TALIFIN NAZARI NA 17
“Ina Ce da Ku Abokai”
“Ina ce da ku abokai gama na gaya muku dukan abin da na ji daga wurin Ubana.”—YOH. 15:15.
WAƘA TA 13 Mu Riƙa Bin Misali Yesu
ABIN DA ZA A TATTAUNA *
1. Me kake bukatar yi don ka zama abokin wani?
IDAN muna so mu ƙulla abokantaka da wani, abu na farko da muke bukatar yi shi ne kasancewa da shi. Yayin da kake gaya masa ra’ayinka da kuma yadda kake ji, za ku zama abokai. Amma a wasu lokuta, ba shi da sauƙi mu zama abokan Yesu. Me ya sa?
2. Wane ƙalubale na farko ne za mu fuskanta?
2 Ƙalubale na farko shi ne ba mu taɓa haɗuwa da Yesu ba. Kiristoci da yawa ma a ƙarni na farko sun fuskanci wannan matsalar. Duk da haka, manzo Bitrus ya ce: “Ko da yake ba ku taɓa ganin Yesu Almasihu ba, amma duk da haka kuna ƙaunarsa. Ko da yake ba ku gan shi a yanzu ba, duk da haka kuna ba da gaskiya gare shi.” (1 Bit. 1:8) Don haka, zai yiwu mu ƙulla abokantaka na kud da kud da Yesu, duk da cewa ba mu taɓa ganin shi ba.
3. Wane ƙalubale na biyu ne muke fuskanta?
3 Ƙalubale na biyu shi ne ba za mu iya tattaunawa da Yesu ba. Sa’ad da muke addu’a, muna tattaunawa ne da Jehobah. Gaskiya ne cewa muna addu’a cikin sunan Yesu, amma ba ma tattaunawa da shi kai tsaye. Yesu ba ya so mu yi addu’a gare shi. Me ya sa? Domin addu’a ibada ce kuma Jehobah ne kaɗai ya kamata mu bauta Mat. 4:10) Duk da haka, muna iya nuna cewa muna ƙaunar Yesu.
wa. (4. Wane ƙalubale na uku ne muke fuskanta, kuma me za mu tattauna a wannan talifin?
4 Ƙalubale na uku shi ne Yesu yana sama, kuma ba za mu iya kasancewa da shi ba. Duk da cewa ba za mu iya kasancewa da Yesu ba, za mu iya koyan abubuwa da yawa game da shi. Za mu tattauna abubuwa huɗu da za su taimaka mana mu ƙarfafa abokantakarmu da shi. Bari mu fara tattauna dalilin da ya sa ƙulla abokantaka da Yesu yake da muhimmanci.
ME YA SA MUKE BUKATAR MU ZAMA ABOKAN YESU?
5. Me ya sa ya wajaba mu zama abokan Yesu? (Ka duba akwatunan nan “ Zama Abokan Yesu Zai Sa Mu Zama Abokan Jehobah” da “ Ka Kasance da Ra’ayi Mai Kyau Game da Yesu.”)
5 Wajibi ne mu zama abokan Yesu idan muna so mu kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. Me ya sa? Ka yi la’akari da dalilai biyu kawai. Na farko, Yesu ya gaya wa almajiransa cewa: ‘Uban yana ƙaunar ku da kansa, saboda kun ƙaunace ni.’ (Yoh. 16:27) Ya ƙara da cewa: “Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina.” (Yoh. 14:6) Yin ƙoƙarin zama abokan Jehobah ba tare da ƙulla abokantaka da Yesu ba, yana kamar shiga ɗaki ba tare da bin ƙofa ba. Yesu ya yi amfani da irin wannan kwatanci sa’ad da yake bayyana kansa a matsayin “ƙofar tumakin.” (Yoh. 10:7) Dalili na biyu shi ne cewa Yesu ya yi koyi da halayen Jehobah. Ya gaya wa mabiyansa cewa: “Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban?” (Yoh. 14:9) Don haka, hanya mai muhimmanci da za mu san Jehobah ita ce ta wajen koya game da Yesu. Yayin da muke koya game da Yesu, za mu ƙaunace shi sosai. Kuma hakan zai sa ƙaunarmu ga Jehobah ma ta yi ƙarfi.
6. Wane dalili ne kuma ya sa yake da muhimmanci mu ƙulla dangantaka da Yesu? Ka bayyana.
6 Muna bukatar mu ƙulla dangantaka mai kyau da Yesu idan muna so a amsa addu’o’inmu. Hakan yana nufin cewa ba kammala addu’armu “cikin sunan Yesu” kaɗai muke bukatar mu yi ba. Muna bukatar mu fahimci yadda Jehobah yake amfani da Yesu don ya amsa addu’o’inmu. Yesu ya gaya wa manzanninsa cewa: ‘Duk dai abin da kuka roƙa cikin sunana zan yi.’ (Yoh. 14:13) Ko da yake Jehobah ne yake ji da kuma amsa addu’o’inmu, ya ba Yesu ikon zartar da shawarwarinsa. (Mat. 28:18) Saboda haka, kafin Allah ya amsa addu’o’inmu, yana fara dubawa ya ga ko mun bi shawarar da Yesu ya bayar. Alal misali, Yesu ya ce: “Idan kuka gafarta wa waɗanda suka yi muku laifi, Ubanku na sama ma zai gafarta muku. Amma idan kuwa ba ku gafarta wa mutane ba, haka ma Ubanku ba zai gafarta muku laifofinku ba.” (Mat. 6:14, 15) Saboda haka, yana da muhimmanci mu riƙa bi da mutane yadda Jehobah da Yesu suke bi da mu!
