Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kada Ka Karaya

Kada Ka Karaya

“Kada ki bar hannuwanki su raunana.”—ZAF. 3:16, Littafi Mai Tsarki.

WAƘOƘI: 81, 32

1, 2. (a) Waɗanne irin matsaloli ne mutane suke fuskanta a yau, kuma mene ne sakamakon hakan? (b) Wane tabbaci ne littafin Ishaya 41:10, 13 ya sa mu kasance da shi?

WATA majagaba da maigidanta dattijo ne ta ce: “Ko da yake ina nazarin Littafi Mai Tsarki sosai, na yi shekaru da yawa ina fama da matsaloli, kuma hakan ya hana ni barci. Ban da haka ma, ya sa na soma rashin lafiya kuma ya shafi yadda nake bi da mutane. A wani lokaci, ji nake kamar in mutu.”

2 Shin ka taɓa samun kanka a irin wannan yanayin? Domin muna rayuwa a cikin duniyar Shaiɗan, mukan fuskanci yanayin da zai sa mu karaya. Matsalolin nan suna kamar abin da aka riƙe ƙwale-ƙwale da shi don ya hana ruwa tafiya da shi. (Mis. 12:25) Wane irin yanayi ne zai iya sa mutum ya karaya? Wataƙila wani da kake ƙauna ya rasu ko kana fama da rashin lafiya mai tsanani ko kana tunanin yadda za ka ciyar da iyalinka ko kuma kana fuskantar hamayya. Irin waɗannan abubuwan suna iya sa ka karaya ko su sa ka baƙin ciki. Amma ka kasance da tabbaci cewa Allah zai taimake ka.—Karanta Ishaya 41:10, 13.

3, 4. (a) Ta yaya aka yi amfani da kalmar nan ‘hannu’ a cikin Littafi Mai Tsarki? (b) Mene ne zai iya sa mu karaya?

3 A cikin Littafi Mai Tsarki, ana yawan amfani da gaɓoɓin jikin ’yan Adam don a kwatanta ayyuka da kuma halaye dabam-dabam. Alal misali, an ambata hannu sau da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki. Idan aka ƙarfafa hannun mutum, hakan yana nufin cewa an ba shi ƙarfin yin wani abu. (1 Sam. 23:16; Ezra 1:6) Ƙari ga haka, yana nufin mutum ya kasance da ra’ayi mai kyau da kuma bege game da nan gaba.

4 An yi amfani da hannun da ke sake don an kwatanta mutumin da ya karaya ko ya fid da rai a kan wani abu ko kuma yana ganin ba shi da bege. (2 Laba. 15:7; Ibran. 12:12) Mutanen da suka sami kansu a cikin irin waɗannan yanayin da aka ambata ɗazu suna saurin fid da rai. A ina ne za ka sami ƙarfafa idan ka sami kanka a cikin wani yanayi mai wuya? Ta yaya za ka sami ƙarfafa don ka jimre da matsaloli kuma ka ci gaba da yin farin ciki?

‘HANNUN UBANGIJI BAI GAJARTA BA, HAR DA BA ZAI IYA CETO BA’

5. (a) Mene ne za mu iya yi sa’ad da muke fuskantar matsaloli, amma mene ne ya kamata mu riƙa tunawa da shi? (b) Mene ne za mu tattauna?

5 Karanta Zafaniya 3:16, 17. Sa’ad da muke fuskantar matsala, maimakon mu ji tsoro kuma mu fid da rai, Ubanmu mai ƙauna Jehobah ya ce, mu ‘zuba dukan alhininmu a bisansa.’ (1 Bit. 5:7) Allah ya gaya wa Isra’ilawa cewa hannunsa mai iko ‘bai gajarta ba, har da ba zai iya ceton’ bayinsa masu aminci ba. Hakan abin ƙarfafa ne a gare mu. (Isha. 59:1) Za mu tattauna misalai guda uku da suka nuna cewa Jehobah yana da iko kuma yana ɗokin taimaka wa mutanensa don su yi nufinsa ko da suna fuskantar matsaloli. Ban da haka, za ka ga yadda waɗannan misalan za su ƙarfafa ka.

6, 7. Wane darasi mai muhimmanci ne za mu iya koya daga yadda Isra’ilawa suka yi nasara a kan Amalakawa?

