Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

”Sai Mun Haɗu a Aljanna!”

”Sai Mun Haɗu a Aljanna!”

“Za ka zauna tare da ni a Firdausi.”​—LUK. 23:43.

WAƘOƘI: 145, 139

1, 2. Waɗanne ra’ayoyi ne mutane suke da shi game da aljanna?

A WANI taron yanki da aka yi a birnin Seoul a Koriya, mutanen da suka zo taron sun cika filin wasan maƙil. Sa’ad da aka gama taron, ’yan’uwan da ke ƙasar suka taru suna gaya wa ’yan’uwa da suka zo daga wasu ƙasashe cewa: “Sai mun haɗu a Aljanna!” A ganinka, wace aljanna ce suke nufi?

2 Mutane suna da ra’ayi dabam-dabam game da aljanna. Wasu sun ce aljanna ƙage ce. Wasu kuma sun ce kana cikin aljanna a duk lokacin da kake murna da wadar zuci. A ganinka, me Aljanna take nufi? Kana begen yin rayuwa a cikinta kuwa?

3. A wane lokaci ne aka fara ambata aljanna a Littafi Mai Tsarki?

3 Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da aljannar da Adamu da Hauwa’u suka zauna a ciki da kuma wadda za a yi a nan gaba. A cikin littafin Farawa ne aka fara ambata Aljanna. Nassosin Ibrananci ya yi magana game da lambun Adnin. Adnin yana nufin “Jin Daɗi,” kuma babu shakka, akwai jin daɗi sosai a lambun. Akwai isashen abinci da mahalli mai kyau da kuma zaman lafiya tsakanin mutane da dabbobi.​—Far. 1:​29-31.

4. Me ya sa za mu iya kiran lambun Adnin aljanna?

4 Kalmar nan pa·raʹdei·sos a Helenanci ne aka fassara zuwa “lambu” a Ibrananci. Littafin nan Cyclopædia wanda M’Clintock da Strong suka rubuta ya ce idan Bahelene ya ji kalmar nan pa·raʹdei·sos, abin da ke shigowa zuciyarsa shi ne lambu mai kyau sosai wanda babu wani abu da zai iya jawo tashin hankali a ciki. Ƙari ga haka, lambu ne mai itatuwa masu ba da ’ya’ya iri-iri kuma yana da kogin da akwai ciyayi a gaɓarsa wanda barewa da garken tumaki ke ci.​—Ka Gwada da Farawa 2:​15, 16.

5, 6. Me ya sa ba ma cikin Aljanna a yau, kuma wace tambaya ce wasu suke yi?

5 A irin wannan aljannar ce Allah ya saka Adamu da Hauwa’u, amma ba su dawwama a ciki ba. Me ya sa? Domin sun ƙarya dokar Allah. A sakamako, suka rasa Aljanna kuma suka hana ’ya’yansu ma zama a ciki. (Far. 3:​23, 24) Amma ko da yake an kori mutane daga lambun, akwai alama cewa ba a halaka lambun ba sai a lokacin da aka yi ambaliyar ruwa a zamanin Nuhu.

6 Wasu suna iya yin mamaki cewa, ‘Zai taɓa yiwu maza da mata da kuma yara su ji daɗin rayuwa a cikin Aljanna a duniyar nan kuwa?’ Idan kana begen yin rayuwa a Aljanna tare da ’yan’uwanka, me ya tabbatar maka da cewa hakan zai faru? Za ka iya bayyana dalilan da suka sa ka tabbata cewa za mu zauna a Aljanna a nan gaba?

ABUBUWAN DA SUKA NUNA CEWA ZA A YI ALJANNA

7, 8. (a) Wane alkawari ne Allah ya yi wa Ibrahim? (b) Wane tunani ne wataƙila alkawarin ya sa Ibrahim ya yi?

7 A cikin littafin da Mahaliccin wannan Aljannar ya sa a rubuta ne za mu iya samun amsoshin tambayoyin nan. Ku yi la’akari da abin da Allah ya gaya wa abokinsa Ibrahim. Ya gaya masa cewa zai sa yaransa su yi yawa kamar “yashin bakin teku.” Sai Jehobah ya yi masa alkawari cewa: ‘Ta wurin zuriyarka, dukan kabilun duniya za su roƙa wa kansu albarka, saboda ka yi biyayya ga abin da na ce maka ka yi.’ (Far. 22:​17, 18) Allah ya maimaita wa ’ya’yan Ibrahim da jikokinsa wannan alkawarin.​—Karanta Farawa 26:4; 28:14.