7. Su waye ne za su amfana daga fansar Yesu?
7 Waɗanda suke da dangantaka mai kyau da Yesu ne za su amfana daga fansar da ya yi. Ta yaya muka san hakan? Yesu ya ce zai “ba da ransa saboda abokansa.” (Yoh. 15:13) Bayin Allah da suka yi rayuwa kafin Yesu ya zo duniya, za su koya game da shi kuma su ƙaunace shi. Za a ta da mutane kamar su Ibrahim da Saratu da Musa da Rahab, kuma suna bukatar su ƙulla dangantaka da Yesu kafin su sami rai na har abada.—Yoh. 17:3; A. M. 24:15; Ibran. 11:8-12, 24-26, 31.
8-9. Kamar yadda aka bayyana a Yohanna 15:4, 5, mene ne dangantakarmu da Yesu za ta taimaka mana mu yi, kuma me ya sa yake da muhimmanci?
8 Muna da gatan yin aiki tare da Yesu Kristi sa’ad da muke wa’azi da kuma koyar da mutane game da Mulkin Allah. Yesu malami ne sa’ad da yake duniya. Shi ne shugaban ikilisiya tun da ya koma sama, kuma ya ci gaba da yin ja-goranci a wa’azi da kuma koyar da mutane. Yana farin ciki don ƙoƙarin da kake yi ka taimaka wa mutane su san shi da kuma Jehobah. Babu shakka, Jehobah da kuma Yesu ne kaɗai za su taimaka mana mu cim ma wannan aikin.—Karanta Yohanna 15:4, 5.
9 Kalmar Allah ta nuna sarai cewa muna bukatar mu ci gaba da ƙaunar Yesu idan muna so mu faranta ran Jehobah. Bari mu tattauna abubuwa huɗu da muke bukatar mu yi domin mu zama abokan Yesu.
YADDA ZA MU ƘULLA ABOTA DA YESU
10. Mene ne za mu fara yi don mu ƙulla abokantaka da Yesu?
10 (1) Ka san Yesu. Muna iya sanin Yesu ta wajen karanta littafin Matiyu da Markus da Luka da kuma Yohanna. Yayin da muka yi tunani a kan abubuwan da muka karanta a Littafi Mai Tsarki game da Yesu, za mu soma ƙaunar Yesu da kuma daraja shi don yadda ya nuna wa mutane alheri. Alal misali, duk da cewa shi ne shugabansu, bai bi da mabiyansa kamar bayi ba. A maimakon haka, ya gaya musu ra’ayinsa Yoh. 15:15) Sa’ad da suke baƙin ciki da makoki, Yesu ma ya yi hakan. (Yoh. 11:32-36) Maƙiyan Yesu ma sun san cewa shi abokin waɗanda suke sauraran sa ne. (Mat. 11:19) Idan muka yi koyi da Yesu, dangantakarmu da mutane za ta yi kyau, za mu ƙara farin ciki kuma za mu ƙaunaci Yesu sosai.
da kuma yadda yake ji. (11. Wane mataki na biyu ne muke bukatar mu ɗauka don mu zama abokan Yesu, kuma me ya sa yake da muhimmanci?
11 (2) Ka kasance da ra’ayin Yesu kuma ka yi irin ayyukansa. Dangantakarmu da Yesu za ta yi danƙo idan muka san shi kuma muka yi koyi da shi. (1 Kor. 2:16) Ta yaya za mu yi koyi da Yesu? Ka yi la’akari da wani misali. Yesu ya fi son taimaka wa mutane, fiye da faranta ransa. (Mat. 20:28; Rom. 15:1-3) Hakan ya sa yana gafartawa da kuma sadaukarwa sosai. Kuma ba ya saurin fushi don abubuwan da mutane suka faɗa game da shi. (Yoh. 1:46, 47) Ba ya riƙe mutane a zuciya domin kuskuren da suka yi. (1 Tim. 1:12-14) Yesu ya ce: “Ta haka kowa zai sani ku almajiraina ne, in dai kuna ƙaunar juna.” (Yoh. 13:35) Ka tambayi kanka, “Ina yin iya ƙoƙarina in yi koyi da Yesu a yadda nake sha’ani da ’yan’uwana maza da mata?”
