Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 18

Na Yi Tseren Har Karshe

Na Yi Tseren Har Karshe

“Na yi kokawa a cikin tseren” har ƙarshe.​—2 TIM. 4:7.

WAƘA TA 129 Za Mu Riƙa Jimrewa

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne ya kamata dukanmu mu yi?

IDAN kana rashin lafiya ko kuma ka gaji, za ka so ka yi tseren da ka san cewa yana da wuya? Da kyar. Amma, manzo Bulus ya ce dukan Kiristoci suna yin tsere. (Ibran. 12:1) Wajibi ne dukanmu mu jimre har ƙarshe idan muna so mu sami ladar da Jehobah zai ba mu.​—Mat. 24:13.

2. Kamar yadda aka nuna a 2 Timoti 4:​7, 8, me ya sa Bulus ya iya ba da wannan shawarar?

2 Ya kasance wa Bulus da sauƙi ya yi magana game da wannan batun domin ya yi “tseren” har ƙarshe. (Karanta 2 Timoti 4:​7, 8.) Amma mene ne ainihin tseren da Bulus ya yi magana a kai?

MENE NE TSEREN?

3. Mene ne tseren da Bulus ya yi magana a kai?

3 A wasu lokuta, Bulus ya yi amfani da wasanni da aka yi a ƙasar Girka ta dā don ya koyar da darussa masu muhimmanci. (1 Kor. 9:​25-27; 2 Tim. 2:5) Bulus ya kwatanta rayuwar Kirista da yin tsere. (1 Kor. 9:24) Mutum zai soma wannan “tseren” sa’ad da ya yi alkawarin bauta wa Jehobah da kuma baftisma. (1 Bit. 3:21) Zai yi nasara a tseren sa’ad da Jehobah ya ba shi ladar rai na har abada.​—Mat. 25:​31-34, 46; 2 Tim. 4:8.

4. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

4 Waɗanne kamani ne ke tsakanin yin tsere da rayuwar Kirista? Suna da yawa. Bari mu tattauna uku cikinsu. Na farko, muna bukatar mu bi hanyar da ta dace. Na biyu, wajibi ne mu mai da hankali don mu gama tseren. Kuma na uku shi ne, mu jimre da matsaloli da za mu fuskanta.

MU BI HANYAR DA TA DACE

Dukanmu muna bukatar mu bi hanyar rai (Ka duba sakin layi na 5-7) *

5. Wace hanya ce ya wajaba mu bi, kuma me ya sa?

5 Don masu yin tsere su yi nasara, wajibi ne su bi hanyar da aka tsara musu. Hakazalika, idan muna so mu sami rai na har abada, wajibi ne mu bi hanyar rai. (A. M. 20:24; 1 Bit. 2:21) Amma, Shaiɗan da mutanensa suna so mu ci gaba da “haɗin kai da su.” (1 Bit. 4:4) Suna mana ba’a don zaɓin da muka yi kuma suna cewa salon rayuwarsu ne ke sa a sami ’yanci. Amma hakan ba gaskiya ba ne.​—2 Bit. 2:19.

6. Mene ne ka koya daga labarin Brian?

6 Duk waɗanda suke bin Shaiɗan za su ga cewa salon rayuwarsu ba zai sa su sami ’yanci ba, amma za su zama bayin Shaiɗan. (Rom. 6:16) Ka yi la’akari da abin da ya faru da Brian. Iyayensa sun ƙarfafa shi ya bi hanyar rayuwar da ta dace. Amma sa’ad da ya zama matashi, ya soma shakka ko hakan zai sa shi farin ciki. Brian ya yanke shawarar yin rayuwar da ba ta dace ba. Ya ce: “Ban san cewa wannan “ ’yanci” da nake nema zai jefa ni cikin mummunar jarrabawa ba. . . . Da sannu sannu, na soma shaye-shaye da iskanci. Da shigewar shekaru, na duƙufa cikin shan ƙwayoyi kuma hakan ya zama min jaraba. Na soma sayar da miyagun ƙwayoyi domin in sami kuɗin shaye-shaye.” Daga baya, Brian ya yanke shawara cewa zai riƙa bin ƙa’idodin Jehobah. Sai ya canja salon rayuwarsa kuma ya yi baftisma a shekara ta 2001. Yanzu, Brian yana farin cikin kasancewa da salon rayuwar da ta dace. *

7. Kamar yadda aka nuna a Matiyu 7:​13, 14, waɗanne hanyoyi biyu ne za mu iya bi?

7 Yana da muhimmanci mu zaɓi hanyar da ta dace da za mu bi! Shaiɗan yana so mu daina bin ƙaramar hanyar da za ta sa mu sami “rai” kuma mu soma bin hanya mai fāɗi da yawancin mutane a duniya ke bi. Mutane da yawa suna bin hanyar kuma tana da sauƙin bi, amma tana kai ga “halaka.” (Karanta Matiyu 7:​13, 14.) Idan muna so mu ci gaba a hanyar rai ba tare da mun bijire ba, wajibi ne mu dogara ga Jehobah kuma mu riƙa saurarar sa.