8 Babu alama a cikin Littafi Mai Tsarki da ta nuna cewa Ibrahim ya yi zato cewa Aljannar da ’yan Adam za su mora tana sama. Saboda haka, sa’ad da Allah ya ce “dukan kabilun duniya” za su sami albarka, babu shakka, Ibrahim ya yi tunanin samun albarka a duniya. Allah ne ya yi alkawarin nan kuma hakan ya nuna cewa “dukan kabilun duniya” za su sami canjin yanayi. Amma da akwai wasu abubuwa a cikin Kalmar Allah da suka tabbatar mana da hakan kuwa?

9, 10. Wane alkawari ne ya sa mu kasance da tabbaci cewa duniya za ta zama aljanna?

9 Dauda wanda shi zuriyar Ibrahim ne ya ambata abin da zai faru a nan gaba sa’ad da aka halaka “mugaye” da “masu aikata abubuwa marasa kyau.” Wane sakamako ne hakan zai kawo? Littafi Mai Tsarki ya ce “mugaye za su ɓace.” (Zab. 37:​1, 2, 10) Kuma “masu sauƙin kai za su gāji ƙasar, su sami farin cikinsu cikin salama a yalwace.” Dauda ya kuma annabta cewa: ‘Masu adalci za su gāji ƙasar, su zauna a ciki har abada.’ (Zab. 37:​11, 29; 2 Sam. 23:2) Yaya kake ganin hakan ya shafi mutanen da suka so su yi nufin Allah? Babu shakka, sun kasance da tabbaci cewa lokaci na zuwa da adalai kaɗai za su yi rayuwa a duniya, kuma duniya za ta sake zama aljanna kamar lambun Adnin.

10 Da shigewar lokaci, yawancin Isra’ilawa da suke da’awar bauta wa Jehobah sun daina bauta masa. Saboda haka, Allah ya ƙyale Babiloniyawa su ci su a yaƙi kuma su kai su zaman bauta. (2 Tar. 36:​15-21; Irm. 4:​22-27) Duk da haka, annabawan Allah sun annabta cewa Isra’ilawa za su koma ƙasarsu bayan shekara 70. Waɗannan annabcin sun cika, amma sun shafe mu a yau. Yayin da muke tattauna wasu cikinsu, ku yi la’akari da yadda suka sa mu kasance da tabbaci cewa duniyar nan za ta zama aljanna.

11. Ta yaya Ishaya 11:​6-9 ya cika, amma wace tambaya ce ba mu amsa ba tukun?

11 Karanta Ishaya 11:​6-9. Allah ya yi alkawari ta annabi Ishaya cewa sa’ad da Isra’ilawa suka koma ƙasarsu, za su zauna cikin kwanciyar rai. Babu kowa da zai riƙa jin tsoron dabbobi ko mutane. Matasa da tsofaffi za su sami tsaro. Shin hakan ya tuna maka da yanayin da Adamu da Hauwa’u suke ciki a lambun Adnin? (Isha. 51:3) Ishaya ya kuma ce dukan duniya, ba Isra’ila kaɗai ba za ta “cika da sanin Yahweh kamar yadda ruwaye sun cika teku.” A wane lokaci ne hakan zai faru?

12. (a) Wace albarka ce mutanen da suka dawo daga bauta a Babila suka samu? (b) Me ya nuna cewa Ishaya 35:​5-10 zai sake cika?

12 Karanta Ishaya 35:​5-10. Ishaya ya sake nanata cewa dabbobi ko mutane ba za su yi wa Isra’ilawa da za su dawo barazana ba. Ƙasarsu za ta ba da ’ya’ya sosai domin za su sami isashen ruwa yadda lambun Adnin yake a dā. (Far. 2:​10-14; Irm. 31:12) A zamanin Isra’ilawa ne kaɗai annabcin zai cika? Ku lura cewa annabcin ya ce Allah zai warkar da makafi da kurame da kuma guragu. Amma hakan bai faru da Isra’ilawan da suka dawo daga Babila ba. Saboda haka, Allah na alkawari ne cewa zai warkar da mutane a nan gaba.

13, 14. Ta yaya Isra’ilawa da aka kai zaman bauta a Babila suka ga cikar littafin Ishaya 65:​21-23, amma wane sashen annabcin ne bai cika ba tukun? (Ka duba hoton da ke shafi na 3.)

13 Karanta Ishaya 65:​21-23. Sa’ad da Isra’ilawa suka dawo daga zaman bauta, ba su tarar da gidaje masu kyau ko kuma gonaki da inabin da aka nome ba. Amma daga baya, yanayin ya canja domin Jehobah ya albarkace su. Babu shakka, sun yi farin ciki sa’ad da suka gina gidaje kuma suka zauna a ciki! Suka shuka gonaki kuma suka ci amfaninta!

