Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Mu Yi Koyi da Jehobah​—Allahn da Ke Karfafa Mu

Mu Yi Koyi da Jehobah​—Allahn da Ke Karfafa Mu

“Albarka ta tabbata ga . . . Allah wanda yake [ƙarfafa mu] . . . a cikin dukan wahalarmu.”​—2 KOR. 1:​3, 4.

WAƘOƘI: 7, 3

1. Ta yaya Jehobah ya ƙarfafa mutane sa’ad da Adamu da Hauwa’u suka yi tawaye?

JEHOBAH ya zama Allahn da ke ƙarfafa mu tun daga lokacin da mutane suka yi zunubi kuma suka zama ajizai. Hakika, nan da nan da Adamu da Hauwa’u suka yi wa Allah tawaye a lambun Adnin, ya sa ’ya’yan da za su haifa su kasance da bege da kuma gaba gaɗi. Da zarar ’yan Adam sun fahimci annabcin da ke littafin Farawa 3:​15, hakan zai ƙarfafa su cewa za a halaka “tsohon macijin nan,” wato Shaiɗan Iblis da dukan munanan ayyukansa.​—R. Yar. 12:9; 1 Yoh. 3:8.

JEHOBAH YA ƘARFAFA BAYINSA A DĀ

2. Ta yaya Jehobah ya ƙarfafa Nuhu?

2 A lokacin da Nuhu yake raye, shi kaɗai ne da iyalinsa suke bauta wa Jehobah. Ƙari ga haka, ana mugunta da lalata a ko’ina kuma wannan yanayin yana iya sa Nuhu sanyin gwiwa. (Far. 6:​4, 5, 11; Yahu. 6) Amma Jehobah ya gaya masa abin da ya ƙarfafa shi ya ci gaba da bauta wa Allah. (Far. 6:9) Jehobah ya gaya wa Nuhu cewa zai halaka mugayen mutanen. Kuma ya gaya masa abin da zai yi don shi da iyalinsa su tsira. (Far. 6:​13-18) Babu shakka, Jehobah ya ƙarfafa Nuhu sosai.

3. Ta yaya Jehobah ya ƙarfafa Yoshuwa? (Ka duba hoton da ke shafi na 15.)

3 Jehobah ya ƙarfafa bawansa Yoshuwa, wanda yake da babban aiki na yi wa mutanen Allah ja-goranci zuwa Ƙasar Alkawari. Hakan ya ƙunshi yaƙan sojoji masu ƙarfi sosai da ke zama a ƙasashen. Babu shakka cewa wannan aikin zai sa Yoshuwa tsoro sosai. Shi ya sa Jehobah ya gaya wa Musa ya ƙarfafa Yoshuwa. Ya ce: “Ka umarci Yoshuwa, ka kuma ƙarfafa shi, gama shi ne zai bi da jama’a su ƙetare Yodan su ci ƙasar. Shi ne kuma zai rarraba musu gādon ƙasar da kake gani.” (M. Sha. 3:28) Kafin Yoshuwa ya soma aikin da aka ba shi, Jehobah ya ƙarfafa shi cewa: “Ka tuna na riga na umarce ka ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali! Kada ka firgita ko ka ji tsoro, gama ka sani ni Yahweh Allahnka ina tare da kai duk inda za ka tafi.” (Yosh. 1:​1, 9) Hakika, wannan furucin ya ƙarfafa Yoshuwa sosai!

4, 5. (a) Ta yaya Jehobah ya ƙarfafa mutanensa a dā? (b) Ta yaya Jehobah ya ƙarfafa Ɗansa?

4 Jehobah ya ƙarfafa mutanensa gabaki ɗaya. Alal misali, Jehobah ya san cewa Yahudawa za su bukaci a ƙarfafa su sa’ad da suka zama bayi a Babila. Don haka, ya yi annabci mai ban ƙarfafa cewa: “Kada fa ka ji tsoro, gama ina tare da kai, kada ka damu, gama ni ne Allahnka; Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka, zan riƙe ka da hannun damana mai nasara.” (Isha. 41:10) Ƙari ga haka, Jehobah ya ƙarfafa Kiristoci na farko, kuma yana ƙarfafa mu a yau.​—Karanta 2 Korintiyawa 1:​3, 4.

