Ta Yaya Ba da Kai Yake Sa a Yabi Jehobah?
“Domin mutane kuma suka ba da kansu da yardan ransu, ku albarkaci Ubangiji.”
WAƘOƘI: 150, 10
1, 2. (a) Mene ne Eliphaz da Bildad suka ce game da bautar da muke yi wa Allah? (b) Ta yaya Jehobah ya tsauta musu?
‘ZAI yiwu mutum shi yi wa Allah wani amfani? Lallai mai-hikima yana da amfani ga kansa. Adalcinka wani abu mai-daɗi ne ga Mai-iko duka? Ko kamiltarka da wani amfani gare shi?’ (Ayu. 22:
2 Waɗannan abokan Ayuba marasa aminci sun ce duk ƙoƙarin da muke yi don bauta wa Jehobah bai da wani amfani a gare shi kuma mutane suna kamar gara ko kuma tsutsa kawai a gaban Allah. (Ayu. 4:19; 25:6) Da farko za mu iya ɗauka cewa Eliphaz da Bildad masu tawali’u ne sosai. (Ayu. 22:29) Domin daga kan dutse ko kuma daga cikin jirgin sama, za a iya ganin cewa ayyukan da mutanen suke yi ba shi da wani amfani. Amma haka ne Jehobah yake ɗaukan ƙwazon da muke yi don mu bauta masa sa’ad da yake kallon mu daga sama? A’a. Jehobah ya nuna hakan a lokacin da ya tsauta wa Eliphaz da Bildad da kuma Zophar don ƙaryar da suka yi. Amma ya kira Ayuba “bawana.” (Ayu. 42:
‘ME KA BA SHI?’
3. Mene ne Elihu ya faɗa game da ƙoƙarin da muke yi don mu bauta wa Jehobah, kuma mene ne yake nufi?
3 Jehobah bai tsauta wa Elihu don tambayoyin da ya yi cewa: “Ko mai-adalci ne kai, me ka ba shi [Allah] ke nan? Me ne kuwa ya karɓa a hannunka?” (Ayu. 35:7) Shin Elihu yana nufin cewa bautar da muke wa Jehobah bai da amfani ne? A’a. Abin da Elihu yake nufi shi ne, Jehobah ba ya samun wata riba daga bautar da muke yi masa. Jehobah kamiltacce ne. Ba za mu iya sa shi ya zama mai arziki da kuma ƙarfi ba. Amma duk wata baiwa ko iko da muke da shi, Allah ne ya ba mu kuma yana lura da yadda muke yin amfani da shi.
4. Da me Jehobah ya kwatanta taimako ko alherin da muke yi ma mutane?
4 Idan muka ƙaunaci mutanen da suke bauta wa Jehobah, shi muke ƙauna. Littafin Misalai 19:17 ya ce: “Mai-jin tausayin fakirai yana ba da rance ga Ubangiji, kuma za ya sāka masa da alherinsa.” Shin wannan ayar tana nufin cewa duk wani taimako ko alherin da muka yi wa bayin Allah fakirai yana da muhimmanci a wurinsa? Shin muna ganin cewa Mahaliccin sama da ƙasa yana ɗauka cewa idan muka taimaka wa mutane, rance ko bashi muka ba shi kuma zai saka mana da alheri? Ƙwarai kuwa, Yesu, Ɗan Allah ya tabbatar mana da hakan.
5. Waɗanne tambayoyi za mu bincika?
5 Jehobah ya gaya wa annabi Ishaya ya yi magana a madadinsa kuma ya faɗi yadda yake jin daɗin mutanen da suke bauta masa da aminci. (Isha. 6:
KO DA MUNA JIN TSORO, JEHOBAH YANA ƘARFAFA MU
6. Me ya sa aka ga cewa sojojin Jabin za su iya cin Isra’ilawa da yaƙi?
6 Sarkin Kan’aniyawa Jabin ya yi shekaru 20 yana “wulaƙanta” Isra’ilawa. Sojojin Jabin mugaye ne sosai shi ya sa Isra’ilawa da suke zama a ƙauyuka suna jin tsoron fita waje. Ban da haka ma, sojojin Jabin suna da karusan ƙarfe 900 amma Isra’ilawa ba su da isassun makaman da za su yaƙe su da shi.
7, 8. (a) Wane umurni ne Jehobah ya ba Barak da farko? (b) Ta yaya Isra’ilawa suka yi nasara a kan sojojin Jabin? (Ka duba hoton da ke shafi na 28.)
7 Duk da haka, Jehobah ya gaya wa annabiya Deborah ta gaya wa Barak cewa: “Tafi, ka ja daga wajen dutsen Tabor, ka ɗauki mutum zambar goma tare da kai daga cikin ‘ya’yan Naphtali da na
8 Da aka sanar da mutane, sai waɗanda suka ba da kansu suka taru a Dutsen Tabor. Barak bai ɓata lokaci wajen bin umurnin da Jehobah ya ba shi ba. (Karanta Alƙalawa 4:
WASU SUN TAIMAKA, WASU KUMA SUN ƘI
9. Wane bayani ne littafin Alƙalawa 5:
9 Ya kamata a bincika Alƙalawa sura 4 da 5 tare idan ana so a fahimce su sosai. Me ya sa? Alal misali, littafin Alƙalawa 5:
10, 11. Waye ne “Meroz” kuma me ya sa aka la’anta shi?
