Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ya Kāre Imaninsa a Gaban Manyan Sarakuna

Ya Kāre Imaninsa a Gaban Manyan Sarakuna

“SHI ma’aikacina ne zaɓaɓɓe, domin yā sanar da sunana ga al’ummai, da sarakuna.” (A. M. 9:15, Littafi Mai Tsarki) Abin da Yesu ya ce ke nan game da wani Bayahude da ya zama Kirista, wanda da daga baya ya zama manzo Bulus.

Ɗaya daga cikin waɗannan ‘sarakunan’ shi ne sarkin Roma mai suna Nero. Yaya za ka ji idan aka ce ka kāre imaninka a gaban irin wannan sarkin? Hakan ba shi da sauƙi amma an ƙarfafa Kiristoci su yi koyi da Bulus. (1 Kor. 11:1) Kuma hanya ɗaya da za mu iya yin koyi da shi ita ce ta yin la’akari da abubuwan da Bulus ya fuskanta da kuma yadda ya bi da tsarin shari’a a zamaninsa.

Dokar da Allah ya ba da ta hannun Musa ita ce dokar da ake bi a ƙasar Isra’ila kuma ita ce Yahudawa suke bi a ko’ina. Bayan ranar Fentakos ta shekara ta 33, bayin Allah ba sa bukatar su bi wannan dokar kuma. (A. M. 15:28, 29; Gal. 4:9-11) Duk da haka, Bulus da kuma Kiristoci suna mutunta dokar, kuma suna yi wa Yahudawa da yawa wa’azi a yankunansu ba tare da matsala ba. (1 Kor. 9:20) Hakika, sau da yawa Bulus yana zuwa majami’u don ya yi wa mutanen da suka san Allahn Ibrahim wa’azi kuma ya tattauna da su daga cikin nassosin Ibrananci.—A. M. 9:19, 20; 13:5, 14-16; 14:1; 17:1, 2.

Manzannin sun zaɓi Urushalima ta zama wurin da za a riƙa ja-gorar wa’azi. Kuma sukan yi koyarwa a haikalin a kai a kai. (A. M. 1:4; 2:46; 5:20) A wani lokaci, Bulus ya tafi Urushalima, kuma daga baya aka kama shi a wurin. Hakan ya sa aka soma shari’ar da ta kai shi har zuwa ƙasar Roma.

BULUS YA YI AMFANI DA DOKAR ROMA DON YA KĀRE IMANINSA

Yaya hukumomin ƙasar Roma suka ɗauki abin da Bulus yake wa’azi a kai? Kafin mu amsa wannan tambayar, bari mu yi la’akari da yadda Romawa suka ɗauki addini. Ba sa tilasta wa mutanen da ke zama a daularsu su bar addininsu, sai dai idan suna ganin cewa zai kawo wa ƙasarsu matsala ko kuma ya lalata ɗabi’ar mutanensu.

Ƙasar Roma ta ba wa Yahudawan da ke zama a daularsu ’yanci sosai. Littafin nan Backgrounds of Early Christianity ya ce: “A daular Roma, Yahudawa suna da babban matsayi. . . . Suna da ’yancin bin nasu addinin kuma ba a tilasta musu su bi addinin ƙasar Roma. A yankunansu, suna yin harkokinsu yadda suke so bisa ga dokarsu.” Ƙari ga haka, ba a tilasta musu su yi aikin soja. * Bulus zai iya yin amfani da ’yancin da dokar Romawa ta ba wa Yahudawa don ya kāre imanin Kiristoci.

Maƙiyan Bulus sun yi ƙoƙarin sa mutane da kuma hukumomi su tsane manzon. (A. M. 13:50; 14:2, 19; 18:12, 13) Bari mu yi la’akari da wani abin da ya faru. Dattawan ikilisiyar da ke Urushalima sun ji jita-jitan da Yahudawa suke yaɗawa game da wa’azin da Bulus yake yi, cewa yana koyar da mutane su “ridda daga Musa.” Irin waɗannan jita-jitan za su iya sa Yahudawan da ba su jima da zama Kiristoci ba su soma tunanin cewa Bulus ba ya bin tsarin Allah. Ƙari ga haka, ’yan Majalisa za su iya cewa addinin Kirista ridda ce daga addinin Yahudawa. Idan hakan gaskiya ce, za a hukunta Yahudawan da suke tarayya da Kiristoci. Za a ware su daga ƙasar kuma ba za a bar su su riƙa yin wa’azi a haikali ko kuma a majami’u ba. Saboda haka, sai dattawan ikilisiya suka ba wa Bulus shawarar ya nuna wa mutane cewa wannan jita-jitan da ake yaɗawa ba gaskiya ba ce, kuma zai yi hakan ne ta wurin zuwa haikali don ya yi abin da Allah bai bukace shi ba, amma yin hakan ba laifi ba ne.—A. M. 21:18-27.

Bulus ya bi shawarar da dattawan suka ba shi, kuma hakan ya ba shi damar kāre wa’azin da yake yi. (Filib. 1:7) Yahudawa sun yi zanga-zanga a haikalin kuma suka so su kashe Bulus. Amma kwamandan sojojin Roma ya ɗauki Bulus don ya tsare shi. A lokacin da ake so a yi wa Bulus bulala ne ya gaya musu cewa shi ɗan Roma ne. Don haka aka kai shi Kaisariya, wurin da Romawa suke mulkin Yahudiya. A wannan wurin, Bulus zai samu damar yin wa’azi da gaba gaɗi a gaban hukumomi. Wataƙila hakan ya sa mutane sun san game da addinin Kirista.

