Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ku Bauta wa Jehobah, Allah Mai Ba da ’Yanci na Gaske

Ku Bauta wa Jehobah, Allah Mai Ba da ’Yanci na Gaske

“A inda Ruhun Ubangiji yake kuwa a nan ’yanci yake.”​—2 KOR. 3:17.

WAƘOƘI: 49, 73

1, 2. (a) Me ya sa mutane a zamanin Bulus suke so su sami ’yanci? (b) Waye ne Bulus ya ce yake ba da ’yanci na gaske?

WASU Kiristoci a ƙarni na farko suna zama a ƙasar Roma. Romawa suna fahariya cewa dokarsu da kuma shari’arsu ce ta fi shahara. Sun kuma ce mazaunar ƙasarsu ne suka fi ’yanci. Amma aikin da bayi suka yi tuƙuru ne ya sa Romawa suka cim ma abubuwan nan. Domin akwai lokacin da kashi 30 cikin 100 na mazaunar ƙasar bayi ne. Babu shakka, hakan ya sa batun zama bayi da kuma samun ’yanci ya zama abin da kowa ke magana a kai har ma da Kiristoci.

2 Wasiƙun da manzo Bulus ya rubuta sun yi magana sosai game da ’yanci. Amma Bulus bai yi wa’azi a kan yadda za a sami ’yanci daga mulkin Roma ba, wanda shi ne abin da mutanen suke so. Maimakon haka, Bulus da Kiristoci sun yi iya ƙoƙarinsu don su taimaka wa mutane su ji wa’azi game da Mulkin Allah da kuma yadda fansar da Yesu Kristi ya bayar take da muhimmanci. Bulus ya yi ƙoƙari ya taimaka wa mutane su san wurin da za su sami ’yanci na gaske. Alal misali, a wasiƙarsa ta biyu ga Kiristocin da ke Korinti, ya ce: “Ubangiji fa, shi ne Ruhu. A inda ruhun Ubangiji yake kuwa a nan ’yanci yake.”​—2 Kor. 3:17.

3, 4. (a) Me ya sa Bulus ya yi furucin da ke 2 Korintiyawa 3:17? (b) Me muke bukata mu yi don mu sami ’yancin da Jehobah ke bayarwa?

3 A wasiƙar Bulus ta biyu ga Korintiyawa, ya faɗi abin da ya faru da Musa sa’ad da ya sauko daga Dutsen Sinai bayan ya kasance da mala’ikan Jehobah. Fuskar Musa tana ta ƙyalli! Da mutanen suka ga Musa, sai suka ji tsoro. Saboda haka, Musa ya rufe fuskarsa da mayafi. (Fit. 34:​29, 30, 33; 2 Kor. 3:​7, 13) Bulus ya ce Jehobah zai cire mayafin “idan mutum ya juyo” ga Allah. (2 Kor. 3:16) Mene ne Bulus yake nufi?

4 Kamar yadda muka gani a talifin da ya gabata, Jehobah, wanda shi ne ya halicci kome ne kaɗai yake da ’yancin yin dukan abin da ya ga dama. Saboda haka, akwai ’yanci a wurin da ‘ruhun’ Jehobah yake. Amma kafin mu sami irin wannan ’yancin, dole ne mu “juyo ga Ubangiji,” wato mu ƙulla dangantaka mai kyau da shi. A lokacin da Isra’ilawa suke jeji, ba su kasance da irin ra’ayin Jehobah ba. Sun zama kamar mutanen da aka rufe musu ido. Tunanin da suke yi shi ne yadda za su yi amfani da ’yancinsu daga ƙasar Masar wajen biyan bukatunsu.​—Ibran. 3:​8-10.

5. (a) Wane irin ’yanci ne ruhun Jehobah yake kawowa? (b) Ta yaya muka san cewa mutumin da ke kurkuku zai iya more ’yancin da Jehobah ke bayarwa? (c) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

5 Amma irin ’yancin da ruhun Jehobah yake sa mu kasance da shi ya fi wanda bayi suke samu. Ban da haka, ruhun Jehobah yana sa mu kasance da ’yancin da mutane suke mafarkin samu. Ruhun zai iya ’yantar da mu daga zunubi da mutuwa da addinan karya da kuma ayyukansu. (Rom. 6:23; 8:2) Babu shakka, wannan abu ne mai kyau! Mutum zai iya amfana daga wannan ’yancin ko da yana cikin kurkuku. (Far. 39:​20-23) Irin wannan ’yancin ne Ɗan’uwa Harold King ya more duk da cewa ya yi shekaru da yawa a kurkuku don imaninsa. Za ku iya jin labarinsa a Tashar JW. (Ku duba ƙarƙashin GANAWA DA LABARAI > JIMRE JARRABAWA.) Muna bukatar mu tattauna tambayoyin nan, ta yaya za mu nuna cewa muna daraja ’yancin da muke da shi? Kuma me zai taimaka mana mu yi amfani da ’yancin yadda ya dace?