6 Ba da daɗewa ba bayan Isra’ilawa sun bar ƙasar Masar, sai Amalakawa suka kai musu hari. Joshua ya bi abin da Musa ya gaya masa kuma da gaba gaɗi ya ja-goranci mutanen Isra’ila a yaƙi. Amma Musa ya kai Haruna da Hur zuwa wani tudu don su ga filin da ake yaƙin. Shin waɗannan maza uku sun yi hakan don suna jin tsoron yaƙin ne? A’a!

7 Musa ya yi wani abu da ya sa suka yi nasara a wannan yaƙin. Ya ɗaga sandar Allah sama. Saboda haka, Jehobah ya sa Isra’ilawa suka soma yin nasara a yaƙin. Amma sa’ad da Musa ya gaji kuma ya soma saukar da hannunsa, sai Amalakawan suka soma cin nasara. Haruna da kuma Hur sun nuna basira kuma suka ‘ɗauki dutse, suka sa shi ƙarƙashin [Musa], ya zauna a kai; Haruna da Hur kuma suna tallaɓe da hannuwansa, ɗaya ga wannan sassa, ɗaya ga wancan; hannuwansa fa suna da ƙarfin tsayawa har faɗuwar rana.’ Hakika, da taimakon Allah, Isra’ilawa sun yi nasara a yaƙin.—Fit. 17:8-13.

8. (a) Mene ne Asa ya yi sa’ad da Kushawa suka kai wa Yahuda hari? (b) Ta yaya za mu iya yin koyi da yadda Asa ya dogara ga Allah?

8 A zamanin Sarki Asa, Jehobah ya nuna cewa shi mai taimakon bayinsa ne. A cikin Littafi Mai Tsarki, an ambata yaƙe-yaƙe da yawa da aka yi. Amma a cikinsu, Zerah Bakushi ne ya zo da rundunar sojoji da yawa. Yana da ƙwararrun sojoji guda 1,000,000, kuma sun ninka na Asa sau biyu. Hakika, wannan abu ne da zai iya sa Asa ya ji tsoro kuma ya fid da rai a yaƙin. Amma bai yi hakan ba. Nan da nan, Asa ya nemi taimakon Jehobah. Ana iya ganin cewa Asa ba zai taɓa cin wannan yaƙin ba, amma a “gun Allah kowane abu mai yiwuwa ne.” (Mat. 19:26, LMT) Allah ya nuna ikonsa kuma “ya buga Kushawa daga gaban Asa,” wanda ‘zuciyarsa . . . ta kamalta a gaban Ubangiji dukan kwanakin ransa.’—2 Laba. 14:8-13; 1 Sar. 15:14.

9. (a) Mene ne ya taimaka wa Nehemiya ya gina ganuwar Urushalima? (b) Ta yaya Jehobah ya amsa addu’ar Nehemiya?

9 Mene ne Nehemiya ya gani sa’ad da ya je Urushalima? Ya ga cewa babu kariya a birnin kuma ’yan’uwansa Yahudawa sun karaya don abubuwan da suke faruwa. Magabtansu suna ta yi musu barazana kuma hakan ya sa sun daina gina ganuwar Urushalima. Shin Nehemiya ma ya karaya don hakan? A’a! Nehemiya ya dogara ga Jehobah kuma ya yi addu’a ya taimaka masa kamar yadda Musa da Asa da kuma sauran amintattun bayin Allah suka yi. Yahudawan suna ganin cewa babu mafita amma Jehobah ya amsa addu’ar Nehemiya kuma ya taimaka masa. Allah ya yi amfani da ‘ikonsa mai-girma, da hannunsa mai-ƙarfi’ don ya ƙarfafa Nehemiya. (Karanta Nehemiya 1:10; 2:17-20; 6:9.) Ka gaskata cewa Jehobah yana amfani da ‘ikonsa mai-girma, da hannunsa mai-ƙarfi’ don ya ƙarfafa bayinsa a yau?

JEHOBAH ZAI ƘARFAFA KA

10, 11. (a) Mene ne Shaiɗan yake yi don ya sa mu mu karaya? (b) Mene ne Jehobah yake amfani da su don ya ƙarfafa mu? (c) A wace hanya ce ka amfana daga koyarwar da ƙungiyar Jehobah take tanadar mana?

