Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Iyaye, Ku Taimaka wa Yaranku Su Kasance da Bangaskiya

Iyaye, Ku Taimaka wa Yaranku Su Kasance da Bangaskiya

“Samari da yan mata . . . Bari su yabi sunan Ubangiji.”—ZAB. 148:12, 13.

WAƘOƘI: 88, 115

1, 2. (a) Wace matsala ce iyaye suke fuskanta, kuma ta yaya za su iya magance wannan matsalar? (b) Waɗanne abubuwa huɗu ne za mu tattauna?

WASU ma’aurata a ƙasar Faransa sun ce: “Mun yi imani da Jehobah, amma hakan ba ya nufin cewa yaranmu za su yi imani da shi. Bangaskiya ba abin da ake gāda ba ne. A hankali ne yaranmu za su zama masu bangaskiya.” Wani ɗan’uwa ɗan Ostareliya ya rubuta cewa: “Taimaka wa yaranka su kasance da bangaskiya sosai ba cin tuwo ba ne. Kana bukatar ka yi amfani da hanyoyi dabam-dabam don ka koyar da su. Kana iya ganin cewa ka amsa tambayar ɗanka amma daga baya za ka ga cewa ya sake yi maka irin wannan tambayar! Amsar da ka ba wa ɗanka yau ba zai gamshe shi a nan gaba ba. Don haka, kana bukatar ka riƙa tattauna wasu batutuwa a kai a kai.”

2 Idan kuna da yara, shin kuna ji kamar ba za ku iya rainon yaranku kuma ku taimaka musu ku kasance da bangaskiya ba? Hakika, ba za ku iya yin hakan da kanku ba! (Irm. 10:23) Dole ne ku dogara ga Jehobah don ya yi muku ja-gora idan kuna so ku yi nasara a yin hakan. Bari mu tattauna abubuwa guda huɗu da za su iya taimaka muku ku sa yaranku su kasance da bangaskiya: (1) Ku san yaranku sosai. (2) Ku mai da hankali ga abubuwan da kuke koya musu. (3) Ku yi amfani da misalan da suka dace. (4) Ku kasance da haƙuri kuma ku riƙa addu’a.

KU SAN YARANKU SOSAI

3. Ta yaya iyaye za su iya bin misalin Yesu sa’ad da suke koyar da yaransu?

3 A yawancin lokaci, Yesu yana tambayar mabiyansa abin da suka yi imani da shi. (Mat. 16:13-15) Za ku iya bin misalinsa. A lokacin da kuke hira da yaranku ko kuma kuke yin wasu ayyuka tare ne ya dace ku yi musu tambayoyi game da ra’ayinsu a kan wani batu da kuma abin da suke shakkar sa. Wani ɗan’uwa ɗan shekara 15 a ƙasar Ostareliya ya rubuta cewa: “Mahaifina yakan tattauna da ni a kan abin da na yi imani da shi kuma yana taimaka mini in yi tunani sosai game da hakan. Yakan tambaye ni: ‘Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce?’ ‘Shin ka gaskata da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce?’ ‘Me ya sa ka gaskata da hakan?’ Mahaifina yana yi mini waɗannan tambayoyin ne don yana so na ba da amsa bisa ga yadda na fahimci batun ba abin da suka gaya mini ba. Yayin da nake girma, ina bukatar in ba da amsoshi masu ma’ana.”

4. Me ya sa yake da kyau ku ɗauki tambayar da yaranku suka yi da muhimmanci? Ka ba da misali.

4 Ku kasance da haƙuri idan yaranku ba su tabbata da koyarwarku ba. Ku taimaka musu su sami amsoshin tambayoyinsu. Wani mahaifi ya ce: “Ku riƙa ɗaukan tambayoyin da yaranku suka yi da muhimmanci. Kada ku ƙi amsa tambayar don kuna ganin bai kamata ku tattauna da su game da batun ba. “ Ya kamata ku ɗauka cewa ɗanku yana so ya fahimci batun shi ya sa yake tambaya. Yesu ma ya yi tambayoyi masu muhimmanci sa’ad da yake ɗan shekara 12. (Karanta Luka 2:46.) Wani yaro ɗan shekara 15 a ƙasar Denmark ya ce: “Iyayena ba su yi fushi ba sa’ad da na gaya musu cewa ina shakkar ko addinin da muke bi ne addini na gaskiya. Maimakon haka, sun damu da ni sosai. Kuma sun yi amfani da Littafi Mai Tsarki wajen amsa dukan tambayoyina.”

