HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Afrilu 2020

Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari da za a yi daga ranar 1 ga Yuni–5 ga Yuli, 2020.

Za A Kawo Hari Daga Arewa!

Talifin nazari na 14: 1-7 ga Yuni, 2020. Wadanne dalili hudu ne suka sa muka bukaci yin gyara a yadda muka fahimci Yona sura 1 da 2?

Mene ne Ra’ayinka Game da Mutanen Yankinku?

Talifin nazari na 15: 8-14 ga Yuni, 2020. Ka yi la’akari da yadda za mu iya yin koyi da Yesu da kuma manzo Bulus ta wajen yin la’akari da abubuwan da mutane suka yi imani da su da abubuwan da suke so da kuma yadda za mu dauki kowa a matsayin wadanda za su iya zama mabiyin Yesu.

Ka Yi Koyi da Jehobah a Sha’aninka da ’Yan’uwa

Talifin nazari na 16: 15-21 ga Yuni, 2020. Jehobah ya taimaka wa Yunana da Iliya da Hajaratu da kuma Lutu. Ka ga yadda za mu iya yin koyi da Jehobah a yadda muke sha’ani da mutane.

“Ina Ce da Ku Abokai”

Talifin nazari na 17: 22-28 ga Yuni, 2020. Muna fuskantar kalubale yayin da muke kokarin kulla abota da Yesu. Amma yaya za mu iya magance kalubalen.

Na Yi Tseren Har Karshe

Talifin nazari na 18: 29 ga Yuni–5 ga Yuli, 2020. Me zai taimaka mana mu ci tseren rai ko da muna fama da tsufa ko kuma ciwo mai tsanani?