Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 15

Mene ne Ra’ayinka Game da Mutanen Yankinku?

Mene ne Ra’ayinka Game da Mutanen Yankinku?

“Ku dubi gonaki da kyau, sun nuna, sun kuma isa girbi.”​—YOH. 4:35.

WAƘA TA 64 Mu Riƙa Yin Wa’azi da Farin Ciki

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Me ya sa Yesu ya yi furucin da ke Yohanna 4:​35, 36?

AKWAI lokacin da Yesu da almajiransa suke wucewa ta gonar hatsi. (Yoh. 4:​3-6) Sauran wajen wata huɗu a girbe hatsin. Yesu ya faɗi abin da ya ba almajiransa mamaki, ya ce: “Ku dubi gonaki da kyau, sun nuna, sun kuma isa girbi.” (Karanta Yohanna 4:​35, 36.) Me Yesu yake nufi?

2 Yesu yana magana ne game da almajirtar da mutane. Ka yi la’akari da abin da ya faru. Ko da yake Yahudawa ba sa yin sha’ani da Samariyawa, amma Yesu ya yi wa wata Basamariya wa’azi kuma ta saurara! A daidai lokacin da Yesu yake magana game da ‘gonakin’ ne Samariyawan da suka ji labarinsa daga wurin matar suke hanya don su je su ji wa’azinsa. (Yoh. 4:​9, 39-42) Wani masanin Littafi Mai Tsarki ya ce game da ayar nan: “Da yake mutanen sun zo wurin Yesu da gaggawa . . . hakan ya nuna cewa suna kama da hatsin da ya isa girbi.”

Me ya kamata mu yi idan mun lura cewa mutanen yankinmu suna a shirye su ji wa’azinmu? (Ka duba sakin layi na 3)

3. Idan kana da irin ra’ayin Yesu, ta yaya mutane za su amfana daga wa’azinka?

3 Mene ne ra’ayinka game da mutanen da kake wa wa’azi? Kana ɗaukan su a matsayin hatsin da ya isa girbi? Idan haka ne, za ka yi abubuwan nan uku. Na ɗaya, za ka ƙara ƙwazo a yin wa’azi. Lokacin da ake yin girbi ba ya daɗewa, saboda haka, ba a ɓata lokaci. Na biyu, za ka yi farin ciki idan mutane suna saurarar wa’azinka. Littafi Mai Tsarki ya ce: Mutane suna murna a lokacin “girbin hatsi.” (Isha. 9:3) Na uku, za ka ɗauki kowane mutum a matsayin wanda zai iya zama mabiyin Yesu kuma hakan zai sa ka yi masa wa’azi a kan batun da zai ratsa zuciyarsa.

4. Mene ne za mu koya daga manzo Bulus a wannan talifin?

4 Wasu cikin almajiran Yesu sun ɗauka cewa Samariyawa ba za su taɓa zama mabiyan Yesu ba, amma Yesu bai da irin wannan ra’ayin. Mu ma muna bukatar mu ɗauki mutanen yankinmu a matsayin waɗanda za su iya zama mabiyan Yesu. Manzo Bulus ya kafa mana misali mai kyau a wannan fannin. Wane darasi ne za mu iya koya daga wurinsa? A wannan talifin, za mu tattauna yadda Bulus ya san (1) abin da mutanen da ya yi wa wa’azi suka yi imani da shi, (2) abubuwan da suke so, da kuma (3) yadda ya ɗauke su a matsayin mutanen da za su iya zama bayin Allah.

ME SUKA YI IMANI DA SHI?

5. Yaya Bulus ya san abubuwan da mutanen da yake wa wa’azi suka yi imani da shi?

5 Bulus yana yawan yin wa’azi a majami’ar Yahudawa. Alal misali, “Bulus ya shiga” majami’ar Tassalunika kuma ya yi “muhawara da . . . [Yahudawa] daga cikin Rubutacciyar Maganar Allah” har ranakun Assabaci guda uku. (A. M. 17:​1, 2) Sa’ad da Bulus yake majami’ar, bai ji tsoro ba domin shi ma Bayahude ne. (A. M. 26:​4, 5) Bulus ya san abubuwan da Yahudawa suka yi imani da su, don haka ya yi musu wa’azi da ƙarfin zuciya.​—Filib. 3:​4, 5.

