Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Matasa, Ku Karfafa Bangaskiyarku

Matasa, Ku Karfafa Bangaskiyarku

“Bangaskiya fa ainihin abin da muke begensa ne, tabbacin al’amuran da ba a gani ba tukuna.”—IBRAN. 11:1.

WAƘOƘI: 41, 69

1, 2. Wane matsi ne matasa suke fuskanta a yau, kuma mene ne za su iya yi don su magance hakan?

’YAR ajin wata ’yar’uwa matashiya a Britaniya ta gaya mata cewa: “Duk da iliminki kin yi imani da Allah?” Wani ɗan’uwa a Jamus ya rubuta cewa: “Malamanmu sun ce labaran da ke cikin Littafi Mai Tsarki ba su faru da gaske ba. Kuma suna ganin ba laifi ba ne ɗalibai su yi imani da juyin halitta.” Wata ’yar’uwa matashiya a Faransa ta ce: “Malamanmu suna mamaki cewa har ila akwai ɗaliban da suka gaskata da Littafi Mai Tsarki.”

2 A matsayinku na matasa da suke bauta wa Jehobah ko kuma waɗanda suke koya game da shi, kuna ganin ana matsa muku ku gaskata da abubuwan da mutane suka yi imani da shi, kamar juyin halitta, maimakon ku gaskata cewa da akwai Mahalicci? Idan haka ne, akwai matakan da za ku ɗauka don ku ƙarfafa bangaskiyarku. Ɗaya daga cikinsu shi ne yin amfani da hankalinku don zai ‘tsare’ ku, kuma zai kāre ku daga ra’ayin ƙarya da zai sa ku daina kasancewa da bangaskiya.—Karanta Misalai 2:10-12.

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Don mu kasance da bangaskiya sosai, wajibi ne mu san Jehobah sosai. (1 Tim. 2:4) Saboda haka, sa’ad da kuke karanta Littafi Mai Tsarki da kuma littattafanmu, yana da muhimmanci ku dakata kuma ku yi tunani a kan abin da kuka karanta. Ƙari ga haka, ku yi ƙoƙari ku fahimci abin da kuke karantawa. (Mat. 13:23) Bari mu ga yadda yin hakan zai taimaka mana mu ƙarfafa bangaskiyarmu ga Jehobah da kuma Littafi Mai Tsarki don sanin hakan za su ‘tabbatar’ mana cewa Jehobah ne Mahalicci da kuma mawallafin Littafi Mai Tsarki.—Ibran. 11:1.

YADDA ZA KU ƘARFAFA BANGASKIYARKU

4. Me ya sa muke bukatar bangaskiya kafin mu iya gaskata da Allah da kuma halitta, kuma wane mataki ne ya kamata mu ɗauka?

4 Wani yana iya gaya maka cewa ya gaskata da juyin halitta domin masanan kimiyya sun koyar da hakan. Mutane da yawa sukan yi tunanin cewa, yaya mutum zai gaskata da Allahn da ba a taɓa ganinsa ba? Hakika, babu wani a cikinmu da ya taɓa ganin Allah ko kuma ya ga sa’ad da aka halicci wani abu. (Yoh. 1:18) Ƙari ga haka, babu ɗan Adam ko shi masanin kimiyya ne da ya taɓa ganin wani abu mai rai ya canja kuma ya zama wani abu dabam. Alal misali, babu wanda ya taɓa ganin maciji ko kaɗangare ya canja kuma ya zama wata dabba kamar zaki ko kuma giwa. (Ayu. 38:1, 4) Saboda haka, wajibi ne dukanmu mu bincika tabbacin da muke da shi kuma mu yi tunani sosai a kan waɗannan abubuwan don mu san abin da suke nufi. Manzo Bulus ya rubuta game da halitta cewa: “Tun halittar duniya al’amuran Allah da ba su ganuwa, wato ikonsa madawwami da Allahntakarsa, a sarari ake ganinsu; ta wurin abubuwa da an halitta ana gāne su; har kuwa su rasa hujja.”—Rom. 1:20.