5 Jehobah ya kuma ƙarfafa Ɗansa, Yesu Kristi. A lokacin da Yesu ya yi baftisma, ya ji murya daga sama ya ce: “Wannan shi ne Ɗana da nake ƙauna, wanda nake jin daɗinsa ƙwarai.” (Mat. 3:17) Babu shakka, waɗannan kalmomi sun ƙarfafa Yesu sosai sa’ad da yake hidima a duniya!

YESU YA ƘARFAFA MUTANE

6. Ta yaya kwatancin Yesu na talanti zai iya ƙarfafa mu?

6 Yesu ya bi misalin Ubansa ta wajen ƙarfafa mutane su kasance da aminci. Ya yi hakan a kwatancin talanti da ya ba da game da ƙarshen zamanin nan. Shugaban ya nuna cewa yana daraja kowanne cikin bayinsa mai aminci da furucin nan: “Madalla, bawan kirki, mai aminci! Ka yi aminci a kan ƙaramin abu. Zan ba ka aikin da ya fi wannan. Ka zo ka yi murna tare da ni.” (Mat. 25:​21, 23) Kwatancin nan ya ƙarfafa almajiran Yesu su ci gaba da bauta wa Jehobah da aminci!

7. Ta yaya Yesu ya ƙarfafa manzanninsa, musamman Bitrus?

7 Sau da sau, manzannin Yesu sun yi gardama a kan wanda ya fi girma a cikinsu. Amma Yesu ya ƙarfafa su su zama masu tawali’u kuma su zama bayi ba shugabanni ba. (Luk. 22:​24-26) Sau da yawa, Bitrus ya yi abubuwan da ba su dace ba. (Mat. 16:​21-23; 26:​31-35, 75) Maimakon Yesu ya yasar da Bitrus, ya ƙarfafa shi kuma ya ce ya ƙarfafa ’yan’uwansa.​—Yoh. 21:16.

YADDA AKA ƘARFAFA MUTANE A DĀ

8. Ta yaya Hezekiya ya ƙarfafa shugabannin sojoji da mutanen Urushalima?

8 Kafin Yesu ya kafa wa bayin Jehobah misalin da za su riƙa bi, sun san cewa suna bukatar su ƙarfafa wasu. Sa’ad da Assuriyawa suke so su kai wa mutanen Urushalima hari, Hezekiya ya tara shugabannin sojoji da mutanen don ya ƙarfafa su. Mutanen ‘sun sami ƙarfafawa sosai da wannan maganarsa.’​—Karanta 2 Tarihi 32:​6-8.

9. Mene ne littafin Ayuba ya koya mana game da ƙarfafa mutane?

9 Ko da yake Ayuba yana bukatar a ƙarfafa shi, ya koya wa abokansa uku masu ‘ta’aziyya ta azaba’ yadda ake ƙarfafa mutum. Ya gaya musu cewa da a ce shi ne, da ‘zai ƙarfafa su, ta’aziyyar bakinsa za ta ba su sauƙi.’ (Ayu. 16:​1-5) Amma daga baya, Elihu da Jehobah sun ƙarfafa Ayuba.​—Ayu. 33:​24, 25; 36:​1, 11; 42:​7, 10.

10, 11. (a) Me ya sa ’yar Yefta take bukatar ƙarfafa? (b) Su waye ne a yau suke bukatar a riƙa ƙarfafa su?

10 Misalin wata a dā da ta bukaci a ƙarfafa ta ita ce ’yar Yefta. Kafin Yefta ya je yaƙi da Ammonawa, ya yi wa Jehobah alkawari cewa idan ya yi nasara a yaƙin, duk mutumin da ya fara fitowa ya marabce shi zai zama na Jehobah. Wannan mutumin zai riƙa wa Jehobah hidima a mazauni muddar ransa. Da Yefta ya dawo, ’yarsa ce ta fara fitowa ta marabce shi, tana rawa tana kiɗa kuma hakan ya sa shi baƙin ciki sosai don ita kaɗai ce ’yarsa. Amma ya cika alkawarinsa kuma ya tura ta ta yi wa Jehobah hidima a Shilo muddar ranta.​—Alƙa. 11:​30-35.

