Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

‘Bari Hakuri Ya Cika Aikinsa’

‘Bari Hakuri Ya Cika Aikinsa’

“Bari haƙuri shi cika aikinsa, domin ku kamilta, ku cika kuma, ba ragaggu ne cikin kome ba.”—YAƘUB 1:4.

WAƘOƘI: 135, 139

1, 2. (a) Mene ne za mu iya koya daga yadda Gidiyon da sojojinsa 300 suka jimre? (Ka duba hoton da ke wannan shafin.) (b) Bisa ga Luka 21:​19, me ya sa jimiri yake da muhimmanci sosai?

KA YI tunanin yaƙin da Alƙali Gidiyon da sojojin Isra’ila suka yi da magabtansu. Hakika, yaƙi ne mai wuya da kuma ban gajiya. Gidiyon da sojojinsa sun kori Midiyanawa da magoya bayansu da dare har na kusan tsawon kilomita talatin da biyu! Littafi Mai Tsarki ya bayyana abin da ya faru bayan haka: “Sa’annan Gideon ya zo Urdun, ya ƙetare, shi, da mutane ɗari uku da ke tare da shi, gajiyayyu.” Amma ba su ci yaƙin ba tukun don har ila suna bukatar su yaƙi sojoji dubu goma sha biyar. Magabtan sun yi shekaru da yawa suna zaluntar Isra’ilawa. Saboda haka, Isra’ilawa sun dāge sai sun yi nasara a kansu. Ƙari ga haka, Gidiyon da sojojinsa suka ci gaba da bin magabtansu har suka ci su a yaƙin!​—⁠Alƙalawa 7:22; 8:​4, 10, 28.

2 Mu ma a yau muna filin dāga, muna yaƙin da ke sa mu gajiya. Magabtanmu sun ƙunshi Shaiɗan da duniyarsa da kuma ajizancinmu. Wasu cikinmu mun yi shekaru da yawa muna yaƙi da waɗannan magabtan, kuma da taimakon Jehobah mun yi nasara a ɓangarori da yawa. Amma, har ila yaƙin bai ƙare ba kuma mukan gaji a wani lokaci. Ƙari ga haka, mukan gaji da jiran ƙarshen wannan mugun zamani. Yesu ya yi mana gargaɗi cewa a kwanaki na ƙarshe za mu fuskanci gwaji mai tsanani kuma za a tsananta mana sosai. Amma ya ce idan muka jimre za mu ci nasara. (Karanta Luka 21:19.) Mene ne jimiri? Mene ne zai taimaka mana mu jimre? Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga waɗanda suka jimre? Kuma ta yaya za mu ‘bar haƙuri ya cika aikinsa’?—Yaƙub 1:4.

MENE NE HAƘURI?

3. Mene ne haƙuri?

3 A cikin Littafi Mai Tsarki, haƙuri yana nufin jimre da wani yanayi mai wuya. Ya ƙunshi yadda muke tunani da kuma yadda muke ji game da gwajin da muke fuskanta. Haƙuri yana taimaka mana mu kasance da gaba gaɗi da kuma aminci. Wani littafin bincike ya ce haƙuri hali ne da ke taimaka mana mu kasance da bege kuma ƙi yin sanyin gwiwa sa’ad da muke fuskantar gwaji. Yana taimaka mana mu yi tsayin daka a lokacin da muke fuskantar gwaji masu tsanani sosai. Hakan zai sa mu shawo kan waɗannan gwajin kuma mu mai da hankali ga yadda za mu cim ma maƙasudinmu.

4. Me ya sa muka ce ƙauna ce take taimaka mana mu kasance da haƙuri?

4 Ƙauna tana motsa mu mu jimre da yanayi dabam-dabam. (Karanta 1 Korintiyawa 13:​4, 7.) Alal misali, idan muna ƙaunar Jehobah za mu iya jimre da kowane yanayi. (Luka 22:​41, 42) Idan muna ƙaunar ‘yan’uwanmu za mu iya jimre da ajizancinsu. (1 Bitrus 4:⁠8) Ƙaunar abokin aurenmu tana taimaka mana mu jimre da “wahala” ko kuma matsalolin da ke tattare da aure. Ƙari ga haka, za ta taimaka musu su kyautata zaman aurensu.—1 Korintiyawa 7:28.

