Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kana Bin Ja-gorar Jehobah a Yau Kuwa?

Kana Bin Ja-gorar Jehobah a Yau Kuwa?

YA YANKE SHAWARA MAI KYAU A ƘASAR POLAND

“NA YI baftisma sa’ad da nake ’yar shekara 15. Bayan wata shida, sai na soma hidimar majagaba na ɗan lokaci. Shekara ɗaya bayan haka, na soma hidimar majagaba na cikkaken lokaci. Na nemi izinin zuwa wajen da ake bukatar masu shela sosai bayan na kammala makarantar sakandare. Ina so in bar garinmu da kuma kakata wadda nake zama da ita kuma ba Mashaidiya ba ce. Na yi baƙin ciki sa’ad da mai kula da da’ira ya gaya mini cewa a garinmu zan yi hidima! Na yi ƙoƙarin ɓoye baƙin ciki na. Na sunkuyar da kaina, kuma na tafi ina tunanin abin da mai kula da da’irar ya gaya mini. Na gaya wa wadda nake wa’azi tare da ita da ita ma majagaba ce cewa: ‘Kamar yadda Yunana ya ƙi zuwa Nineba da farko, ni ma na ƙi zuwa inda aka tura ni, amma daga baya Yunana ya je inda aka tura shi. Saboda haka, ni ma zan je inda aka tura ni.’

“Yanzu na yi shekara huɗu ina hidimar majagaba a garinmu, kuma na fahimci muhimmancin bin ja-gorar da aka ba ni. Yadda na canja tunanina ya taimaka mini sosai. Yanzu ina farin ciki sosai. A wata ɗaya, ina nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane 24. Ƙari ga haka, na soma nazarin Littafi Mai Tsarki da kakata da ba ta son Shaidun Jehobah. Na gode wa Jehobah sosai.”

AN SAMU SAKAMAKO MAI KYAU A ƘASAR FIJI

Wata ɗalibar Littafi Mai Tsarki tana bukatar ta zaɓi tsakanin halartar taron yanki da kuma zuwa bikin tunawa da ranar haihuwar wani dangin mijinta tare da maigidanta. Mijin ya amince ta halarci taron, sai ta gaya masa cewa za ta halarci bikin bayan ta dawo daga taron. Amma da ta dawo daga taron, sai ta yanke shawara cewa ba za ta je bikin ba, domin ba ta so ta sa kanta a cikin yanayin da zai iya ɓata dangantakarta da Jehobah.

Mijinta ya gaya wa danginsa cewa matarsa ta halarci “taron Shaidun Jehobah,” amma idan ta dawo za ta zo bikin. Sai suka ce masa “Shaidun Jehobah ba sa yin bikin tunawa da ranar haihuwa don haka ba za ta zo ba!” *

Mijinta ya ji daɗi cewa matarsa ta yanke shawara bisa ga imaninta da kuma lamirinta. Daga baya, abin da ta yi ya ba ta damar gaya wa maigidanta da kuma wasu game da Mulkin Allah. Mene ne sakamakon? Mijin ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ya soma halartar taro tare da matarsa.

^ sakin layi na 7 Ka duba “Tambayoyi Daga Masu Karatu” a cikin Hasumiyar Tsaro na 1 ga Maris, 2002.