Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Johannes Rauthe yana wa’azi a shekara ta 1920

DAGA TARIHINMU

“Na Taimaka wa Mutane Su San Jehobah”

“Na Taimaka wa Mutane Su San Jehobah”

SA’AD DA Hasumiyar Tsaro na 1 ga Satumba, 1915 take bayani a kan abin da ya faru a Yaƙin Duniya na Ɗaya da ta shafi kusan ƙasashe 30, ta ce: “Ba za a iya kwatanta yaƙe-yaƙen da ake yi yanzu a Turai da wanda aka yi a dā ba.” Ƙari ga haka, saboda yadda ake tsananta wa ’yan’uwa, Hasumiyar Tsaro ɗin ta daɗa cewa: “A ƙasar Jamus da Faransa, an hana ɗaliban Littafi Mai Tsarki wa’azi game da [Mulkin Allah].”

Duk da cewa ana yaƙe-yaƙen da ya shafi dukan duniya, ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun ƙudura niyyar yaɗa bishara game da Mulkin Allah ko da yake ba su fahimci ainihin dalilin da ya sa bai kamata su yi yaƙi ba. Wilhelm Hildebrandt ya sa an turo masa mujallun The Bible Students Monthly a Faransanci don ya yaɗa bishara. An aiko shi Faransa ba a matsayin colporteur wato (majagaba) ba amma don ya zama sojan Jamus. Wannan soja da ke sanye da kayan soja da ya kamata ya zama maƙiyi yana yaɗa bisharar salama kuma hakan ya sa Faransawa da suke wucewa mamaki.

Wasiƙun da ke cikin Hasumiyar Tsaro sun nuna cewa ɗaliban Littafi Mai Tsarki da ke Jamus sun ƙudura niyyar yaɗa bisharar Mulkin Allah yayin da suke aikin soja. Ɗan’uwa Lemke wanda ya yi aiki da dakarun mayaƙan ruwa ya ce mutane biyar daga cikin jirginsu sun nuna suna so su koya game da Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka ya ce, “ko a cikin wannan jirgin, na taimaka wa mutane su san Jehobah.”

Georg Kayser ya je yaƙi, amma ya dawo gida a matsayin bawan Jehobah. Mene ne ya faru? Ya samu wani littafin da ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka wallafa, kuma hakan ya sa ya soma bauta wa Allah da dukan zuciyarsa, kuma ya daina yaƙi. Sai ya nemi wani aiki dabam. Bayan an daina yaƙin, ya yi shekaru da yawa yana hidimar majagaba.

Ɗaliban Littafi Mai Tsarki ba su fahimci wasu abubuwa game da abin da ya sa bai dace su yi yaƙi ba. Duk da haka, halinsu ya bambanta da na mutanen da suka yi yaƙin. Sa’ad da ’yan siyasa da kuma shugabannin coci suke ƙarfafa mutane su yi yaƙi, ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun goyi bayan “Sarkin Salama.” (Isha. 9:6) Ko da yake wasu daga cikinsu sun shiga aikin soja, sun kasance da tabbacin da wani ɗalibin Littafi Mai Tsarki mai suna Konrad Mörtter yake da shi da ya ce, “Na fahimci cewa Kalmar Allah ta ce bai kamata Kirista ya yi kisankai ba.”—Fit. 20:13. *

Hans Hölterhoff yana amfani da amalanke na wa’azi don ya nuna mujallar nan The Golden Age

A Jamus babu wata doka da ta amince da ƙin shiga aikin soja, amma ɗaliban Littafi Mai Tsarki fiye da 20 sun ƙi shiga aikin soja. Saboda haka, an ce wasu a cikinsu kamar Gustav Kujath ya haukace kuma aka kai shi asibitin mahaukata inda aka riƙa ɗura masa ƙwaya. An tura Hans Hölterhoff kurkuku don shi ma ya ƙi shiga aikin soja kuma ya ƙi yin duk wani aikin da ya shafi yaƙi. Saboda haka, masu gadi suka ɗaure shi da wani irin kaya har sai da hannuwansa da ƙafafunsa suka sandare. Sa’ad da suka ga cewa ya ƙi ƙarya amincinsa sai masu gadin suka yi kamar za su kashe shi don su tsoratar da shi, duk da haka Hans ya riƙe aminci har aka daina yaƙin.

Wasu ’yan’uwan da aka kama sun ƙi ɗaukan makamai, amma sun ce a ba su aikin da bai shafi yin yaƙi ba. * Johannes Rauthe ya yi hakan kuma sai aka tura shi aiki a hanyar jirgin ƙasa. An ba Konrad Mörtter aiki a matsayin mataimakin nas ko kuma likitoci. Reinhold Weber kuma ya yi aikin nas. August Krafzig wanda aikinsa shi ne kula da kayan sojoji ya yi farin ciki cewa aikin da aka ba shi bai ƙunshi yin yaƙi ba. Waɗannan ɗaliban Littafi Mai Tsarki da wasu sun ƙudura niyyar bauta wa Jehobah domin suna ƙaunarsa kuma suna so su kasance da aminci a gare shi.

Ma’aikatan gwamnati sun soma tsananta wa ɗaliban Littafi Mai Tsarki saboda matakin da suka ɗauka a lokacin yaƙi. Bayan wannan lokacin, ɗaliban Littafi Mai Tsarki a Jamus sun sha zuwa kotu don suna wa’azi. Don a taimaka musu, an kafa sashen da ke kula da shari’a a ofishin Shaidun Jehobah da ke birnin Magdeburg a ƙasar Jamus.

Shaidun Jehobah sun ci gaba da ba da ƙarin haske a kan batutuwan da suka shafi yin yaƙi da kuma harkokin siyasa. Sa’ad da aka soma Yaƙin Duniya na Biyu, Shaidun Jehobah sun ƙudurta cewa ba za su yi yaƙi ba kuma sun ƙi shiga aikin soja. Hakan ya sa aka ɗauke su maƙiyan ƙasa a Jamus kuma aka soma tsananta musu sosai. Wannan tsanantawar wani labari ne dabam da za a ba da a talifi na gaba na “Daga Tarihinmu.”—Daga tarihinmu a Turai.

^ sakin layi na 7 Ka karanta abin da ya faru da ɗaliban Littafi Mai Tsarki a lokacin Yaƙin Duniya na Ɗaya a talifi nan “Daga Tarihinmu—Sun Yi Tsayin Daka a ‘Lokacin Gwaji’” a Hasumiyar Tsaro na 15 ga Mayu, 2013.

^ sakin layi na 9 Wannan matakin da suka ɗauka yana cikin kundi na shida na littafin nan Millennial Dawn (1904) da kuma mujallar Zion’s Watch Tower (Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona) na Jamusanci na Agusta na shekara ta 1906. Mujallar Hasumiyar Tsaro na Satumba na shekara ta 1915 ta ba da ƙarin haske cewa bai kamata ɗaliban Littafi Mai Tsarki su shiga aikin soja ba. Amma wannan tallafin bai fito a Jamusanci ba.