MENE NE ZAI TAIMAKE KA KA JIMRE?

5. Me ya sa Jehobah ne zai fi taimaka mana mu jimre da yanayinmu?

5 Ka roƙi Jehobah ya ƙarfafa ka. Jehobah shi ne “Allah na haƙuri da na ta’aziya.” (Romawa 15:⁠5) Ya fahimci yanayinmu da yadda muke ji da kuma tarbiyyarmu fiye da kowa. Saboda haka, ya san ainihin abin da muke bukata don mu jimre. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Za ya biya muradin waɗanda ke tsoronsa; Za ya kuma ji kukarsu, ya cece su.” (Zabura 145:19) Amma ta yaya Allah zai amsa addu’o’inmu kuma ya ba mu ƙarfin jimrewa da matsaloli?

Jehobah ya fahimci yanayinmu da yadda muke ji kuma ya san ainihin abin da muke bukata don mu jimre

6. Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce, ta yaya Jehobah zai yi mana “hanyar tsira” sa’ad da muke fuskantar gwaji?

6 Idan muka roƙi Jehobah ya taimaka mana mu jimre, ya yi alkawari zai yi mana “hanyar tsira.” (Karanta 1 Korintiyawa 10:13.) Ta yaya yake yin hakan? A wani lokaci, yana iya kawar da gwajin. Amma a yawancin lokaci, zai sa mu kasance da “haƙuri da jimrewa tare da farinciki.” (Kolosiyawa 1:11) Ƙari ga haka, da yake ya san kasawarmu sosai, Jehobah ba zai ƙyale yanayinmu ya yi muni ainun kuma ya fi ƙarfinmu har mu kasa kasancewa da aminci ba.

7. Ka ba da misalin da ya nuna cewa muna bukatar abubuwa masu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah don mu jimre da matsaloli.

7 Ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da littattafan da ƙungiyar Jehobah take wallafawa don ka ƙarfafa bangaskiyarka. Me ya sa hakan yake da muhimmanci? Alal misali: Idan mutum yana so ya hau wani dutse mai tsawo sosai, yana bukatar ya ci abinci sosai fiye da yadda ya saba ci. Hakazalika, muna bukatar mu riƙa koyan abubuwan masu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah kuma muna bukatan hakan sosai don mu jimre da yanayi dabam-dabam da muke fuskanta kuma mu cim ma maƙasudinmu. Wajibi ne mu riƙa yin nazari Littafi Mai Tsarki kuma mu riƙa halartan taro. Yin waɗannan ayyuka za su ƙarfafa bangaskiyarmu sosai.​—Yohanna 6:27.

8, 9. (a) Bisa ga abin da ke littafin Ayuba 2:​4, 5, mene ne gwajin da muke fuskanta ya ƙunsa? (b) Wane yanayi ne za ka iya yin tunaninsa sa’ad da kake fuskantar gwaji?

8 Ka tuna da amincinka ga Allah. Sa’ad da muke fuskantar gwaji, mu tuna cewa hakan ya ƙunshi amincinmu ga Allah, ba wahalar da muke sha kawai ba. Amma yadda muka bi da gwajin zai nuna ko mun ɗauki Jehobah a matsayin Maɗaukakin Sarki ko a’a. Ta yaya? Magabcin Allah, wato Shaiɗan ba ya son sarautar Allah kuma ya zargi Jehobah cewa ‘yan Adam suna bauta masa don abubuwan da yake ba su. Shaiɗan ya ce mutum zai iya ba da duk wani abin da “yake da shi . . . a bakin ransa.” Shaiɗan ya gaya wa Jehobah game da Ayuba: “Miƙa hannunka yanzu kaɗai, ka taɓa ƙashinsa da namansa, sai shi la’anta ka a fuskarka.” (Ayuba 2:​4, 5) Shin Shaiɗan ya canja tun lokacin da ya yi wannan maganar ne? A’a! Shekaru da yawa bayan lokacin da aka jefo shi daga sama zuwa duniya, ya ci gaba da zargin bayin Allah masu aminci. (Ru’ya ta Yohanna 12:10) Har ila, Shaiɗan yana da’awa cewa ‘yan Adam suna bauta wa Allah don abubuwan da yake ba su ne. Yana so mu yi tawaye da sarautar Allah kuma mu daina bauta masa.

