ya saka su cikin lambu mai kyau kuma suna iya yin rayuwa har abada.

4 Abin baƙin ciki, Adamu da Hauwa’u suka yi wa Allah rashin biyayya kuma suka daina abokantaka da shi. Hakan ya jawo mugun sakamako. Kamar furannin da aka yanke, Adamu da Hauwa’u suka tsufa kuma daga baya suka mutu. Yaransu ma suna shan wahala don zunubinsu. (Rom. 5:12) Duk da haka, yawancin mutane ba sa yin biyayya ga Allah, don suna yin abin da suka ga dama. (Afis. 2:​1-3) Sakamakon da haka ya jawo ya nuna cewa “babu hikima . . . wadda za ta ci nasara a kan” Jehobah.​—K. Mag. 21:30.

5. Mene ne Allah ya tabbatar da cewa ’yan Adam za su yi, kuma yaya hakan ya zama gaskiya?

5 Duk da haka, Jehobah ya san cewa wasu mutane, har da matasa da yawa za su so su koya game da shi kuma su bauta masa. (Zab. 103:​17, 18; 110:3) Waɗannan matasa suna da daraja a wurin Allah! Kana cikin waɗannan matasan kuwa? Idan haka ne, babu shakka kana jin daɗin “abubuwa masu kyau” daga Allah waɗanda suke sa ka farin ciki sosai. (Karanta Zabura 103:5; K. Mag. 10:22) Kamar yadda za mu tattauna yanzu, waɗannan “abubuwa masu kyau” sun ƙunshi abubuwan da Allah ya tanadar don ku ƙarfafa dangantakarku da shi da yadda za ku sami abokan kirki da yadda za ku kafa maƙasudai masu kyau da kuma yadda za ku sami ’yanci na gaske.

JEHOBAH YANA TANADA ABUBUWAN DA KE ƘARFAFA ABOTARKU DA SHI

6. Me ya sa ya kamata mu riƙa yin amfani da abubuwan da za su ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah kuma yaya yake yi mana tanadin su?

6 Kuna bukatar abubuwan da za su ƙarfafa abotarku da Mahaliccinku, ba kamar dabobbi da ba sa bukatar yin hakan ba. (Mat. 4:4) Idan muka saurari Jehobah, za mu zama masu basira da hikima kuma mu riƙa yin farin ciki. Yesu ya ce: “Masu farin ciki ne waɗanda suka san cewa suna bukatar ƙulla dangantaka da Allah.” (Mat. 5:​3, New World Translation) Allah ya ba mu Littafi Mai Tsarki kuma yana yin amfani da “bawan nan mai aminci, mai hikima,” don ya tanadar da abubuwa da yawa da za su taimaka mana mu ƙarfafa dangantakarmu da shi. (Mat. 24:45) Ƙari ga haka, ya tanadar da abubuwa dabam-dabam da za su ƙarfafa mu!​—Isha. 65:​13, 14.

7. Ta yaya za ku amfana idan kuka yi amfani da abubuwan da Allah ya yi tanadin su don ku ƙarfafa dangantakarku da shi?

7 Abubuwan da Allah ke tanadar don mu ƙarfafa dangantakarmu da shi suna sa mu zama masu hikima da basira, kuma za su kāre mu a hanyoyi da yawa. (Karanta Karin Magana 2:​10-14.) Alal misali, waɗannan abubuwan za su taimaka muku ku san koyarwar da ba gaskiya ba ce, kamar koyarwa cewa babu Mahalicci. Kuma za su kāre ku daga koyarwar ƙarya cewa samun kuɗi da dukiya ne za su sa mutum farin ciki. Ƙari ga haka, za su taimaka muku ku guji sha’awoyi ko halaye da za su jawo muku matsala. Saboda haka, ku ci gaba da biɗan hikima da basira, ku riƙa ɗaukan su a matsayin abubuwa masu tamani! Yayin da kuke yin hakan, za ku ga cewa Jehobah yana ƙaunar ku kuma yana son ku yi rayuwar da za ta amfane ku.​—Zab. 34:8; Isha. 48:​17, 18.

