TARIHI
Bayarwa Ta Sa Ni Farin Ciki
A LOKACIN da nake ɗan shekara 12 ne na fahimci cewa ina da wani abu mai tamani da zan iya ba wa mutane. Sa’ad da ake wani babban taro, wani ɗan’uwa ya tambaye ni ko zan so in yi wa’azi. Sai na ce, E, ko da yake ban taɓa yin wa’azi ba. Da muka kai yankin da za mu yi wa’azi, sai ya ba ni wasu ƙasidu da ke magana a kan Mulkin Allah kuma ya ce mini: “Ka je ka yi wa mutanen da ke wancan layin wa’azi, ni kuma zan yi a wannan layin.” Sai na soma wa’azi gida-gida duk da cewa na tsorata. Amma na yi mamaki cewa na ba da dukan ƙasidu da nake da su. Hakika, mutane da yawa suna son abin da na ba su.
An haife ni a shekara ta 1923 a garin Chatham da ke Kent a ƙasar Ingila. Mutane sun zata cewa duniya za ta gyaru bayan Yaƙin Duniya na Ɗaya, amma hakan bai faru ba. Hakan ya sa mutane da yawa baƙin ciki har da iyayena. Ƙari ga haka, iyayena ba sa son limaman cocin Baftist don ba sa damuwa da kowa sai kansu. Sa’ad da nake ɗan shekara tara, mahaifiyata ta soma halartan taron da ’yan International Bible Students Association suke yi. Waɗannan mutanen ne suka canja sunansu zuwa Shaidun Jehobah. Ƙari ga haka, wata ’yar’uwa ta yi amfani da littafin nan The Harp of God don ta koya mana Littafi Mai Tsarki. Na ji daɗin abin da nake koya.
NA KOYI DARASI DAGA ’YAN’UWAN DA SUKA MANYANTA
A lokacin da nake matashi, na ji daɗin koya wa mutane Kalmar Allah don ina so su kasance da bege. A yawancin lokaci, ina zuwa wa’azi gida-gida ni kaɗai amma ina amfana sosai idan na yi wa’azi tare da mutane. Alal misali, wata rana ni da wani ɗan’uwa da ya manyanta muna kan hanyar zuwa yankin da za mu yi wa’azi a kan keke, sai na ga wani limami yana wucewa, kuma na ce, “Ga akuya nan tafe.” Ɗan’uwan ya sauƙo daga kan kekensa kuma ya gaya min mu zauna a kan wani katako. Sai ya ce: “Wane ne ya ba ka ikon shari’anta wani a matsayin akuya? Bari mu ci gaba da yin wa’azi da farin ciki kuma mu bar Jehobah ya shari’anta mutane.” A waɗannan shekarun, na koyi cewa yin wa’azi yana sa mutum farin ciki sosai.—Mat. 25:31-33; A. M. 20:35.
Wani ɗan’uwa kuma ya koya mini cewa, wani lokaci muna bukatar mu jimre da matsaloli idan muna son mu yi farin ciki sa’ad da muke wa’azi. Matar ɗan’uwan ba ta son Shaidun Jehobah. Akwai ranar da ya gayyace ni zuwa gidansa don mu ɗan shaƙata. Ta ji haushi sosai cewa ya fita wa’azi, saboda haka ta soma jifan mu da fakitin shayi. Maimakon ya yi mata faɗa, sai ya soma kwashe fakitin shayin kuma ya mayar da
su yana murmushi. Bayan shekaru da yawa, halinsa ya sa matarsa ta canja kuma an yi mata baftisma a matsayin Mashaidiyar Jehobah.Na ci gaba da son yi wa mutane wa’azi, kuma a watan Maris na shekara ta 1940, an yi wa ni da mahaifiyata baftisma a garin Dover. A watan Satumba na shekara ta 1939, sa’ad da nake ɗan shekara 16, Britaniya ta sanar da cewa za ta yaƙi Jamus. A watan Yuni na shekara ta 1940, na tsaya a baƙin ƙofar gidanmu ina kallon dubban sojoji da suka tsira daga yaƙin da aka yi a garin Dunkirk suna wucewa a manyan motoci. Fuskokinsu na cike da baƙin ciki, kuma ina so in gaya musu game da Mulkin Allah. Ƙari ga haka, a wannan shekarar ƙasar Biritaniya ta soma yi wa ƙasarmu ruwan bama-bamai. Kowane dare ina ganin jiragen sama masu yawa na ƙasar Jamus suna wucewa ta yankinmu. Muna jin ƙarar bama-bamai suna faɗowa kuma hakan yana tsorata mu sosai. Idan gari ya waye, muna ganin gidaje da yawa da aka halaka a yankinmu. Hakan ya sa na ƙara fahimtar cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai magance matsalolinmu.