KADA MU YARDA KOME YA JANYE HANKALINMU A TSEREN

Kada mu bar kome ya janye hankalinmu (Ka duba sakin layi na 8-12) *

8. Idan mai tsere ya yi tuntuɓe, mene ne zai yi?

8 Masu tseren dogon zango suna mai da hankali don kada wani abu ya janye hankalinsu sa’ad da suke tseren. Amma, wani da suke tseren tare yana iya sa su tuntuɓe ko kuma suna iya faɗi a rami. Idan sun faɗi, za su tashi su ci gaba da gudu. Suna mai da hankali a kan ladar da za su samu ba a kan abin da ya sa su tuntuɓe ba.

9. Me ya kamata mu yi idan mun yi tuntuɓe?

9 Muna iya yin tuntuɓe sau da yawa a tseren kuma mu yi kuskure a furucinmu da ayyukanmu. Kuma waɗanda muke tsere tare suna iya yin abin da zai ɓata mana rai. Bai kamata hakan ya sa mu mamaki ba. Dukanmu ajizai ne kuma muna tsere a matsatsiyar hanyar rai. Hakazalika, a wasu lokuta muna iya ɓata wa ’yan’uwanmu rai yayin da muke bauta wa Jehobah. Bulus ya ce a wasu lokuta muna iya yi wa juna “laifi.” (Kol. 3:13) Amma, maimakon mu riƙa mai da hankali ga abin da ya sa mu tuntuɓe, mu riƙa sa rai a ladar da za mu samu. Idan mun faɗi, bari mu tashi mu ci gaba da tseren. Amma idan muka yi fushi kuma muka ƙi tashi, ba za mu kammala tseren kuma mu sami lada ba. Ƙari ga haka, idan mun ci gaba da fushi, za mu iya sa ya yi wa ’yan’uwanmu wuya su ci gaba da bauta wa Jehobah.

10. Ta yaya za mu guji sa mutane “tuntuɓe”?

10 Wata hanya kuma da za mu guji sa ’yan’uwanmu “tuntuɓe” ita ce ta wajen bari su yi abin da suke so, maimakon cusa musu ra’ayinmu. (Rom. 14:​13, 19-21; 1 Kor. 8:​9, 13) Ga abubuwa da suka sa muka bambanta da masu tsere na zahiri. Suna gasa da juna kuma kowannensu yana ƙoƙari ya ci gasar shi kaɗai. Sun fi mai da hankali ga kansu kawai. Saboda haka, suna iya ture sauran masu tseren don su sha gabansu. Amma mu Kiristoci ba ma gasa da juna. (Gal. 5:26; 6:4) Muradinmu shi ne mu taimaka wa mutane da yawa su yi nasara a tseren kuma su sami ladan rai na har abada. Saboda haka, muna ƙoƙarin bin shawarar Bulus cewa “kada ku kula da kanku kaɗai, amma ku kula da waɗansu kuma.”​—Filib. 2:4.

11. Mene ne masu tsere suke mai da wa hankali, kuma me ya sa?

11 Ban da kallon hanyar da suke bi, masu tsere suna mai da hankali a kan layin da za su kai da zai nuna cewa sun kammala tseren. Ko da ba su hangi layin ba, suna tunanin yadda za su wuce layin kuma su sami lada. Mai da hankali a kan ladar da za su samu yana sa su ci gaba da tseren.

12. Mene ne Jehobah ya tabbatar mana da shi?

12 Jehobah ya tabbatar mana da cewa idan muka kammala tseren da muke yi, zai ba mu ladar rai na har abada a sama ko a duniya. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta wannan ladar don mu ga yadda za mu more rayuwa a nan gaba. Idan muka ci gaba da tunani a kan wannan begen, hakan zai taimaka mana mu guji kome da zai sa mu tuntuɓe na dindindin.