Ka yi amfani da abubuwan bincike da kake da shi a yarenku sa’ad da kake tattaunawa da mutane (Ka duba sakin layi na 5)

5. Ta yaya aka taimaka mana mu riƙa yin amfani da hankalinmu?

5 ‘Fahimtar’ wani abu yana nufin gane abin da ba za a iya gani nan da nan ba. (Ibran. 11:3) Saboda haka, mutane masu fahimi ba sa amfani da idanunsu da kunnuwansu kawai, amma suna amfani da tunaninsu. Ƙungiyar Jehobah ta tanadar mana da abubuwan yin bincike da za su taimaka mana. Waɗannan abubuwan za su iya taimaka mana mu ‘ga’ Mahaliccinmu da idanunmu na bangaskiya. (Ibran. 11:27) Waɗannan abubuwan sun ƙunshi wasu talifofin Hasumiyar Tsaro. [1] Ƙari ga haka, a cikin mujallar Awake! akan gana da masanan kimiyya da kuma wasu da suka bayyana abin da ya sa suka soma gaskatawa da Allah. Jerin talifofin nan masu jigo “Was It Designed?” sun nuna misalan halittu masu ban sha’awa. Sau da yawa masanan kimiyya sukan kwaikwayi waɗannan halittu masu ban al’ajabi.

6. Me ya sa yake da kyau ku yi amfani da abubuwan da ƙungiyar Jehobah take tanadar mana, kuma ta yaya kuka amfana?

6 Wani matashi ɗan shekara 19 a Amirka ya yi magana a kan ƙasidu biyu a Turanci da suka tattauna game da kimiyya da suka taimaka masa. Ya ce: “Waɗannan ƙasidun sun taimaka mini sosai. Na yi nazarinsu sau da yawa.” Wata ’yar’uwa a Faransa ta rubuta cewa: “Talifofin nan ‘Was It Designed?’ suna da ban sha’awa! Sun nuna cewa ƙwararrun injiniyoyi suna iya kwaikwayon halittu amma abubuwan da suke ƙerawa ba za su taɓa yin daidai da wanda aka halitta ba.” Wasu iyaye a Afirka ta Kudu da suke da yarinya ’yar shekara 15 sun ce: “Talifi na farko da ’yarmu take karantawa a cikin Awake! shi ne inda ake ganawa da masanan kimiyya da kuma wasu.” Kai kuma fa? Kana karanta waɗannan abubuwan kuwa? Za su sa ka kasance da bangaskiya sosai kamar bishiya da jijiyarta ta kahu cikin ƙasa. Kasancewa da irin wannan bangaskiyar zai taimaka maka ka guji koyarwar ƙarya.—Irm. 17:5-8.

KU GASKATA DA LITTAFI MAI TSARKI

7. Me ya sa Allah yake so ka auna dukan abubuwa?

7 Shin ya kamata mu yi tambayoyin da suka dace game da Littafi Mai Tsarki? E! Jehobah yana so mu “auna” dukan abubuwa don mu tabbatar wa kanmu cewa hakan gaskiya ne. Ba ya so ka gaskata da wani abu domin wasu sun yi hakan. Saboda haka, ka yi tunani sosai don ka san gaskiyar al’amarin. Hakan zai sa ka kasance da bangaskiya sosai. (Karanta 1 Tasalonikawa 5:21; 1 Timotawus 2:4.) Hanya ɗaya da za ka yi hakan ita ce ta wurin yin nazarin wasu batutuwan da za ka so ka ƙara yin bincike a kansu.

8, 9. (a) Waɗanne batutuwa ne wasu suke jin daɗin yin nazari a kai? (b) Ta yaya wasu suka amfana ta yin bimbini a kan abin da suka yi nazarinsa?