5. Mene ne iyaye za su ci gaba da yi ko da yaransu suna da bangaskiya?

5 Ku san tunanin yaranku da ra’ayinsu da kuma damuwarsu. Kada ku yi tunanin cewa yaranku suna da bangaskiya don suna halartar taron Kirista da kuma fita wa’azi tare da ku. A kowane lokaci, ku riƙa tattaunawa da su game da Jehobah. Ku yi addu’a a madadin yaranku da kuma tare da su. Ku san gwajin da suke fuskanta kuma ku taimaka musu su yi tsayayya da hakan.

KU MAI DA HANKALI GA ABUBUWAN DA KUKE KOYA MUSU

6. Ta yaya iyaye suke amfana idan suka koya wa yaransu abubuwan da ke zuciyarsu?

6 Yesu yana ƙaunar Jehobah da Kalmarsa da kuma mutane, shi ya sa yake koyar da mutane a hanyar da ke ratsa zuciyarsu. (Luk. 24:32; Yoh. 7:46) Hakazalika, iyaye za su iya ratsa zuciyar yaransu idan suna ƙaunar Jehobah da kuma Kalmarsa. (Karanta Kubawar Shari’a 6:5-8; Luka 6:45.) Don haka, iyaye suna bukatar su riƙa nazarin Littafi Mai Tsarki sosai kuma su yi amfani da abubuwan da muke da su na bincike. Ku so abubuwa game da halitta kuma ku riƙa karanta littattafanmu da suke tattauna wannan batun. (Mat. 6:26, 28) Idan kuka yi hakan, za ku samu ƙarin ilimi da kuma gode wa Jehobah don abubuwan da ya halitta. Ƙari ga haka, zai taimaka muku ku koyar da yaranku da kyau.—Luk. 6:40.

7, 8. Mene ne iyaye za su iya yi idan suna nazarin Littafi Mai Tsarki sosai? Ka ba da misali.

7 Idan iyaye suna nazarin Littafi Mai Tsarki sosai, hakan zai sa su tattauna abubuwan da suke koya da yaransu. Ku riƙa tattaunawa da yaranku a kowane lokaci ba kawai sa’ad da kuke yin shirin zuwa taron Kirista ko kuma ibada ta iyali ba. Kada ku tilasta musu amma ku yi hakan cikin natsuwa da kuma farin ciki. Abin da wasu ma’aurata a ƙasar Amirka suka yi ke nan. Suna tattaunawa game da Jehobah sa’ad da suka ga wani abu mai kyau ko kuma suke cin abinci mai daɗi. Ma’auratan sun ce: “Mun tuna wa yaranmu cewa dukan abubuwan da Jehobah ya yi mana tanadinsu, ya yi ne don yana ƙaunarmu.” Wasu ma’aurata a Afirka ta Kudu suna son tattaunawa da yaransu mata biyu game da halitta sa’ad da suke gyaran lambu. Sukan gaya musu yadda iri yake tsirowa. Iyayen sun ce: “Muna iya ƙoƙarinmu don mu sa yaranmu su daraja rai da kuma abubuwa masu ban al’ajabi game da halitta.”

8 Wani mahaifi a ƙasar Ostareliya ya kai ɗansa ɗan shekara 10 ma’adanar kayayyakin tarihi don ya taimaka masa ya ƙara gaskatawa da Allah da kuma halitta. Mahaifin ya ce: “Mun ga wasu irin halittu na ruwa masu kama da dodon koɗi. Wasu kuma sun yi kama da kyankyasai amma suna da ƙafafu masu yawa. Amma babu waɗannan halittun kuma. Wani abin mamaki shi ne halittun suna da kyau kuma suna da wuyar fahimta kamar waɗanda muke gani a yau. Da a ce gaskiya ne cewa ƙananan halittu suna juyawa su zama manyan halittu kuma wai mutane sun samo asali ne daga gwaggon biri, me ya sa waɗannan halittu na dā suke da wuyar fahimta? Na koyi darasi sosai daga waɗannan halittun kuma na koya wa ɗana hakan.”