11 Ko da yake yin hakan ya sa Yefta baƙin ciki sosai, amma al’amarin zai fi damun ’yarsa. Duk da haka, ’yar Yefta tana a shirye ta cika alkawarin da mahaifinta ya yi. (Alƙa. 11:​36, 37) Hakan yana nufin cewa ba za ta yi aure ba kuma ba za ta haifi yara da za su sa sunan iyalinsu ya ci gaba da wanzuwa ba. Babu shakka, tana bukatar a ƙarfafa ta sosai. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wannan ya zama dalilin al’ada a cikin Isra’ila, wato ’yan matan Isra’ila sukan fita kowace shekara domin nuna baƙin cikinsu na kwana huɗu domin su tuna da ’yar Yefta mutumin Gileyad.” (Alƙa. 11:​39, 40) Wannan labarin ya sa mu tuna da Kiristocin da ba su yi aure ba domin suna so su mai da hankali sosai ga “sha’anin Ubangiji.” Zai dace mu riƙa ƙarfafa waɗannan ’yan’uwa maza da mata.​—1 Kor. 7:​32-35.

MANZANNIN YESU SUN ƘARFAFA ’YAN’UWANSU

12, 13. Ta yaya Bitrus ya ‘ƙarfafa ’yan’uwansa’?

12 Kafin Yesu Kristi ya mutu, ya gaya wa manzo Bitrus cewa: “Bitrus, Bitrus! Ka ji nan! Shaiɗan ya nemi izni ya gwada ku duka, ya tankaɗe ku kamar yadda ake tankaɗe alkama daga dusa. Amma na yi maka addu’a, Bitrus, kada bangaskiyarka ta kāsa. Bayan da ka juyo wurina, ka ƙarfafa ’yan’uwanka.”​—Luk. 22:​31, 32.

Wasiƙun manzanni sun ƙarfafa ikilisiyoyi a ƙarni na farko, kuma suna ƙarfafa mu a yau (Ka duba sakin layi na 12-17)

13 Manzo Bitrus yana cikin mutanen da suka yi wa ikilisiyar Kirista na farko ja-goranci. (Gal. 2:9) Ya ƙarfafa ’yan’uwansa ta yadda ya kasance da gaba gaɗi a lokacin Fentakos da kuma bayan lokacin. Bayan Bitrus ya bauta wa Jehobah shekaru da yawa, sai ya rubuta wa ’yan’uwansa wasiƙa cewa: “Na rubuta muku wannan ’yar wasiƙa . . . in ƙarfafa ku, in kuma sanar da ku cewa wannan shi ne alheri mai gaskiya na Allah. Ku tsaya da ƙarfi a cikinsa.” (1 Bit. 5:12) Wasiƙun Bitrus sun ƙarfafa Kiristoci a zamaninsa. Har ila, wasiƙun suna ƙarfafa mu a yau. Me ya sa? Domin muna jiran Jehobah Allah ya cika dukan alkawuran da ya yi mana!​—2 Bit. 3:13.

14, 15. Ta yaya littattafan da manzo Yohanna ya rubuta suke ƙarfafa mu?

14 Manzo Yohanna yana cikin waɗanda suka ja-goranci ikilisiyar Kirista ta farko. Ya rubuta labari mai ƙayatarwa game da hidimar Yesu. Littafin da ya rubuta ya ƙarfafa Kiristoci shekaru da yawa kuma ya ci gaba da ƙarfafa mu a yau. Alal misali, a littafin Yohanna ne kaɗai aka rubuta furucin Yesu cewa ƙauna ce halin da ke nuna mu almajiran Yesu ne na gaske.​—Karanta Yohanna 13:​34, 35.

15 Ban da haka ma, wasiƙu uku da Yohanna ya rubuta suna ɗauke da koyarwa mai muhimmanci. Sa’ad da muka yi sanyin gwiwa don kuskurenmu, muna farin ciki cewa hadayar da Yesu ya ba da tana “tsabtace mu daga dukan zunubi.” (1 Yoh. 1:7) Kuma idan zuciyarmu ta ci gaba da damun mu don laifi da muka yi, za mu sami ƙarfafa sa’ad da muka karanta cewa “Allah ya fi zuciyarmu.” (1 Yoh. 3:20) Yohanna ne kaɗai ya rubuta cewa “Allah ƙauna ne.” (1 Yoh. 4:​8, 16) Wasiƙarsa ta biyu da ta uku ta ƙarfafa Kiristoci da suka ci gaba da ‘bin gaskiya.’​—2 Yoh. 4; 3 Yoh. 3, 4.

16, 17. Ta yaya manzo Bulus ya ƙarfafa Kiristoci a ƙarni na farko?