8 Wasu suna jin daɗin nazarin annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki, ko kuma su gwada ko labaran da ke cikin Littafi Mai Tsarki ya yi daidai da abin da masu ilimin tarihi da masanan kimiyya ko kuma masu tona kayan tarihi suka faɗa. Alal misali, Jehobah ya furta annabcin da ke cikin Farawa 3:15 bayan da Adamu da Hauwa’u suka yi masa tawaye kuma suka ƙi sarautarsa. Wannan shi ne annabci na farko da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuma ya taimaka mana mu fahimci cewa yadda Allah yake sarauta ne ya fi kyau, kuma mulkinsa ne zai kawo ƙarshen dukan wahala. Ta yaya za ku iya yin nazarin littafin Farawa 3:15? Za ku iya rubuta ayoyin Littafi Mai Tsarki da suka ba da ƙarin haske a kan yadda wannan annabcin zai cika. Bayan haka, kuna iya yin bincike don ku san lokacin da aka rubuta waɗannan ayoyin kuma ku rubuta su bi da bi. Ba da daɗewa ba, za ku fahimci cewa marubutan Littafi Mai Tsarki sun yi bayani dalla-dalla a kan wannan annabcin duk da cewa sun yi rayuwa a lokatai dabam-dabam. Hakan zai taimaka muku ku san cewa “ruhu mai tsarki ne” ya yi musu ja-gora.—2 Bit. 1:21.

9 Wani ɗan’uwa a Jamus ya yi tunani a kan yadda kowane littafin da ke cikin Littafi Mai Tsarki ya yi bayani dalla-dalla game da Mulkin Allah. Ya ce: “Hakan gaskiya ne ko da yake maza 40 ne suka rubuta Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, da yawa a cikinsu sun yi rayuwa a lokaci dabam-dabam kuma ba su san juna ba.” Wata ’yar’uwa daga Ostareliya ta yi nazarin wani talifi a cikin Hasumiyar Tsaro na 15 ga Disamba, 2013, kuma ta fahimci yadda Idin Ƙetarewa yake da alaƙa da Farawa 3:15 da kuma zuwan Almasihu. Ta ce: “Wannan nazarin ya koya mini abubuwa masu ban al’ajabi game da Jehobah. Yadda Jehobah ya shirya wannan idin don Isra’ilawa da kuma yadda Yesu ya cika wannan annabcin ya burge ni sosai. Na dakata kuma na yi tunani a kan yadda wannan Idin Ƙetarewar yake da muhimmanci sosai!” Me ya sa wannan ’yar’uwar ta ji hakan? Ta yi tunani ne sosai a kan abin da ta karanta kuma ta ‘fahimce’ shi. Hakan ya ƙarfafa bangaskiyarta kuma ya sa ta kusaci Jehobah sosai.—Mat. 13:23.

10. Ta yaya yadda marubutan Littafi Mai Tsarki suka faɗa gaskiya ya sa kuka gaskata abin da suka rubuta?

10 Wani batu kuma da zai ƙarfafa bangaskiyarmu shi ne yadda mutanen da suka rubuta Littafi Mai Tsarki suke da gaba gaɗi kuma suka faɗi gaskiya. Marubuta da yawa a zamanin dā sukan rubuta abubuwa masu kyau kawai game da ƙasashensu da kuma shugabanansu. Amma, annabawan Jehobah ba su yi hakan ba. Sun rubuta kasawar mutanensu, har da sarakunansu. (2 Laba. 16:9, 10; 24:18-22) Ƙari ga haka, sun rubuta kurakuransu da kuma na wasu bayin Allah. (2 Sam. 12:1-14; Mar. 14:50) Wani matashi a Biritaniya ya ce: “Da kyar ka ga irin waɗannan mutane masu faɗin gaskiya a yau, hakan ya sa mun ƙara kasancewa da tabbaci cewa Jehobah ne mawallafin Littafi Mai Tsarki.”