KU YI AMFANI DA MISALAN DA SUKA DACE

9. Me ya sa yin amfani da misalai yake da amfani, kuma wane misali ne wata mahaifiya ta yi amfani da shi?

9 Yesu yana yawan amfani da misalai sa’ad da yake koyarwa don ya ratsa zuciyar masu sauraronsa kuma ya sa su tunani. (Mat. 13:34, 35) Saboda da haka, iyaye ku yi amfani da misalan da za su sa yaranku tunani sosai. Abin da wata mahaifiya a ƙasar Japan ta yi ke nan. Tana da yara maza biyu, ɗaya shekararsa takwas ɗayan kuma goma. Ta yi amfani da wani misali don ta koya musu cewa yadda Jehobah ya tsara wannan duniyar ya nuna cewa yana ƙaunar mu. Ta ba su madara da sukari da kuma ganyen shayi. Sai ta gaya musu su yi mata shayi. Ta ce: “Sun mai da hankali sosai wajen yin shayin. Da na tambaye su me ya sa suka yi hakan, sai suka ce saboda suna so su yi shayin yadda zan ji daɗinsa. Sai na bayyana musu cewa hakazalika, Allah ya yi amfani da abubuwa dabam-dabam don ya yi wannan duniyar a hanyar da za mu iya jin daɗinta.” Yaran sun ji daɗin wannan misalin kuma ba za su taɓa mantawa da misalin ba!

Za ku iya yin amfani da misalai masu sauƙi don ku sa yaranku su ƙara gaskatawa da Allah da kuma halitta (Ka duba sakin layi na 10)

10, 11. (a) Waɗanne misalai ne za ku iya yin amfani da su don ku sa yaranku su ƙarfafa bangaskiyarsu ga Allah? (Ka duba hoton da ke shafi na 28.) (b) Waɗanne misalai ne kuka taɓa yin amfani da su?

10 Za ku iya yin amfani da takardar bayani shirin abinci don ku taimaka wa yaranku su gaskata da Allah. Ta yaya? Kuna iya yin kek ko kuma ƙuliƙuli tare da yaranku. Bayan haka, sai ku bayyana musu amfanin bin takardar da ke bayyana yadda za a yi waɗannan abubuwan. Ƙari ga haka, ku ba wa yaranku ’ya’yan itacen nan da ake kira aful kuma ku tambaye su: “Shin kun san cewa akwai wani tsari da wannan aful yake bi kafin ya girma?” Daga nan sai ku raba aful ɗin gida biyu kuma ku ba su ƙwayarsa. Kuna iya gaya musu cewa aful ɗin yana farawa ne daga ƙwayar kuma tsarin da yake bi ba irin wanda aka “rubuta” a cikin takarda ba ne. Kuna iya tambayar su: “Idan akwai wanda ya rubuta takardar bayanin yadda za a yi kek ko ƙuliƙuli, wane ne ya tsara yadda aful yake girma?” Idan kuna da yaran da suka yi girma, kuna iya cewa tsarin da bishiyar aful ɗin take bi shi ne matattarin sanin asalin halitta, wato DNA. Kuna iya duba wasu misalan da ke cikin shafuffuka 10 zuwa 20 na ƙasidar nan The Origin of Life—Five Questions Worth Asking, tare da yaranku.