16 A ƙarni na farko, manzo Bulus ne ya fi ƙarfafa ’yan’uwansa. Jim kaɗan bayan mutuwar Yesu, yawancin manzannin Yesu sun kasance a Urushalima, kuma wannan wurin ne hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci take zama. (A. M. 8:14; 15:2) Kiristoci da ke Yahudiya sun yi wa’azi game da Kristi ga mutane da suka yi imani da Allah ɗaya. Amma, ruhu mai tsarki ya sa Bulus ya yi wa’azi ga Helenawa da Romawa da kuma wasu da suke bauta wa alloli da yawa.​—Gal. 2:​7-9; 1 Tim. 2:7.

17 Manzo Bulus ya je wuraren da yanzu ake kira Turkiya da Girka da kuma Italiya. Ya yi wa’azi ga mutanen da ba Yahudawa ba kuma ya kafa sababbin ikilisiyoyi. Waɗannan da suka zama Kiristoci sun ‘sha wahala daga mutanen ƙasarsu.’ Saboda haka, suna bukatar ƙarfafa. (1 Tas. 2:14) A wajen shekara ta 50 bayan haihuwar Yesu, Bulus ya rubuta wasiƙa zuwa ga ikilisiyar da ke Tasalonika don ya ƙarfafa su. Ya ce: “Kullum muna gode wa Allah saboda ku duka, muna kuma sa ku cikin addu’o’inmu koyaushe. Muna tunawa da ku a gaban Allahnmu, Ubanmu, game da ayyukanku na bangaskiya, da aikin ƙauna wanda kuke yi, da kuma tsayawarku daram.” (1 Tas. 1:​2, 3) Ƙari ga haka, ya gaya musu cewa: “Ku ƙarfafa juna, ku yi ta gina juna.”​—1 Tas. 5:11.

HUKUMAR DA KE KULA TANA ƘARFAFA ’YAN’UWA

18. Ta yaya hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci a ƙarni na farko ta ƙarfafa Filibus?

18 Hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci a ƙarni na farko ta ƙarfafa dukan Kiristoci har da dattawa. Hukumar ta tallafa wa Filibus sa’ad da ya yi wa Samariyawa wa’azi game da Kristi. Hukumar ta tura Bitrus da Yohanna su yi addu’a a madadin sababbi don su sami ruhu mai tsarki. (A. M. 8:​5, 14-17) Babu shakka, Filibus da waɗannan sababbi Kiristoci sun sami ƙarfafa don yadda hukumar ta tallafa musu!

19. Yaya Kiristoci a ƙarni na farko suka ji sa’ad da aka karanta musu wasiƙa daga hukumar da ke kula da ayyukansu?

19 Dokar da aka ba da ta hannun Musa ta bukaci Yahudawa su yi kaciya. Saboda haka, Hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci a ƙarni na farko ta bukaci ta tsai da shawara ko ya kamata Kiristocin da ba Yahudawa ba su yi kaciya. (A. M. 15:​1, 2) Hukumar ta yi addu’a don neman taimakon ruhu mai tsarki kuma ta bincike Nassosi. Sai ta tsai da shawara cewa sababbi ba sa bukatar su yi kaciya kuma ta tura wasiƙa zuwa ikilisiyoyi. Wakilan hukumar ne aka tura su idar da waɗannan wasiƙun zuwa ikilisiyoyi. Mene ne sakamakon? “Da jama’ar suka karanta wasiƙar kuwa, suka yi farin ciki saboda ƙarfafawar da suka samu.”​—A. M. 15:​27-32.

20. (a) Ta yaya Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu a yau take ƙarfafa dukanmu? (b) Wace tambaya ce za a amsa a talifi na gaba?

20 A yau, Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu tana ƙarfafa waɗanda suke hidima a Bethel da majagaba na musamman da masu kula da da’ira da masu aikin gine-gine da masu wa’azi a ƙasashen waje da dai sauransu. Ƙari ga haka, tana ƙarfafa dukan Kiristoci a faɗin duniya kuma hakan yana sa ’yan’uwa farin ciki sosai kamar Kiristoci a ƙarni na farko! Ban da haka, a shekara ta 2015 Hukumar ta wallafa ƙasidar nan Ka Komo ga Jehobah, wannan ƙasidar ta ƙarfafa mutane da yawa a faɗin duniya. Amma, ’yan’uwan da ke ja-goranci ne kaɗai za su yi koyi da Jehobah ta wajen ƙarfafa mutane? Za a amsa wannan tambayar a talifi na gaba.