8. Me ya sa ya dace ku kusaci Allah yanzu, kuma yaya hakan zai amfane ku a nan gaba?

8 Nan ba da daɗewa ba, Jehobah zai halaka mugaye, shi ne kaɗai zai iya kāre mu kuma ya yi mana tanadin abubuwan da muke bukata, har da abincin da za mu ci! (Hab. 3:​2, 12-19) Saboda haka, yanzu ne za ku kusaci Jehobah kuma ku dogara gare shi sosai. (2 Bit. 2:9) Idan kuka yi hakan, ko da mene ne ya faru, za ku ji kamar Dauda wanda ya ce: Ya Jehobah “kullum ina sane da kasancewarka, saboda kana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.”​—Zab. 16:8.

JEHOBAH YANA BA KU ABOKAN KIRKI

9. (a) Mene ne littafin Yohanna 6:44 ya ce Jehobah yake yi? (b) Me ya sa taron Shaidun Jehobah ya bambanta?

9 Jehobah yana jawo waɗanda yake so su bauta masa, kuma a hankali yana sa masu zuciyar kirki su soma bauta masa. (Karanta Yohanna 6:44.) A lokaci na farko da ka haɗu da wanda ba ya bauta wa Jehobah, mene ne ka san game da shi? Wataƙila ka san sunansa da siffarsa kawai. Amma ba haka yake ba sa’ad da ka haɗu da wanda yake bauta wa Jehobah. Ka riga ka san abubuwa da yawa game da shi, kuma ya san game da kai ko da mutumin ya fito daga wata ƙasa ko ƙabila, ko kuma al’adarsa dabam ce!

Jehobah yana son mu sami abokan kirki kuma mu kafa maƙasudai masu kyau (Ka duba sakin layi na 9-12)

10, 11. Mene ne mutanen Jehobah suke jin daɗinsa, kuma ta yaya hakan yake amfanar mu?

10 Alal misali, nan da nan kun fahimci juna cewa kuna “tsabtacciyar magana,” wato harshe mai tsarki. (Zaf. 3:9) Saboda haka, kun san abin da kuka yi imani da shi game da Allah da ƙa’idodinsa a batun ɗabi’a kuma kun san abin da zai faru a nan gaba, da dai sauransu. Ƙari ga haka, waɗannan abubuwa ne suke da muhimmanci ku sani game da mutum domin za su taimaka muku ku amince da juna. Ban da haka, za su sa ku ƙulla abota da za ta jure.

11 Saboda haka, idan kuna bauta wa Jehobah, za ku faɗi da gaske cewa kuna da abokan kirki. Kuma kuna da su a faɗin duniya, sai dai ba ku haɗu da su ba tukun! Ban da mutanen Jehobah, su waye ne suke jin daɗin wannan kyauta mai tamani?

JEHOBAH YANA SA KU KAFA MAƘASUDAI MASU KYAU

12. Waɗanne maƙasudai masu kyau ne za ku iya kafawa?

12 Karanta Mai-Wa’azi 11:9–12:1. Kun kafa maƙasudai da kuke ƙoƙari ku cim ma kuwa? Wataƙila kuna ƙoƙari ku riƙa karanta Littafi Mai Tsarki a kowace rana. Ko kuma kuna ƙoƙari ku kyautata kalaminku da yadda kuke koyarwa. Yaya kuke ji sa’ad da kuka lura cewa kuna samun ci gaba ko kuma mutane suka yaba muku don ƙoƙarin da kuke yi? Babu shakka, hakan yana sa ku farin ciki. Me ya sa? Domin kuna yin koyi da Yesu ta wajen yin abin da Jehobah yake so.​—Zab. 40:8; K. Mag. 27:11.

