Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Me Ya Sa Kake Bukatar Ka Koyar da Wasu?

Me Ya Sa Kake Bukatar Ka Koyar da Wasu?

“Kyakyawar koyarwa ni ke ba ku.”—MIS. 4:2.

WAƘOƘI: 93, 96

1, 2. Me ya sa muke bukatar mu koyar da wasu su samu ci gaba a ƙungiyar Jehobah?

YESU ya ɗauki yin wa’azi game da Mulkin Allah da muhimmanci sosai. Duk da haka, ya nemi lokaci don ya koyar da wasu su zama masu kula da kuma waɗanda suke koyar da Kalmar Allah. (Mat. 10:5-7) Ko da yake Filibbus mai wa’azi ne sosai, ya taimaka wa yaransa mata huɗu su ƙware wajen koya wa mutane Littafi Mai Tsarki. (A. M. 21:8, 9) Me ya sa irin wannan koyarwar take da muhimmanci a yau?

2 Domin adadin mutanen da suke son nazarin Littafi Mai Tsarki yana ƙaruwa sosai a dukan duniya. Ana bukatar a koyar da sababbin da ba su yi baftisma ba don su san muhimmancin nazarin Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, ana bukatar a koya musu yadda za su yi wa’azi kuma su koyar da mutane. A cikin ikilisiyoyinmu, ana bukata a ƙarfafa ’yan’uwa maza su ƙoƙarta don su cancanci zama bayi masu hidima da kuma dattawa. Ta wajen “koyarwa” da kyau, Kiristoci da suka manyanta za su taimaka wa sababbi su samu ci gaba a ƙungiyar Jehobah.—Mis. 4:2.

KA KOYA WA SABABBI YADDA ZA SU YI NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI

3, 4. (a) Ta yaya Bulus ya nuna cewa yin nazari yana taimaka mana mu ƙware a wa’azi? (b) Kafin mu ƙarfafa ɗalibanmu su yi nazarin Littafi Mai Tsarki, mene ne ya kamata mu riƙa yi?

3 Me ya sa nazarin Littafi Mai Tsarki yake da muhimmanci? Amsar tana cikin abin da manzo Bulus ya gaya wa Kiristocin da ke Kolossi. Ya ce: “Saboda wannan mu kuma, tun ran da muka ji wannan, ba mu fasa yin addu’a da roƙo domin ku cika da sanin nufin [Allah] cikin dukan hikima mai-ruhaniya da fahimi kuma, da za ku yi tafiya wadda ta cancanta ga Ubangiji, kuna gamshe shi sarai, kuna ba da ’ya’ya cikin kowane kyakkyawan aiki, kuna ƙaruwa kuma cikin [cikakken] sanin Allah.” (Kol. 1:9, 10) Me ya sa yake da muhimmanci sababbi su riƙa karanta da kuma yin nazarin Nassosi? Domin hakan zai sa su zama masu hikima, kuma za su fahimci yadda za su “yi tafiya wadda ta cancanta ga Ubangiji.” Ƙari ga haka, zai taimaka musu su ci gaba da “ba da ’ya’ya cikin kowane kyakkyawan aiki,” musamman ma a yin wa’azi. Don mu bauta wa Jehobah yadda ya dace, wajibi ne mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai, kuma ya kamata mu taimaka wa waɗanda muke nazari da su su yi hakan.

4 Idan ba ma yin nazarin Littafi Mai Tsarki, ba za mu iya taimaka wa ɗalibanmu su san muhimmancin yin hakan ba. Hakika, muna bukatar mu riƙa yin nazarin Littafi Mai Tsarki sosai. Saboda haka, zai dace ka tambayi kanka: ‘Shin ina yin amfani da Littafi Mai Tsarki don in amsa tambaya mai wuya da mutane suka yi ko kuma sa’ad suka faɗi abin da ya saɓa wa koyarwar Nassi? Sa’ad da na karanta game da yadda Yesu da Bulus da kuma wasu suka nace a hidimarsu, hakan ya taimaka mini in nace a hidimata ga Jehobah kuwa?’ Dukanmu muna bukatar ilimi da kuma shawara daga Kalmar Allah. Ƙari ga haka, idan muka gaya wa mutane yadda nazarin Littafi Mai Tsarki ya amfane mu, hakan zai ƙarfafa su su amfana ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki sosai.