11. Ta yaya matasa za su ƙara nuna godiya don amfanin bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki?

11 Mutane da yawa sun ga amfanin barin Littafi Mai Tsarki ya yi musu ja-gora, kuma hakan ya tabbatar musu cewa Allah ne ya hure waɗanda suka rubuta Littafi Mai Tsarki. (Karanta Zabura 19:7-11.) Wata matashiya a Japan ta ce: “Muna farin ciki a iyalinmu idan muka yi abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Mukan kasance da salama da haɗin kai, kuma muna ƙaunar juna.” Bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki yana taimaka mana mu guji koyarwar ƙarya. (Zab. 115:3-8) Koyarwar da ke nuna cewa babu Allah yana shafan mutane kuwa? E, alal misali koyarwar juyin halitta yana sa mutane su mai da halittu allahnsu maimakon Jehobah. Waɗanda suka ce babu Allah suna da’awa cewa ’yan Adam ne za su iya kawo rayuwa mai kyau a nan gaba. Amma, har yanzu ba su iya magance matsalolin da mutane suke fuskanta ba.—Zab. 146:3, 4.

YADDA ZA KU TATTAUNA DA WASU

12, 13. Wace hanya ce ta fi dacewa a tattauna batun halitta ko kuma Littafi Mai Tsarki da abokan makaranta da malamai ko kuma wasu?

12 Ta yaya za ku iya tattaunawa da mutane game da halitta da kuma Littafi Mai Tsarki? Da farko, kada ku yi saurin tunanin cewa ku san abin da wasu suka yi imani da shi. Wasu mutane sun ce sun gaskata da juyin halitta amma suna ganin akwai Allah. Suna ganin Allah ya yi amfani da juyin halitta don ya halicci abubuwa masu rai. Wasu sun gaskata da juyin halitta domin suna ganin cewa idan hakan ba gaskiya ba ce ba za a riƙa koyar da shi a makaranta ba. Ƙari ga haka, wasu sun daina yin imani da Allah domin abubuwa marasa kyau da addinai suke yi. Saboda haka, sa’ad da kuke tattaunawa da wani game da halitta, zai dace ku yi masa tambayoyi tukuna don ku san abin da mutumin ya yi imani da shi. Zai so ya saurare ku idan kuka kasance da sauƙin kai kuma kuna shirye ku saurare shi.—Tit. 3:2.

13 Idan wani ya ce kai wawa ne don ka yi imani da halitta, kana iya gaya masa cikin ladabi ya bayyana maka yadda aka soma rayuwa idan babu Mahalicci. Ƙari ga haka, kana iya ce masa idan koyarwar juyin halitta gaskiya ce, da halitta na farko za ta ci gaba da fito da kamanninta. Wani farfesan kemistri ya ce wasu daga cikin abubuwan da halittar take bukata don ta iya fito da kamaninta su ne (1) wani abu kamar fata da zai kāre ta, (2) yadda za ta samu kuzari kuma ta yi amfani da shi, (3) yadda za ta samu bayanin da zai ja-goranci siffarta da kuma girmarta, da kuma (4) yadda za ta ci gaba da fito da wannan bayani. Farfesan ya daɗa cewa: “Muna mamakin yadda halittu suke da wuyar fahimta komin ƙanƙantarsu.”

14. Mene ne za ka yi idan ba ka yi shirin tattauna batun juyin halitta da wani ba?

14 Idan ba ka yi shirin tattauna batun juyin halitta da wani ba, kana iya yin abin da Bulus ya yi. Ya rubuta: “Kowane gida akwai mai-kafa shi; amma wanda ya kafa dukan abu Allah ne.” (Ibran. 3:4) Irin wannan kwatanci zai taimaka! Hakika, wani mai basira sosai ne ya ƙera abubuwa masu kyau. Ƙari ga haka, kana iya yin amfani da littattafan da suka dace da batun da kuke tattaunawa. Wata ’yar’uwa ta yi amfani da ƙasidu biyu da aka ambata ɗazu don ta taimaka wa wani matashin da bai gaskata cewa akwai Allah ba amma ya gaskata da juyin halitta. Bayan mako guda, sai matashin ya ce, “Yanzu na gaskata cewa akwai Allah.” Hakan ya sa aka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Yanzu wannan matashin ya zama Mashaidi.