KA CI GABA DA TSEREN DUK DA MATSALOLI

Ya kamata mu ci gaba a tseren rai ko da muna fuskantar matsaloli (Ka duba sakin layi na 13-20) *

13. Ta yaya yanayinmu ya fi na masu tsere na zahiri?

13 A tseren da ake yi a ƙasar Girka ta dā, masu tseren suna fama da gajiya da ciwon jiki. Suna dogara ga horarwa da aka musu da kuma ƙarfinsu. Muna kamar masu tseren nan domin ana horar da mu sosai. Amma yanayinmu ya fi na masu tseren nan, don Jehobah zai iya sa mu yi ƙarfi kuma ya taimaka mana. Idan muka dogara ga Jehobah, ya yi alkawari cewa zai horar da mu kuma ya sa mu yi ƙarfi!​—1 Bit. 5:10.

14. Ta yaya 2 Korintiyawa 12:​9, 10 suke taimaka mana mu magance matsaloli?

14 Bulus ya jimre da ƙalubale da yawa. Ban da tsanantawa da aka yi masa da wulaƙanci da ya sha, ya gaji a wasu lokuta kuma ya fuskanci abin da ya kira “ƙaya a jiki.” (2 Kor. 12:7) Amma bai yarda waɗannan ƙalubalen su sa ya karaya ba, maimakon haka sun ba shi damar dogara ga Jehobah. (Karanta 2 Korintiyawa 12:​9, 10.) Domin Bulus ya yi hakan, Jehobah ya taimaka masa ya magance dukan matsalolinsa.

15. Ta yaya za mu amfana idan muka yi koyi da Bulus?

15 Mu ma za mu iya fuskantar tsanantawa saboda imaninmu. Ban da haka, muna iya fama da rashin lafiya ko kuma gajiya. Amma idan mun yi koyi da Bulus, ƙalubalen nan za su ba mu damar dogara ga Jehobah don ya taimaka mana.

16. Me za ka iya yi, ko da kana fama da rashin lafiya?

16 Kana fama ne da rashin lafiya da ke hana ka fita ko kuma kana amfani da keken guragu? Shin kana ciwon ƙafa ne ko kuma ba ka gani sosai? Idan haka ne, za ka iya yin tseren nan da matasa masu koshin lafiya? Ƙwarai kuwa! ’Yan’uwa tsofaffi da suke rashin lafiya suna yin wannan tsere don su sami rai na har ababa. Ba sa yin wannan aikin da ƙarfinsu. Maimakon haka, suna dogara ga Jehobah ta wajen saurarar taro ta waya ko kuma wanda aka saka a dandalin JW. Kuma suna yi wa ma’aikatan kiwon lafiya da danginsu wa’azi.

17. Ta yaya Jehobah yake ɗaukan mutanen da ke fama da rashin lafiya?

17 Kada ka yarda rashin lafiya ya sa ka ji kamar ba za ka iya kammala tseren ba. Jehobah yana ƙaunar ka don kana da bangaskiya da kuma jimiri. Kana bukatar ka dogara gare shi sosai a yanzu, kuma ba zai taɓa yasar da kai ba. (Zab. 9:10) A maimakon haka, zai kusace ka sosai. Ka yi la’akari da labarin wata ’yar’uwa da take fama da rashin lafiya. Ta ce: “Yayin da rashin lafiyata take tsanani, zarafin da nake da shi na yin wa’azi ya ragu. Amma na san cewa Jehobah yana daraja ɗan ƙoƙari da nake don in yi wa’azi, kuma hakan yana sa ni farin ciki.” Idan ka karaya, ka tuna cewa Jehobah yana tare da kai. Ka yi koyi da Bulus kuma ka tuna da abin da ya faɗa cewa: “Na gamsu da rashin ƙarfina, . . . . Gama sa’ad da ina da rashin ƙarfi, a lokacin ne nake da ƙarfi.”​—2 Kor. 12:10.

18. Me ya sa ƙalubalen da wasu suke fuskanta yake da wuya sosai?

18 Wasu masu tseren rai suna kuma fuskantar wani ƙalubale. Suna fama da matsaloli da mutane ba sa iya gani. Alal misali, suna fama da baƙin ciki mai tsanani ko kuma alhini. Me ya sa wannan ƙalubalen yake da wuyan jimrewa sosai? Domin idan mutum ya karya hannu ko kuma yana amfani da keken guragu, kowa zai san cewa yana fama da rashin lafiya kuma za a so su taimaka masa. Amma, ba a iya sanin mutanen da ke fama da baƙin ciki mai tsanani ko kuma alhini. Matsalolin da suke fama da shi na kamar na mutumin da ya karya hannu ko kafa, amma da kyar mutane su kula da su domin ba su san abin da suke fama da shi ba.