5. Ta yaya za a iya taimaka wa sababbi su riƙa yin nazarin Littafi Mai Tsarki?

5 Kana iya tambayar kanka, ‘Ta yaya zan koya wa ɗalibina ya riƙa nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai?’ Za ka iya somawa ta wurin nuna masa yadda zai riƙa shirya nazarin da kake yi da shi. Ƙari ga haka, kana iya ba shi shawara ya karanta wasu sashen rataye na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? kuma ya karanta nassosin da ke cikinsu. Ka taimaka masa ya riƙa shirya taro don ya yi kalami. Ka ƙarfafa shi ya riƙa karanta kowane mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! Idan a yarensu suna da Watchtower Library ko kuma Watchtower LABURARE NA INTANE, kana iya nuna masa yadda ake amfani da su wajen amsa tambayoyin Littafi Mai Tsarki. Babu shakka, idan ya yi amfani da waɗannan abubuwan, ba da daɗewa ba ɗalibinka zai riƙa son yin nazarin Kalmar Allah.

6. (a) Ta yaya za ka taimaka wa ɗalibinka ya so Littafi Mai Tsarki da dukan zuciyarsa? (b) Wane mataki ne ɗalibin Littafi Mai Tsarki zai ɗauka idan ya so Nassosi da dukan zuciyarsa?

6 Hakika, bai kamata mu matsa wa mutane su riƙa karanta kuma su yi nazarin Littafi Mai Tsarki ba. Ya kamata ɗalibin ya ji daɗin nazarinsa kuma hakan zai taimaka masa ya san Jehobah da kyau. Ƙari ga haka, za mu iya yin amfani da abubuwan da ƙungiyar Jehobah take tanadinsu don mu taimaka wa ɗalibinmu ya so Littafi Mai Tsarki sosai. Da shigewar lokaci, ɗalibi mai zuciyar kirki zai ji kamar yadda wannan marubucin zabura ya ji sa’ad da ya ce: “Ya yi mini kyau in kusaci Allah: Na mai da Ubangiji Yahweh mafakata, domin in labarta dukan ayyukanka.” (Zab. 73:28) Ruhun Allah zai taimaka wa ɗalibin da yake son ya kusaci Jehobah.

KA KOYA MUSU YADDA ZA SU YI WA’AZI DA KUMA KOYARWA

7. Ta yaya Yesu ya taimaka wa manzanninsa su ƙware a yin wa’azi? (Ka duba hoton da ke shafi na 25.)

7 A cikin littafin Matta sura 10, Yesu ya ba manzanninsa guda 12 umurni game da wa’azi. Yesu ya ba su umurni a kan abubuwan da suka fi muhimmanci. [1] Manzannin sun saurare shi sa’ad da yake koya musu yadda za su yi wa’azi da kyau. Bayan haka, sai suka tafi wa’azi. Da yake sun lura da yadda Yesu yake wa’azi, hakan ya taimaka musu su ƙware wajen koyar da mutane game da Littafi Mai Tsarki. (Mat. 11:1) Hakazalika, mu ma za mu iya taimaka wa ɗalibanmu su ƙware a yin wa’azi. Bari mu ga hanyoyi biyu da za mu iya yin hakan.

8, 9. (a) Ta yaya Yesu ya tattauna da mutane sa’ad da yake wa’azi? (b) Ta yaya za mu iya taimaka wa sababbi su tattauna da mutane kamar yadda Yesu ya yi?

8 Ka riƙa tattaunawa da mutane. A yawancin lokaci, Yesu yana magana da mutane game da Mulkin Allah. Alal misali, ya tattauna da wata mata da ta zo ɗiban ruwa a wata rijiyar da ke kusa da garin Sychar. (Yoh. 4:5-30) Ƙari ga haka, ya tattauna da wani mai karɓan haraji mai suna Matta Lawi. Ko da yake littattafan Linjila ba su yi magana sosai a kan tattaunawar su ba, amma daga baya Matta ya zama mabiyin Yesu. Matta da kuma wasu sun saurari maganar da Yesu ya yi a wani bikin da aka yi a gidan Matta.—Mat. 9:9; Luk. 5:27-39.

9 A wani lokaci kuma, Yesu bai gaya wa Natanayilu baƙar magana ba duk da cewa Natanayilu yana da ra’ayin da bai dace ba game da mutanen Nazarat. Kuma hakan ya sa ya canja ra’ayinsa. Ko da yake Yesu ɗan Nazarat ne, Natanayilu ya saurari abin da Yesu yake koyarwa. (Yoh. 1:46-51) Saboda haka, muna da ƙwaƙƙwaran dalilin da ya sa ya kamata mu koya wa sababbi yadda za su riƙa tattaunawa da mutane cikin natsuwa. [2] Idan muka taimaka wa sababbi su yi hakan, za su yi farin cikin ganin yadda mutane suke saurarar wa’azinmu sa’ad da suke tattaunawa da su yadda ya kamata.

10-12. (a) Ta yaya Yesu ya taimaka wa waɗanda suke so su saurari wa’azin da yake yi? (b) Ta yaya za mu iya taimaka wa sababbi su ƙware a yin wa’azi?