NA SOMA WA’AZI NA CIKAKKEN LOKACI
A shekara ta 1941 ne na soma yin abin da ya sa ni farin ciki sosai a rayuwa. Kafin wannan lokacin, ina koyan yadda ake gyaran jiragen ruwa da ake yaƙi da su a garin Chatham. Wannan aiki ne da mutane suke son su yi don ana samun kuɗi sosai. Tun da daɗewa, mutanen Jehobah sun san cewa bai kamata Kiristoci su yaƙi juna ba. A shekara ta 1941, mun koya cewa bai kamata mu yi aiki a wurin da ake ƙera makamai ba. (Yoh. 18:36) Tun da yake a wurin da nake aiki ne ake ƙera jirgin yaƙi mai tafiya a ƙarƙashin ruwa, sai na tsai da shawarar barin aikin kuma na soma hidima na cikakken lokaci. Na soma hidima a wani birni mai ban sha’awa a birnin Cirencester a Cotswolds.
Na yi watanni tara a kurkuku sa’ad da nake ɗan 18 domin na ƙi shiga aikin soja. Na ji tsoro sa’ad da aka rufe ni ni kaɗai a cikin ɗakin kurkukun. Amma ba da daɗewa ba, masu gadi da fursunoni suka soma tambayata dalilin da ya sa aka kawo ni, sai na bayyana musu imanina.
Bayan na fito daga kurkuku, sai na soma wa’azi tare da Leonard Smith * a garuruwa dabam-dabam da ke jihar Kent. Daga shekara ta 1944, dubban jiragen sama suna ta ruwan bama-bamai a jihar Kent. Gidanmu yana wuraren da jiragen suke bi, wato tsakanin wurin da sojojin Nazi suke a Turai da kuma Landan. Ana kiran waɗannan jiragen sama masu ruwan bama-bamai doodlebugs, wato, wani ƙwari da ke tashi a sama. Hakan yana da ban tsoro, don idan injin jirgin ya daina aiki, ka san cewa ’yan daƙiƙa kaɗan jirgin zai faɗi kuma bama-baman za su fashe. Ƙari ga haka, muna nazarin Littafi Mai Tsarki da wani iyali da ke da yara uku. A wasu lokatai, muna zama a ƙarƙashin tebur na ƙarfe don ya kāre su idan gidan ya faɗi. Daga baya, dukan iyalin sun yi baftisma.
YIN WA’AZI A ƘASAR WAJE
Bayan yaƙin, na yi shekaru biyu ina hidimar majagaba a kudancin ƙasar Ireland. Ba mu san cewa ƙasar Ireland ta bambanta da ƙasar Ingila ba. Muna zuwa gida-gida don neman masauki, kuma mukan gaya musu cewa mu masu wa’azi a ƙasar waje ne. Ƙari ga haka, muna rarraba mujallunmu a kan titi. Yin hakan bai dace ba domin yawancin mutane a ƙasar suna zuwa cocin Katolika. Akwai wani lokaci da wani mutum ya yi mana barazana kuma na gaya wa ɗan sanda, sai ya ce, “To, me kake ganin dama zai yi?” Ba mu san cewa firistoci suna da iko sosai ba. Sukan sa a sallami mutane daga aikinsu idan suka karɓi littattafanmu, kuma sun sa an kore mu daga masaukinmu.