6. Ta yaya mutanen da Bulus ya yi wa wa’azi a kasuwa suka bambanta da waɗanda ya yi wa wa’azi a majami’a?

6 ’Yan hamayya sun sa Bulus ya gudu daga Tassalunika da kuma Biriya zuwa Atina. Bayan haka, ya soma “muhawara a cikin majami’a da Yahudawa, da waɗansu Helenawa masu yi wa Allah sujada.” (A. M. 17:17) Amma sa’ad da Bulus yake wa’azi a kasuwa, ya yi wa waɗansu mutane dabam wa’azi. Wasu cikin mutanen nan su ne masu ilimin falsafa da kuma waɗanda ba Yahudawa ba da suka ce wa’azin da Bulus yake yi “sabuwar koyarwar” ce. Suka ce masa: “Ba mu taɓa jin irin waɗannan maganganu ba.”​—A. M. 17:​18-20.

7. Kamar yadda Ayyukan Manzanni 17:​22, 23 suka nuna, ta yaya Bulus ya yi wa’azi a hanyar da za a fahimta?

7 Karanta Ayyukan Manzanni 17:​22, 23. Yadda Bulus ya yi wa ’yan Atina wa’azi ya bambanta da yadda ya yi wa Yahudawa a majami’a. Wataƙila Bulus ya tambayi kansa, ‘Mene ne ’yan Atina suka yi imani da shi?’ Ya lura da mahallin mutane da kuma yadda suke ibada. Bulus ya yi magana a kan abubuwan da shi da kuma mutanen Atina suka yi imani da su. Wani masani ya ce: “Da yake Bulus Bayahude ne da kuma Kirista, ya san cewa Girkawa ba sa bauta wa Allahn ‘gaskiya’ da Yahudawa da kuma Kiristoci suke bauta wa. Amma ya bayyana musu cewa sun san Allahn da yake yi musu wa’azi a kai.” Don haka, ya yi musu wa’azi yadda za su fahimta. ʼYan Atina sun gina bagadi don “Allahn da ba a sani ba,” shi ya sa Bulus ya gaya musu cewa wa’azin da yake yi daga wannan Allahn ne. Ko da yake mutanen ba su san Nassosi ba, Bulus bai ɗauka cewa ba za su iya zama Kiristoci ba. Maimakon haka, ya ɗauke su a matsayin hatsin da ya nuna kuma ya isa girbi. Hakan ya sa ya yi musu wa’azi yadda za su fahimta.

Ka yi koyi da Bulus ta wajen zama mai lura da yin wa’azi a hanyar da mutane za su fahimta da kuma ɗaukan kowa a matsayin waɗanda zai iya zama mabiyin Yesu (Ka duba sakin layi na 8, 12, 18) *

8. (a) Mene ne zai taimaka maka ka san abubuwan da mutanen yankinku suka yi imani da su? (b) Idan mutum ya ce yana da nasa addinin, mene ne za ka ce masa?

8 Ka zama mai lura kamar Bulus. Ka nemi abubuwan da za su taimaka maka ka san abin da masu gida suka yi imani da shi. Mene ne mutumin ya manna a gidansa ko kuma motarsa? Shin sunansa ko tufafinsa ko adonsa ko kuma yadda yake magana ya sa ka san addininsa? Wataƙila ya gaya maka kai tsaya cewa yana da nasa addinin. Sa’ad da hakan ya faru da wata majagaba ta musamman mai suna Flutura, takan ce, “Ban zo don in cusa miki ra’ayina ba, amma ina so mu tattauna wannan jigo . . . ”

9. Wane batu ne za ka iya tattaunawa da mutumin da ke bin addini?

9 Wane batu ne za ka iya tattaunawa da mutumin da ke bin addini? Ka nemi batun da ku biyu kuka yi imani da shi. Wataƙila ya yi imani da Allah guda ko ya yi imani cewa Yesu ne Mai Cetonmu ko kuma ya yi imani cewa muna rayuwa a kwanakin ƙarshe. Ka yi amfani da abubuwan da ku biyu kuka yi imani da shi don ka yi masa wa’azi a hanyar da za ta ratsa zuciyarsa.