10 Ka koyar da waɗanda suke son saƙonmu. Yesu yana da ayyuka da yawa. Duk da haka, ya saurari mutanen da suke son wa’azinsa kuma ya koya musu abubuwa da yawa. Alal misali, wata rana, Yesu ya yi wa mutane magana sa’ad da yake cikin ƙwale-ƙwale. Bayan haka, ta hanyar mu’ujiza, Yesu ya sa Bitrus ya kama kifaye da yawa kuma ya ce masa: “Daga nan gaba za ka kama mutane.” Mene ne sakamakon abin da Yesu ya yi? Littafi Mai Tsarki ya ce Bitrus da kuma abokansa sun “zo da jiragensu a wajen gaɓa, suka rabu da abubuwa duka, suka bi shi.”—Luk. 5:1-11.

11 Nikodimu yana cikin ’yan Majalisa kuma yana so ya saurari wa’azin da Yesu yake yi. Amma yana jin tsoron abin da mutane za su ce idan aka gan shi yana magana da Yesu. Saboda haka, ya zo wurin Yesu da daddare. Maimakon ya kore shi, Yesu ya tattauna da shi kuma ya bayyana masa wasu abubuwa game da Mulkin Allah. (Yoh. 3:1, 2) Wane darasi ne muka koya daga hakan? Yesu ya yi amfani da lokacinsa wajen koya wa mutane gaskiya game da Allah kuma ya ƙarfafa bangaskiyarsu. Hakazalika, ya kamata mu ma mu ziyarci mutane a lokacin da ya dace kuma mu ba da lokacinmu wajen taimaka musu su fahimci Littafi Mai Tsarki.

12 Idan muna fita wa’azi tare da sababbi, hakan zai taimaka musu su ƙware a yin wa’azi. Za mu iya taimaka musu su koma don su ziyarci waɗanda suke son saƙonmu. Ƙari ga haka, za mu iya ce musu su bi mu sa’ad da muke so mu koma ziyara da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane. Idan muka yi hakan, sababbi za su so su koma don su ziyarci waɗanda suke son saƙonmu, kuma hakan zai taimaka musu su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ɗalibansu. Ban da haka, za su koyi cewa suna bukatar su kasance da haƙuri ko tsawon jimrewa da kuma naciya a wa’azi.—Gal. 5:22; ka duba akwatin nan “ Nacewa Yana da Muhimmanci.”

KA KOYA MUSU SU ƘAUNACI ’YAN’UWANSU

13, 14. (a) Mene ne ra’ayinka a kan misalan Littafi Mai Tsarki game da waɗanda suka yi aiki tuƙuru don su taimaka wa ’yan’uwansu? (b) Ta wace hanya ce za ka iya taimaka wa sababbi da kuma matasa su ƙaunaci ’yan’uwansu maza da mata?

13 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah yana so mu ƙaunaci ’yan’uwanmu kuma mu yi musu hidima. (Karanta 1 Bitrus 1:22; Luka 22:24-27.) Ɗan Allah ya ba da kome har da ransa don ya yi wa wasu hidima. (Mat. 20:28) Littafi Mai Tsarki ya ce Dokas “cike take da ayyukan nagarta” da kuma ba da gudummawa. (A. M. 9:36, 39) Wata ’yar’uwa a Roma mai suna Maryamu ta yi wa waɗanda suke cikin ikilisiya “ɗawainiya da yawa.” (Rom. 16:6) Ta yaya za mu iya taimaka wa sababbi su san muhimmanci taimaka wa ’yan’uwansu maza da mata?

Ka koyar da sababbi su ƙaunaci ’yan’uwa (Ka duba sakin layi na 13, 14)

14 ’Yan’uwan da suka manyanta suna iya gayyatar sababbi sa’ad da suke so su ziyarci waɗanda suke rashin lafiya da kuma tsofaffi. Idan zai yiwu, iyaye za su iya tafiya da yaransu sa’ad da suke so su yi irin wannan ziyarar. Dattawa suna iya yin aiki da wasu don su taimaka wa tsofaffi su sami isashen abinci da kuma gyara musu gidansu. Hakika, idan matasa da kuma sababbi suka ga yadda muke kula da juna, za su koyi yin hakan. Akwai wani dattijon da a duk lokacin da ya fita wa’azi, yakan ziyarci ’yan’uwan da suke zama a ƙauyukan da ke yankinsu don ya san yadda suke. Hakan ya koya wa wani ɗan’uwan da yake yawan fita wa’azi da shi cewa muna bukatar mu ƙaunaci kowa a cikin ikilisiya.—Rom. 12:10.