10 A waƙar da Deborah da Barak suka yi don su yabi Jehobah saboda nasarar da ya ba su, sun ce: “La’antar da Meroz, in ji mala’ikan Ubangiji, la’antar da mazaunanta da la’ana mai-zafi; gama sun ƙi zuwa wurin gudunmuwar Ubangiji, gudunmuwar Ubangiji tare da masu-ƙarfi.”
11 An la’anta Meroz sosai shi ya sa yake da wuya a san ko wane ne shi. Shin birni ne da mazaunansa suka ƙi ba da kansu sa’ad da aka nemi taimakonsu? Idan yana cikin biranen da Sisera ya gudu ya je don ya sami mafaka, mutanen birnin sun ƙi ne su yi amfani da zarafin da suke da shi na kama shi? Shin za a ce ba su ji yadda Jehobah ya ce ana neman masu ba da kai ba ne? Mutane dubu goma daga yankinsu suka taru don hakan. Ka yi tunanin cewa mutanen Meroz sun ga Sisera yana gudu a titunansu shi kaɗai, amma suka ƙi su kama shi. Da hakan zai zama musu zarafi mai kyau na goyon bayan Jehobah don su sami albarka. Amma ba su yi hakan ba kuma shi ya sa ayoyi na gaba suka nuna cewa Jael ta fi su ƙarfin hali!
12. Ta yaya halin mutanen da aka ambata a littafin Alƙalawa 5:
12 A littafin Alƙalawa 5:
13. Ta yaya halin Reuben da Dan da kuma Asher ya yi dabam da na Zebulun da kuma Naphatali?
13 Waɗanda suka ba da kansu sun ga yadda Jehobah ya nuna cewa shi mai iko ne sosai. Suna iya gaya wa mutane game da “ayyukan adalci na Ubangiji.” (Alƙa. 5:11) Amma littafin Alƙalawa 5:
KA YABI JEHOBAH!
14. Ta yaya muke tallafa wa Jehobah a yau?
14 A yau ba a umurce mu mu riƙa yaƙi ba, a maimakon haka, an gaya mana mu riƙa yin wa’azi da ƙwazo. Ana bukatar masu wa’azi a ƙungiyar Jehobah sosai fiye da dā. Miliyoyin ‘yan’uwa maza da mata da kuma matasa suna ba da kansu don yin hidima ta cikakken lokaci kamar
15. Ta yaya za mu tabbata cewa ba ma barin wani abu ya hana mu yin hidimar Jehobah?
15 Zai dace kowanenmu ya tambayi kansa: ‘Ina barin wasu ne kawai su riƙa yin aikin da Allah ya ba mu? Shin na fi mai da hankali ga samun kayan duniya kuma in manta da hidimar Jehobah? Ko kuma ina bin misalin Barak da Deborah da Jael da kuma mutane 10,000 da suka ba da kansu? Ban da haka ma, ina da bangaskiya da ƙarfin halin yin amfani da duk abin da nake da shi don yin hidimar Jehobah? Shin ina son in ƙaura zuwa wani birni ko ƙasa don in nemi kuɗi ba tare da mai da hankali ga yadda hakan zai shafi iyalina da kuma ikilisiyarmu ba?’ *
16. Me za mu iya ba Jehobah da bai da shi?
16 Jehobah yana mutunta bayinsa shi ya sa ya ba su gatan goyon bayan sarautarsa. Da yake Shaiɗan yana son mutane su goyi bayansa, tallafa wa Jehobah zai nuna wanda kake biyayya da shi. Bangaskiya da kuma aminci ne yake sa ka ba da kanka kuma hakan yana faranta wa Jehobah rai. (Mis. 23:
17. Mene ne Alƙalawa 5:31 ya faɗa game da abin da zai faru a nan gaba?
17 Nan ba da daɗewa ba, duniya za ta cika da mutanen da suke goyon bayan Jehobah. Muna son ganin wannan lokacin! Kamar Deborah da Barak za mu iya ce: “Maƙiyanka duk su lalace haka, Ya Ubangiji; Amma masu-ƙaunarsa su zama kamar rana sa’anda ta ke fitowa a cikin ikonta.” (Alƙa. 5:31) Za a amsa wannan addu’ar sa’ad da Jehobah ya kawo ƙarshen muguwar duniyar Shaiɗan! A lokacin da aka soma yaƙin Armageddon, babu amfanin neman mutanen da za su ba da kai don su hallaka magabta. A wannan lokacin, za mu ‘tsaya shuru, mu ga ceton Ubangiji.’ (2 Laba. 20:17) Amma kafin lokacin, muna da zarafin goyon bayan Jehobah sosai da ƙwazo da kuma ƙarfin hali.
18. Mene ne ba da kai da kuke yi zai iya motsa mutane su yi?
18 “Domin mutane kuma suka ba da kansu da yardan ransu, Ku albarkaci Ubangiji!” Saboda haka, sai Deborah da Barak suka soma yabon Mahalicci da waƙarsu, ba halittunsa ba. (Alƙa. 5:
^ sakin layi na 6 Karusan ƙarfe yana nufin karusai masu dogayen wuƙaƙe da ke a lanƙwashe da ake amfani da su a yaƙi. Kuma babu wanda ya isa ya yi kusa da irin waɗannan makaman yaƙin.
^ sakin layi na 8 Za a sami ƙarin bayani a kan wannan labarin a shafuffuka na 12-15 na Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Agusta, 2015 a Turanci.
^ sakin layi na 15 Ka duba talifin nan “Anxiety About Money” da ke Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Yuli, 2015 a Turanci.