10. Me muke bukatar mu ƙoƙarta mu yi, kuma me ya sa?

10 Ka tuna cewa ba kowa ba ne yake amincewa da dukan abin da ake koyarwa a addininsu ba. Don haka, ko da ka san addinin wani, ka tambaye shi abin da ya yi imani da shi. Wata mai suna Donalta a Albaniya ta ce: “Wasu da muke haɗuwa da su suna ce mana suna bin addini, amma daga baya sai su ce ba su yi imani da Allah ba.” Ƙari ga haka, wani mai wa’azi a ƙasashen waje a Ajantina ya ce wasu mutane sun yi imani da Dunƙulen-alloli-uku, amma wataƙila ba su amince cewa Allah da Ɗansa da kuma ruhu mai tsarki ɗaya ba ne. Ya ƙara da cewa: “Sanin hakan yana taimaka mana mu san yadda za mu yi wa mutumin wa’azi.” Saboda haka, ka ƙoƙarta ka san ainihin abin da mutane suka yi imani da shi. Don ka zama “kowane irin abu ga ko waɗanne irin mutane” yadda manzo Bulus ya yi.​—1 Kor. 9:​19-23.

ME SUKE SO?

11. Kamar yadda Ayyukan Manzanni 14:​14-17 suka nuna, ta yaya Bulus ya yi amfani da abubuwan da ’yan Listra suke so don ya yi wa’azi?

11 Karanta Ayyukan Manzanni 14:​14-17. Manzo Bulus ya san abin da mutane suke so kuma ya yi amfani da su don ya tattauna da su a hanyar da za su fahimta. Alal misali, mutanen da ya yi wa wa’azi a Listra ba su san Nassosi ba sosai. Don haka, Bulus ya yi musu wa’azi a hanyar da za su fahimta. Ya yi magana game da samun amfanin gona da kuma jin daɗin rayuwa. Ya yi amfani da kalmomi da misalin da masu sauraro za su fahimta.

12. Ta yaya za ka san abin da mutum yake so kuma ka yi masa wa’azi dangane da yanayinsa?

12 Ka yi amfani da basira don ka san abubuwan da mutanen yankinku suke so kuma ka yi musu wa’azi dangane da yanayinsu. Ta yaya za ka san abin da mutum yake so sa’ad da ka haɗu da shi ko kuma ka je gidansa? Ka lura da kyau. Wataƙila yana shara ko karatu ko gyarar mota ko kuma wani abu dabam. Kana iya yin amfani da abin da yake yi don ka soma tattaunawa da shi. (Yoh. 4:7) Irin rigar da mutum ya saka tana iya sa ka san al’adarsa ko aikinsa ko kuma kulob ɗin ’yan wasa da yake so. Wani mai suna Gustavo ya ce: “Na soma tattaunawa da wani saurayi ɗan shekara 19 da aka yi zanen wani mawaƙi a rigarsa. Na tambaye shi game da mawaƙin kuma ya gaya mini dalilin da ya yake son mawaƙin. Wannan tattaunawar ya sa na soma nazari da shi kuma yanzu shi Mashaidi ne.”