15. Me ya sa yake da muhimmanci dattawa su tabbata cewa maza suna samun ci gaba a cikin ikilisiya?

15 Tun da yake Jehobah yana amfani da maza don koyarwa a cikin ikilisiya, yana da muhimmanci ’yan’uwa maza su zama ƙwararrun malamai. A matsayinka na dattijo, shin za ka iya saurarawa sa’ad da wani bawa mai hidima yake maimaita jawabin da zai yi? Idan ka taimaka masa, zai ƙware sosai wajen koyar da Kalmar Allah.—Neh. 8:8. [3]

16, 17. (a) Ta yaya Bulus ya taimaka wa Timotawus ya samu ci gaba? (b) Ta yaya dattawa za su koyar da waɗanda za su zama masu kula a cikin ikilisiya?

16 Ana bukatar masu kula sosai a cikin ikilisiyar Kirista, kuma waɗanda za su yi irin wannan aikin a nan gaba suna bukatar a riƙa koyar da su. Bulus ya faɗi yadda za a yi wannan koyarwar sa’ad da ya gaya wa Timotawus cewa: “Kai . . . ɗana, ka ƙarfafa a cikin alherin da ke cikin Kristi Yesu. Abubuwan da ka ji daga gare ni kuwa a gaban shaidu da yawa, sai ka danƙa ma mutane masu-aminci, waɗanda za su iya su koya ma waɗansu kuma.” (2 Tim. 2:1, 2) Timotawus ya koyi abubuwa sa’ad da ya yi hidima tare da manzo Bulus wanda ya manyanta. Timotawus ya yi amfani da abin da ya koya daga Bulus a hidimarsa da kuma wasu fannoni na ibadarsa ga Jehobah.—2 Tim. 3:10-12.

17 Bulus yana fita tare da Timotawus domin yana so ya tabbata cewa ya koyar da Timotawus sosai. (A. M. 16:1-5) Dattawa suna iya yin koyi da Bulus ta wajen kai ziyarar ƙarfafa tare da bayi masu hidima da suka cancanta a lokacin da ya dace. Ta yin hakan, dattawa suna ba wa waɗannan ’yan’uwan damar ganin koyarwa da bangaskiya da haƙuri da kuma ƙaunar da dattawa suke bukatar su kasance da shi. Hakan zai sa a riƙa koyar da waɗanda za su kula da “garken Allah.”—1 Bit. 5:2.

ME YA SA HORAR DA WASU YAKE DA MUHIMMANCI?

18. Me ya sa yake da muhimmanci mu horar da wasu?

18 Ana bukatar masu wa’azi sosai, shi ya sa yake da muhimmanci a horar da wasu. Ƙari ga haka, ya kamata a koya wa ’yan’uwa maza yadda ake kula da ikilisiya. Za mu iya bin misalin da Yesu da Bulus suka kafa na koyar da mutane. Jehobah yana so a koyar da bayinsa sosai don su kula da ayyukansu a ƙungiyarsa. Shi ya sa Allah ya ba mu gatan taimaka wa sababbi su ƙware don yin aikin da aka ba su a cikin ikilisiya. Ƙari ga haka, irin wannan koyarwar tana da muhimmanci sosai kuma ana bukatarta cikin gaggawa domin yanayin wannan duniyar yana ƙara taɓarɓarewa kuma muna ci gaba da samun damar yin wa’azi.

19. Me ya sa ya kamata ka kasance da tabbaci cewa za ka yi nasara a ƙoƙarin da kake yi don ka koyar da mutane?

19 Hakika, koyar da mutane takan ɗauki lokaci kuma yin hakan yana bukatar yin aiki tuƙuru. Amma Jehobah da Ɗansa ƙaunatacce za su taimaka mana kuma su ba mu hikima na yin irin wannan koyarwa. Ƙari ga haka, za mu yi farin ciki sa’ad da muka ga waɗanda muka horar da su suna aiki da ƙwazo. (1 Tim. 4:10) Hakazalika, mu ma muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu don mu sami ci gaba a bautarmu ga Jehobah.

^ [1] (sakin layi na 7) Abubuwan da Yesu ya ambata sun ƙunshi: (1) Su yi wa’azi game da Mulkin Allah. (2) Su yi hamdala da abin da Allah yake tanadar musu. (3) Kada su riƙa gardama da waɗanda suke wa wa’azi. (4) Su dogara ga Allah sa’ad da ake tsananta musu. (5) Kada su ji tsoro.

^ [2] (sakin layi na 9) Shafuffuka na 62-64 na littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education, ya ba da shawarwari masu kyau a kan yadda za mu tattauna da mutane sa’ad da muke wa’azi.

^ [3] (sakin layi na 15) Littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education, shafi na 52-61, ya bayyana abubuwan da mutum zai yi don ya ƙware a yin jawabi a gaban jama’a.