10 Mun san cewa Shaiɗan zai ci gaba da yin iya ƙoƙarinsa don ya hana mu bauta wa Jehobah. Yana amfani da gwamnati da shugabannin addinai da kuma ’yan ridda don ya cim ma hakan. Me ya sa Shaiɗan yake yin hakan? Don yana so ya hana mu yin wa’azi. Amma ta wurin ruhu mai tsarki, Jehobah yana ba mu ƙarfin da za mu iya jimrewa. (1 Laba. 29:12) Yana da muhimmanci mu roƙi Jehobah ya ba mu ruhu mai tsarki don ya taimaka mana mu jimre da duk wata matsalar da Shaiɗan zai kawo. (Zab. 18:39; 1 Kor. 10:13) Ƙari ga haka, ya kamata mu gode wa Jehobah don taimakon da muke samu daga Kalmarsa. Ka yi tunanin abubuwan da muke koya daga littattafanmu da ke bayyana Littafi Mai Tsarki da muke samu a kowane wata. Sa’ad da ake gina ganuwar Urushalima ne aka faɗi kalmomin da ke cikin littafin Zakariya 8:9, 13 (karanta) kuma waɗannan kalmomin abin ƙarfafa ne a gare mu.

11 Abubuwan da muke koya a taronmu na Kirista da manyan taron da kuma makarantun da muke zuwa suna ƙarfafa mu sosai. Suna taimaka mana mu kasance da ra’ayin da ya dace da kuma kafa maƙasudai a bautarmu ga Jehobah. Ƙari ga haka, suna taimaka mana mu yi abubuwan da ya kamata mu yi a matsayinmu na Kiristoci. (Zab. 119:32) Shin kana barin waɗannan koyarwar su ƙarfafa ka?

12. Mene ne za mu yi don mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah?

12 Jehobah ya taimaka wa Isra’ilawa su ci Amalakawa da kuma Kushawa a yaƙi. Ƙari ga haka, ya ƙarfafa Nehemiya da kuma abokansa don su iya gina ganuwar Urushalima. Hakazalika, don mu iya yin wa’azi da ƙwazo, Jehobah zai ba mu ƙarfin jimrewa da hamayya da kasala da kuma ɗawainiyar wannan duniyar. (1 Bit. 5:10) Kada mu yi tunanin cewa Jehobah zai yi mu’ujiza a madadinmu. Maimakon haka, mu yi iya ƙoƙarinmu wajen karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana da kuma yin shiri don halartan taro. Kuma mu riƙa yin nazarin Littafi Mai Tsarki da ibada ta iyali da kuma addu’a ga Jehobah. Kada mu bar wani abu ya sa mu daina amfana daga hanyoyin da Jehobah yake amfani da su don ya ƙarfafa mu. Idan ka lura cewa ba ka yin waɗannan abubuwan da aka ambata, ka roƙi Jehobah ya taimake ka. Za ka ga yadda Jehobah zai ƙarfafa ka da kuma ba ka ƙarfin jimrewa. (Filib. 2:13) Me za ka iya yi don ka ƙarfafa wasu?

KU ƘARFAFA JUNA

13, 14. (a) Ta yaya aka ƙarfafa wani ɗan’uwa bayan mutuwar matarsa? (b) A wace hanya ce za mu iya ƙarfafa wasu?

13 Jehobah ya ba mu ’yan’uwa da za su iya ƙarfafa mu sa’ad da muke fuskantar matsaloli. Manzo Bulus ya ce: “Ku ta da hannuwan da ke reto, ku ƙarfafa gwiwoyinku marar ƙarfi; ku yi miƙaƙun karafku kuma domin sawayenku.” (Ibran. 12:12, 13) A ƙarni na farko, an ƙarfafa mutane da yawa. Haka ma yake a yau. Alal misali, wani ɗan’uwa ya fuskanci wasu matsaloli bayan matarsa ta mutu. Ya ce: “Na fahimci cewa ba za mu iya zaɓan lokacin da za a gwada bangaskiyarmu ba. Amma addu’a da nazarin Littafi Mai Tsarki sun taimaka mini sosai. Ƙari ga haka, taimakon da ’yan’uwana maza da mata suka yi mini ya ƙarfafa ni sosai. Hakan ya sa na san cewa yana da muhimmanci mutum ya kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah ko da yana fuskantar mawuyacin yanayi.”