MU DARAJA ’YANCIN DA ALLAH YA BA MU

6. Ta yaya Isra’ilawa suka nuna rashin godiya don ’yanci da Jehobah ya ba su?

6 Idan mutum ya ba mu kyautar abu mai tamani sosai, babu shakka za mu nuna masa godiya. Amma Isra’ilawa ba su nuna godiya ga Jehobah don yadda ya ’yantar da su daga Fir’auna da kuma mutanensa ba. Bayan ’yan watanni da samun ’yanci, sun soma marmarin abubuwan da suke ci da sha a ƙasar Masar. Suka soma gunaguni a kan abin da Jehobah yake ba su. A wajen su, “kakamba, da kabewa, da albasa mai ganye da mai ƙwaya, da tafarnuwa” sun fi ’yancin bauta wa Jehobah da suka samu muhimmanci. Hakan ya sa Jehobah fushi da su. (L. Kid. 11:​5, 6, 10; 14:​3, 4) Wane darasi ne za mu iya koya daga misalin nan?

7. Ta yaya Bulus ya bi umurnin da ke 2 Korintiyawa 6:​1, kuma ta yaya mu ma za mu yi hakan?

7 Manzo Bulus ya ƙarfafa Kiristoci cewa su ɗauki ’yancin da Jehobah ya ba mu ta wurin Ɗansa Yesu Kristi da daraja sosai. (Karanta 2 Korintiyawa 6:1.) Bulus ajizi ne, wato bawa ga zunubi da mutuwa kuma hakan ya sa shi baƙin ciki sosai. Duk da haka, ya ce: “Godiya ta tabbata ga Allah gama ya cece ni ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu!” Me ya sa ya faɗi haka? Bulus ya ce: “Gama ta wurin Almasihu Yesu ƙa’idar ruhun nan mai ba da rai ta ’yantar da ni daga ƙa’idar zunubi da mutuwa.” (Rom. 7:​24, 25; 8:2) Kamar Bulus, ya kamata mu ɗauki ’yanci daga zunubi da mutuwa da Jehobah ya ba mu da muhimmanci sosai. Saboda fansar da Yesu ya bayar, muna iya bauta wa Allah da zuciya mai kyau, kuma mu yi hakan da farin ciki.​—Zab. 40:8.

Kana amfani da ’yancinka don bauta wa Jehobah ko don yin abin da ka ga dama? (Ka duba sakin layi na 8-10)

8, 9. (a) Wane gargaɗi ne manzo Bitrus ya bayar game da yin amfani da ’yancinmu? (b) Waɗanne ƙalubale ne muke fuskanta a yau?

8 Ban da nuna godiya don ’yancinmu, muna bukatar mu mai da hankali don kada mu yi amfani da ’yancinmu na yin zaɓi yadda bai dace ba. Manzo Bitrus ya yi gargaɗi cewa kada mu yi amfani da ’yancinmu don yin munanan abubuwa. (Karanta 1 Bitrus 2:16.) Babu shakka, wannan gargaɗin ya tuna mana da abin da ya faru da Isra’ilawa a lokacin da suke jeji. Kuma gargaɗin ya fi dacewa da mu a yau. Shaiɗan yana amfani da kayan duniya, kamar su tufafi da abinci da abin sha da nishaɗi da shaƙatawa da dai sauran su don ya rinjaye mu. Masu tallace-tallace a yau suna iya ƙoƙarinsu su sa mutane su sayi abin da ba sa bukata. Babu shakka, yana iya kasancewa da sauƙi mu soma yin amfani da ’yancinmu a hanyar da ba ta dace ba!