19. Wane darasi muka koya daga Mefiboshet?

19 Idan kana fama da wata matsala kuma kana ganin cewa mutane ba su fahimci yanayinka ba, misalin Mefiboshet zai ƙarfafa ka. (2 Sam. 4:4) Shi gurgu ne kuma Sarki Dauda ya yi masa rashin adalci, duk da yake bai yi wani laifi ba. Bai mai da hankali a kan rashin adalci da aka yi masa ba, amma ya nuna godiya don alherin da aka yi masa. Alal misali ya nuna godiya don yadda Dauda ya yi masa alheri a dā. (2 Sam. 9:​6-10) Saboda haka, sa’ad da Dauda ya yi masa rashin adalci, Mefiboshet ya san dalilin da ya sa ya yi hakan. Bai yarda kuskuren da Dauda ya yi ya sa shi fushi ba. Kuma bai ɗaura wa Jehobah laifi don abin da Dauda ya yi ba. Mefiboshet ya mai da hankali a kan abin da zai iya yi don ya goyi bayan sarkin da Jehobah ya naɗa. (2 Sam. 16:​1-4; 19:​24-30) Jehobah ya sa a rubuta labarin Mefiboshet a cikin Kalmarsa don mu amfana.​—Rom. 15:4.

20. Ta yaya alhini ke shafan wasu, kuma wane tabbaci ne suke da shi?

20 Wasu ’yan’uwa suna fama da alhini, kuma hakan yana hana su sake jiki sa’ad da suke cuɗanya da mutane. Ba ya musu sauƙi su kasance a wurin da jama’a suke, amma ba sa fasa halartan taron ikilisiya da na da’ira da kuma na yanki. Ƙari ga haka, yana musu wuya su tattauna da baƙi, duk da haka suna wa mutane wa’azi. Idan kana fama da wannan matsalar, ka san cewa ba kai kaɗai ke fama da ita ba. Ka tuna cewa Jehobah yana farin ciki don ƙoƙarce-ƙoƙarce da kake yi. Da yake ba ka yi sanyin gwiwa ba, Jehobah yana yi maka albarka kuma yana ba ka ƙarfin da kake bukata. * (Filib. 4:​6, 7; 1 Bit. 5:7) Idan kana bauta wa Jehobah duk da cewa kana fama da rashin lafiya, ka san cewa kana faranta wa Jehobah rai.

21. Me Jehobah zai taimaka wa dukanmu mu cim ma?

21 Akwai bambanci sosai tsakanin tsere na zahiri da kuma wanda Bulus ya yi magana a kai. A tseren da ake yi a zamanin dā, mutum ɗaya ne kawai ke samun lada. Amma a tseren rai, duk wanda ya jimre har ƙarshe zai samu ladan rai na har abada. (Yoh. 3:16) A tsere na zahiri, dole ne kowa ya kasance da koshin lafiya, idan ba haka ba, ba zai iya kammala tseren ba. Akasin haka, da yawa a cikinmu na fama da rashin lafiya, amma muna jimrewa. (2 Kor. 4:16) Jehobah zai taimaka mana mu yi tseren nan har ƙarshe!

WAƘA TA 144 Mu Riƙa Ɗokin Samun Ladan!

^ sakin layi na 5 A yau, bayin Jehobah da yawa suna fama da tsufa da kuma rashin lafiya mai tsanani. Kuma a wasu lokuta, dukanmu muna gajiya. Saboda haka, za mu iya ganin cewa ba za mu iya yin tseren nan ba. A wannan talifin, za mu tattauna yadda za mu iya jimrewa a wannan tseren rai, kuma mu sami ladan rai na har abada da manzo Bulus ya yi magana a kai.

^ sakin layi na 6 Ka duba talifin nan “Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane” da ke Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Janairu, 2013.

^ sakin layi na 20 Don samun ƙarin bayani game da yadda za ka jimre da alhini da kuma labaran yadda wasu suke magance wannan matsalar, ka duba shirin da aka yi a watan Mayu 2019 a Tashar JW. Ka duba ƙarƙashin LABURARE > TASHAR JW.

^ sakin layi na 63 BAYANI A KAN HOTO: Yin wa’azi da ƙwazo yana taimaka ma wannan ɗan’uwa tsoho ya kasance a hanyar rai.

^ sakin layi na 65 BAYANI A KAN HOTO: Muna iya sa mutane tuntuɓe ta wajen tilasta musu su ƙara giya da suke sha ko kuma idan mun cika shan giya.

^ sakin layi na 67 BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗan’uwa da aka kwantar a asibiti, ya ci gaba da tseren rai ta wajen yi wa masu kula da shi wa’azi.