Ba da daɗewa ba, mutane suka gaya mana cewa idan muka je wani wuri, mu riƙa wa’azi nesa da masaukinmu inda wani firist dabam ne yake hidima. Daga baya kuma, sai mu yi wa mutanen da ke inda masaukinmu yake wa’azi. A garin Kilkenny, muna nazari da wani matashi sau uku a mako duk da cewa wasu mutane suna masa barazana. Na ji daɗin koyar da Littafi Mai Tsarki sosai kuma hakan ya sa na tsai da shawarar halartan Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead don na zama mai wa’azi a ƙasar waje.
Bayan na sauke karatu na wata biyar a New York, sai aka tura mu huɗu da ke ajin wa’azi a ƙananan yankunan da ke Tekun Caribbea. A watan Nuwamba na shekara ta 1948, mun bar birnin New York a jirgin ruwa mai tsawon ƙafa 59, da ake kira Sibia. Na yi farin ciki sosai don ban taɓa shiga jirgin ruwa ba. Wani a cikinmu mai suna Gust Maki ya iya tuƙa jirgin ruwa sosai. Ya koya mana yadda ake ɗaga da kuma saukar da filafilai dabam-dabam, da yadda ake amfani da kamfas, wato wani na’ura da ke nuna hanyar da za a bi, da kuma yadda za mu tuƙa jirgin sa’ad da ake iska. Ɗan’uwa Gust ya yi kwanaki 30 yana tuƙa jirginmu duk da ruwa da iska mai haɗari sosai da aka yi har muka kai ƙasar Bahamas.
YIN WA’AZI A DUKAN YANKUNAN DA KE BAKIN TEKU
Mun yi ’yan watanni muna wa’azi a ƙananan yankunan da ke bakin teku a ƙasar Bahamas. Bayan haka, sai muka kama tafiya zuwa yankunan Leeward da Windward, masu nisan kilomita 800 daga Virgin Islands kusa da Puerto Rico da kuma Trinidad. Mun yi shekara biyar muna wa’azi kawai a yankunan da ba Shaidu. A wasu lokatai, mukan yi makonni ba mu iya aika ko kuma karɓan saƙo. Amma, mun yi farin ciki cewa muna wa’azi game da kalmar Jehobah a yankunan da ke bakin teku!—Irm. 31:10.
Sa’ad da muka kai bakin teku, mutanen ƙauyen suna taruwa kuma su riƙa kallonmu. Wasu a cikinsu ba su taɓa ganin jirgin ruwa ko kuma bature ba. Mutanen masu fara’a ne da masu son addini kuma suna karanta Littafi Mai Tsarki sosai. Sau da yawa sukan ba mu ɗanyen kifi da ’ya’yan itacen da ake kiran pear da kuma gyaɗa. Jirginmu ƙarami ne, don haka babu isashen wurin kwanciya da dahuwa ko kuma wanki, amma mun yi maneji da hakan.
Mukan zo bakin teku kuma mu ziyarci mutane daga safe har yamma. Muna gaya musu cewa za a ba da jawabin da aka ɗauko daga Littafi Mai Tsarki. Idan yamma ta yi, sai mu kaɗa kararrawar da ke
jirginmu. Wani abin sha’awa shi ne yadda mutane suke saukowa daga tuddai riƙe da fitilunsu. A wasu lokatai, mutane ɗari sukan zo, kuma su zauna har dare suna mana tambayoyi. Suna son rera waƙa, saboda haka mukan buga da gurza waƙoƙin Mulki kuma mu rarraba musu. Yayin da muke rera waƙoƙin, mutanen suna rera waƙoƙin tare da mu, kuma muryoyinsu na da daɗin ji sosai. Mun yi farin ciki sosai a lokacin!Bayan mun gama nazarin Littafi Mai Tsarki da su, wasu daga cikin ɗaliban sukan bi mu don mu yi nazari da wasu iyalai. Ko da yake ya kamata mu tafi bayan mun yi ’yan makonni a wani wuri, mukan gaya wa waɗanda suke son saƙonmu sosai su ci gaba da nazari da wasu kafin mu dawo. Ganin yadda suka ɗauki aikinsu da muhimmanci ya sa mu farin ciki.