14 Ka lura cewa annabcin ya ce shekarunmu za su zama kamar na “itace.” Za a taɓa yin lokacin da shekarunmu za su zama kamar na “itace” kuwa? Akwai wasu itatuwa da suke yin dubban shekaru. Dole ne ’yan Adam su kasance da ƙoshin lafiya kafin su dawwama haka. Kuma idan sun sami zarafin yin rayuwa a irin yanayin da Ishaya ya annabta, hakan zai zama abin ban sha’awa sosai! Babu shakka, annabcin zai cika!

Ta yaya alkawarin da Yesu ya yi game da Aljanna zai cika? (Ka duba sakin layi na 15, 16)

15. Waɗanne alkawura ne aka ambata a littafin Ishaya?

15 Ka yi tunanin yadda alkawuran nan suka nuna cewa za mu yi rayuwa a aljanna a nan gaba. Duniya gabaki ɗaya za ta cika da mutanen da Jehobah ya yi musu albarka. Dabbobi da mugayen mutane ba za su jawo wa kowa la’ani ba. Za a warkar da makafi da kurame da kuma guragu. Mutane za su gina gidaje kuma za su ci abinci masu gina jiki. Shekarun mutane za su fi na itatuwa yawa. Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana da cewa alkawuran nan za su cika a nan gaba. Amma wasu suna iya cewa annabcin nan ba ya nufin cewa za a yi aljanna a duniya. Idan wani ya gaya maka haka, wace amsa ce za ka iya ba shi? Mene ne zai iya tabbatar maka da cewa za mu zauna a aljanna a nan gaba? Yesu wanda shi ne mutum mafi girma da ya taɓa rayuwa a duniyar nan ya ba mu ƙwarin gwiwa.

ZA KA ZAUNA TARE DA NI A ALJANNA

16, 17. A wane yanayi ne Yesu ya yi magana game da Aljanna?

16 Maƙiyan Yesu sun hukunta shi kuma sun kashe shi duk da cewa bai yi wani laifi ba. Sa’ad da Yesu yake gab da mutuwa, ɗaya daga cikin masu laifi da aka kashe su tare ya ce masa: “Ya Yesu, ka tuna da ni sa’ad da ka shiga mulkinka!” (Luk. 23:​39-42) Alkawarin da Yesu ya yi wa wannan mutumin ya shafi rayuwarmu duka. Yana littafin Luka 23:43. Wasu marubuta sun saka waƙafi kafin kalmar nan “yau.” Ga misali: “Hakika ina gaya maka, yau ɗin nan za ka zauna tare da ni a Aljanna.” Akwai ra’ayi dabam-dabam game da wurin da ya dace a saka waƙafin. Amma me Yesu yake nufi sa’ad da ya ce “yau”?

17 Ana amfani da waƙafi a harsuna da yawa a yau don a bayyana wani abu, amma ba a yawan yin amfani da waƙafi a rubuce-rubucen Helenanci na dā. Saboda haka, hakan yana iya sa mu yi tambaya cewa: Yesu yana so ya ce ne, “Ina gaya maka, a yau za ka kasance tare da ni a Firdausi?” Ko kuwa yana nufin, “Ina gaya maka a yau, za ka kasance tare da ni a Firdausi”? Mafassara suna iya saka waƙafi kafin kalmar nan “yau,” ko kuma a bayanta daidai da abin da suke ganin Yesu yake nufi. Kuma za ka ga hakan cikin wasu fassarar Littafi Mai Tsarki na zamani.

18, 19. Mene ne zai taimaka mana mu fahimci abin da furucin Yesu yake nufi?

18 Amma ku tuna cewa Yesu ya taɓa gaya wa mabiyansa cewa: “Ɗan Mutum zai yi kwana uku, dare da rana a cikin ƙasa.” Ya ƙara da cewa: “Za a ba da Ɗan Mutum ga hannun mutane, za su kuma kashe shi. A rana ta uku kuma za a tashe shi.” (Mat. 12:40; 16:21; 17:​22, 23; Mar. 10:34) Manzo Bitrus ya tabbatar da faruwar wannan abu. (A. M. 10:​39, 40) Babu shakka, Yesu bai je Aljanna a ranar da shi da wannan mai laifin suka mutu ba. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Yesu ya yi ’yan kwanaki a “kabari,” har sai lokacin da Allah ya tashe shi daga mutuwa.​—A. M. 2:​31, 32. *

19 Waɗannan bayanan sun nuna cewa Yesu ya yi amfani da furucin nan: “Hakika ina gaya maka yau” don ya gabatar da maganarsa. Ana yawan gabatar da magana a wannan hanyar a zamanin dā har ma a zamanin Musa. Akwai lokacin da Musa ya ce: “Waɗannan kalmomin da nake umarce ku a yau, za ku sa su a cikin zuciyarku.”​—M. Sha. 6:6; 7:11; 8:​1, 19; 30:15.