12. Wane mataki na uku ne muke bukatar ɗauka don mu zama abokan Yesu, kuma ta yaya za mu yi hakan?
12 (3) Ka goyi bayan ’yan’uwan Yesu. Idan mun goyi bayan shafaffu, Yesu yana ɗaukan hakan a matsayin alherin da muka yi masa. (Mat. 25:34-40) Hanya mafi muhimmanci da za mu iya goyon bayan shafaffu ita ce ta yin wa’azi da ƙwazo da kuma almajirtarwa kamar yadda Yesu ya umurci mabiyansa su yi. (Mat. 28:19, 20; A. M. 10:42) Sai da taimakon “waɗansu tumaki” ne shafaffu za su iya cim ma wa’azin da aka ce su yi. (Yoh. 10:16) Idan kana sa ran yin rayuwa a duniya, za ka nuna cewa kana ƙaunar shafaffu da kuma Yesu a duk lokacin da ka fita wa’azi.
13. Ta yaya za mu iya bin shawarar Yesu da ke Luka 16:9?
13 Ƙari ga haka, muna iya zama abokan Jehobah da kuma Yesu ta wajen yin amfani da dukiyarmu don mu tallafa wa hidimarsu. (Karanta Luka 16:9.) Alal misali, za mu iya tallafa wa aikin da ake yi a faɗin duniya da gudummawar kuɗi. Ana yin amfani da kuɗaɗen nan don wa’azi a wurare masu nisa, da gina wuraren ibada da kula da su, da kuma tanadar da kayan agaji ga waɗanda bala’i ya shafa. Ƙari ga haka, za mu iya ba da gudummawar kuɗi don mu tallafa wa ikilisiyarmu da kuma ikilisiyoyin da muka san cewa suna da bukata. (K. Mag. 19:17) Ta waɗannan hanyoyin ne za mu iya goyon bayan ’yan’uwan Yesu.
14. Kamar yadda Afisawa 4:15, 16 suka nuna, wane mataki na huɗu ne za mu ɗauka don mu zama abokan Yesu?
14 (4) Ka goyi bayan shirye-shiryen ƙungiyar Jehobah. Za mu zama abokan Yesu na kud da kud idan muna bin ja-gorancin mutanen da ya naɗa su kula da mu. (Karanta Afisawa 4:15, 16.) Alal misali, yanzu muna tabbatar da cewa ikilisiyoyi da yawa ne suke yin amfani da Majami’ar Mulki guda. Hakan ya sa an haɗa wasu ikilisiyoyi kuma an yi gyara a yankunan da ’yan’uwa suke wa’azi. Wannan tsarin ya sa ƙungiyar Jehobah ta rage kuɗaɗen da take kashewa. Amma hakan ya sa wasu masu shela su yi canje-canje. Waɗannan ’yan’uwa maza da mata masu aminci sun daɗe suna hidima a ikilisiyarsu kuma sun kusaci ’yan’uwa sosai, amma an ce su koma wata ikilisiya. Babu shakka, Yesu yana matuƙar farin cikin ganin yadda mabiyansa suke goyon bayan wannan tsarin!
ABOKAN YESU HAR ABADA
15. Ta yaya za mu kyautata abokantakarmu da Yesu a nan gaba?
15 Mutanen da Jehobah ya shafe su da ruhu mai tsarki suna sa ran kasancewa da Yesu a Mulkinsa a sama. Za su ga Yesu, su tattauna da shi, kuma su yi cuɗanya da shi. (Yoh. 14:2, 3) Yesu zai ƙaunaci da kuma kula da mutanen da suke sa ran yin rayuwa a duniya. Duk da cewa ba za su ga Yesu ba, dangantakarsu da shi za ta yi danƙo, kuma za su more rayuwar da Jehobah da Yesu suka tanadar musu.—Isha. 9:6, 7.
16. Ta yaya abokantaka da Yesu yake taimaka mana?
16 Sa’ad da muka amince mu zama abokan Yesu, za mu sami albarku da yawa. Alal misali, muna amfana daga yadda yake ƙaunar mu da kuma tallafa mana. Muna da begen yin rayuwa har abada. Kuma mafi muhimmanci ma, za mu sami dukiya mafi kyau, wato dangantaka da Jehobah. Gata ce babba a ce mu abokan Yesu ne!
WAƘA TA 17 “Na Yarda”
^ sakin layi na 5 Manzannin Yesu sun yi shekaru suna tattaunawa da kuma hidima da shi, hakan ya sa sun zama aminan juna. Yesu yana so mu zama abokansa, amma muna fuskantar ƙalubalen da manzanninsa ba su fuskanta ba. A wannan talifin, za mu tattauna wasu cikin ƙalubalen da kuma shawarwarin da za su iya taimaka mana mu ci gaba da zama abokan Yesu na kud da kud.
^ sakin layi na 55 BAYANI A KAN HOTUNA: (1) Sa’ad da muke ibada ta iyali, muna iya yin nazari a kan rayuwar Yesu da kuma hidimarsa a duniya. (2) A cikin ikilisiya, muna iya yin ƙoƙari mu zauna lafiya da ’yan’uwanmu. (3) Muna goyon bayan ’yan’uwan Yesu ta wajen saka ƙwazo a wa’azi. (4) Sa’ad da aka haɗa ikilisiyoyi, muna bukatar mu bi shawarwarin da dattawa suka yanke.