Kowannen mu a cikin ikilisiya zai iya ƙarfafa wasu (Ka duba sakin layi na 14)

14 Haruna da Hur sun taimaka wa Musa a lokacin yaƙi. Mu ma za mu iya neman hanyoyin da za mu taimaka wa wasu. Su wane ne muke bukatar mu taimaka wa? Tsofaffi da waɗanda suke fama da rashin lafiya ko hamayya daga iyalinsu ko kaɗaici ko kuma waɗanda aka yi musu mutuwa. Ƙari ga haka, za mu iya ƙarfafa matasan da suke fama da matsi daga tsararsu ko kuma suke so su shahara ko su yi suna a wannan duniyar. (1 Tas. 3:1-3; 5:11, 14) Ka nemi hanyar da za ka iya taimaka wa wasu a Majami’ar Mulki, a wa’azi ko sa’ad da kake shaƙatawa da su ko kuma sa’ad da kake tattaunawa a waya.

15. Ta yaya kalamanka za su iya ƙarfafa wasu?

15 Bayan Asa ya yi nasara a yaƙin da ya yi da Kushawa, annabi Azariah ya ƙarfafa shi da mutanensa cewa: “Amma sai ku yi ƙarfi, kada hannunku su sake: gama za ku sami ladan aikinku.” (2 Laba. 15:7) Hakan ya motsa Asa ya yi iya ƙoƙarinsa don ya sa Isra’ilawa su koma bauta ta gaskiya. Hakazalika, kalamanka suna iya shafan rayuwar wasu. Za ka iya taimaka musu su bauta wa Jehobah yadda ya dace. (Mis. 15:23) Kuma a taro, ka riƙa yin kalamai, domin kalamanka suna iya ƙarfafa wasu.

16. Ta yaya dattawa za su ƙarfafa wasu a cikin ikilisiya kamar yadda Nehemiya ya yi? Ka ambata yadda ’yan’uwa suka taɓa taimaka maka.

16 Da taimakon Jehobah, Nehemiya da abokansa sun soma gina ganuwar Urushalima kuma sun kammala ta a cikin kwana 52! (Neh. 2:18; 6:15, 16) Nehemiya bai ja-goranci aikin kawai ba amma shi ma ya yi aikin gina ganuwar Urushalima tare da mutanen. (Neh. 5:16) Hakazalika, dattawa da yawa suna bin misalin Nehemiya ta wajen taimakawa sa’ad da ake gina da kuma tsabtace Majami’un Mulki. Ƙari ga haka, suna ƙarfafa waɗanda suka karaya ta wajen fita wa’azi tare da su ko kuma kai musu ziyarar ƙarfafa.—Karanta Ishaya 35:3, 4.

KADA KA KARAYA

17, 18. Wane tabbaci muke da shi sa’ad da muke cikin matsala?

17 Idan muna aiki tare da ’yan’uwanmu maza da mata, hakan zai sa mu kasance da haɗin kai. Kuma yana ƙara dankon abokantaka tsakaninmu da su. Ƙari ga haka, yana sa mu ƙara kasance da tabbaci cewa nan ba da daɗewa ba Mulkin Allah zai kawo mana albarka. Sa’ad da muka ƙarfafa ’yan’uwanmu, muna taimaka musu su jimre da matsaloli kuma su kasance da ra’ayin da ya dace da kuma bege game da nan gaba. Ban da haka, muna ƙarfafa dangantakarmu da Allah sa’ad da muka ƙarfafa su, kuma hakan yana sa mu riƙa mai da hankali ga abubuwan da Jehobah ya shirya mana a nan gaba.

18 Idan muka yi la’akari da yadda Jehobah ya taimaka da kuma ƙarfafa bayinsa a dā, hakan zai ƙarfafa bangaskiyarmu kuma zai sa mu ƙara dogara a gare shi. Saboda haka, kada ka karaya sa’ad da kake fuskantar mawuyacin yanayi! Amma ka roƙi Jehobah ya ƙarfafa ka kuma ka bar shi ya yi maka ja-gora don ka sami albarka a Mulkinsa.—Zab. 73:23, 24.