A yau, waɗannan yankunan da ke bakin teku sun zama wuraren zuwa yawon buɗe ido, amma a lokacin, wurare ne da ke kewaye da ruwa da kuma bishiyoyin dabino. Mukan je waɗannan yankuna da dare. Ƙari ga haka, wani babban kifi da ake kira Dolphin sukan yi iyo kusa da jirginmu, kuma ƙarar jirginmu ne kawai ake ji a cikin tekun. Wata yana haskaka tekun sosai da har za a ga wurare masu nisa.
Mun je Puerto Rico don mu canja jirginmu zuwa jirgi mai inji bayan mun yi shekara biyar muna wa’azi a waɗannan yankunan da ke bakin teku. Sa’ad da muka kai wajen, sai na soma soyayya da wata kyakkyawar yarinya mai suna Maxine Boyd da ke wa’azi a ƙasar waje. Tana wa’azi da ƙwazo tun tana ƙarama. Daga baya, ta yi hidima a ƙasar Dominican Republic, kuma a shekara ta 1950, gwamnatin da cocin Katolika ta kafa ta kore ta daga ƙasar. Da yake ina cikin waɗanda suke tuƙa jirgin, an ba ni izinin zama a Puerto Rico har tsawon wata ɗaya. Ba da daɗewa ba zan riƙa tafiya da jirgi zuwa yankunan da ke bakin teku kuma zan yi shekaru kafin in dawo. Saboda haka, sai na gaya wa kaina, ‘Idan kana son wannan yarinyar, gara ka yi mata magana nan da nan.’ Bayan makonni uku, sai na yi mata magana cewa ina son in aure ta, kuma muka yi aure bayan makonni shida. Sai aka tura ni da matata hidima a matsayin masu wa’azi a ƙasar Puerto Rico, saboda haka ban samu zarafin shiga sabon jirgin ba.
Mun soma ziyarar ikilisiyoyi a shekara ta 1956. ’Yan’uwa da yawa da ke wurin talakawa ne, amma muna jin daɗin kai musu ziyara. Alal misali a ƙauyen Potala Pastillo, akwai wasu iyalai guda biyu da suke da yara da yawa, kuma nakan busa musu sarewa. Ƙari ga haka, na tambayi ɗaya cikin ƙananan yaran mai suna Hilda, ko tana son ta bi mu wa’azi. Sai ta ce: “Ina so, amma ba zan iya ba. Ba ni da takalmi.” Mun saya mata takalmi, kuma ta bi mu wa’azi. Bayan shekaru da yawa, a shekara ta 1972, ni da matata mun kai ziyara a Bethel da ke Brooklyn. Sai muka haɗu da wata ’yar’uwa da ta sauke karatu daga Makarantar Littafi Mai Tsarki na Gilead. Tana so ta tafi wurin da aka tura ta hidima a ƙasar Ecuador, kuma ta tambaye mu: “Kun gane ni kuwa? Ni ce yarinyar da ba ta da takalmi daga ƙauyen Pastillo.” Hilda ce! Kuma mun yi farin ciki sosai har muka yi kuka.
A shekara ta 1960, an tura mu hidima a ofishin Shaidun Jehobah da ke Puerto Rico. Ofishin yana yankin Santurce, a birnin San Juan kuma gidan bene ne mai hawa biyu. Da farko, ni da Lennart Johnson ne muke yawancin aikin. Shi da matarsa ne suka fara zama Shaidu Jehobah a Dominican Republic, kuma sun zo ƙasar Puerto Rico a shekara ta 1957. Daga baya, matata Maxine ta yi aiki a inda ake karɓan saƙonnin da mutane suka turo don neman mujallu kuma tana aika fiye da dubu ɗaya a mako. Tana jin daɗin wannan aikin domin mutane da yawa suna koya game da Jehobah.