9 Sa’ad da kake fuskantar wani gwaji, ka yi tunanin wannan yanayin. Shaiɗan da aljanu suna kallonka don su ga abin da za ka yi kuma suna da’awa cewa ba za ka kasance da aminci ba. A wani ɓangaren kuma, Jehobah da Sarkinmu Yesu Kristi da shafaffun da suka je sama da kuma dubban mala’iku suna ganin yadda kake fama kuma suna ƙarfafa ka. Idan ka jimre kuma ka kasance da aminci ga Jehobah, za su yi farin ciki sosai. Sai ka ji muryar Jehobah yana gaya maka cewa: “Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata: domin in mayar da magana ga wanda ya zarge ni.”​—Misalai 27:11.

Yesu ya mai da hankali ga ladar da zai samu idan ya jimre

10. Ta yaya za ka iya yin koyi da Yesu ta wajen mai da hankali ga ladan da za ka samu idan ka jimre da gwaji?

10 Ka mai da hankali ga ladan da za ka samu. A ce kana tafiya mai nisa da daddare, sai ka tsaya a hanya, kuma ko’ina ya yi duhu. Duk da haka, kana da tabbaci cewa idan ka ci gaba da yin tafiya, ba da daɗewa ba gari zai waye kuma za ka ga haske. Rayuwa tana kamar wannan tafiya mai nisa. Za ka fuskanci yanayi mai wuya kuma kana iya jin cewa matsalolinka sun shawo kanka. Yesu ma ya fuskanci irin wannan yanayin don sa’ad da ake rataye shi a kan gungumen azaba, an wulakanta shi kuma ya sha azaba sosai. Babu shakka, wannan yanayi ne mai wuya sosai a rayuwarsa! Amma mene ne ya taimaka masa ya jimre? Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu ya mai da hankali ga “farin cikin da aka sa gabansa.” (Ibraniyawa 12:​2, 3, Littafi Mai Tsarki) Yesu ya mai da hankali ga ladan da za a ba shi idan ya jimre. Ƙari ga haka, abin da ya fi masa muhimmanci, shi ne zai kasance cikin waɗanda za su tsarkake sunan Allah da kuma amince da sarautar Allah. Ya san cewa gwajin na ɗan lokaci ne kuma ladar da zai samu zai dawwama. A yau, gwajin da muke fuskanta zai iya shawo kanmu, amma ya kamata mu tuna cewa gwajin na ɗan lokaci ne kawai.

“WAƊANDA SUKA JIMRE”

11. Me ya sa ya kamata mu tattauna labaran “waɗanda suka jimre”?

11 Muna da misalai da yawa na waɗanda suka jimre gwaji dabam-dabam. Sa’ad da manzo Bitrus yake ƙarfafa Kiristoci su jimre da gwaji da yawa daga Shaiɗan, ya rubuta cewa: “Ku tsaya masa fa, kuna tabbatawa cikin bangaskiyarku, kuna kuwa sani ‘yan’uwanku da ke cikin duniya suna shan waɗannan azabai da kuke sha.” (1 Bitrus 5:⁠9) Labaran “waɗanda suka jimre” suna koya mana yadda za mu kasance da aminci kuma suna tabbatar mana cewa za mu iya yin nasara. Ƙari ga haka, labaran suna tuna mana cewa za mu sami lada idan muka kasance da aminci. (Yaƙub 5:11) Bari mu tattauna wasu misalai. [1]​—Ka duba ƙarin bayani.