13. Ta yaya za ka sa mutum ya so a yi nazari da shi?

13 Sa’ad da kake so wani ya yarda a yi nazari da shi, ka yi magana a hanyar da zai ƙosa a yi nazarin da shi kuma ka nuna masa yadda zai amfana. (Yoh. 4:​13-15) Alal misali, wata da ke son wa’azinmu ta gayyaci wata ’yar’uwa mai suna Hester cikin ɗakinta. Saʼad da Hester ta ga wani takardar da matar ta manna a bangon ɗakinta, ta lura cewa matar farfesa ce. Don haka, Hester ta bayyana mata cewa muna ilimantar da mutane ta nazarin Littafi Mai Tsarki da muke yi da su da kuma taronmu. Matar ta yarda a yi nazari da ita, ta halarci taro washegari, kuma bayan haka ta halarci taron da’ira. Bayan shekara ɗaya sai ta yi baftisma. Ka tambayi kanka: ‘Mene ne mutanen da nake koma ziyara wurinsu suke so? Zan iya bayyana musu nazarin da muke yi da mutane a hanyar da za su so a yi nazarin da su?’

14. Ta yaya za ka yi nazari da kowane ɗalibi dangane da yanayinsa?

14 Sa’ad da ka soma yin nazari da ɗalibin, ka riƙa yin shiri sosai kafin ku yi nazari. Ƙari ga haka, ka yi la’akari da iyalinsa da abubuwan da ya sani da kuma abubuwan da yake so. Sa’ad da kake shirin, ka zaɓi nassosin da za ka karanta, da bidiyoyin da za ka nuna masa da kuma misalan da za ka yi amfani da su don ka bayyana masa gaskiya. Ka tambayi kanka: ‘Me ɗalibin zai so a tattauna da shi da zai ratsa zuciyarsa?’ (K. Mag. 16:23) A ƙasar Albaniya, wata mata da wata majagaba mai suna Flora take nazari da ita, ta ce: “Ba zan taɓa yarda cewa za a yi tashin matattu ba.” Flora ba ta tilasta mata ba. Ta ce: “Na fahimci cewa tana bukatar ta fara sanin Allahn da ya yi alkawarin ta da matattu kafin ta amince da koyarwar.” Daga lokacin, a duk sa’ad da suka yi nazari, Flora tana nanata yadda Jehobah yake da ƙauna da hikima da kuma iko. Daga baya, ɗalibar ta amince da koyarwar tashin matattu. A yanzu, ita Mashaidiya ce.

ZA SU IYA ZAMA ALMAJIRAN YESU

15. Kamar yadda Ayyukan Manzanni 17:​16-18 suka nuna, mene ne ʼyan Atina suke yi, kuma me ya sa Bulus bai daina yi musu wa’azi ba?

15 Karanta Ayyukan Manzanni 17:​16-18. Manzo Bulus bai yasar da ʼyan Atina ba, duk da cewa suna bauta wa gumaka, suna yin lalata, kuma suna fifita koyarwar ƙarya. Ƙari ga haka, bai daina yi musu wa’azi ba, duk da cewa sun zazzage shi. Bulus da kansa ya zama Kirista duk da cewa a dā shi “mai saɓon Allah ne, mai tsananta masa, kuma mai wulaƙanta shi.” (1 Tim. 1:13) Kamar yadda Yesu ya ɗauki Bulus a matsayin mutumin da zai iya zama mabiyansa, haka ma Bulus ya ɗauki mutanen Atina. Hakika wasu cikinsu sun zama Kiristoci.​—A. M. 9:​13-15; 17:34.

16-17. Mene ne ya nuna cewa kowane mutum zai iya zama almajirin Yesu? Ka ba da misali.

16 A ƙarni na farko, mutane da suka fito daga wurare dabam-dabam sun zama mabiyan Yesu. Sa’ad da Bulus ya rubuta wasiƙa ga Kiristocin da ke Korinti, ya faɗi cewa a dā wasu a ikilisiyar suna sata da kuma lalata. Ya ƙara da cewa: “Haka waɗansunku ma suke dā, amma an tsabtace ku.” (1 Kor. 6:​9-11) Da a ce kai ne, za ka ɗauka cewa waɗannan mutanen ba za su zama mabiyan Yesu ba?