Na ji daɗin yin hidima a Bethel, don aiki ne da ake yi don taimaka wa mutane. Amma yana da nasa kaluɓalen. Alal misali, aiki ya yi mini yawa sosai sa’ad da aka yi taron ƙasashe na farko a Puerto Rico a shekara ta 1967. Ɗan’uwa Nathan Knorr, wanda yake shugabanci a lokacin ya zo Puerto Rico. Akwai masu wa’azi a ƙasashen waje da za su halarci taron. Ko da yake na shirya motar da za ta kai su masaukinsu, Ɗan’uwa Knorr ya ɗauka cewa ban yi hakan ba. Daga baya, ya ja kunnena sosai cewa in riƙa tsara ayyuka da kyau kuma ya ce bai ji daɗin abin da ya faru ba. Ba na son in yi gardama da shi, amma ina ganin an ce na yi abin da ban yi ba kuma hakan ya sa ni baƙin ciki na ɗan lokaci. Duk da haka, lokacin da ni da
matata muka sake haɗuwa da Ɗan’uwa Knorr, ya gayyace mu ɗakinsa kuma ya yi mana abinci.Mun ziyarci iyalina a Ingila sau da yawa daga Puerto Rico. Mahaifina bai soma bauta wa Jehobah ba sa’ad da ni da mahaifiyata muka soma yin hakan. Amma sa’ad da masu ba da jawabai daga Bethel suka zo, mahaifiyata takan sa su zauna a gidanmu. Mahaifina ya ga cewa waɗannan ’yan’uwan masu tawali’u ne sosai ba kamar limaman coci da suka tsane shi shekarun baya ba. Daga baya, ya yi baftisma a shekara ta 1962.
Matata Maxine ta rasu a shekara ta 2011. Ina ɗokin ganinta sa’ad da ta tashi daga mutuwa. Hakan yana sa ni farin ciki sosai. Ni da matata Maxine mun yi shekaru 58 tare, kuma mun ga yadda mutanen Jehobah a Puerto Rico suka ƙaru daga 650 zuwa 26,000. Ƙari ga haka, a shekara ta 2013, an haɗa ofishin Shaidun Jehobah da ke Puerto Rico da ofishinmu da ke Amirka, kuma an tura ni hidima a ofishinmu da ke Wallkill a New York. Bayan na yi shekara 60 ina hidima a yankunan da ke bakin teku, ji nake na zama ɗan ƙasar. Amma, lokaci ya yi da zan bar ƙasar.
“ALLAH YANA SON MAI-BAYARWA DA DAƊIN RAI”
Har ila, ina jin daɗin bauta wa Allah a Bethel. Yanzu na ba shekara 90 baya, kuma aikina shi ne ƙarfafa ’yan’uwan da suke Bethel. An gaya min cewa na ziyarci ’yan’uwa fiye da 600 tun lokacin da na zo Wallkill. Wasu da suka ziyarce ni suna so su tattauna matsalolinsu ko kuma na iyalinsu. Wasu kuma suna neman shawara a kan yadda za su ji daɗin hidimarsu a Bethel. Har ila wasu da suka yi aure ba daɗewa ba sukan zo neman shawara a kan zaman aure. Ƙari ga haka, wasu kuma an gaya musu su bar Bethel su koma yin wa’azi na cikakken lokaci. Ina sauraron dukan waɗanda suke magana da ni, kuma a lokacin da ya dace, nakan gaya musu: “‘Allah yana son mai-bayarwa da daɗin rai.’ Saboda haka, ku ci gaba da farin ciki a hidimarku, Jehobah ne kuke wa hidimar.”—2 Kor. 9:7.
Idan kana son ka ji daɗin hidimarka a Bethel ko kuma a wani wuri. Kana bukatar ka mai da hankali a kan dalilin da ya sa abin da kake yi yake da muhimmanci. Kowace hidima da muke yi a Bethel tana da muhimmanci. Muna taimaka wa “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” wajen koya wa ’yan’uwa da ke dukan duniya game da Jehobah. (Mat. 24:45) A duk inda muke bauta wa Jehobah, muna da zarafin yabon sa. Bari mu riƙa yin farin ciki a duk abin da ya gaya mana mu yi don “yana son mai-bayarwa da daɗin rai.”
^ sakin layi na 13 Tarihin Leonard Smith yana cikin Hasumiyar Tsaro na 15 ga Afrilu, 2012..