13. Ta yaya bauta wa Allah ya fi neman kayan duniya?

13 Idan kuka mai da hankali ga bautarku ga Jehobah, kuna yin aikin da zai sa ku farin ciki domin ba aikin banza ba ne. Manzo Bulus ya ce: ‘Ku tsaya daram, ku kafu, kullum kuna yalwata cikin aikin Ubangiji, domin kuwa kun san famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.’ (1 Kor. 15:58) Amma ba za ku yi farin ciki ba idan kuka mai da hankali ga yin arziki da kuma zama sanannu. Ko da kun yi nasara, za ku ji kamar kun yi hasarar wani abu. (Luk. 9:25) Mun koyi hakan daga misalin Sarki Sulemanu.​—Rom. 15:4.

14. Mene ne za ku iya koya daga biɗe-biɗen da Sulemanu ya yi?

14 Sulemanu wanda shi mutumi ne mai arziki da kuma iko sosai, ya ce: “Bari in sa raina cikin jin daɗi in san yadda jin daɗi yake.” (M. Wa. 2:​1-10) Sulemanu ya gina gidaje da gonaki da wurin shaƙatawa kuma ya yi dukan abin da ransa yake so. Waɗannan abubuwa sun sa Sulemanu farin ciki ne da gamsuwa? A’a. Shi da kansa ya gaya mana cewa: “Na yi tunani a kan dukan aikin hannuwana, . . . na ga wannan ma duka banza ne . . . Babu abin da yake da amfani.” (M. Wa. 2:11) Hakan ya koya mana darasi mai muhimmanci! Za ku yi amfani da wannan darasin a rayuwarku kuwa?

15. Me ya sa nuna bangaskiya yake da muhimmanci, kamar yadda aka ambata a littafin Zabura 32:​8, yaya yin hakan zai taimaka muku?

15 Jehobah ba ya son ku koyi darasi bayan kun sha wahala sosai. Hakika, kuna bukatar ku kasance da bangaskiya don ku yi wa Allah biyayya kuma ku sa bautarsa a kan gaba. Hakan yana da muhimmanci kuma ba za ku taɓa yin da-na-sani ba. Ƙari ga haka, Jehobah ba zai taɓa manta “da ƙaunar da kuka nuna masa” ba. (Ibran. 6:10) Saboda haka, ku yi aiki tuƙuru don ku ƙarfafa bangaskiyarku. Hakan zai sa ku yi zaɓi mai kyau kuma za ku ga cewa Jehobah yana son ku yi nasara a rayuwa.​—Karanta Zabura 32:8.

ALLAH YANA SA KU SAMI ’YANCI NA GASKE

16. Me ya sa za mu ɗauki samun ’yanci da tamani kuma mu yi amfani da shi a hanyar da ta dace?

16 Manzo Bulus ya ce: ‘A inda ruhun Ubangiji yake kuwa a nan ’yanci yake.’ (2 Kor. 3:17) Jehobah yana son ’yanci kuma ya halicce ku da son samun ’yanci. Amma yana son ku yi amfani da ’yancinku a hanya mai kyau kuma hakan zai kāre ku. Wataƙila kun san matasan da suke kallon hotunan batsa ko kuma waɗanda suke lalata. Kun san wasu da suka sa ransu cikin kasada ta wurin yin wasanni masu haɗari ko kuma masu shan mugayen ƙwayoyi da yin maye. Da farko, zai zama kamar suna jin daɗin rayuwa, amma sau da yawa yin waɗannan abubuwan sukan jawo munanan sakamako, kamar kamuwa da cuta ko mutuwa ko kuma halin ya zama musu jiki. (Gal. 6:​7, 8) Hakika, ‘ ’yancinsu’ ba na gaske ba ne.​—Tit. 3:3.

17, 18. (a) Ta yaya yin biyayya ga Allah yake sa mu sami ’yanci? (b) Ta yaya Adamu da Hauwa’u suka fi mutane a yau samun ’yanci?