9 Ban da haka, umurnin manzo Bitrus ya shafi wasu batutuwa a rayuwa, kamar batun zuwa makaranta da kuma irin aikin da mutum zai yi. Alal misali, a yau ana taƙura wa matasa su yi aiki tuƙuru domin su sami shiga manyan jami’o’i. Ana sa su soma tunanin cewa idan mutum ya yi karatu a manyan jami’o’i, zai sami aikin da ake biyan albashi mai tsoka. Ƙari ga haka, ana yawan nuna musu cewa albashin mutanen da suka yi karatu a jami’a ya fi na waɗanda ba su je jami’a ba. Da yake wannan shawara ce babba da matasa suke bukatar su yanke, suna iya tunanin cewa zuwa jami’a ya fi. Amma mene ne matasa da kuma iyayensu suke bukatar su sani?

10. Me ya kamata mu tuna sa’ad da muke amfani da ’yancinmu don yanke shawarwari?

10 Wasu suna iya tunani cewa tun da su ne za su yanke wa kansu shawara a wannan batun, suna da ’yancin zaɓan abin da suke so, idan har zuciyarsu ta yarda da zaɓin da suka yi. Wataƙila abin da Bulus ya gaya wa Kiristoci a Korinti game da abinci ne ya sa suke wannan tunanin. Bulus ya ce: “Don me fa tunanin zuciyar wani zai hana ’yancina?” (1 Kor. 10:29) Gaskiya ne cewa muna da ’yancin yi wa kanmu zaɓi a batun zuwa makaranta da kuma irin aikin da za mu yi, amma muna bukatar mu tuna cewa ba mu da ’yancin yin dukan abin da muka ga dama. Ƙari ga haka, mu za mu fuskanci sakamakon shawarar da muka yanke. Shi ya sa Bulus ya ce: “Dukan abubuwa an yarda mana, amma ba dukan abubuwa ne suke da amfani ba. Dukan abubuwa an yarda mana, amma ba dukan abubuwa ne suke ginawa ba.” (1 Kor. 10:23) Hakika, wannan ya nuna mana cewa da akwai abubuwan da suka fi abin da muke so muhimmanci.

MU YI AMFANI DA ’YANCINMU DON BAUTA WA ALLAH

11. Me ya sa Jehobah ya ’yantar da mu?

11 Bitrus ya gargaɗe mu cewa kada mu yi amfani da ’yancinmu yadda bai dace ba. Amma ya faɗi yadda ya kamata mu yi amfani da ’yancin, ya ce: “Amma ku yi zaman bayin Allah.” Ayar nan ta nuna cewa Jehobah ya yi amfani da Yesu don ya ’yantar da mu daga zunubi da mutuwa domin yana so mu yi rayuwa a matsayin “bayin Allah.”

12. Wane misali ne Nuhu da iyalinsa suka kafa mana?

12 Hanya mafi kyau na yin amfani da ’yancinmu yadda ya dace, shi ne ta wurin bauta wa Allah. Yin hakan zai taimaka mana mu guji zama bayi ga kayan duniya. (Gal. 5:16) Ka tuna abin da Nuhu da iyalinsa suka yi. Sun yi rayuwa ne a zamanin da mutane suke yin mugunta sosai. Amma sun guji neman kayan duniya. Ta yaya suka yi hakan? Sun mai da hankali ga yin aikin da Jehobah ya ba su, wato gina jirgin ruwa da tara abincin da su da kuma dabbobin za su ci. Ban da haka ma, sun ci gaba da yin wa’azi. “Nuhu kuwa ya yi kome daidai yadda Allah ya umarce shi.” (Far. 6:22) Wane sakamako ne ya samu? Da aka halaka duniya a lokacin, Nuhu da iyalinsa sun tsiri.​—Ibran. 11:7.

13. Wane aiki ne aka ba Yesu da ya ba wa mabiyansa?

13 Wane umurni ne Jehobah ya ba mu a yau? A matsayinmu na mabiyan Yesu, mun san cewa Allah ya umurce mu mu yi wa’azi. (Karanta Luka 4:​18, 19.) A yau, Shaiɗan ya rufe wa yawancin mutane a duniyar nan ido. Saboda haka, ba su san cewa su bayi ne ga addinan ƙarya da kayan duniya ba. (2 Kor. 4:4) Jehobah ya ba mu gatan bin misalin Yesu. Yana so mu taimaka wa mutane su san shi, wato Allah mai ’yanci kuma su bauta masa. (Mat. 28:​19, 20) Wannan ba aiki mai sauƙi ba ne kuma yana ɗauke da wasu ƙalubale. A wasu ƙasashe, mutane ba sa son su san Allah har ma suna fushi idan muka yi musu wa’azi. Amma tambayar da muke bukatar mu yi wa kanmu ita ce, ‘Zan yi amfani da ’yancina don in daɗa ƙwazo a wa’azi game da Mulkin Allah kuwa?’

