Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Me ya sa maƙiyan Yesu suka ɗauki batun wanke hannu da muhimmanci?

Batun wanke hannu yana ɗaya daga cikin batutuwan da maƙiyan Yesu suka yi amfani da shi don su yi sūkar shi da mabiyansa. Dokar da Allah ya ba wa Musa ta bayyana abubuwan da za su sa mutum ya kasance marar tsarki, kamar abubuwan da ke ɗiga daga jikin mutum da kuturta da kuma gawan mutum ko kuma na dabbobi. Ƙari ga haka, dokar ta bayyana yadda mutum zai tsarkake kansa ta wajen yin hadaya da yin wanka da wanke tufafinsa da kuma yayyafa ruwan tsarkakewa.—Lev., surori ta 11-15; Lit. Lis., sura ta 19.

Malaman Yahudawa sun ƙara tasu dokokin a kan dokar da aka ba da ta hannun Musa. Wani mai bincike ya ce malaman Yahudawa sun ƙara nasu dokoki game da abin da zai sa mutum ya kasance marar tsarki da kuma yadda zai iya ƙazantar da mutane. Ƙari ga haka, waɗannan malaman sun kafa dokoki a kan abubuwan da za su iya kasancewa da tsarki ko marasa tsarki da kuma abin da mutum yake bukatar ya yi kafin ya sake kasancewa da tsarki.

Maƙiyan Yesu sun tambaye shi cewa: “Don me almajiranka ba su bi takalidai na datiɓai ba, amma suna cin gurasarsu da hannuwa marasa-tsarki?” (Mar. 7:5) Waɗannan malaman ba su damu da lafiyar jiki na mutanen ba, amma suna bin al’adarsu cewa wajibi ne mutum ya zuba ruwa a hannunsa kafin ya ci abinci. Mai binciken da aka ambata ɗazu ya daɗa cewa: “Sukan yi mahawara a kan tasoshin da za a yi amfani da su da irin ruwan da ya dace da wanda ya kamata ya zuba ruwan yayin da ake wanke hannu da kuma iyakan hannu da ya kamata a wanke.”

Mene ne Yesu ya ce game da waɗannan dokokin da ’yan Adam suka kafa? Yesu ya gaya wa malaman addinan Yahudawa na ƙarni na farko cewa: ‘Daidai Ishaya ya yi annabci a kanku masu-riya, kamar yadda an rubuta, wannan al’umma tana girmama ni da leɓunansu, amma zuciyarsu tana nesa da ni. Amma a banza suke yi mini sujjada, koyarwa da suke yi dokokin mutane ne. Kuna barin dokar Allah, kuna riƙe da takalidin mutane.’—Mar. 7:6-8.