Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
Littafin Zabura 144:12-15 yana magana ne game da mutanen Allah ko kuma mugayen mutanen da aka ambata a aya ta 11?
Za a iya fahimtar kalmar Ibrananci da aka yi amfani da ita a ayoyin nan a hanyoyi biyu. Saboda haka, waɗannan abubuwan da za a tattauna za su taimaka mana mu fahimci ayoyin yadda ya kamata:
Ka yi la’akari da abin da aka faɗa a cikin sauran ayoyi da ke zaburar. Da yake an yi amfani da “bari” a aya ta 12, hakan yana nufin cewa masu adalci ne za su sami albarka da aka ambata a ayoyi 12 zuwa 14. Wato waɗanda suka ce a ‘fitar da su kuma a kuɓutar’ da su daga hannun mugayen mutane (aya ta 11). An nuna hakan ma a aya ta 15, inda aka ambata “masu albarka” sau biyu kuma hakan ya shafi “mutanen da Yahweh ne Allahnsu!”
Wannan bayanin ya jitu da ayoyin Littafi Mai Tsarki da suka ce Allah zai albarkaci masu aminci. A wannan zaburar, an nuna begen da Dauda yake da shi cewa Allah zai albarkaci Isra’ilawa bayan ya cece su daga hannun magabtansu. Allah zai sa su yi farin ciki kuma su sami wadata. (L. Fir. 26:9, 10; M. Sha. 7:13; Zab. 128:1-6) Alal misali, littafin Maimaitawar Shari’a 28:4 ya ce: “’Ya’yan da za ku haifa za su zama masu albarka, haka nan kuma amfanin gonakinku, da ’ya’yan dabbobinku, da ’ya’yan shanunku, da ’ya’yan tumakinku da na awakinku.” Hakika, a lokacin da Sulemanu ɗan Dauda yake sarauta, al’ummar ta sami kwanciyar hankali da kuma wadata. Ban da haka ma, sarautar Sulemanu ta nuna abin da zai faru sa’ad da Almasihu zai soma sarauta.—1 Sar. 4:20, 21; Zab. 72:1-20.
Fahimtar wannan Zabura ta 144 ya sa mun ga cewa zaburar tana magana ne a kan begen da bayin Jehobah suke da shi. Wannan begen shi ne cewa Allah zai halaka mugayen mutane kuma ya sa masu adalci su riƙa rayuwa cikin kwanciyar hankali kuma su zama masu wadata.—Zab. 37:10, 11.