Littafin Ayyukan Mazanni sura 24 ta bayyana abin da Bulus ya fuskanta a gaban wani gwamnan Roma da yake mulkin Yahudiya mai suna Felix. Wannan gwamnan ya san wasu daga cikin koyarwar Kiristoci. Yahudawan sun ce Bulus yana karya dokar Romawa a aƙalla ta hanyoyi uku. Sun ce Bulus yana ta da zaune tsaye tsakanin Yahudawan da ke daular; sun ce yana ja-gorar ɗarika mai haɗari. Kuma yana ƙoƙarin ya ƙazantar da haikalin wanda take ƙarƙashin kariyar Romawa. (A. M. 24:5, 6) Waɗannan abubuwan da suka faɗa zai iya sa a yi wa Bulus hukuncin kisa.

Ya kamata Kiristoci a yau su yi la’akari da yadda Bulus ya bi da wannan yanayin. Bulus ya natsu kuma ya daraja su. Ya nuna musu cewa bisa ga Doka da kuma abin da annabawa suka rubuta, yana da ’yancin bauta wa ‘Allah na ubanninsa.’ Kuma a dokar Romawa, an ba wa Yahudawan da ke daularsu irin wannan ’yancin. (A. M. 24:14) Bayan haka, Bulus ya kāre da kuma bayyana imaninsa a gaban Porcius Festus da kuma Sarki Hirudus Agaribas.

A ƙarshe, don kada a yi maguɗi, Bulus ya ce: “Na ɗaukaka roƙo zuwa wurin Kaisar.” A lokacin, Kaisar ne sarki mafi iko a duniya.—A. M. 25:11.

BULUS A KOTUN KAISAR

Wani mala’ika ya gaya wa Bulus cewa: “Dole za ka tsaya gaban Kaisar.” (A. M. 27:24) Lokacin da ya soma sarauta, sarki Nero ya ce ba zai yi shari’a shi kaɗai ba. Ya yi shekara takwas ba ya shari’a shi kaɗai amma yakan tura wa wasu hakkin yin hakan. Littafin nan The Life and Epistles of Saint Paul ya ce duk sa’ad da aka kawo wa Nero ƙara, yana saurarar ƙarar a fadarsa kuma yakan nemi shawarar ƙwararrun mutane a batun.

Littafi Mai Tsarki bai ce ko Nero ya saurari ƙarar da aka kawo game da Bulus ba kuma bai ce ko ya ba wa wani hakkin yi wa Bulus shari’a ba. Amma a dukan waɗannan yanayin, Bulus ya bayyana musu cewa shi yana bauta wa Allahn Yahudawa kuma yana ƙarfafa mutane su riƙa girmama masu mulki. (Rom. 13:1-7; Tit. 3:1, 2) Kamar dai Bulus ya yi nasara a yadda ya kāre imaninsa a gaban sarakuna domin kotun Kaisar ya sake shi.—Filib. 2:24; Fil. 22.

YADDA MUKE KĀRE IMANINMU

Yesu ya gaya wa mabiyansa: “Kuma a gaban mahukunta da sarakuna za a kawo ku sabili da ni, domin shaida garesu da Al’ummai.” (Mat. 10:18) Babban gatan ne mu riƙa wa’azi game da Yesu a gaban sarakuna. Ƙoƙarin da muke yi don mu kāre imaninmu yana iya kawo sakamako mai kyau. Hakika, ko da mene ne ’yan Adam suka yi, Jehobah ne kaɗai yake ba mu hakkin yin wa’azi. Mulkin Allah ne kawai zai iya kawo ƙarshen wahala da kuma rashin adalci.—M. Wa. 8:9; Irm. 10:23.

Ko a yau, Kiristoci suna ɗaukaka sunan Jehobah sa’ad da suka kāre imaninsu. Kamar yadda Bulus ya yi, muna bukatar mu natsu kuma mu kasance da aminci da kuma gaba gaɗi. Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa ba sa bukatar su ‘yi tattalin yadda za su amsa: gama zai ba su baki da hikima wadda dukan maƙiyansu ba za su sami iko su yi tsayayya ba ko kuwa su yi musunta’ ba.—Luk. 21:14, 15; 2 Tim. 3:12; 1 Bit. 3:15.

Sa’ad da Kiristoci suka kāre imaninsu a gaban sarakuna da gwamnoni, hakan zai iya ba wa mutanen da ba su san mu ba damar sani game da Jehobah. Wasu shari’ar da aka yi a kotu sun sa an yi canje-canje a tsarin dokoki kuma hakan ya ba mu damar yin wa’azi da kuma ibada. Ko da mene ne sakamakon waɗannan shari’o’i, Jehobah yana farin ciki da yadda bayinsa suka kasance da gaba gaɗi sa’ad da suke fuskantar gwaji.

Muna sanar da sunan Jehobah sa’ad da muke kāre imaninmu

^ sakin layi na 8 Wani marubuci mai suna James Parkes ya ce: “Yahudawa . . . suna da ’yancin bin al’adarsu. Wannan ba wani abin a zo a gani ba ne ga Romawa domin bisa ga al’adarsu suna ba wa mutanen da suke daularsu ’yancin bin addinin da suke so.”