Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Ci gaba da Roƙon Jehobah Ya Albarkace Ka

Ka Ci gaba da Roƙon Jehobah Ya Albarkace Ka

“Ka gwada ƙarfi da Allah da mutane kuma, har kuwa ka yi nasara.”—FAR. 32:28.

WAƘOƘI: 60, 38

1, 2. Waɗanne ƙalubale ne bayin Jehobah suke fuskanta?

DAGA zamanin Adamu har zuwa zamaninmu, amintattun bayin Allah sun yi fama da matsaloli da yawa. Manzo Bulus ya rubuta wa Kiristoci Ibraniyawa cewa sun “jure tsananin fama da shan wuya” don su sami amincewar Jehobah da kuma albarkarsa. (Ibran. 10:32-34, Littafi Mai Tsarki) Bulus ya kwatanta famar da Kiristoci suke yi da na wanda ’yan wasan guje-guje ko ’yan damben Girka suke yi. (Ibran. 12:1, 4) A yau, muna yin tsere na samun rai na har abada. Don haka, akwai abubuwa da yawa da za su iya ɗauke hankalinmu, su sa mu karaya da kuma baƙin ciki.

2 Da farko, muna bukatar mu yi fama ko kuma kokawa da Shaiɗan da kuma duniyarsa. (Afis. 6:12) Yana da muhimmanci sosai mu guji barin abubuwan duniya “masu-ƙarfi” su shafi rayuwarmu. Waɗannan abubuwan sun ƙunshi koyarwar ƙarya da ilimin falsafa da kuma ayyuka marasa kyau kamar su yin lalata da shan sigari da yin maye da kuma shan mugayen ƙwayoyi. Tun da yake mu ajizai ne, dole ne mu ci gaba da kokawa da kasawarmu da kuma abin da zai sa mu karaya.—2 Kor. 10:3-6; Kol. 3:5-9.

3. Ta yaya Allah yake taimaka mana mu yi kokawa da maƙiyanmu?

3 Idan muna so mu yi nasara a kan Shaiɗan da kuma duniyarsa, dole ne mu yi kokawa sosai. Bulus ya yi amfani da misalin ɗan dambe kuma ya ce: “Dambena kuwa ba naushin iska nake yi ba.” (1 Kor. 9:26, LMT) Muna bukatar mu yi kokawa da maƙiyanmu kamar yadda ɗan dambe yake yi da abokin gabansa. Yayin da muke wannan kokawar, Jehobah yana koyar da mu da kuma taimaka mana. Yana amfani da Kalmarsa don ya yi mana ja-gora. Ban da haka, yana taimaka mana ta wurin littattafanmu da taronmu na Kirista da kuma manyan taro. Shin kana yin abin da kake koya? Idan ba ka yin hakan, kamar kana “naushin iska” ne maimakon maƙiyinka.

4. Ta yaya za mu guji barin mugunta ta rinjaye mu?

4 Maƙiyanmu za su iya kai mana hari a lokacin da ba mu zata ba. Don haka, a kowane lokaci muna bukatar mu kasance a shirye. Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu cewa: “Kada mugunta ta rinjaye ku, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.” (Rom. 12:21) Wannan furucin kada ku bar “mugunta ta rinjaye ku” ta nuna cewa za mu iya yin nasara a kan mugunta idan muka ci gaba da kokawa. Amma idan muka daina kokawa, Shaiɗan da duniyarsa da kuma kasawarmu za su iya shawo kanmu. Kada ka bar Shaiɗan ya rinjaye ka kuma ya sa ka karaya!—1 Bit. 5:9.

5. (a) Idan muna so Allah ya amince da mu, mene ne ya kamata mu riƙa tunawa da shi? (b) Labaran su wane ne za mu tattauna?