12. Wane darasi ne muka koya daga misalin mala’ikun da aka saka a Adnin?

12 Cherubim mala’iku ne masu iko sosai. Sa’ad da Adamu da Hawwa’u suka yi zunubi, Jehobah ya ba wasu cherubim sabon aiki a duniya. Wannan aikin dabam ne da wanda suke yi a sama. Misalinsu ya koya mana cewa za mu iya jimre sa’ad da aka ba mu aiki mai wuya. Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah “ya sanya Cherubim, da takobi mai-harshen wuta mai-juyawa a kowace fuska” a gabashin gonar Adnin, “domin a tsare hanyar itace na rai.” [2] (Ka duba ƙarin bayani.) (Farawa 3:24) Littafi Mai Tsarki bai ce mala’ikun sun yi gunaguni ko kuma sun ɗauka cewa sun fi ƙarfin wannan aikin ba. Ƙari ga haka, ba su gaji ba kuma ba su karaya ba. Maimakon haka, sun ci gaba da yin aikinsu har suka gama, wataƙila sun yi fiye da shekaru 1,600 suna yin haka, wato har lokacin Rigyawa a zamanin Nuhu!

13. Ta yaya Ayuba ya sami ƙarfin jimre gwajin da ya fuskanta?

13 Ayuba mutum mai aminci ne. Wani lokaci za ka yi baƙin ciki domin abokinka ko kuma wani a iyalinku ya faɗi wani abu da ya sa ka sanyin gwiwa. Ko kuma kana rashin lafiya mai tsanani ko kana baƙin ciki domin wani da kake ƙauna ya mutu. Ko da mene ne ya faru, misalin Ayuba zai iya ƙarfafa ka. (Ayuba 1:​18, 19; 2:​7, 9; 19:​1-3) Ayuba bai san dalilin da ya sa ya soma shan wahala farat ɗaya ba, amma bai karaya ba. Mene ne ya taimake shi ya jimre? Na farko shi ne yana ƙaunar Jehobah kuma ba ya son ya ɓata masa rai. (Ayuba 1:⁠1) Ayuba yana son ya faranta wa Allah rai a kowane lokaci har da lokacin da yake jin daɗi da kuma lokacin da yake wahala. Ƙari ga haka, Jehobah ya taimaka wa Ayuba ya ga ikonsa ta wajen gaya masa game da wasu cikin halittunsa masu ban al’ajabi. Hakan ya ƙara tabbatar wa Ayuba cewa Jehobah zai kawo ƙarshen wahalar da yake sha a lokacin da ya dace. (Ayuba 42:​1, 2) Abin da ya faru ke nan. “Ubangiji kuma ya fito da Ayuba daga bautar . . . ya mayar wa Ayuba sau biyu duk abin da yake da shi a dā.” Jehobah ya ba shi dogon kwana kuma ya yi rayuwa mai gamsarwa.​—Ayuba 42:​10, 17.

14. Bisa ga 2 Korintiyawa 1:​6, ta yaya yadda Bulus ya jimre ya taimaka wa wasu?

14 Manzo Bulus. Shin kana fuskantar hamayya ko kuma ana tsananta maka sosai? Shin kai dattijo ne a ikilisiya ko kuma mai kula da ɗa’ira da kake ganin aiki ya yi maka yawa? Idan haka ne, misalin Bulus zai iya taimaka maka. Bulus ya sha wahala sosai, kuma a kowane lokaci, ya damu da yanayin ‘yan’uwa a ikilisiyoyi. (2 Korintiyawa 11:​23-29) Amma Bulus bai karaya ba kuma misalinsa ya ƙarfafa wasu su jure. (Karanta 2 Korintiyawa 1:6.) Hakazalika, idan kana jurewa, za ka ƙarfafa wasu su yi hakan.

HAƘURI ZAI “CIKA AIKINSA” A GARE KA KUWA?

15, 16. (a) Ta yaya haƙuri zai cika “aikinsa”? (b) Ka ba da misalai a kan yadda za mu iya sa haƙuri ya “cika aikinsa.”