11 Iyaye da yawa sun jin daɗin tattauna jerin talifofin nan “Was It Designed?” da ke cikin Awake! da yaransu. Idan yaransu ƙanana ne, iyayen za su iya bayyana musu abin da ke cikin talifin a hanyar da zai yi wa yaransu sauƙin fahimta. Alal misali, wasu ma’aurata a ƙasar Denmark sun kwatanta jiragen sama da tsuntsaye. Sun ce: “Jiragen sama suna kama da tsuntsaye sosai. Amma jiragen sama suna yin ƙwai da kuma ƙyanƙyasa su? Shin tsuntsaye suna bukatar a yi musu ja-gora kafin su sauko ƙasa? Za ka iya gwada ƙarar jirgin sama da kukar tsuntsu? Saboda haka, tsakanin wanda ya yi jirgin sama da kuma wanda ya halicci tsuntsaye, wane ne ya fi basira?” Irin waɗannan misalan da kuma tambayoyi za su taimaka wa yaranku su zama masu yin tunani sosai kuma su ƙarfafa bangaskiyarsu ga Allah.—Mis. 2:10-12.

12. Ta yaya za ku iya yin amfani da misalai don ku nuna wa yaranku cewa duk abin da Littafi Mai Tsarki ya ce gaskiya ne?

12 Za ku iya yin amfani da misalai masu kyau don ku koya wa yaranku cewa duk abin da Littafi Mai Tsarki ya ce gaskiya ne. Alal misali, kuna iya karanta littafin Ayuba 26:7. (Karanta.) Bayan kun karanta, kada ku gaya wa yaranku nan da nan cewa Jehobah ne ya hure annabinsa ya rubuta wannan ayar. Maimakon haka, ku ƙyale su su yi amfani da hankalinsu da kuma tunaninsu. Kuna iya cewa mutane a zamanin Ayuba ba su san na’urar kawo nesa kusa ko kuma jirgin da ke zuwa sararin sama ba. Aikin ɗanku shi ne ya nuna cewa yakan yi wa mutane wuya su gaskata cewa ba a rataye duniya a kan kome ba. Ƙari ga haka, yana iya nuna cewa dole ne wani abu kamar ƙwallo ko kuma dutse ya tsaya a kan wani abu. Hakan zai taimaka wa yaron ya koya cewa ko da yake an rubuta Littafi Mai Tsarki da daɗewa, abin da ke cikinsa gaskiya ne domin Jehobah ne ya sa aka rubuta waɗannan abubuwan.—Neh. 9:6.

KU NUNA MUSU AMFANIN BIN ƘA’IDODIN LITTAFI MAI TSARKI

13, 14. Ta yaya iyaye za su taimaka wa yaransu su riƙa bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki?

13 Yana da muhimmanci iyaye su koya wa yaransu amfanin bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. (Karanta Zabura 1:1-3.) Alal misali, kuna iya gaya wa yaranku cewa su yi tunanin an ce musu su je wurin da babu kowa kuma aka ce su zaɓi waɗanda za su so su zauna tare da su a wurin. Bayan haka, ku tambaye su, “Idan kuna so ku yi zaman lafiya a wurin, waɗanne irin mutane ne za ku zaɓa?” Kuna iya tattaunawa da su game da shawarwari masu kyau da ke cikin littafin Galatiyawa 5:19-23.

14 Irin wannan misalin zai koya wa yaranku darasi guda biyu. Na farko shi ne, bin ƙa’idodin da Allah ya kafa suna kawo zaman lafiya da kuma haɗin kai. Na biyu shi ne, ta wannan koyarwar, Jehobah yana shirya mu don yin rayuwa a sabuwar duniya. (Isha. 54:13; Yoh. 17:3) Ƙari ga haka, kuna iya nuna musu yadda bin waɗannan ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki suka taimaka wa ’yan’uwanmu. Kuna iya ɗauko waɗannan labaran daga jerin talifofin nan “Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane” da ke cikin Hasumiyar Tsaro. Ko kuma ku tambayi wani a cikin ikilisiya ya ba ku labarin yadda Littafi Mai Tsarki ya taimaka masa ya canja salon rayuwarsa don ya faranta wa Jehobah rai. Irin waɗannan misalan suna nuna cewa bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki yana da amfani!—Ibran. 4:12.