17 A yau, mutane da yawa suna yin canje-canje don su zama mabiyan Yesu. Alal misali, a ƙasar Ostareliya wata majagaba ta musamman mai suna Yukina ta fahimci cewa kowane mutum zai iya zama almajirin Yesu. Akwai ranar da majagabar ta ga wata mata da ta yi zane-zane a jikinta kuma ba ta yi ado mai kyau ba. Yukina ta ce: “Na ɗan yi jinkiri kafin na soma tattaunawa da ita. Sai na lura cewa tana son Littafi Mai Tsarki kuma wasu cikin zane-zanen jikinta ayoyin littafin Zabura ne!” Matar ta soma yin nazari da kuma halartan taro. *

18. Me ya sa bai dace mu shari’anta mutane ba?

18 A lokacin da Yesu ya ce gonaki sun isa girbi, shin yana sa rai ne cewa yawancin mutane za su zama mabiyansa? A’a. An riga an annabta cewa mutane ƙalilan ne za su zama mabiyan Yesu. (Yoh. 12:​37, 38) Yesu yana da ikon sanin abin da ke zuciyar mutum. (Mat. 9:4) Duk da cewa ya fi mai da hankali a kan mutane ƙalilan da za su zama mabiyansa, ya yi wa kowa wa’azi da himma. Ba mu san abin da ke zuciyar mutane ba, don haka, kada mu shari’anta mutanen da muka haɗu da su! A maimakon haka, mu ɗauki mutanen a matsayin waɗanda za su iya zama mabiyan Yesu. Wani mai wa’azi a ƙasashen waje mai suna Marc da ke hidima a Burkina Faso ya ce: “A yawancin lokaci mutanen da nake zato za su sami ci gaba suna daina yin nazarin. Amma waɗanda nake zato cewa ba za su sami ci gaba ba, su ne suke samun ci gaba sosai. Saboda haka, na ga ya fi dacewa mu bari Jehobah ya yi mana ja-goranci da ruhunsa.”

19. Ta yaya muke bukatar mu ɗauki mutane a yankinmu?

19 Idan ka yi tunani a kan mutanen da ke yankinku, za ka iya yin zato cewa da yawa cikinsu ba za su iya yin canji ba. Amma ka tuna abin da Yesu ya gaya wa almajiransa. Ya ce gonaki sun nuna, sun kuma isa girbi. Mutane za su iya canja salon rayuwarsu kuma su zama mabiyan Yesu. Jehobah ya san cewa mutanen yankinku za su iya zama bayinsa kuma yana daraja su. (Hag. 2:7) Idan muna ɗaukan mutane yadda Jehobah da Yesu suke ɗaukan su, za mu yi ƙoƙari mu san al’adunsu da abubuwan da suke so. Ba za mu ɗauke su a matsayin baƙi ba, amma a matsayin mutanen da za su iya zama ʼyan’uwanmu.

WAƘA TA 57 Ku Yi wa Dukan Mutane Wa’azi

^ sakin layi na 5 Ta yaya ra’ayinmu game da mutanen yankinmu yake shafan yadda muke wa’azi da kuma koyarwa? A wannan talifin, za mu tattauna yadda manzo Bulus da Yesu suka ɗauki mutanen da suke wa wa’azi. Kuma za mu ga yadda za mu iya yin koyi da yadda suka yi la’akari da imanin mutane da abubuwan da suke so, kuma suka ɗauki kowa a matsayin mutanen da za su iya zama bayin Allah.

^ sakin layi na 17 Jerin talifofin nan “Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane” na ɗauke da labaran mutanen da suka canja salon rayuwarsu. Ana wallafa talifofin a Hasumiyar Tsaro har zuwa 2017. Yanzu ana wallafa su a dandalin jw.org®. Ka duba ƙarƙashin GAME DA MU > LABARAN SHAIDUN JEHOBAH.

^ sakin layi na 57 BAYANI A KAN HOTUNA: Sa’ad da wasu ma’aurata suke wa’azi gida-gida sun lura da (1) wani gida mai tsabta da aka shuka fure da (2) gidan da akwai yara a ciki da (3) gida mai datti ciki da waje da kuma (4) gidan da mutanen suke bin addini. A ina za ka sami mutumin da zai iya zama mabiyin Yesu?