20. Me ya taimaka mana mu fahimci furucin Yesu?

20 Wani mafassarin Littafi Mai Tsarki a Gabas ta Tsakiya ya ce: “Kalma mai muhimmanci a wannan furucin ita ce ‘yau,’ kuma ya kamata a fassara ta haka, ‘Hakika ina gaya maka yau ɗin nan, za ka zauna tare da ni a Aljanna.’ A ranar ce ya yi alkawarin kuma a nan gaba ne zai cika. Haka mutane a ƙasashen gabas suke magana kuma tana nufin cewa a ranar ce aka yi alkawarin kuma lallai zai cika.” Ga yadda aka fassara ayar a juyin Syriac na ƙarni na biyar: “Amin, ina gaya maka yau cewa za ka kasance tare da ni a Lambun Adnin.” Ya kamata wannan alkawarin ya ƙarfafa mu.

21. Mene ne bai faru da mutumin nan mai laifi ba, kuma me ya sa?

21 Sa’ad da Yesu ya yi wa mutumin alkawarin shigan Aljanna, ba yin rayuwa a sama yake nufi ba. Me ya tabbatar mana da hakan? Dalili na farko shi ne, mutumin bai san cewa Yesu ya yi alkawari da almajiransa masu aminci cewa za su yi mulki da shi a sama ba. (Luk. 22:29) Ƙari ga haka, mutumin bai ma yi baftisma ba. (Yoh. 3:​3-6, 12) Hakan ya nuna cewa aljanna a duniya ce Yesu yake nufi. Wasu shekaru bayan haka, manzo Bulus ya faɗi wani wahayin da ya gani na wani mutum da “aka ɗauke shi zuwa” aljanna. (2 Kor. 12:​1-4) Ko da yake an zaɓi Bulus da sauran manzannin su yi rayuwa a sama, amma yana magana ne game da aljanna a nan gaba. * Duniya za ta zama aljanna kuwa? Kai ma za ka yi rayuwa a wurin?

ABIN DA ZA KA YI ZATONSA

22, 23. Wane bege ne muke da shi?

22 Ka lura cewa Dauda ya yi begen lokacin da ‘masu adalci za su gāji ƙasar.’ (Zab. 37:29; 2 Bit. 3:13) Dauda yana magana ne game da lokacin da mutane a duniya za su riƙa bin ƙa’idodin Allah. Annabcin da ke littafin Ishaya 65:22 ya ce: “Kamar yadda yawan shekarun itace suke, haka yawan shekarun mutanena za su kasance.” Hakan yana nufin cewa mutane za su yi rayuwa na dubban shekaru. Kana ganin hakan zai faru? Ƙwarai kuwa. Allah ya yi alkawari a littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:​1-4 cewa zai albarkaci mutane kuma zai cire “mutuwa.”

23 Abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da aljanna yana da sauƙin fahimta. Adamu da Hauwa’u sun rasa gatan yin rayuwa a Aljannar a lambun Adnin, amma duniya za ta zama aljanna a nan gaba. Allah ya yi alkawari cewa zai albarkaci mutane a duniya. Dauda ya ce masu adalci za su gāji duniya su zauna a cikinta har abada. Annabcin da ke littafin Ishaya ya sa mu san abubuwan da za mu mora a Aljanna. Amma a wane lokaci ne hakan zai faru? A lokacin da alkawarin da Yesu ya yi wa mai laifin ya cika. Kai ma za ka iya kasancewa a wannan Aljannar. A lokacin, furucin da aka yi wa ’yan’uwan nan a Koriya zai cika: “Sai mun haɗu a Aljanna!”

^ sakin layi na 18 Wani Farfesa mai suna Marvin Pate ya ce: “Mutane sun daɗe suna yin imani cewa ‘yau’ da aka ambata a ayar tana nufin sa’o’i ashirin da huɗu. Amma matsalar wannan ra’ayin ita ce ta saɓa wa wasu koyarwar Littafi Mai Tsarki da suka nuna cewa an fara binne Yesu a kabari sa’ad da ya mutu (Mat. 12:40; A. M. 2:31; Rom. 10:7) bayan haka, sai ya koma sama.”

^ sakin layi na 21 Ka duba “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” a wannan mujallar.