15, 16. Ta yaya za ku kyautata yadda kuke tattauna Littafi Mai Tsarki da mutane, kuma mene ne maƙasudinku?

15 Za ku iya bin ƙa’idar da aka tattauna ɗazu sa’ad da kuke tattaunawa da wanda yake shakkar abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Ku yi masa tambayoyi don ku san ainihin abin da ya yi imani da shi da kuma batutuwa da yake son tattaunawa. (Mis. 18:13) Idan yana so batutuwan da suka shafi kimiyya, zai iya saurararku sa’ad da kuke ambata abubuwan da suka nuna cewa Littafi Mai Tsarki daidai ne in ya zo ga batun kimiyya. Wasu mutane suna iya saurararku idan kuka nuna musu wani abu da ke cikin littattafan tarihi kuma kuka nuna musu cewa Littafi Mai Tsarki ya annabta hakan shekaru da yawa kafin su faru. Ko kuma ku nuna musu wani abu a cikin Littafi Mai Tsarki da zai kyautata rayuwarsu, kamar ƙa’idodin da ke cikin Huɗuba a kan Dutse.

16 Ku tuna cewa kuna so ku faɗi abin da zai ratsa zuciyar mutanen ba don ku ci musu ba. Saboda haka, ku saurari abin da za su faɗa. Ku yi tambayoyin da suka dace kuma ku furta ra’ayinku cikin ladabi da sauƙin kai, musamman ma sa’ad da kuke tattaunawa da tsofaffi. Hakan zai sa su saurari ra’ayinku. Ƙari ga haka, za su san cewa kun yi tunani sosai a kan abubuwan da kuka yi imani da su. Kuma wannan abu ne da matasa da yawa ba su yi ba. Hakika, ku tuna cewa ba wajibi ba ne ku saurari waɗanda suke so su yi muku ba’a don abin da kuka yi imani da shi.—Mis. 26:4.

KU KASANCE DA TABBACI GAME DA IMANINKU

17, 18. (a) Mene ne zai taimaka muku ku kasance da tabbaci game da imaninku? (b) Wace tambaya ce za mu tattauna a talifi na gaba?

17 Ban da sanin muhimman koyarwar Littafi Mai Tsarki, muna bukatar mu yi wasu abubuwa don mu kasance da bangaskiya sosai. Saboda haka, ku riƙa yin binciken Kalmar Allah sosai kamar kuna neman dukiyoyi masu tamani. (Mis. 2:3-6) Ku yi amfani da abubuwan da muke da shi a yarenmu, kamar Watchtower LABURARE NA INTANE da kuma Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah. Ƙari ga haka, kuna iya kafa maƙasudin karance Littafi Mai Tsarki a cikin watanni 12. Hanyar da ta fi kyau da za mu ƙarfafa bangaskiyarmu ita ce ta wurin karanta Kalmar Allah. Sa’ad da wani mai kula da da’ira yake tunani game da lokacin da yake matashi, ya ce: “Karanta Littafi Mai Tsarki gabaki ɗaya ya taimaka mini in fahimci cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ce. Na fahimci labaran Littafi Mai Tsarki da na karanta tun ina ƙarami. Hakan ya taimaka mini sosai don in sami ci gaba a ƙungiyar Jehobah.”

18 Iyaye ne suke da hakkin koya wa yaransu game da Jehobah. Ta yaya za su taimaka musu su kasance da bangaskiya sosai? Za a tattauna wannan tambayar a talifi na gaba.

^ [1] (sakin layi na 5) Ka duba talifin nan “Al’amura Nasa da Ba Su Ganuwa, . . . a Sarari Ake Ganinsu” a cikin Hasumiyar Tsaro na 1 ga Satumba, 2013 shafi na 15, da kuma talifin nan “Halitta Tana Bayyana Allah Mai Rai” a cikin Hasumiyar Tsaro na 15 ga Oktoba, 2013, shafuffuka na 7-19.