5 Idan muna so mu yi nasara, wajibi ne mu riƙa tuna dalilin da ya sa muke kokawa. Dalilin kuma shi ne muna so mu sami albarkar Allah. Littafin Ibraniyawa 11:6 ta ce: “Mai-zuwa wurin Allah dole ya ba da gaskiya cewa yana da rai, kuma shi mai-sākawa ne ga dukan waɗanda ke biɗarsa.” Wannan ayar tana nufin cewa wajibi ne mu yi fama sosai idan muna so Allah ya amince da mu. (A. M. 15:17) A cikin Littafi Mai Tsarki, da akwai misalai da yawa na maza da mata da suka yi iya ƙoƙarinsu don su sami albarkar Jehobah. Wasu daga cikinsu su ne Yakubu da Rahila da Yusufu da kuma Bulus. Waɗannan mutanen sun fuskanci yanayi mai wuya a rayuwarsu, duk da haka sun yi nasara, kuma sun sami albarkar Jehobah. Ta yaya za mu bi misalin su?

ZA KA SAMI ALBARKA IDAN KA NACE

6. Mene ne ya taimaka wa Yakubu ya nace, kuma mene ne sakamakon hakan? (Ka duba hoton da ke shafi na 8.)

6 Yakubu ya yi fama da matsaloli da yawa amma ya jimre domin yana ƙaunar Jehobah, kuma ya ɗauki dangantakarsa da Allah da muhimmanci sosai. Ban da haka, ya gaskata cewa Jehobah zai cika alkawarin da ya yi cewa zai albarkaci ’ya’yansa. (Far. 28:3, 4) Shi ya sa sa’ad da Yakubu ya kusan shekara 100, ya yi kokawa da mala’ika don ya sami albarkar Allah. (Karanta Farawa 32:24-28.) Shin Yakubu yana da ƙarfin da zai iya kokawa da mala’ika ne? A’a! Amma ya ƙudura aniya kuma ya nace Jehobah ya albarkace shi! Shi ya sa aka sa masa suna Isra’ila da take nufin “wanda ya yi kokawa da Allah.” Jehobah ya amince da Yakubu kuma ya albarkace shi. Abin da mu ma muke so ke nan.

7. (a) Wane yanayi na baƙin ciki ne Rahila ta fuskanta? (b) Me ta yi kuma ta yaya aka albarkace ta?

7 Rahila matar Yakubu ce da yake ƙauna sosai kuma tana so ta ga yadda Jehobah zai cika alkawarin da ya yi wa mijinta. Amma da akwai matsala. Ba ta da ’ya’ya kuma hakan babban matsala ce musamman ma a zamaninsu. Ta yaya Rahila ta ci gaba da ƙoƙartawa duk da yanayin da take ciki? Ba ta fid da rai ba. Ta ci gaba da roƙon Jehobah ya ba ta ɗa. Jehobah ya amsa addu’ar Rahila kuma ya albarkace ta da yara. Shi ya sa Rahila ta ce: ‘Da gawurtacciyar kokawa na yi kokawa . . . har na yi nasara!’—Far. 30:8, 20-24, LMT.

8. Wane yanayi mai wuya ne Yusufu ya fuskanta, kuma wane misali mai kyau ne ya kafa mana?

8 Babu shakka, misalin da Yakubu da kuma Rahila suka kafa ya taimaka wa ɗansu Yusufu musamman ma sa’ad da yake cikin matsala. A lokacin da Yusufu yake ɗan shekara 17, rayuwarsa ta taɓarɓare. ’Yan’uwansa sun tsane shi sosai, don haka suka sayar da shi kuma ya zama bawa. Daga baya, ya yi shekaru da yawa a kurkuku duk da cewa bai aikata wani laifi ba. (Far. 37:23-28; 39:7-9, 20-21) Yusufu bai karaya ba kuma bai yi tunanin cewa zai rama abin da aka yi masa ba. Amma ya mai da hankali ga dangantakarsa da Jehobah kuma ya ɗauke ta da tamani sosai. (Lev. 19:18; Rom. 12:17-21) Misalin Yusufu zai taimaka mana sosai. Alal misali, ko da mun daɗe muna fama da matsaloli ko a’a, muna bukatar mu ci gaba da kokawa da kuma naciya don Jehobah ya yi mana albarka. Idan muka yi haka, za mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai yi mana albarka.—Karanta Farawa 39:21-23.