15. Mene ne zai taimaka wa iyaye su koyar da yaransu da kyau?

15 Ku riƙa tunani sosai don ku san yadda za ku sa yaranku su ji daɗin abin da kuke koya musu. Ku sa su riƙa yin tunani sosai a kan abin da kuke koya musu kuma ku riƙa yin la’akari da shekarunsu. Ku yi tunanin hanyoyi dabam-dabam da za ku iya yin amfani da su don ku sa yaranku su ji daɗin koyarwar kuma su ƙarfafa bangaskiyarsu. Wani mahaifi ya ce: “Kada ku gaji da neman sababbin hanyoyi don ku koyar da abubuwan da kuka tattauna da yaranku a dā.”

KU KASANCE DA AMINCI DA HAƘURI KUMA KU RIƘA ADDU’A

16. Me ya sa iyaye suke bukatar su kasance da haƙuri? Ka ba da misali.

16 Yaranku suna bukatar ruhu mai tsarki don su kasance da bangaskiya sosai. (Gal. 5:22, 23) Kamar ’ya’yan itace, zai ɗauki lokaci kafin yaranku su kasance da bangaskiya sosai. Saboda haka, kuna bukatar ku kasance da haƙuri kuma ku riƙa nacewa sa’ad da kuke koyar da yaranku. Wani mahaifi mai yara biyu a ƙasar Japan ya ce: “Ni da matata muna kula da yaranmu sosai. Tun daga lokacin da suke ƙanana, a kowace rana, ina nazari da su na minti 15, amma ban da ranar da za mu je taron Kirista. Yin nazari na minti goma sha biyar bai yi mana ko kuma yaranmu yawa ba.” Wani mai kula da da’ira ya rubuta cewa: “Sa’ad da nake matashi, ina da tambayoyi da yawa ko kuma abubuwan da nake shakkar su. Amma da shigewar lokaci, na samu amsoshin waɗannan tambayoyin a taronmu ko sa’ad da muke ibada ta iyali ko kuma nazarin Littafi Mai Tsarki. Shi ya sa yake da muhimmanci iyaye su ci gaba da koyar da yaransu.”

Idan kuna so ku koyar da yaranku da kyau, wajibi ne ku san Kalmar Allah sosai (Ka duba sakin layi na 17)

17. Me ya sa iyaye suke bukatar su kafa misali mai kyau, kuma ta yaya wasu ma’aurata suka kafa wa yaransu mata misali mai kyau?

17 Wani abu mafi muhimmanci shi ne misalin da kuke kafawa. Yaranku suna kallon abubuwan da kuke yi kuma hakan yakan shafe su sosai. Saboda haka, ku ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarku. Ku nuna wa yaranku cewa kuna ƙaunar Jehobah sosai. Wasu ma’aurata a yankin Bermuda suna addu’a tare da yaransu sa’ad da suke cikin matsala, kuma suna roƙon Jehobah ya yi musu ja-gora. Ƙari ga haka, suna ƙarfafa yaransu su riƙa addu’a da kansu. Ma’auratan sun ce: “Mun ƙarfafa ’yarmu ta fari ta dogara ga Jehobah, ta ci gaba da ƙwazo a hidimarta kuma kada ta riƙa damuwa ainun. Ta san cewa Jehobah ne yake taimaka mana, sa’ad da ta ga sakamakon yin waɗannan abubuwan. Kuma hakan ya sa ta ƙara gaskatawa da Allah da kuma Littafi Mai Tsarki.”

18. Wane abu mai muhimmanci ne iyaye za su riƙa tunawa da shi?

18 Iyaye, kada ku manta cewa ba za ku iya tilasta wa yaranku su kasance da bangaskiya ba. A matsayinku na iyaye, kuna iya yin shuki ne da kuma ban ruwa. Amma Allah ne kaɗai zai sa shukin ya yi girma. (1 Kor. 3:6) Saboda haka, ku roƙe shi ya ba ku ruhu mai tsarki, kuma ku yi iya ƙoƙarinku wajen koyar da yaranku game da Jehobah. Idan kuka yi hakan, Jehobah zai albarkace ku sosai.—Afis. 6:4.