17 Mutane nawa ne ka sani cewa sun soma rashin lafiya domin suna bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki? Hakika, yin biyayya ga Jehobah zai sa mu sami ƙoshin lafiya da ’yanci. (Zab. 19:​7-11) Ban da haka, idan kuka yi amfani da ’yancinku a hanyar da ta dace, wato kuna bin dokokin Allah da ƙa’idodinsa, kuna nuna wa iyayenku da Allah cewa kun manyanta kuma za su ba ku ƙarin ’yanci. Allah ya yi mana alkawari cewa nan ba da daɗewa ba, zai ba bayinsa masu aminci ’yanci. Littafi Mai Tsarki ya kira wannan ’yancin, “ ’yancin nan na ɗaukakar da za a yi wa ’ya’yan Allah.”​—Rom. 8:21.

18 Irin wannan ’yanci ne Adamu da Hauwa’u suka ji daɗinsa. Dokoki nawa ne Allah ya ba su a lambun Adnin? Ɗaya ce kawai. Ya ce kada su ci ’ya’yan wani itace. (Far. 2:​9, 17) Kana ganin cewa dokar da Allah ya ba su tana da wuya sosai? Ko kaɗan! Ka gwada dokar da dokoki masu yawa da ’yan Adam suke kafawa a yau kuma suke tilasta wa mutane su bi.

19. A waɗanne hanyoyi ne ake koya mana mu zama masu ’yanci?

19 Jehobah yana nuna hikima a yadda yake bi da bayinsa. Maimakon ya kafa mana dokoki masu yawa, yana haƙuri da mu sa’ad da yake koya mana mu riƙa nuna ƙauna. Yana son mu riƙa bin ƙa’idodinsa kuma mu tsani mugunta. (Rom. 12:9) A huɗubar da Yesu ya yi a kan dutse, ya taimaka mana mu fahimci dalilan da suke sa mutane yin mugunta. (Mat. 5:​27, 28) Da yake Kristi ne Sarkin Mulkin Allah, zai ci gaba da koyar da mu a aljanna don mu kasance da ra’ayinsa game da abin da ke daidai da abin da ba daidai ba. (Ibran. 1:9) Yesu zai sa mu zama kamiltattu a jikinmu da kuma tunaninmu. Ka yi tunanin yadda rayuwa za ta kasance sa’ad da babu abin da zai motsa mu mu yi zunubi kuma ba za mu sha wahala domin ajizancinmu ba. A ƙarshe kuma za mu sami ‘ ’yancin nan na ɗaukaka’ da Jehobah ya yi mana alkawarinsa.

20. (a) Ta yaya Jehobah yake amfani da ’yancinsa? (b) Ta yaya za mu amfana idan muka bi misalin Allah?

20 Babu shakka a aljanna, ’yancinmu zai kasance da iyaka. Me ya sa? Domin za mu bukaci nuna ƙauna ga Allah da kuma mutane. Kuma yin hakan zai nuna cewa muna yin koyi da Jehobah. Ko da yake Jehobah yana da ’yanci da babu iyaka, ya zaɓi ya riƙa nuna ƙauna a duk abubuwan da yake yi har da yadda yake bi da mutane. (1 Yoh. 4:​7, 8) Saboda haka, ya dace a ce za mu sami ’yanci na gaske idan muka yi koyi da Allah.

21. (a) Mene ne ra’ayin Dauda game da Jehobah? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

21 Kuna nuna godiya don dukan “abubuwa masu kyau” da Jehobah ya yi muku kuwa? Ya tanadar muku da abokan kirki da abubuwan da za su ƙarfafa dangantakarku da shi, da maƙasudai masu kyau da kuma begen samun ’yanci na gaske a nan gaba. (Zab. 103:5) Wataƙila kuna ji yadda Dauda ya ji sa’ad da ya furta abin da ke Zabura 16:11 cewa: “Kana nuna mini hanya, hanyar da za ta kai ga rai, kasancewarka tare da ni, cikakken farin ciki ne, zama a hannun damanka, jin daɗi ne har abada.” A talifi na gaba, za mu tattauna wasu koyarwa masu muhimmanci da ke Zabura ta 16. Hakan zai taimaka muku ku san yadda za ku yi rayuwa mai gamsarwa.