9. Ta yaya za mu bi misalin Yakubu da Rahila da kuma Yusufu?

9 Wataƙila kana fama da wasu matsaloli. Mai yiwuwa an maka rashin adalci ko an nuna maka wariya ko kuma an yi maka rashin mutunci. Ƙari ga haka, wataƙila wani ya yaɗa ƙarya game da kai don yana kishin ka. Maimakon ka karaya, ka tuna da abin da ya taimaka wa Yakubu da Rahila da kuma Yusufu su yi farin ciki a ibadarsu ga Jehobah. Allah ya ƙarfafa da kuma yi musu albarka domin sun ɗauki dangantakarsu da shi da tamani sosai. Sun ci gaba da kokawa kuma sun yi aikin da ya jitu da addu’arsu. Muna rayuwa a kwanaki na ƙarshe. Don haka, muna bukatar mu kasance da bangaskiya sosai! Kana iya ƙoƙarinka don ka sami amincewar Jehobah?

KA YI KOKAWA DA ANIYA DON JEHOBAH YA ALBARKACE KA

10, 11. (a) Me ya sa muke bukatar mu yi kokawa don mu sami albarkar Allah? (b) Mene ne zai taimaka mana mu yi abin da ya dace?

10 Me ya sa muke bukatar mu yi kokawa don Allah ya albarkace mu? Domin mu ajizai ne. Wasu suna fama da sha’awoyin banza. Wasu kuma suna yin iya ƙoƙarinsu don su yi wa’azi da ƙwazo. Wataƙila, kai kuma kana fama da rashin lafiya ko kuma kaɗaici. Ƙari ga haka, yakan yi wa wasu wuya su gafarta wa mutum idan ya yi musu laifi. Allah yana wa waɗanda suka kasance da aminci albarka. Saboda haka, ko da mun daɗe muna bauta wa Jehobah ko a’a, dukanmu muna bukatar mu guji duk wani abin da zai iya ɓata dangantakarmu da shi.

Kana roƙon Jehobah ya taimake ka? (Ka duba sakin layi na 10, 11)

11 Idan Kirista yana fama da sha’awoyin banza, yana iya yi masa wuya ya yi abin Jehobah yake so. (Irm. 17:9) Idan kana fama da hakan, ka roƙi Jehobah ya ba ka ruhu mai tsarki. Addu’a da kuma ruhu mai tsarki za su ba ka ƙarfin zuciyar yin abin da ya dace kuma ka sami albarkar Jehobah. Ka riƙa yin abin da ka yi addu’a a kai. Ka riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana kuma ka ba da lokaci don yin Ibada ta Iyali da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki.—Karanta Zabura 119:32.

12, 13. Mene ne ya taimaka wa wasu Kiristoci guda biyu su daina sha’awar banza?

12 Akwai misalai da yawa a kan yadda Kalmar Allah da ruhu mai tsarki da kuma littattafanmu suka taimaka wa Kiristoci su daina sha’awoyin banza. Wani matashi ya karanta talifin nan “How Can You Resist Wrong Desires?” da ke cikin Awake! na 8 ga Disamba, 2003. Ya ce: “Ina fama da tunanin banza. Sa’ad da na karanta a cikin talifin cewa ‘mutane da yawa sun yi fama da sha’awoyin banza kuma daina hakan bai yi musu sauƙi ba,’ hakan ya sa na ga cewa ba ni kaɗai ba ne a cikin ƙungiyar Jehobah nake fama da wannan matsala ba.” Wannan matashin ya ƙara amfana daga talifin nan “Alternative Life-Styles—Does God Approve?” da ke cikin Awake! na 8 ga Oktoba, 2003. A talifin, ya ga cewa famar da wasu suke yi kamar “ƙaya” ce a jikinsu. (2 Kor. 12:7, LMT) Duk da haka, ba su karaya ba. Sun ci gaba da kokawa kuma sun kasance da bege don nan gaba. Matashin ya ce: “Tun da waɗannan mutanen sun kasance da aminci, ni ma zan iya yin hakan. Ina matuƙar godiya ga Jehobah da ya yi amfani da ƙungiyarsa don ya taimaka mana a wannan mugun zamanin.”