15 An hure almajiri Yaƙub ya rubuta cewa: “Bari haƙuri shi cika aikinsa, domin ku kamilta, ku cika kuma, ba ragaggu ne cikin kome ba.” (Yaƙub 1:⁠4) Ta yaya haƙuri zai cika “aikinsa” a gare mu? Gwajin da muke fuskanta zai sa mu gane cewa muna bukatar mu daɗa kasancewa masu haƙuri da masu godiya da kuma ƙaunar mutane. Yayin da muke jimre da gwajin, za mu kyautata yadda muke nuna waɗannan halayen kuma hakan zai taimaka mana mu ƙara kusantar Jehobah.

Idan muka jimre gwaji, za mu kyautata halayenmu (Ka duba sakin layi na 15, 16)

16 Da yake yin haƙuri zai sa mu zama Kiristoci masu halin kirki, ba za mu so mu ƙarya dokar Jehobah don mu guji wahala ba. Alal misali, idan kana fama da tunanin banza, kada ka bar gwajin ya shawo kanka! Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka daina tunanin banza. Shin kana da wani a cikin iyalinku da ke tsananta maka? Kada ka karaya! Ka ƙudura niyya cewa za ka ci gaba da bauta wa Jehobah. Hakan zai sa ka ƙara dogara ga Jehobah. Ka tuna cewa: Idan muna so Allah ya amince da mu, wajibi ne mu jimre.​—Romawa 5:​3-5; Yaƙub 1:12.

17 Wajibi ne mu jimre har ƙarshe, ba na ɗan lokaci ba. Alal misali, a ce wani jirgin ruwa yana nitsewa. Don fasinjojin su tsira, wajibi ne su yi iyo zuwa bakin teku. Wanda ya karaya tun daga farko zai nitse. Ƙari ga haka, wanda ya karaya kafin ya isa bakin teku, shi ma zai nitse. Idan muna so mu shiga sabuwar duniya, muna bukatar mu ci gaba da kasancewa da jimiri. Saboda haka, ya kamata mu kasance da halin manzo Bulus, wanda ya ce: Ba za mu yi “yaushi” ba, wato ba za mu karaya ba.​—⁠2 Korintiyawa 4:​1, 16.

17, 18. (a) Ka ba da misalin da ya nuna cewa yin jimiri har zuwa ƙarshen zamani yana da muhimmanci. (b) Yayin da ƙarshen yake gabatowa, wane tabbaci ne muke da shi?

18 Kamar Bulus, muna da tabbaci sosai cewa Jehobah zai taimaka mana mu jimre har ƙarshen zamani. Bulus ya ce: “Cikin dukan waɗannan al’amura mun fi gaban masu-nasara ta wurin wanda ya ƙaunace mu. Gama na kawar da shakka, ba mutuwa, ba rai, ba mala’iku, ba sarautai, ba al’amuran yanzu, ba al’amura na zuwa, ba ikoki, ba tsawo, ba zurfi, ba kuwa wani halittaccen abu, da za ya iya raba mu da ƙaunar Allah, wadda ke cikin Kristi Yesu Ubangijinmu.” (Romawa 8:​37-39) A wani lokaci mukan gaji. Amma bari mu yi koyi da Gidiyon da mutanensa. Sun gaji, amma ba su karaya ba kuma sun ci gaba da bin magabtansu.​—Alƙalawa 8:4.

^ [1] (sakin layi na 11) Za ka sami ƙarfafa idan ka karanta labaran mutanen Allah da suka jimre a zamaninmu. Alal misali, littafin Yearbook of Jehovah’s Witnesses na shekara ta 1992 da 1999 da kuma 2008 suna ɗauke da labarai masu ban ƙarfafa na ‘yan’uwanmu daga ƙasashen Ethiopia da Malawi da kuma Rasha.

^ [2] (sakin layi na 12) Littafi Mai Tsarki bai ambaci yawan cherubim da aka aika su yi aikin nan ba.