14, 15. Wace shawara ce Shaidun Jehobah da yawa suka yanke game da yin wa’azi? (Ka duba hoton da ke shafi na 8.)

14 Bayin Jehobah da yawa sun san cewa ƙarshen zamanin nan ya yi kusa sosai, kuma hakan ya motsa su su sauƙaƙa rayuwarsu don su soma hidimar majagaba. Wannan abin ƙarfafa ne sosai. (1 Kor. 9:​19, 23) Wasu suna yin hidima a yankinsu, wasu kuma sun ƙaura zuwa inda ake bukatar masu shela sosai. A cikin shekara biyar da suka shige, mutane fiye da 250,000 sun soma hidimar majagaba kuma yanzu da akwai majagaba na kullum fiye da 1,100,000. Abin sha’awa ne yadda mutane da yawa suke amfani da ’yancinsu a hanya mai kyau!​—Zab. 110:3.

15 Mene ne ya taimaka wa ’yan’uwan nan su yi amfani da ’yancinsu yadda ya dace? Ka yi la’akari da misalin John da Judith da suka yi shekara 30 suna yin hidima a ƙasashe dabam-dabam. Sun ce a shekara ta 1977 da aka soma Makarantar Hidima ta Majagaba, ana ƙarfafa ɗaliban su ƙaura zuwa wurin da ake bukatar masu shela. Don yin wannan hidimar, John ya ce ya canja aikin da yake yi sau da yawa don su sauƙaƙa rayuwarsu. Sai suka ƙaura zuwa wata ƙasa don yin wa’azi. Mene ne ya taimaka musu su iya koyan sabon yare da al’ada kuma su saba da sanyi da kuma zafin ƙasashen da suka je? Sun yi addu’a ga Jehobah kuma sun dogara gare shi don ya taimaka musu. Yaya waɗannan shekarun da suka yi suna yi wa Jehobah hidima ya shafi rayuwarsu? John ya ce: “Na yi amfani da dukan ƙarfina a aiki mafi muhimmanci. Kuma hakan ya sa na san Jehobah sosai. Ban da haka, yanzu ne na fahimci abin da Yaƙub 4:8 yake nufi, da ya ce: ‘Ku yi kusa da Allah, shi kuwa zai yi kusa da ku.’ Hakan ya taimaka mini in sami abin da nake nema, wato rayuwa mai ma’ana da kuma gamsuwa.”

16. Ta yaya dubban ’yan’uwa suka yi amfani da ’yancinsu yadda ya dace?

16 Yanayin wasu bai ƙyale su su yi hidimar majagaba na shekaru da yawa kamar John da Judith ba. Amma ’yan’uwa da yawa suna ba da kai don yin aikin gine-gine a faɗin duniya. Alal misali, a lokacin da ake gina hedkwatarmu da ke Warwick a New York, wajen mutane 27,000 ne suka ba da kansu don yin aikin. Wasu sun yi makonnin biyu suna aikin, wasu kuma shekara ɗaya ko fiye da hakan. Da yawa daga cikin ’yan’uwan nan sun yi sadaukarwa sosai don su yi wannan hidimar. Babu shakka, wannan misali ne mai kyau na mutanen da suka yi amfani da ’yancinsu don su yabi Jehobah!

17. Wace albarka ce waɗanda suke yin amfani da ’yancinsu yadda ya dace za su more?

17 Muna godiya domin mun san Jehobah Allah, kuma muna moran ’yancin da bauta ta gaskiya ke kawo. Bari mu nuna ta irin zaɓin da muke yi cewa mun daraja wannan ’yancin. Maimakon mu riƙa yin amfani da ’yancinmu yadda bai kamata ba, zai dace mu yi amfani da shi domin mu bauta wa Jehobah. Idan muka yi hakan, za mu more albarkar da Jehobah ya yi alkawari a cikin Littafi Mai Tsarki cewa zai yi mana. Ya ce: “Halitta da kanta za ta sami tsira daga bautar da take wa ruɓewa, za ta kuma sami ’yancin nan na ɗaukakar da za a yi wa ’ya’yan Allah.”​—Rom. 8:21.