13 Ka yi la’akari da labarin wata ’yar’uwa a ƙasar Amirka. Ta ce: “Ina so in gode muku don kuna ba mu abin da muke bukata a lokacin da ya dace. A yawanci lokaci, ina ji kamar don ni ne aka rubuta wasu talifofin. Na yi shekaru da yawa ina sha’awar abin da Jehobah ba ya so. A wani lokaci ma, ina ji kamar in fid da rai. Na san cewa Jehobah yana da jin kai kuma shi mai gafartawa ne. Amma na kasa daina wannan sha’awar, don haka ina ganin ban cancanci samun taimakonsa ba. Kuma hakan ya sa ba na jin daɗin rayuwata. . . . Amma da na karanta talifin nan ‘Kana da “Zuciya Wadda Za ta San” Jehobah?’ da ke cikin Hasumiyar Tsaro na 15 ga Maris, 2013, sai na ga cewa Jehobah yana so ya taimake ni.”

14. (a) Yaya Bulus ya ji game da kasawarsa? (b) Mene ne zai taimaka mana mu yi nasara da kasawarmu?

14 Karanta Romawa 7:21-25. Bulus ma ya yi fama da sha’awoyin banza da kuma kasawarsa. Amma ya kasance da tabbaci cewa zai yi nasara idan ya dogara ga Jehobah kuma ya gaskata da fansar Yesu. Mu kuma fa? Za mu iya yin nasara idan muka bi misalin Bulus. Ƙari ga haka, kada mu dogara ga kanmu amma mu dogara ga Jehobah kuma mu gaskata da fansar Yesu Kristi.

15. Me ya sa addu’a za ta iya taimaka mana mu jimre da gwaji?

15 A wani lokaci, Allah yana barin mu mu fuskanci matsaloli don mu nuna yadda za mu bi da batun. Alal misali, me za mu yi idan mu (ko wani daga cikin iyalinmu) ya kamu da wata cuta mai tsanani ko kuma idan aka yi mana rashin adalci? Ya kamata mu yi wa Jehobah addu’a ya ba mu ƙarfin jimrewa kuma ya taimaka mana kada mu daina farin ciki ko kuma bauta masa. Idan muka yi hakan, muna nuna cewa mun dogara gare shi. (Filib. 4:13) Misalan Kiristoci a zamanin Bulus da kuma zamaninmu sun nuna cewa yin addu’a za ta ƙarfafa mu kuma ta ba mu ƙarfin zuciya don mu ci gaba da jimrewa.

KA CI GABA DA ROƘON JEHOBAH YA ALBARKACE KA

16, 17. Me ka ƙudurta cewa za ka yi?

16 Shaiɗan yana so ka karaya kuma ka daina bauta wa Jehobah. Amma ka ƙudurta cewa za ka ci gaba da yin abin da ya dace. (1 Tas. 5:21) Ka kasance da tabbaci cewa za ka iya yin nasara a kan Shaiɗan da duniyarsa da kuma azancinka. Ka dogara ga Allah kuma ka kasance da bangaskiya cewa zai ba ka ƙarfin jimrewa.—2 Kor. 4:7-9; Gal. 6:9.

17 Ka ci gaba da kokawa. Ka ci gaba da roƙon Jehobah kuma ka riƙa nacewa. Ka kasance da gaba gaɗi cewa Jehobah zai ‘zuba maka albarka, har da ba za a sami wurin da za a karɓa ba.’—Mal. 3:10.